Kundi Uku Book Compelet By Ameera Adam

Author :  Ameera Adam Category :  Read Hausa Novels

Chapter   8 / 14

21K to 24K   out of 40.4K words

sannan ya ce.
"Ya zama dole mu nemo wa kanmu mafita."

Cikin sauri ya buɗe wata ƙaramar ƙofa da ke bangon Yamma na cikin ɗakinsa, wani tsoho ne tukuf a zaune. Sai da Sarki Dikko ya zaune a gefensa sannan ya ce.

"Muhimmiyar magana ce ta kawo ni wurinka Babagana."

"Na riga da na san haka, domin banza ba ta kai zomo kasuwa."
Tsohon ya furta muryarsa tana rawa, Sarki Dikko ya ce.
"Ina mai cigaba da ba ka haƙuri bisa killace ka da na yi a nan na tsahon shekaru, duk da na tabbata duniya ta jima da binne shafin rayuwarka."
Babagana ya saki murmushin takaici sannan ya ce.
"Lokaci zai zo da zan bayyana a idon al'umma, a wannan gaɓar da za ta zo kuwa ina matuƙar tausayinka Sarki Dikko."
Sarki Dikko ya zuba masa manyan idanunsa da suka kaɗa jajir, ya dafa kafaɗar Babagana ya ce.

"Kafin lokacin mun gama samun biyan buƙatun kanmu har mun hallaka ka."

"Lokaci ne zai nuna, don yana gab da zuwa a daidai wannan gaɓar." Babagana ya furta yana sakin murmushi, duk tsahon shekarun da Babagana ya ɗauka a wannan ɗakin bai taɓa jin Babagana ya furta doguwar magana haka ba. Don haka tsoro ya so mamaye zuciyarsa, amma gudun kada ya nuna a gabansa ya sa shi cewa.
"Babagana ban san abin da kuka taka ba har kuke ƙoƙarin nuna mana ƙwarin gwiwarku? Shin mene ne abin da kuka taka?"

Kamar yadda yake yi akai-akai, haka yanzun Babagana ya fara tari sama-sama. Sai da Sarki Dikko ya miƙa masa ruwa ya sha, sannan ya ce.
"Ƙwarin gwiwata tana gab da zuwa, sai dai a wanne lokaci? Ni kaina ban sani ba, amma na sani ba za ta taɓa bari gangar jikina ta mace a hannunka ba."

Ajiyar zuciyar Sarki Dikko ya yi sannan ya ce.
"Mu ajiye tattaunawarmu a gefe, za mu ajiye mata lokaci domin mu samu tattaunawa."
Jinjina kai Babagana ya yi ya ce, "Ina sauraronka, wataƙila ina da masaniya a game da damuwarka."

Gyara zama Sarki Dikko ya yi ya ce, "Bayan Waziri babu wanda ya san da wannan sirrin namu Babagana."

"Ba iya Waziri ba, har waɗanda ba ka taɓa tsammani ba sun san da wannan matsalar taka, kai dai ka saka ido mutanen da ke kewaye da kai. Hatta shi kansa Waziri ban gama aminta da shi ba, amma wannan ra'ayinka ne ka ɗauki shawarata ko ka watsar da ita."
Shiru Sarki Dikko ya yi da jin kalaman Babagana, ya ƙura masa ido yana kallo tare da sake jinjina baiwa da hikimar da yake da ita. Sai da ya gyara zamansa sannan ya ce.
"Dattijo Babagana, shin kuna nufin bayan Waziri akwai waɗanda suka san ina haifar yara masu nakasa?"
Gyaɗa masa kai Babagana ya yi ya ce. "Ba ka yi mamakin yadda aka yi ni da nake kulle a ƙarƙashin ikonka a tsawon shekaru na sani ba, sai waɗanda suke rayuwar 'yanci a doron ƙasa? Shi ya sa na ce ka cigaba da kula da hagunka da damanka, domin za ka sha mamaki idan ka ji masu son bankaɗa labulen sirrinka."

"Sautari muna mamakin da tambayar kanmu, shin kuna taimakonmu ne ko kuwa mu maƙiyan juna ne Babagana?" Sarki Dikko ya furta yana kallon Babagana, shi ma kallonsa yake sai kuwa ya saki murmushi ya ce.
"Kada ka saki jiki ɗari bisa ɗari da ni Sarki Dikko, domin murmushin maƙiyi ba abin yarda ba ne. Duk wani taimako da za ka ga na yi maka, ina yi ne domin na haskawa mai shirin fitar da ni hanya."

"Wace ce ita?"

Sarki Dikko ya wurga masa tambaya a kausashe, a madadin Babagana ya ba shi amsa sai ya saki murmushi ya ce.
"Bari na saukaka maka bincikenka, mace wacce ta kasance tana yawo a cikin rayuwarka. Amma ka rubuta ka ajiye, duk daren daɗewa za ta zo har cikin nan sannan ta tono duk wani ƙulli da ka binne kuma ta bayyana a idon duniya."

Haɗiye yawu mai ɗaci Sarki Dikko ya yi ya ce, "Mun ji duk kalamanku, ita ma wannan maganar mu ajiye ta a gefe. A ina zan samu Kursum? Kuma a wannen yanki zan haɗu da ɗan'uwanka tsoho Sulaimanu? Domin Boka Tsumbur yana buƙatarsu a cikin aikin da ya yi mana."
"Ba ni zan baka wannn amsar ba, amsarka tana cikin littafin 'Ruwa A Wuta' wanda ka binne shi tare da gawar Sarauniya Humaira."
A hargitse Sarki Dikko ya ɗago yana kallonsa, Babagana ya gyaɗa masa kai ya ce.
"Domin kuwa ga dukkan alamu tarihi ne yake yunƙurin maimaita kansa."
Ajiyar zuciya suka saki su duka biyun, daga haka Sarki Dikko ya miƙe ya ce. "Na bar ka lafiya Babagana, ina fatan za ka cigaba da hutawa cikin aminci." Yana gama faɗa bai jira cewar Babagana ba ya fice daga ɗakin. Sai da ya tabbatar ya rufe ƙofar, sannan ya cire kubar ya wuce maɓoyarsa ta sirri sannan ya zauna ya zabga tagumi.

Yana nan zaune babu jimawa, ya ji sallamar Jakadiya daga bakin ƙofa. Sai da ya ba ta izinin shigowa sannan ta shiga cikin girmamawa ta zube a ƙasa tana faɗin.
"Allah Ya taimake ka, Ubangiji Ya ƙara maka lafiya. Allah Ya sauki Fulani Hauwa kulu lafiya, sai dai a gafarce ni abin da ta haifa Allah Ya yi masa rasuwa."
Sarki Dikko ko a jikinsa, saboda ya san ko babu komai yana da waɗanda za su gaje shi su ɓangaren sarauta a wannan lokacin. Don haka ya ce, "A cewa Shamaki su yi duk abin da ya dace, idan an kintsa Fulani muna buƙatar ganawa da su." Godiya Jakadiya ta yi masa ta fice, sannan ta ƙarasa ɗakin Fulani Hauwa kulu. Sai dai tana zuwa ta same ta a bakin ƙofa, ta zube a ƙasa ta ce.
"Allah Ya taimake ki ranka shi daɗe ya ce a sanar da Shamaki ya yi abin da ya dace." Gyaɗa kai Fulani Hauwa kulu ta yi, ta ce.
"Ki je kawai Jakadiya, duk abin da ya dace zan aiwatar wa abin cikina, daga haka kuma zan binne shi a ɗakina domin hankalina zai fi kwanciya." Jakadiya tana son sake magana, ganin babu fuska ya sa ita yi godiya sannan ta fice daga sashen Fulani Hauwa kulu. Bayan fitarta Fulanin ta shige ɗakinta, ta shafa cikinta tana sakin murmushi sannan ta ce.
"Tun da na gama da wannan shafin, a yanzu ne zan dawo Fulani Karima kamar yadda nake a baya, ba Fulani Hauwa kulun da aka sanni ba."

Masarautar Judala

Kukan da jaririya Batul take tsalawa shi ya tashi mafi yawan bayin da ke kwance suna bacci, jiki a sanyaye Indo ta ƙarasa cikinsu hannunta rungume da jaririyar. Sai da dogaran suka ga su Indo sun zauna, sannan suka wuce suna cigaba da faɗan kamar yadda suke yi a baya.
Ɗaya bayan ɗaya haka suka dinga bin ta da kallon tuhuma, wasu suka fara mamakin yadda ƙaramar yarinya ta haihu lafiya ƙalau ba tare da sun ji nishinta ba. Wasu kuma ganin yadda take raɓe-raɓe, ta sake birkicewa ya sa suka fara zargin ko ba 'ya ce ta halaliya ba. Kallon Zinaru ta yi idonta yana cigaba da zubar da hawaye, Zinaru ta kawar da kai gefe alamar can ta matse miki tana sakin guntun tsaki.

"Ke yarinya ki ba ta ta sha mana, wannan ai ɗaukan hakki ne. Ba kya ganin yadda take tsala kuka?"
Wata dattijuwa da aka kamo su tare da su Indo ta furta, birkicewa ta sake yi ta shiga inda-inda ganin haka ya sa suka sake tabbatar da lallai haihuwar fari ce Indo ta yi. Saboda sun lura da yadda take jin nauyin shayar da ita, murmushi Dattijuwar ta saki ta ce.
"Ƙuruci dangin hauka, yarinya ai kowa kika gani da haka ya fara. Bari ki gani, idan aka ce za a bi ta kunya ai da ke ma ba ki kawo haka ba."
Dattijuwa ta sake furtawa, sannan ta miƙe ta isa gaban Indo. Sakata ta yi ta gyara zamanta, ta saka hannu tana ƙoƙarin ciro maman Indo. Wata mata daga gefe ta ce.
"To ko ruwan maman ne bai zo ba? Kin san wasu fa dama sai zuwa wani lokaci yake sauka."
Kamar Indo ta zuba ruwa a ƙasa ta sha ta, bakinta har rawa yake ta ce.
"Eh bai zo ba."

"To 'yar nan ai ba shiru za ki yi ba, yanzu kin ga mu baƙi ne a wurin nan. Ballantana a tatsar mata nonon akuya."
A daidai lokacin da dattijuwar ta furta haka Uwar bayi ta ƙarasa cikin gadara ta ce. "Kai! Ba ma son shashancin banza da wofi, lafiya kuka cika mutane da surutu tun asuba ba ta yi ba? Jaririyar wace da ba za ta kula da ita, sai ta hana mutane bacci?"
Gabaɗaya shiru suka yi, sai dattijuwar ce ta sake cewa.
"Tuba muke yi, dama yarinyar nan ce ta haihu. To kuma yanzu haka jaririyar sai kuka take ga babu ruwa a maman."
A wulaƙance Uwar bayi ta dubi Indo da ke raɓe tana zare ido, ta taɓe baki ta dube su ta ce.
"Kuma duk cikinku babu mai shayarwa? Ba za a samu wata ta ba ta kafin nata ya zo ba?"
Shiru suka yi babu wanda ya iya magana, sai wata busasshiyar mata ce ta ɗaga hannu ta ce.
"Allah Ya taimake ki yanzu haka shayarwa nake, idan mahaifiyar jaririyar ta lamunce sai na shayar da ita."

A sheƙe Uwar bayi ta dubi Indo ta ce, "Kin ji ai abin da ta faɗa, idan kuma ba za ki ba ta ba sai ki bar ta ta yi ta tsala kuka." Tana gama maganar ta yi gaba, har ta fara tafiya ta waigo ta ce. "Idan na sake jin hayaniya har na sake fitowa, to kuwa za ku yaba wa aya zaƙinta."
Tsuru-tsuru suka yi duk tsoro ya sake mamaye su, a hankali Indo ta ƙarasa wurin matar da ta ce za ta shayar da jaririya Batul. Ta miƙa mata ita cikin sanyin jiki ta yi mata godiya, zuciya ɗaya matar ta karɓi Batul ta zauna sannan ta saka mata mama a baki. Batul tana kai bakinta jikin matar sai gani suka yi matar ta yanke jiki ta faɗi.

Ummou Aslam Bint Adam🌚

[26/11, 21:49] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.

SHAFI NA GOMA

*AF'S DATA PLUG*
_MTN AND AIRTEL DATA AVAILABLE...!!🔥_

Monthly data — valid for 30 days

_📶MTN DATA_
• 500MB — 450
• 1GB — 700
• 1.5GB — 1000
• 2GB — 1,300
• 3GB — 1,900
• 5GB — 2,100

_📶AIRTEL DATA_
• 1GB — 750
• 2GB — 1,400
• 3GB — 2,150
• 3.5GB — 1,800
• 5GB — 2,850
• 6GB — 2,900
• 10GB — 5,600

𝙋𝙖𝙮𝙢𝙚𝙣𝙩 :
Opay — 7049439332
AFNAN ADAM
𝙒𝙝𝙖𝙩𝙨𝘼𝙥𝙥 𝙉𝙤: 09040772027

_Thank you❤_

Masarautar Kajjura

Shiru Jakadiya ta yi kamar mai nazari, saboda sai a lokacin take ganin girman wautar da ta aikata na sakin bakin da ta yi a wurin Fulani Zainaba. Cikin inda-inda ta ce.
"Na'am... ranki... shi daɗe, dam... dama na ce a yi mini afuwa ban san wurin da turakar sirrin take ba."

Kallon tsaf Fulani Zainaba ta yi mata, ta ƙarasa gabanta murya a kausashe ta ce.
"Idan har kika ɓoye mini wani abu, to tabbas sai na haɗa miki tuggun da ba za ki taɓa fita ba. Ko a kan mutuwar Fulani Khadija, ina iya zarge wuyanki har gaban Mai martaba. Don haka ina son ki feɗe mini biri har wutsiyarsa, idan ba haka ba za ki gane ba ki da wayo."
Cikin Jakadiya ne ya kaɗa, cike da tsoro ta ce.
"Don Allah ki yi mini rai, ki yi mini aikin gafara ranki shi daɗe."
Gyaɗa mata kai Fulani Zainaba ta yi ta ce, "Ina sauraronki."

Sai da Jakadiya ta waiga, ta ƙara matsawa gaban Fulani har sai da ya kasance suna jin numfashin juna sannan ta ce.
"Ranki shi daɗe, wani ɓoyayyan sirrin ɗakinsa ne da ke cikin turakarsa. Idan kika shiga rumfar (Falo) ki tsaya a daidai tsakiyarsa, idan kika ɗaga kanki sama daga jikin azarar za ki hangi wata gajeriyar aska a saƙale a sama, ita wannan askar ta tsafi ce. Ita ce za ki ɗauka, ki shafa jinin sarki gambo a jiki. Saboda a yadda na taɓa jin labari, an ce duk shigar da zai yi ɗakin sai ya yanki jikinsa da wannan askar. Jininsa ya taɓa jikin askar, a haka zai zo saitin tsakiyar rumfar ya fara haskawa da ita. A nan za ki ga daidai ƙofar da take shimfiɗar wurin tana yayewa, da zarar kin soka askar ƙasar wurin za ta dare. Idan za ki shiga ki tabbatar askar tana hannunki na hagu, kuma da ita za ki shiga har cikin ɗakin. To da zarar kin shiga, shimfiɗar wurin za ta haɗe ta koma yadda take."

A fili Fulani Zainaba ta sauke ajiyar zuciya, tare da sharce gumin da yake saman goshinta. Cikin damuwa ta ce.
"Jakadiya dole sai ta wannan hanyar?"
Gyaɗa kai Jakadiyanta yi ta ce, "Ai ba a nan ma gizo yake saƙar ba ranki shi daɗe!"

"A ina ne?"

Fulani Zainaba ta yi saurin wurga mata tambaya, gyara zama Jakadiya ta yi ta ce.
"A wurin fitowar ne, don a yadda na ji labari an ce a yadda Sarki Gambo ya sihirce ɗakin ba ya fitowa a take a lokacin da ya shiga, har sai doshin magriba. Sai dai ina jiye miki tsoron kada Sarki Gambo ya gano ki ranki shi daɗe, domin na tabbata sai ya zartar miki da mummunan hukunci, don an ce ya taɓa hallaka ƙaninsa Galadima wanda suke uwa ɗaya uba ɗaya saboda wannan ɗakin. To da yake dai jita-jita ce, amma zancan da nake yi miki Galadima ya yi ɓatan dabo har yau ba a sake ganinsa ba. Dalilin haka ya sa ake yi masa wannan zargin, amma Allah Shi ya bar wa kansa sani."
Jakadiya ta numfasa sannan ta cigaba da cewa.

"Saboda an ce ba iya waɗannan takardun ne a cikin ɗakin ba, ɗakin ya haɗa duk wani babban sirri da ƙudurin Sarki Gambo. Don a wata majiya da na ji, an ce akwai wata doguwar hanya idan aka bi ta har maɓoyar da Kursum take rayuwa. Don har kawo yanzu, babu wanda ya tabbatar da ainahin abin da ke ƙunshe a cikin ɗakin. Saboda babu wanda ya taɓa shiga cikinsa ya fito har ya cigaba da rayuwa, sakamakon kisan wulaƙancin da yake sa wa ayi wa mutum. Saboda a zargin da ake yi, mutane kusan uku ne suka taɓa gangancin shiga."
Kan Fulani Zainaba ne ya cunkushe, ta miƙe ta fara zagaye tana nazartar kalaman Jakadiya. Duk sai ta ji gwiwarta ta yi sanyi, don gani take ba za ta iya cimma alƙawarin da ta ɗaukar wa marigayin mijinta Najibullah ba.

"Ke da tsoho Sulaimanu kaɗai, kuka rage waɗanda za ku cika muradin ahalina. Sai kuma jinina da ke jikinki idan kin sauka lafiya, Zainaba ina ji a jikina za ki yi tsawon rai har ki cika mini burina."
Fulani Zainaba ta tuna kalaman marigayi Najibullah, nan take ta hau girgiza kai ta ce.
"In Shaa Allahu zan iya, zan cika maka burinka matuƙar ina numfashi. Idan har ni da tsoho Sulaimanu mun gagara cika muradinka, jininmu da ke rayuwa a masarautar nan zai kawo ƙarshen komai In Shaa Allah Najibullah. Na zaɓi ya yi ɓoyayyar rayuwa ne, har zuwa lokacin da zai ɗauki fansar zuri'arku."
Jakadiya tana daga zaune ta yi kasaƙe, tana nazari da mamakin yadda aka yi Fulani Zainaba take da ɗa a cikin masarautar ba tare da kowa ya sani ba.

Gyaran muryar da Fulani Zainaba ta yi ya sa Jakadiya ta sake russunar da kai ƙasa ta ce.
"Amma Allah Ya taimake ki, idan kin lamunce zan sanar da ke wata maganar."
Cikin sauri Fulani Zainaba ta waiga ta ce, "Je ki kanki tsaye Jakadiya."
Jakadiya ta yi gyaran murya sannan ta ce, "Allah Ya taimake ki akwai abin da ban sanar da ke ba, amma don girman Allah ki dubi darajar Allah ki rufa mini asiri ranki shi daɗe."
Shiru Fulani ta yi don ta fahimci maganar Jakadiya tana da matuƙar muhimmanci, don haka ta zauna a kujerar da ke fuskantarta ta ce.

"Na yi miki alƙawari Jakadiya, tsakanina da Allah babu mahaulikin da zai san da wannan tattaunawar tamu."

Jinjina kai Jakadiya ta yi ta yi ƙasa da murya ta ce, "Allah Ya taimake ki, bayan ke fa akwai wacce take dakon bankaɗa labulen sirrin Sarki Gambo. Wato Fulani Sadiya, don ta jima tana son ta samu irin wannan damar da kike son samu. Kuma ni na san Fulani hatsabibiya ce, matuƙar ta samu labarin kin ziyarci ɗakin sirrin Sarki Gambo, na tabata za ta iya aikata komai domin cikar muradinta."
Ajiyar zuciya Fulani Zainaba ta sauke ta ce, "Na fahimci komai Jakadiya, tun ranar da Sarki Gambo ya kawo ni sashen matansa a matsayina na matarsa. Na fara nazartar hali da ɗabi'ar Fulani Sadiya, don haka har yanzu

8 / 14