Sauyin Yanayi Book Compelet Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   8 / 20

21K to 24K   out of 58.4K words

gama shawo kansa, kawai abunda zance miki shine su turo ayi auran kawai"

Rik'e baki kawai Asiya tayi tana kallon K'awar tata, shaid'aniya uwar shaid'anu. Yo idan ba shaid'aniya ba, waye zai haka?.

Kamo hannunta Mama tayi tana fiskewa ta ce "ke karkiyi wani mamaki fa, kamar kin manta wace ni?".

Ture komai Asiya tayi tana cewa "tunda kin gama da wannan, kema tukaicinki babba ne, idan abun ya kasance"

"Baki da damuwa komai zai kasance yadda muke so".

Dariya suka saki a tare harda tab'a hannu.

*Copa Cabana Estate Lokogoma District Abuja Nigeria*

Waya ce manne a kunnan Momy suna waya da Asiya.

Daga cikin wayar Asiya ta ce "Hajiya an gama komai fa, yanzu haka wakilanku kawai zaku turo a d'aura auran, ku tafi da amarya"

"Da kyau, haka nake sonji. Zan turo miki naira million biyar, ki d'auki naira million biyu, kiba wacce tayi hanyar abun ya yiwu, naira million d'aya, shi kuma Abban yarinyar ki basa cik'on naira million biyun"

Wata shewa had'e bud'a Asiya ta saki tana cewa "saike Hajiyarmu, uwar gida, a gidan Alhaji Bin Muhammad daga ke ba k'ari, Allah dai ya biya".

Dariya kawai Momy ta saki tana kashe wayar. Ba'a jima ba kuwa saiga message na account number na Asiyar. Nan take ta tura mata kud'in gaba d'aya.

Zaune take a gaban Daddy bayan ta gama koro masa jawabin abunda take so ayi.

"Daddyn Salman, ina ganin yarinyar ita ce ta dace da zama da Salman, domin yarinyar tana da hankali da tunani, zata zauna dashi tsakani da Allah badan komai nasa na duniya ba, domin duk sauran da yake aura duk dan kud'insa ko kyansa ke rud'arsu".

Daddy ya aje wani biro dake hannunsa yana rubutu a wasu takardu ya ce "kina ganin ita yarinyar ba'a danne mata hak'k'inta ba?, kin sanfa yadda rayuwar yaron nan take ciki"

Kamo hannun Daddy Momy tayi cike da kissa ta ce "ba wani danne hak'k'inta da akai. Hasalinma taimakonta akai, saboda ita kanta tasan ko a hanya bata isa ganin Salman ba, yaro mai kud'i ga kyau ga nasaba, komai ya had'a, kawai wannan ciwon ne ke basa matsala a rayuwa, kuma da sannu komai zai shige, idan komai ya wuce ita ce da riba nake gani ai"

Wani murmushin jin dad'i Daddy yayi, yaji dad'in yadda ta fahimtar dashi, kuma ya fahimta sosai. Inda daga k'arshe ya ce "to ita yarinyar y'ar ina ce?, yaushe kuma kike ganin za'aje domin tabbayo auran nata?"

"Y'ar Hadejia ce, kuma tabbayo aure duk bai taso ba, d'aurasa kawai za'ai, domin duk na gama da wannan, yanzu haka Abban yarinyar yasan da maganar, ku kawai yake jira"

"Ai shikenan tunda abu yazo gidan sauk'i. Zanje da kaina tare da wasu manya dana aminta dasu a d'auro auran zuwa gobe insha Allahu".

Cike da farin ciki Momy ta baro part d'in Daddy. Tafe take tana maganar zuci.

"Hmm Alhaji kenan, kaifa gani kake kamar son d'anka nake ko?, ina duk duniya ba abunda na tsana yanzu kamar shegen yaron can naka, amma da sannu zan kawo k'arshensa".

*NANAH* POV

Wani irin sansanin y'an Ta'adda ne su Auta suka tsinci kansu ciki. Auta ba abunda yake sai kuka yanata neman inda zai hangi Nanah.

An zube su wani waje duk ciyayi ga rana ta kwanyare.

Kowa ka gani wajan sab'anin y'an Ta'addar cike suke da tashin hankali.

Kamar ance Auta ya waiga ya hango Nanah dake d'aure a jikin wata bishiya har yanzu a sume take bata farka ba. Gashin kanta ya sakko ya rufe mata fuska.

Da gudu Auta ya nufi inda take, yana aikin kiran sunanta.

Wani d'an Ta'adda ne ya matso ya kwasa masa tsawa, yana cewa "kaiii ina zaka je haka?, koma inda kake kar yanzu na fasa maka kai da wannan Bindigar"

A tsorace ce Auta ya ke duban D'an Ta'addar. Amma duk da haka tsaye yake inda Nanah take ya rik'e tsintsiyar hannunta sai jijjigata yake.

A hankali Nanah ta fara motsa hannun nata, kamin komai nata ya fara dawowa dai-dai, dashi-dashi take ganin mutane, hatta muryar Auta sama-sama take iya jiyota, kamin ta ware idonta akan Auta.

Auta ko jin Nanah na motsa hannunta yasa shi sakin murmushin k'arfin hali yana sake kiran sunanta.

Kallon Auta take kamar wacce ta samu tab'in hankali. Kamin komai a hankali ya fara dawo mata, duk abubuwan da suka wakana a daran jiya.

Tana gama tunanowa ta fashe da wani irin kuka mai k'arfi jikinta na rawa, ta kama leb'en bakinta ta cije tana durzar kuka. Ganin yadda take kuka yasa Auta ma fashewa da kuka.

Wani daga cikin y'an Ta'addar ne ya k'ara matsowa inda suke, bai tsaya wata-wata ba, ya damk'e gashin kan Nanah ya jashi zuwa baya da k'arfi, har saida ta saki wata k'arar azaba. Fuskarta ce ta bayyana.

Hawaye duk sun b'ata mata fuska. Cike da rashin imani yake kallonta ya ce "zakiyi mana shuru a wajan nan, ko sai na kashe wannan bakin naki, maima mutane kukan banza?"

Wani irin bak'in ciki ne ya rufe Nanah, data na dama wallahi saita kashe duk wani d'an Ta'adda dake wajan yanzu, to amma bata da damar hakan.

Sakinta yayi yana maido dubansa inda Auta yake.

Ya wani k'ankance ido ya ce "ni wai miye ma anfanin tahowa da wannan yaron?, ai da an rage masa wahalar duniya, an aikasa can kiyama".

Zare ido Nanah tayi tana jin wani sabon tashin hankali na saukar mata.

Tafiya suka farayi suka bar wajan da Nanah take. Suna magana, ganin haka yasa Auta rungume Nanah dake d'aure kamar wata akuya.

Ba abunda y'an Ta'addar suke sai shan tab'a da giya. Ga y'an matan da suka dad'e da satowa suna faman dafa masu abinci, wasu ma sun maida su k'aruwan k'arfi da yaji, sun maida su kamar wasu matansu.

K'iri-k'iri sai kaga k'aton gardi, daya ji sha'awar mace, zai d'auki mace kamar kayan wanki yayi cikin wata rufma da ita, ya biya ma kansa buk'ata, ya kuma tashi ya zuge wandonsa. Yadda suke afka masu kamar wasu dabbobi.

Yadda Nanah ta lura da yawan matan wajan suna sato sune kawai dan su rink'a masu bauta, da biyan buk'atarsu kawai. Hakan yasa Nanah shiga wani sabon tashin hankali marar musaltuwa.

Motsi kad'an tana nanik'e da Auta, wadda ji take kamar ta mayar dashi ciki.

Wata irin yinwa ta fara addabar wa'inda suka sato, ciki harda Auta, ya fara kuka, yana gaya ma Nanah yinwa yake ji. Dan rabonsa da abinci tun jiya cikin dare gashi har gare ya waye rana na neman fad'uwa.

Wasu hawaye ne suka shiga zuboma Nanah na tausayin Auta, ita dan ita zata iya zama a haka, zata iya jurewa na d'an wani lokaci, kai zama ta iya hakura har zuwa wata safiyar. Shifa?, yaro ne.

Gashi anbi an wani d'aure mata hannu, tana son rarrashin Auta, tama rasa wacce kalma zata fara basa hakuri da ita.

Kukan da Auta yake ne ya fara isar y'an Ta'addar. Hakan yasa wadda Nanah bazata tab'a manta sunansa ba, Mai suna Tajo ya nufo inda suke.

Duk duniya idan akwai wadda ta tsana to bazai wace wannan Tajo ba, shine ya rabata da farin cikin rayuwarta, wato Innarta, shine ya ruguza masu rayuwa, shine ya rabasu da jigwan rayuwarsu. Da tana da dama saita kashe Tajo kamar yadda ya kashe Inna.

Da jajayen idonsa yake kallon su Nanah, ganin irin kallon da Nanah ke aika masa dashi, na tsananin tsana da fusata, yasa Tajo shekewa da wata dariya yana nuna Nanah da hannunsa.

Can ya tsagaita dariyar yana kallon Nanah da ba alamar tsoro yanzu a cikin idonta. Ya ce "keee uban mi yaron nan yake so ya ishemu da kuka?".

Shuru tayi bata da niyar magana ga Auta daya k'ara balun d'in kukansa.

Haushi abun ya bama Tajo, hakan yasa ya d'auke Nanah da wani gigitaccan mari. Wadda yasa taga giftawar wasu taurari. Duk da haka taji zafin marin daya kai mata, amma tayi shuru tana kallonsa da jajeyen idonta da suka kad'a sukai jawur.

Ganin fa bazata tanka masa ba, yasa Tajo jawo Auta ya daka masa tsawa yana cewa "kaii kayi ma mutane shuru ko yanzu nasa wuk'a na yanka maka wuya wallahi"

Auta bai daina kuka ba, majina da hawaye duk sun b'ata masa fuska.

Wani dogon tsaki Tajo yaja yana shafa sumar kansa, ya d'an daga kansa sama, sak'on d'aya biyu....... Kawai ya kaima Auta wani bugu a saman kai, nan take Auta ya zube a sume.

Wani sab'on kuka ne ya kufce ma Nanah tana kiran sunan Auta iya k'arfinta, duk tunaninta ko mutuwa yayi.

Cikin muryar kuka take magana tana kallon Tajo cike da tsana ta ce "ku sani Allah bazai tab'a kyale ku ba, Allah saiya isar mana akan zaluncin da kuke mana. K'aramin yaro ma baku kyale ba, tsabar baku da imani, Allah ya isarmu wallahi bamu yafe ba".

Dariya Tajo ya saki yana matsowa inda Nanah take, ya damko wuyanta yana cewa "au ashe kina magana y'an mata?, na d'auka ai kurma muka d'akko. Dama mu ai bamu ce ku yafe ba. Ya ishe mu da kukan banza ne, shine na sashi yin baccin dole, kin gane?, zai farka ai ba mutuwa yayi ba, amma ki sani ya sake mana irin haka, to zaibar duniya ne gaba d'aya. Ya kamata ki kula, bama son damuwa ne".

Wani abu mai d'aci Nana ta had'iye a mak'oshinta tana bin Tajo da kallo. Ji take inama tana da dama data shak'e masa wuta shima harsai ya daina numfashi.

Cikin dare Nanah tajiyo kukan Auta daya farka, sanyin dake cikin dajin ne ya farkar dashi, ga kuma inda yake kwance tsinnaku duk sun cijeshi a jiki. Da sauri Nanah ta kira sunansa a hankali. Da lalube ya k'araso inda Nanah take, yana zuwa ta rufe masa baki da tafin hannunta data samu Tajo ya kwance mata shi, d'azo daya gama gaggaya mata magana.

A hankali Nanah ta ce "dan Allah Auta kayi shuru, kayi hakuri kaji?, zuwa safiya za'a baka wani abu kaci, kana kallo mutanan nan basu da imani fa, kana so ka mutu ne?".

Da sauri Auta ya girgiza mata kai.

Ta ce "to yawwa ka daina kuka idan baka so kaji?".

Ba yadda Auta yayi dole tasa yayi shuru ya mak'ale a jikin Nanah.

Suna haka, sukaji ihun wata matashiyar yarinya, daga jin yadda take ihun tana neman taimako, zaka san cewa so ake a keta mutumcinta ne.

Yadda Nanah ke jin yarinyar na cewa "wayyo Allah, ku taimaka min zai kashe ni, na shiga uku ina zan kai wannan mutunin, zai lalata min rayuwa dan Allah ku ceceni".

Waro idonta Nanah tayi tana kallon wata ruffa da abun ke faruwa hasken fitila ta gani a wajan, ihun yarinyar na fitowa daga cikin rufar. Tana iya jiyo yadda suke kokowa da yarinyar, tana son kwance kanta. Tana jin shi kuma yadda yake ta kai mata maruka ba k'ak'k'autawa.

Allah sarki yarinyar duk da irin dukan da yake kai mata so kawai take ta kwaci kanta, sai kuka take tana kiran azo a taimaketa.

Ganinfa tana son b'ata masa lokaci, gashi duk ta ji masa ciwo yasa ya harzuk'a bai san sadda ya d'akko bindiga ba ya sakar mata harsashi.

A mugun rud'e Nanah ta toshe kunnuwanta had'e da k'ara rungume Auta daya fasa wata gigitacciyar k'ara yana sumewa a jikin Nanah, domin harga Allah ya mugun tsorota sosai. Nanah tama rasa wane hali take ciki, duk ta rud'e ta fice daga yaccinta. Ga Auta da bata jin motsinsa a jikinta, ga yarinyar da tana da tabbacin ita ce aka halba. Tana iya jiyo yadda D'an Ta'addar ke ta'asarsa saman kan yarinyar duk da halbinta da yayi, amma tsabar mugunta da rashin imani a haka ya afka mata.....

_________________________

Mike shirin faruwa ne da Salma wai?, ya rayuwar Salman zata kasance a nan gaba ne wai?, shin Momy wacce irin zuciya ce da ita ne ta rashin imani?, kaiii wannan Mama ma akwai y'ar kwal uba fa🤭. Shin wai tsaya ma Hajiya zata amince da aurar da ake son d'aura ma d'iyarta wadda bata san dashi ba?, Yaya Salma zata ji idan taji an d'aura mata aure da wani, waninma wadda bata tab'a gani ba?...*KAIII JAMA'A AKWAI CAKWAKIYA A BOOK D'INGA, NA TSAYA A NAN DOMIN NIMA INA SON SANIN DUK AMSOSHIN NAN*

_________________________

*To a nan na kawo k'arshen Free pages*

*Game son ci gaban book d'in nan zai biya D'ARI BIYAR NE KACAL*

Ta wannan account number d'in.

8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank

Saika turo shaidar biya ta wannan number d'in 08130479973

P 11

*Unguwar Dubantu Hadejia Jigawa State Nigeria*

Kwance Salma take tana bacci. Wani irin juyi take bisa gadon tana zabura, had'e da firgita, ga wata irin zufa data wanke mata jiki. Hajiya ce ta shigo d'akin jin yadda Salma ke zabura, da wani nishi da take saki.

Ganin yadda Salma keyi yasa Hajiya ba shiri ta zauna a kusa da ita, ta fara tofa mata duk wata addu'a data zo bakinta.

Tana fara tofa mata addu'ar kuwa ta daina zabura. Sai kuma ta bud'e idonta a d'an firgice take kallon Hajiya. Can ta sauk'e ajiyar zuciya ta kwanta jikin Hajiya tana sauk'e lumfashi kamar wacce tayi gudu.

Hajiya ta shafa kanta tana cewa "Salma lafiyarki kuwa?, mafarki kikayi ne haka?, hala bakiyi addu'a ba kika kwanta?".

Salma cikin murya mai sanyi ta ce "Hajiya nayi addu'a, kawai dai wani irin mafarki nayi mai ban tsoro, akwai sark'ak'iya cikin mafarkin, Hajiya mafarkin nan ya tsaya min a rai".

D'an jan lumfashi Hajiya tayi, tana duban Salma da kulawa ta ce "karki sa mafarki nan a ranki, domin shi ba gaskiya bane, ki yawaita yin addu'a duk halin da kika tsinci kanki Salma, babu abunda yafi k'arfin Allah, kuma babu abunda al'qur'ani baya maganinsa, ki rik'e wannan kinji?".

Murmushin kawai Salma ta sakarma Hajiya tana jin dad'in yadda lokaci d'aya ta samu natsuwar zuciya, saboda abunda Hajiya ta fad'a mata.

Hajiya zatayi magana taji sallamar Abba a tsakar gida yana kwala mata kira. Ga kuma wata hayaniya dake tashi a tsakar gidan nasu.

Lokaci d'aya Salma taji gabanta ya fad'i, dafe k'irjinta tayi tana karanto addu'a.

Hajiya a d'an rud'e ta fito tsakar gidan, Salma na bayanta.

Ganin Abba tsaye rik'e da goro da alawa, manya manya ya shigo dasu ga wasu mata Manya masu ji da gayu biye dashi. Yasa Hajiya kallonsu da mamaki.

Mama dake zaune a k'ofar d'akinta, ita dasu Maryam duk sunsan miye ke faruwa da abunda ke shirin faruwa. Kallonsu Hajiya tayi ganin wani murmushi da suke saki, ya k'ara sawa Hajiya jin wata fad'uwar gaba, wacce bata shirya jinta ba. A wajan Salma ma hakane. Canta tsinkayi muryar Khadija cikin habaici tana cewa "hmmm yau wata sai gidan majanunin mijinta".



A kid'ime Hajiya dai ke binsu da ido kawai daga ita har Salma jira suke suji miye abunda Abba zaice masu.

Abba dake faman fiddo alewa ya ce "kinga wannan goron da alawar na d'aurin aure ne"

Hajiya gabanta na ci gaba da bugawa tayi k'arfin halin cewa "d'aurin aure kuma Abban Salma?, to waye akama aure?".

"Mi kike ci na baka na zuba?, ai yanzu zaki ji kona waye".

Abba ya sake d'agowa yana duban Salma, ganin ita yake kallo yasa Salma jin, y'an cikinta sun murd'a tashin hankali ya rufeta lokaci d'aya.

Kamin ta gama tunanin data lula taji saukar maganar Abba kamar saukar aradu a saman kanta. Yana cewa "Salma ce aka d'aure ma aure yanzun nan, kuma yau za'a wuce da ita gidan mijinta".

Salma da Hajiya jin maganar suke kamar ba dai-dai Abba yake fad'a ba, ji suke kamar a mafarki ne zasu tashi baccin da suke yi.

Jin yadda Abba ke k'ara jaddada zancan yasa Hajiya kallonsa cike da tsananin mamakinsa. Tama rasa miye zata ce ma wannan bawan Allah.

Da kyar ta fisgo magana daga bakinta ta ce "Abban Salma, anya kaji miye kace kuwa?".

"Mahaukaci kike mayar dani komi?".

"Ni ban mayar dakai Mahaukacin ba, amma maganar ce tazo min kamar hankali ma bazai tab'a d'auka ba, ya za'ai ace wai an d'aura ma y'ata aure ni ban sani ba, ita kuma bata sani ba"

"Saboda kece ubanta ko?, ni nake da ikon aurar da ita ga duk wadda naso, kuma nayi niya. Dan haka na k'ara fad'a miki an d'aura auran Salma, da mijinta Salman Bin Muhammad, kuma a yau za'a wuce da ita garin Abuja, zataje ta ci gaba da kula da mijinta domin yanzu haka yana buk'atarta a kusa dashi".

"Abban Salma nafa kasa gasgata abunda kake fad'i, abunda bazai tab'a yiwuba ba kenan fa"

"Ni kike fad'a haka a gaban mutane?, ni kike son tozartawa akan y'ata wacce nake da cikakken iko da ita?. Yo ko mahaukaci na bata ai dole ta amsheshi ta zauna dashi, dan haka ki iya bakinki Hajiya".

Rai a mugun b'ace Hajiya ta nuna Abba tana cewa "Ka sani akwai Allah kuma yana ganinka, Allah ba azzalumin sarki bane, wannan abun da kayi akwai San kai a ciki. Ita kad'ai ce d'iyarka ne?, mi yasa baka bada su Maryam ba, sai ita saboda anga babu wata riba da za'aci, ni komai y'ay'ana sune abun wulakantawa a gare ka".

Hajiya ta idasa maganar had'e da fashewa da kuka mai zuma zuciya.

Da sauri Salma ta matso kusa da Hajiya itama tana kuka. Rungume Mahaifiyarta tayi suka cigaba da kuka abun tausayi.

Duk da haka Abba ko a kwalar rigarsa ya sake cewa "nidai na gama maganata, kuma dole ki bada Salma a tafi da ita gidan mijinta, wannan umarni na ne, idan kikai wani abu sab'anin haka kuma, a bakin auranki Hajiya".

Da

8 / 20