Author : Ameera Adam Category : Read Hausa Novels
ce.
"Malami waɗanne irin mafita kuka hango mana? Muna fatan ba za ta ɓata mana lokacin da za a fuskanci 'yan biyunmu suna da tawaya ba?"
Cigaba da binciken tsubbunsa Malami ya yi, sai da ya sake ɗaukar lokacin sannan ya ɗago ya ce.
"Mafitar guda biyu ce kamar yadda na faɗa maka da farko, kuma a karo na biyu haka binciken ya sake maimaita mana. Mafita ta farko, zan yi aiki da idanun mikiya, kan baƙin maciji da kuma ƙoƙan kan ɗan'uwan wancan tsohon."
Cikin sauri Sarki Gambo ya ce. "Wanne tsoho kenan?"
"Tsoho Sulaimanu!"
Malami ya furta yana kallon Sarki Gambo, cikin mamaki Sarki Gambo ya ce.
"Malami ban fahimci abin da kuke nufi ba, shin shi tsoho Sulaimanu yana da ɗan'uwa ne? Ko kuwa shi kansa tsoho Sulaimanu kuke nufi?" Malami ya girgiza kai ya ce.
"Tsoho Sulaimanu yana da ɗan'uwa Babagana, kuma su ɗin tagwaye ne. Sai dai wannan wani sirri ne da ba kowa ne ya san da shi ba, kuma kaifin ƙwaƙwalwa da hangen nesan Babagana ya zarce tunanin mai tunani. Domin zan iya ce maka ya fi mikiya hangen nesa, don haka zan haɗa wannan aikin da ƙoƙon kansa. Idan na haɗa idon mikiya da ƙoƙon kansa, za su haska mini duk wani duhun sihirin da aka gudanar a kan tagwayenka, shi kuma kan maciji zan yi amafani da shi ne domin ka san duk duniya babu dabbar da ta kai maciji jin motsi ko magana duk ƙanƙantarta. Ragowar mahaɗin kuwa ruwan ƙoramar fadar sarauniya Humaira ne, amma wannan mai sauƙi ne. Domin ina da kyakkyawar alaƙa da Aljani Dakkum, na tabbata shi zai ɗeɓo mini shi."
Ajiyar zuciya Sarki Gambo ya sauke, cikin damuwa ya ce.
"Amma ya aka yi a duk binciken da kuke yi mana ba ku taɓa sanar da mu haka ba? Ya aka yi ba mu san da zancan Babagana ba?"
"Saboda komai yana da sila Sarki Gambo, a yanzu ma mafitarka ce ta sa muka binciki maka wannan maganar." Malami ya numfasa sai ya cigaba da cewa.
"Mafita ta biyu kuma, sai dai ka ziyarki kogin Sutturu, wanda yake ɗauke da hatsabibiyar bishiyar kukar nan da ake bautawa. Amma wannan ziyarar taka za ta kasance mafi hatsarin gaske, domin kuwa akwai tarun ƙalubale a cikinta, za ka iya dawowa a raye za ka kuma iya haɗuwa da ajalinka. Domin ba iya ziyarar za ka kai ba, akwai waɗansu abubuwa da za ka gudanar a cikin wannan bishiyar kukar. Sai dai kuma, tunkarar mutuwarka sai ya fiye maka sauƙi a kan ka tunkari wannan bishiyar kukar."
"Mun fi aminta da zaɓin farko! Shin a ina za mu samu shi wannan tsohon Babagana? Don shi kaɗai ne abin da zai nemi wahalar da mu, tun da mikiya da maciji ba za su yi wahalar samu ba." Sarki Gambo ya furta yana kallon Malami. Murmushi Malami ya yi ya ce.
"A yanzu haka Babagana yana ɓoye a fadar sarki Dikko, kuma wannan fadar ta kasance hatsabibiyar da sihiri bai cika tasiri ba. Da ace mutum ɗaya tana raye, ita ce za ka iya samun shiga salin-alin ba tare da wani mummunan al'amari ya faru da ita ba."
"Wace ce ita?"
Sarki Gambo ya tambaya bakinsa yana rawa. Malami ya ajiye bangon ƙur'anin hannunsa ya ce.
"Fulani Karima! Sai dai kuma koda ace tana raye, zai yi wuya ta karɓi buƙatarka hannu bibbiyu. "
A wannan karon damuwar Sarki Gambo ta sake yawa, cikin sanyin jiki ya ce.
"Mene ne mafita tun da ba ta raye?"
"Mafita ɗaya ce ka nemi amintacciyar baiwarka, ko wata makusanciyarka. Ka aikata masarautar Sarki Dikko, domin ta san duk wani shige da fican makircin da za ta yi ta samu nasarar auren Sarki Dikko."
Malami yana gama faɗa Sarki Gambo ya furzar da iska mai zafi ya ce.
"Idan har wannan ce mafita an gama Malami, domin a kan tagwayena babu abin da ba zan iya aikatawa ba."
Malami ya jinjina kai ya ce.
"Za ka iya tafiya Sarki Gambo, ragowar tattaunawar za mu yi ta daga baya."
Da yake zuciyar Sarki Gambo a cunkushe take da damuwa, miƙewa ya yi ya fice ba tare da ya yi wa Malami sallama ba.
Sarki Gambo yana zuwa turakarsa ya aika aka kira masa Fulani Sadiya, sai da ta sheƙa kwalliya sannan ta ƙarasa cikin takun isa da ƙasaita.
"Barka da hutawa sadaukina!"
Fulani Sadiya ta furta tana sakin shu'umin murmushi, don kallo ɗaya ta yi masa ta fahimci yana cikin matsananciyar damuwa.
"Barka dai Fulani!"
Ya amsa mata murya babu yabo babu fallasa, Fulani Sadiya ta sake narke murya cike da kissa ta ce.
"Ina kewar Sarki na tsawon kwanaki, sai dai damuwar da ta cunshe shi tana yunƙurin shata layi tsakanina da shi."
Shi kansa ya san ya yi kewarta, don haka cikin shauƙin so ya ƙarasa kusa da ita ya riƙo hannunta. Da ɗayan hannunsa ya tallafo kanta, suka fuskanci juna kowannensu yana sauke ajiyar zuciya. Zame alƙyabbar jikinta ta yi, ta lumshe ido cike da jan hankali ta ce.
"A kullum na kan tuhumi zuciyata, ko na jefa mata tarin tambayoyin dalilin da ya sa ta afka da'irar ƙaunarka."
Kalamanta ne suka fara tasiri a kansa, don haka a kasalance ya ɗago haɓarta ya haɗe bakinsu wuri ɗaya. Fulani Sadiya ƙwararriyar ce wurin gogewa a kissa da kisisina, don haka duk irin fushin da Sarki Gambo yake ciki matuƙar zai gayyato ta makwancinsa, to tabbas za ta yaye masa kaso mafi yawa daga cikin damuwar da yake ciki.
Cikin salonta, ta shiga sarrafa shi har sai da ta lura saƙon da take isar masa ya gama mamaye ilahirin jikinsa. Zare jikinta ta yi daga na shi, cikin wani irin yanayi ta ce.
"Gwarzona!"
"Me ya sa kika dakatar da mu? Alhalin kin san jikinku ya zame mana madogarar da ke yaye duk damuwar da muke ciki."
Tallafo fuskarsa ta yi, ta sa bakinta ta sakar masa sumba a saman laɓɓansa. Tabbas idan ta ce Sarki Gambo mummuna ta san ta sharara ƙaryar da duk wanda ya ji zai ƙaryatata, tana yunƙurin janye fuskarta ya janyo ta jikinsa ya rungume ta tsam kamar wani zai ƙwace fa. Ɗago idanunta ta yi ta dube shi, kamar mai raɗa cikin sauyin yanayin da ya shiga ya ce.
"Muna cikin damuwa Fulani."
"Dalilin da ya kawo ni turakarka kenan ranka shi daɗe, domin damuwar da nake ciki ta ninke taka."
Ɗan ɗagowa ya yi ya zuba mata ido cike da kulawa.
Book 1 ya kusa ƙarewa, masu son cigaban book 2&3 za tura 700 ta acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta nan 07062062624 idan littafi ya kammala zuwa doc 1k ne.
_MTN AND AIRTEL DATA AVAILABLE...!!🔥_
Monthly data — valid for 30 days
_📶MTN DATA_
• 500MB — 450
• 1GB — 700
• 1.5GB — 1000
• 2GB — 1,300
• 3GB — 1,900
• 5GB — 2,100
_📶AIRTEL DATA_
• 1GB — 750
• 2GB — 1,400
• 3GB — 2,150
• 3.5GB — 1,800
• 5GB — 2,850
• 6GB — 2,900
• 10GB — 5,600
𝙋𝙖𝙮𝙢𝙚𝙣𝙩 :
Opay — 7049439332
AFNAN ADAM
𝙒𝙝𝙖𝙩𝙨𝘼𝙥𝙥 𝙉𝙤: 09040772027
_Thank you❤_
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[30/11, 21:36] Ameerah Adam: *KUNDI UKU*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Gargaɗi: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Daga Masarautu, Sarakuna da sunayen yanki duka ƙirƙira ne. Idan ya yi daidai da labarin wani/wata arashi ne.
SHAFI NA SHA HUƊU
Masarautar Judala
Sai da Zuwaira ta gyaɗa wa Indo kai, sannan ta cigaba da cewa.
"Tun ranar da Baushe mai magani ya sanar da ni wace ce yarinyar nan, da irin al'amuran da ke tattare da ita. Ya bayyana mini miyagun ƙaddarorin da za su afka wa rayuwarta, don babban abin da ya fi ba ni tsoro yadda na ga ya jiƙe sharkaf da gumi a lokacin da yake yi binciken tauraronta." Zuwaira ta ɗan yi jim sai kuma ta cigaba.
"Na san za ki yi mamaki a lokacin da na shayar da Batul har na yanke jiki na faɗi, tun kusan shekarun baya nake fama da wannan lalurar. Kuma Baushe da kansa ya sanar da ni sammu ne aka yi mini wanda ba zan samu warkewa ba har sai na haɗu da ita. Kuma na san za ki yi mamaki idan na ce miki ni mayya ce."
Cikin alamun tsoro Indo ta ja da baya, ƙirjinta yana bugawa ta cigaba da kallon Zuwaira. Ganin haka ya sa Zuwaira ta saki murmushi haɗe da gyaɗa mata kai ta ce.
"Ƙwarai kuwa ni 'yar sarkin mayun yankinmu ce, maita gadon gidonmu ce gaba da baya. Kakata da ta haifi mahaifina an ce saboda yadda maita ta huda ɓargon jikinta, ko tsuntsu ne ya zo giftawa ta saman gidanmu sai dai gawarsa ba shi ba. Wani zubin kuwa idan abin ya ciyo ta, ta rasa dabbar da za ta ci. Sai ta je kasuwar mahauta, ta sayi ɗanyen nama ta shige ɗaki ta cinye. Amma kuma duk wannan maitar ta kakata, ba ta taɓa cin ɗan mutum ba har ta ƙare rayuwarta."
Indo a tsorace ta sauke ajiyar zuciya tana gyaɗa kai, don wasu kalaman na Zuwaira jin su take ba tare da tana fahimtarta ba. Ita kanta Zuwaira ta lura da haka, ta dafa kafaɗarta ta ce.
"Kada kalamaina su tsorata ki Indo, ni ba mai cutarwa ba ce. Kawai ina sanar da ke wani sirri ne, domin tun da na fahimci kina tare da Suryu hankalina ya kwanta da ke. Duk da wani tsagin na zuciyata yana tantamar kasancewarki mahaifiyarta, domin ban ga alamun da Baushe ya ce mahaifiyarta tana da shi a jikinki ba. Ya ce mini mahaifiyarta zuciyar zaki gare ta na rashin tsoro, ke kuma na ga tsoro ƙarara a saman fuskarki. Sai dai kuma na tabbata ko da ba ke ce mahaifiyarta ba, tabbas zuciyarki mai kyau ce Indo." Sai a lokacin hankalin Indo ya ɗan kwanta, Zuwaira ta kawar da ƙwaryar da ta yi wa Batul wanka gefe sannan ta cigaba da faɗin.
"Daga mahaifina har mahaifiyata ƙungurman mayu ne, har sai da ta kai mahaifina ya ci mutum ɗari ba ɗaya wanda silar haka ne ta sa a ka naɗa shi sarkin mayun yankinmu. Duk da dama can mahaifinsa shi yake riƙe da wannan sarautar, amma kasancewar mahaifina yana da tarin 'yan'uwa daga waɗanda suke uwa ɗaya uba ɗaya zuwa 'yan uba. Sai suka taso shi a gaba saboda kowa so yake ya gaji sarautar mahaifinsu, sai dai duk miyagun sihirin da suke yi na jifan mahaifina bai yi tasiri a kansa ba. Da suka lura mahaifina yana son damƙa mini ragamar sarautar hannunsa, sai suke shiga jifana da asiri kala-kala. Kuma ni abin da ba su sani ba, ko kaɗan ban taɓa sha'awar riƙe kambun da mahaifina yake kai ba. Don mun sha kai ruwa rana da mahaifina, a kan sai na ci adadin mutanen da ake ci kafin a damƙa maka ragamar sarautar maita. Me zai sa na cutar da 'yan'uwana Indo? Bayan kuma Ubangiji bai hallice mu don mu cutar da kowa ba, kuma me zai hana mu dinga taimakon bayar da magani a madadin cutarwa?"
Indo ta jinjina kai ta ce, "Haka ne kam Inna Zuwaira."
Zuwaira ta ji daɗin sunan da Indo ta faɗa mata, don ta tabbata a haife kam za ta haifi Indo.
"To don na nuna wa mahaifina haka, sai ƙilu ta ja bau. Mahaifina ya sako ni a gaba, haka dangin mahaifina da suke zargin za a damƙa mini sarauta suka sako ni a gaba. A taƙaice dai har sai da mahaifina ya so bayar da kurwata a bikin bada kurwa da ake yi a yankinmu duk shekara, amma sai mahaifiyata ta tsaya kai da fata don ganin hakan ba ta tabbata ba. In taƙaice miki labari, ban san hawa da sauka ba sai kawai na wayi gari da wasu baƙin cututtuka. Yau da lafiya gobe babu, hatta mijin da na aura mun haɗu ne a wurin neman magani. Da Innata ta kai ni shi kuma ya nuna yana sona, amma duk sanin sirrin maganinsa sai ya gagara gano ainahin abin da yake damuna. A haka na fara haihuwar yara suna mutuwa, abin da ban sani ba ashe dangin mahaifina ne suke kashe mini su suna cinyewa. Wannan ɗan da kika ga na zo da shi masarautar nan, shi kaɗai ne ya rayu a cikin yara goma da na haifa. Shi ma tun cikinsa yana ƙarami na fara zuwa wurin Baushe mai magani, a nan ya dinga ba ni taimakon magunguna har Allah Ya sa na haife shi lafiya. Ranar da na fara shayar da shi, a ranar na ga abin al'ajabi. A madadin ruwan mama ya zuba, sai ya zamana wani baƙin jini ne yake fita. Jaririna ya ƙi karɓa, bayan da na koma wurin Baushe ya ba ni magani sai na samu lafiya. A nan ya sake sanar da ni duk irin cutukan da ke jikina, tare da makarinsu da kuma yadda za a yi na samu lafiya."
Buɗe baki Zuwaira ta yi, ta zaro wani abu fari mai tsayi kamar zare. Ita dai Indo tana takure a gefe sai raba idanuwa take yi, kama hannun Batul ta yi za ta saka mata. Da sauri Indo ta janye Batul gabanta yana faɗuwa ta ce.
"Don Allah kada ki sa ta zama mayya ita ma, don Allah ki ƙyale ta haka."
Murmushi Zuwaira ta yi, busasshiyar fuskarta da babu tsokar kirki ta sake yamutsewa. Da yake Indo ta gama tsora ta da ita, har gani ta yi fuskar Zuwaira tana neman razana ta. Tana cikin haka ta ji Zuwaira ta ce.
"Ba ƙanƙarar maita ba ce Indo, ina tunanin har yanzu ba ki san wace ce Batul ba. Shi ya sa kike tsammanin zan iya cutar da ita, wannan dalilin ne ya sa na sake tabbatar da ba ke ce mahaifiyarta ba."
Indo ta waiga tana kalle-kalle don kada wani ya ji tattaunawarsu, ta yi ƙasa da murya ta ce.
"Don girman Allah kada ki furta wannan maganar a cikin mutane, tabbas Batul ba 'yata ba ce. Ba ni na haife ta ba, amma ƙaddara ta haifar mini ita kuma zan riƙe ta hannu bibbiyu."
Nan take Indo ta kwashe duk abin da ya faru tsakaninta da Karima ta sanar da ita, Zuwaira ta jinjina kai ta ce.
"Shi ya sa na ce zuciyarki mai kyau ce Indo, kuma In Shaa Allahu zan cigaba da nuna wa duniya ke ɗin mahaifiyarta ce. Kuma na ɗauke ki tamkar 'yar cikina, haka kuma Batul kamar jika ta. Sai dai ni ma ina neman alfarma a wurinki."
Idanu Indo ta zuba mata alamar tama sauraronta, Zuwaira ta ce.
"Ki yi mini alƙawarin ba za ki taɓa sanarwa da kowa cewa ni mayya ba ce, haka kuma ba za ka dinga wasu-wasin zan cutar da ku ke da Batul ba. Sannan duk halin da kike ciki, ki mini alƙawarin ba za ki ɓoye mini ba."
Gyaɗa kai Indo ta yi ta ce, "Zan faɗa miki amfanin wannan zaren da zan saka mata, kema kuma idan ba za ki damu ba. Zan saka miki shi a dantsen hannunki, idan kuma ba ki da muradi shi kenan ba zan tilasta miki ba."
Zuwaira tana gama maganar ta naɗa zare ya zama kamar awarwaro, sai ta kamo hannun Batul ta zura mata shi, wani irin haske suka gani a jikin hannun nata. Nan take zaren ya fara kwanciya a fatar hannunta, daga ƙarshe ya shige cikin jikinta gabaɗaya tamkar wani abu bai taɓa wanzuwa ba.
Daga Indo har Zuwaira kallon juna suka yi, bakin Indo yana rawa ta ce.
"Ya... ya... aka yi ne Inna Zuwaira?"
Zuwaira da ta gama tsora ta ta ce, "Wallahi ban san yadda aka haihu a ragaya na, ni a iya sanin da na yi wannan zaren yana zama a jikin hannu ne ba tare da ya ɓace ba. Amma ita nata ki duba ki ga har wata wuta ya yi kafin ya ɗauke." Kamar Indo za ta yi kuka ta miƙe tana jijjiga Batul da ta fara mutsu-mutsu za ta yi kuka. Suna cikin haka sai suka ga daidai wurin tsintaiyar hannun nata ya yi ja kamar an saka awarwaro a wuta an ciro an saka mata a wurin, wanda hakan ne ya tabbatar wa Zuwaira shatin zaren da ta saka mata a hannun ne.
Uwar Bayi
Uwar bayi sai da ta fito daga fadar sarki Giɗaɗo sannan ta ankara da irin katoɓara da kuma suɓutar bakin da ta yi. Musamman da ta tuna abin da ya faru da Dogari Mamma, gabanta ne ya shiga faɗuwa sai kuma ta tuna wane ne Sarki Gidaɗo da hatsabibancinsa. Da wannan ta ɗan ji faɗuwar gaban ta ragar mata, tana shiga soron farko ta ji kamar an hankaɗa ta har sai da ta kusa faɗuwa. Waigawa ta yi ba ta ga kowa ba, tana juyo da kanta don ta cigaba da tafiya sai ta hangi wata dattijuwa a gabanta. Da sauri ta ja baya tana sauke ajiyar zuciya, tsohuwar ta fara matsawa gabanta cikin muryar tsufa ta ce.
"Uwar bayi sannu da ƙoƙari, ko babu komai za ki taka muhimmiyar rawa a wannan tafiyar..."
Daga haka sai tsohuwar ta wuce soro na biyu, cikin sauri Uwar bayi ta bi ta. Sai dai tana zuwa soron ba ta ji koda takun tafiyar