Kundi Uku Book Compelet By Ameera Adam

Author :  Ameera Adam Category :  Read Hausa Novels

Chapter   6 / 14

15K to 18K   out of 40.4K words

Jiki a sanyaye dogaransa suka sunkuyar da kansu ƙasa, Sarki Gambo ya fara zubar da hawayen tausayin halin da jariransa suke ciki. Ya jima a haka, sannan aka iso aka sanar da shi an gama haɗa gawar Fulani Khadija za a sallace ta. Da ƙyar Sarki Gambo ya iya miƙa wa Shamaki su, ya bayar da umarnin a kai su ɓangaren Fulani Sadiya domin ta kula da su. Sannan ya ce a tabbatar da an tatsi nonon awaki an ba su don gudun kada yunwa ta illata su.
Cikin ƙanƙanin lokaci mutane da dama suka sallaci gawar Fulani Khadija, don mahaifinta ne ya jagoranci sallar gawarta. Bayan da aka kai ta gidanta na gaskiya, mahaifiyar Fulani ta nemi da a bata jariran domin ta kula da su. Amma fir Sarki Gambo ya ƙi amincewa, saboda tsananin soyayyarsu da yake ji a cikin zuciyarsa. Kusan wuni guda Sarki Gambo ya yi yana karɓar gaisuwar Fulani Khadija, sai yamma liƙis ya shiga turakarsa. Da shigarsa babu jimawa, Jakadiya ta zo nema wa Fulani Zainaba iso wurinsa. Ya yi matuƙar mamaki, don haka kai tsaye ya amsa wa baƙuntarta.

Sallama ɗauke a bakinta ta shiga, sai dai kamar kullum fuskarta a cunkushe take babu ɗigon fara'a. Sai da ta durƙusa har ƙasa ta gaishe shi sannan ta ji ya ce.
"Mun yi matuƙar mamakin ganinku Fulani Zainaba, yau kusan shekara goma kenan da shigowarku rayuwarmu. Sai dai ba ku taɓa neman izinin ganinmu a turaka ba, idan ba mu muka nemi ƙeɓewa da ku ba."

"Saboda babu buƙatar hakan a tattare da ni, a yanzu ma akwai dalilin da ya kawo ni turakarka."
Fulani Zainaba ta furta cikin tsana, Sarki Gambo ya saki murmushi ya ce.
"Zainaba ba za ki taɓa sauyawa ba."

"Zan sauya Sarki Gambo, amma lokaci alƙali ne yana nan tafe."
Ta ba shi amsa kai tsaye, sai kuwa ya ƙura mata ido. Ita ma ba ta janye idonta ba, ta cigaban da kallonsa har sai da ya matso gabanta ya ce.
"Dalilainmu masu muhimmanci ne suka sa muka bar ku a raye Zainaba, tun da kun san ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba."
Fulani Zainaba ta saki murmushin takaici ta ce, "Ni kuma Ubangiji Ya ja da kwana ne, domin na fahimtar da kai kuskuren da ka tafka a baya."
A fusace Sarki Gambo ya ɗago, Fulani Zainaba ta girgiza kai cike da takaici ta ce.
"Na zo na ji ya aka yi Fulani Khadija ta mutu? Don ina zargin wani abu a mutuwar baiwar Allahr nan. Sanar da ni, ya aka yi aka haihu a ragaya? Domin a sanin mugun halin da na yi maka tun daga shigowata gidan nan, na tabbata babu abin da ba za ka iya aiwatarwa ba."
Da sauri Sarki Gambo ya dube ta, cikin zafin rai ya ƙarasa ya maƙure wuyanta.


*Ummou Aslam Bint Adam*🌚
07062062624

[24/11, 17:29] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.

SHAFI NA BAKWAI

ADVERT

*MUM NIMRAH'S GRILL FISH AND SHAWARMAR*
'Yar uwata kema kina fama da kwadayin kayan kwalam da makulashe?To ina yi miki albishir da ki garzayo wajan Mum nimrah's grill fish and shawarma don farantawa bakinki, mai gidanki, yaranki, iyayenki da zuciyar ki da haddaden grill catfish or tilapia.😋💃🏻 Sai kuma beefshawarma Akan farashi me sauki.
zaki sameta akan number 08140365134 domin yin order a WhatsApp.
Location: Kano
Sai kun zo💃🏻

Masarautar Judala

Ayarin rukunin bayi ne suke tafe cikin gajiyawa saboda irin doguwar tafiyar da suka yi, ba su ƙarasa cikin masarautar Judala ba sai kusan lokacin da dare ya tsala. A sashen bayi aka zuba su tamkar wasu kayan wanki, a galabaice suke saboda yunwa da ƙishirwa. Don haka suna zuwa a kan ruwa suka fara dira kamar waɗanda suka shekara ba su gan shi ba, bayan da suka sha suka yi ƙat sai ya zamana cikkunansu ya ƙulle saboda rashin abinci. Ƙanan yara maza da mata suka shiga kukan yunwa, da yake ba lokacin abinci ba ne a kan dole iyayensu suka lallashe su don su haƙure wa zuwa wayewar gari.

A lokacin da dare ya tsala sosai, a ƙalla kusan ƙarfe biyu da rabi na dare. Fitsari ne ya tashi Indo, don haka ta dubi katafaren filin da suke kwance. Da tarin bushiyoyin da ke zagaye da su, haka kawai ta ji tsoro ya kama ta. Saboda ko a garinsu babban dalili ne yake fitar da ita waje da daddare, don haka a hankali ta miƙa hannu ta tashi Zinaru tana yin ƙasa da murya ta ce.
"Zinaru! Zinaru!"
Cikin gajiya da magagin bacci Zinaru ta ce, "Tuba muke don Allah ku yi haƙuri ku bar mu a ƙauyukanmu, kada ku kai mu masarautarku mu zame muku bayi."
Sake taɓa ta Indo ta yi don ta fahimci firgicin da suka shiga a lokacin da za a kamo su, daga garinsu ne ya sa Zinaru take surutai har a cikin bacci.

"Zinaru Indo ce, don Allah ki raka ni na yi fitsari."

Sai a lokacin Zinaru ta sake wartsakewa, ta miƙe tana hamma tare da murza idanu tana kalle-kalle.
"Yanzu Indo a wannan dokar dajin za mu tafi fitsari, ni fa wallahi tsoro nake ji."
Indo da fitsari ya gama matsarta ta ce, "Wallahi ni ma tsoron nake ji Zinaru, amma ko ɗan gabancan ki taimaka ki raka ni."
A hankali suka fara takawa zuwa bayan ɗakunan Bayin da suke jere, kasancewar duk mutane ne a warwatse ya sa suka ƙara tafiyar da ɗan nisa. Musamman da ya kasance akwai hasken farin wata, sai tsoron da suke ciki ya ragu sosai.

A bakin wata ƙatuwar bishiyar tsamiya Indo da Zinaru suka tsugunna ba tare da addu'a ba, sai da suka gama sannan suka rasa abin da za su yi tsarki da shi. Don haka suka laluba suka ɗauki duwatsu suka shafa a madadain ruwan da ba su samu ba. Miƙewa suka yi suna waigowa suka ganta jingine, a jikin wani ƙaton shuri da ke kallon bishiyar tsamiyar da suke tsaye. Gaban Indo da Zinaru ya yi mummunan bugawa, har sai da kusan lokaci ɗaya suka saka hannuwa biyu suka dafe ƙirjinsu.

"Wash! Wayyo cikina da marata, ku taimaka ku zo ku agaza mini."
Matar ta furta tana yarfe hannu alamar tana cikin tsananin ciwo, sai a lokacin suka lura da tsohon cikin jikinta. Zinaru ce ta yi ta maza ta ce.
"Da me za mu taimaka miki?"

"Naƙuda nake yi wash!"

Ta furta gumi yana sake tsattsafo mata, kallon juna suka yi, jikin Indo ne ya shiga rawa. Ganin haka ya sa Zinaru ta ja hannunta don su yi gaba, cikin galabaita matar ta ce.
"Ku ma mata ne, watarana ba ku san inda za ku tsinci kanku ba, don Allah ku taimaka mini."
Sosai kalamanta suka tausasa zuciyar Indo, ta tsaya cak wuri ɗaya. Da sauri Zinaru ta kalle ta, Indo ta ƙarasa gaban matar cike da tausayawa ta ce.
"Kema kina daga cikin tawagar bayin da aka kawo ne?"

Kai matar ta gyaɗa mata a daidai wannan lokaci suka ji ta saki nishi, nan take jaririyar 'yarta ta faɗo. Tsoro ne ya kama Indo, kasancewar bata taɓa ganin an yi haihuwa a gabanta ba. Da sauri ta ƙarasa wurin Zinaru da ke tsaye har lokacin tana kallonsu, cikin sauri ta ce.
"Zinaru don Allah ki zo ki taimaka mata ke ce kika taɓa haihuwa."

Wani mugun kallo ta watsa mata, cikin masifa ta ce.
"Saboda ni ma ba ni da hankali kamar ke ko? Wai Indo ba za ki zo mu tafi ba?"
Shiru Indo ta yi, ta waiga tana kallon matar tana yankewa jaririyar cibi. Wani ƙaton ganyen ayaba ta ga tana ƙoƙarin cirowa, da sauri Indo ta ciro ta miƙa mata. Sai ta ga ta ɗora jaririyar akansa, ta dubi Indo tana sakin murmushi a galabaice ta ce.

"Sunana Karima kuma a cikin masarautar nan nake, sunan da zan saka wa wannan Jaririyar Batul. Don Allah ki taimaka ki yi mini wata alfarma, ki riƙe mini yariyar nan akwai kayana a bayan shingen can da zan ɗauko."

Kamar Indo ba za ta yi magana ba, jiki a sanyaye ta miƙa hannu ta karɓi jaririyar. Zinaru da ke can gefe tana ganin haka ta saki ƙwafa haɗe da yin tsaki ta yi gaba, tana sake jaddada rashin hankalin da Indo take yi.
Daidai wurin da Karima ta tashi nan ta nuna wa Indo, sai a lokacin ta lura da mazaunin matar a kan ƙaton gidan tururuwa ta yi shi. Ya jiƙe sharkaf da jini, ga waɗansu manyan tururuwai da ba ta taɓa ganin irinsu ba sun zagaye jinin suna ta tsotsa.

"Baiwar Allah zuciyata a cike take da fargaba da ruɗa ni, don Allah kada ki cutar da ni."

Indo ta furta zuciyarta tana rawa kamar za ta saka kuka, kama hannunta Karima ta yi, nan take Indo ta ji wani yarr tsigar jikinta ta fara tashi. Ga wani irin sanyi da ta ji hannunta kamar ta tsamo daga cikin ƙanƙara, ta sakar wa da Indo murmushi ta ce.
"Ba zan cutar da ke ba, ungo riƙe wannan."
Karima ta furta tana miƙa mata abu kamar wacce take shirin ba ta abu. Zuciya ɗaya Indo ta miƙa hannunta, Karima ta zuba mata ido har sai da tsoro ya sake mamaye Indo sannan ta ce.

"A duk inda kike zan cigaba da bibiyar rayuwarki, ina son ki riƙe mini Batul tamkar 'yar cikinki. Akwai tarin ƙalulaben da za su afko cikin rayuwarki, sai dai duk abin da ya sha miki duhu. Ki zo bakin shurin nan za ki samu mafita, duk adadin shekarun da zan ɗauko zan dawo gare ki Indo..."

"Don Allah me kike faɗa ne? Ban fahimce ki ba."

Karima ba ta tanka mata ba, ta tsugunna ta damƙi ƙasar gjdan turuwar, sannan ta damƙi ta saman shurin. Ta shafa a fuskar Indo, sannan ta shafa a fuskar jaririyarta Batul da ke hannun Indo. Nan take Indo ta ji wata irin juwa tana yunƙurin ɗaukarta, tun tana ganin Karima har ta fara yi mata dishi-dishi. Ba ta yi tsammani ba, ta ji Karima ta matso wurinta ta fara yi mata raɗa a kunne mai kama da barin wasiyya.Tana buɗe idonta ta ji jariraiya Batul ta tsanyare da matsanancin kuka, sai dai ba kukan ne ya fi ɗaga mata hankali ba. Rashin ganin mahaifiyar Batul ya fi hautsina hanjin cikinta, tana fara waige-waige ta ji Zinaru ta ce.
"Indo ba za ki ajiye 'yar nan ki zo mu tafi ba?"

Cikin sauri Indo ta ce, "Ban ganta ba Zinaru, na shiga uku wallahi ban ganta ba."
Kafin Zinaru ta bata amsa suka ga Dogaran sun ƙaraso da sauri suna cewa.
"Kai baƙaƙen munafukai, wato da guduwa za ku yi? Allah Ya tona muku asirinku ku wuce mu je."
Daga Zinaru har Indo rasa mai bakin magana aka yi, Dogarin da ke gaba sai a lokacin ya lura da jaririyar da ke hannun Indo tana kuka. Cikin mamaki ya ce.
"Ke! Dama haihuwa kika yi shi ne har za ki gudu?"

Indo da ta rasa bakin magana sai ta fashe da kuka, saboda gabaɗaya tsoro ya kamata ita da ko auren fari ba ta yi ba ya za ta yi da jaririya sabuwar haihuwa.

"Ko ba magana nake yi miki ba?"

Dogarin ya sake buga mata tsawa, Indo da ta rasa mafita cikin kuka ta ce, "A'a ba guduwa zan yi ba."
"To ku wuce mu koma, ƙananan munafukai. An faɗa muku duk girman masarautar nan idan kun shigo za ku iya fita ne?"
Zinaru da Indo suka yi carko-carko musamman Indo da damuwa ta cunkushe mata kai.
"Indo kin ga irin abin da nake gudu ko? Wai ina uwar jaririyar nan? An ya kuwa ba gamo muka yi da aljana ba?"
Kamar Indo tana jira ta ce, "Wallahi Zinaru ban san inda ta yi ba, kamar ƙiftawar ido tana gama yi mini siddabaru na neme ta na rasa. Ni yau na shiga uku."
Duk maganganun da suke yi ƙasa-ƙasa suke yin su, shi ya sa ma Dogaran ba su san wainar da suke toyawa ba.

"Indo ki faɗa musu gaskiya kawai."
Zinaru ta faɗa tana satar waigensu. Indo ta sauke ajiyar zuciya ta ce.
"Yanzu wannan labarin mai kama da almara waye ya zai yarda da shi? Idan aljana ce me ya sa 'yarta ta kasance mutum, wallahi ina cikin tashin hankali Zinaru." Indo ta ƙarasa maganar cikin kuka, musamman da ya kasance ita ma jaririyar ban da kuka babu abin da take tsalawa.

Sarki Giɗaɗo

Tun bayan fitar Galadima abin duniya ya haɗu ya haɗe masa, dafe kansa ya yi cike da damuwa. Ganin ba shi da mafita ya sa ya miƙe ya haye kan gadonsa ya kwanta yana tunanin makomar rayuwarsa, da yadda duniya take neman yi masa atishawar tsaki ba tare da ya shirya ba. Abu ɗaya ya sani yana da gawurtattun maƙiya guda biyu, Sarki Dikko da Sarki Gambo. Wanda zuciyarsa ta fi karkata da kaso casa'in da tara a kan su suke yunƙurin dakushe tarihin zuri'arsa daga masarautar Judala. Kusan duka wunin da ya yi haka ya ƙarasa shi sukuku, jiki babu ƙwari. Sai zuwa washegari ya ɗan saki jikinsa, ganin Fulani Zannira ta shiga matsananciyar damuwa.
Da daddare bayan sallar Isha'i, Fulani Zannira da Sarki Giɗaɗo suna zaune suna hira a turakarsa. Shamaki ya doka sallama a bakin ƙofar, yana nema wa Galadima izinin shiga. A ɗabi'ar Sarki Giɗaɗo matuƙar aka yi sallar Isha'i ya rufe ganin kowanne irin baƙo. Amma ga mamakin Fulani Zannira sai ta ga jikinsa yana rawa ya amsa wa Shamaki, sannan ya dube ta ya ce.
"Fulani kuna iya shiga daga ciki, domin akwai muhimmiyar tattaunawar da za mu yi da Galadima."
Duk da ta yi mamaki, da yake Zannira mace ce mai kawar da kai, amma sai ta saki murmushi ta ce.

"Ni mai bin umarninka ce ranka shi daɗe."
Martanin murmushi ya mayar mata, ya taka mata har bakin ƙofa cike da ɗokantuwar ganin Galadima. A rumfar (Falo) da Sarki Giɗaɗo yake ganawa da baƙi suka zauna shi da Galadima. Cikin girmamawa Galadima ya ce.

"Allah Ya taimake ka, Ubangiji ya ba ka yawan rai ina fatan na same ka lafiya ranka shi daɗe."
Sarki Giɗaɗo ya sauke ajiyar zuciya ya ce.
"Kun same mu kafiya Galadima, tun da muka ji labarin neman isonku muka tabbatar akwai alkairi a tattare da zuwanku."
Galadima ya russunar da kai ya ce, "Wannan haka yake ranka shi daɗe, akwai wata ƙasaitacciyar bokanya da muka samu nasarar gano ta. Sai dai ta kasance ƙungurmar kafira, mai bin addinin kiristanci. Sunan da ake kiranta Bokanya Kande, ta kasance hatsabibiya kuma makira. Babban abin farincikin kuma har kawo yanzu, ba kowanne basarake ne ya san da zamanta ba."

Nan take Sarki Giɗaɗo ya faɗaɗa fara'arsa, cikin zaƙuwa ya ce.
"Galadima a tafi kai tsaye."

Galadima ya saki murmushi ya ce, "Allah Ya taimake ka na samu izinin ganawa da hadimanta, sai dai sun sanar da ni babban sharaɗinta ba ta taɓa ganin mutum ido da ido har sai ya yi imani da Allahn da take bautawa, sannan kuma ya amince Allahnta shi ne mai gaskiya, kuma mai zartar da kowanne hukunci. A taƙaice dai, kusan ridda take sa mutum ya yi."

Shiru Sarki Giɗaɗo ya yi, yana cikin nazari Galadima ya ce.
"Amma fa an tabbatar mini da aikinta tamkar yankan wuƙa haka take yin sa. Kuma tana aiki da mabambamtan jinsin aljanu kala-kala, a taƙaice dai buƙatarka za ta biya ranka shi daɗe."
A fili Sarki Giɗaɗo ya sauke ajiyar zuciya ya ce.
"Mun amince Galadima."
Galadima ya jinjina kai ya ce, "Amma kuma yana da kyau mu yi fitar sirri ranka shi daɗe."

"Yanzu haka a shirye muke Galadima, idan babu damuwa za mu iya tafiya. Sai dai ba ma son masarauta ta fahimci ba mu kwana a gida ba."
A fili Galadima ya saki murmushi mai sauti ya ce.
"Ranka shi daɗe, Bokanya Kande sha'aninta fa ya shallake duk tunanin mai tunani. Saboda a ziyarar da na kai, hadimanta sun ba ni wuridin da zan furta a zuciya wanda za mu buɗe ido mu gan mu a tsibirinta."
Daɗi sosai Sarki Giɗaɗo ya ji, nan take ya shiga Turakarsa ya sauya kayan jikinsa. Yana fitowa ba su ɗauki lokaci ba, Galadima ya dafa tsakiyar kan Sarki Giɗaɗo. Ya saka shi suka rufe ido, sannan ya fara biya wuridin tsafin da zai kai su tsibirin da take rayuwa.

Wata irin sassanyar murya suka ji tana raira waƙar mai matuƙar daɗi, hakan ne ya alamtawa Galadima sun ƙarasa tsibirin Bokanya Kande. Suna buɗe ido suka ga ƙaton cross a gabansu, Galadima ya dubi Sarki Giɗaɗo ya ce.
"Ranka shi daɗe, ni iya hurumin da aka lamunce mini kenan. Kai ne za ka
runtse idonka, idan ka dafa wancan gicciyen (Cross) za a biya maka kalmaman imani da Allahn Bokanya Kande.
Kamar Sarki Giɗaɗo yana jira, cikin sauri ya

6 / 14