Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
da y'an India, wai shine mijinta. Anya kuwa wannan ba aljani bane?, domin harga Allah idan ka kallesa kyansa har wani fisgar mutum yake, kallo d'aya kuma idan kayi masa sai kaji tsigar jikinka na tashi, had'e da fad'uwa gaba.
Da sauri Salma ta d'auke idonta daga kallon Salman ta waigo inda Daddy yake ta gaida shi a ladabce.
Da murmushi kwance akan fuskarsa yake amsawa yana cewa "y'ar albarka, ga mijinki nan, dan Allah kayi hakuri dashi fa, domin miskili ne sosai, kuma kayi hakuri da duk abunda zaki gani a zamanku tare dashi, sai kin jure komai wata rana zai wuce kamar ba'ayi ba, ki basa kulawa dan Allah".
Lokaci d'aya taji tausayin Daddy ya kamata, yadda taga yana rok'on ta kula da d'ansa zaka san ba k'aramin so ne yake ma D'an nasa ba.
Cikin sanyin murya Salma ta ce "insha Allahu Daddy zanyi k'ok'arin haka, Allah kuma ya basa lafiya".
Sosai Daddy yayi farin ciki da ganin cewa matar d'ansa ta wannan karon ba kamar sauran bace, wannan mai hankali ce da sanin ya kamata, ga iya zance ta iya magana a tsanake, lallai yana da tabbacin wannan lokacin D'ansa ya dace da mata, sai masa fatan Allah yasa shima yaso ta, ya kuma yarda da ita a matsayin matarsa.
A cikin mota su Momy bayan sun baro asibitin zasu koma gida, dan Salma da kanta ta ce suje su huta zata zauna dashi. Momy ta sallami sauran matan da suka taho da Salma.
Momy Allah-Allah take su isa gida kota kira Asiya. Domin yadda taga yarinyar kamar fa zata iya b'ata mata shiri ne, gashi komai ya k'ure mata, tunda an riga da an d'aura auran, bata da ikon cewa Salman ya saki matarshi yanzu.
Ai ko suna isa Momy tayi cikin d'akinta da sauri. Daddy ya bita da kallo yana mamakin saurin miye take haka?.
Tana shiga ta aje jakarta ko zama batai ba, ta d'akko waya ta dannama Asiya kira.
Tana d'auka bak'o sallama bare gaisuwa ta fara cewa "Asiya ya naga matar da kika sa na aurama Salman kamar akwai ilimin addini a tare da ita?, kuma akwai natsuwa a tare da ita ga hankali kuma".
Daga cikin wayar Asiya ta ce "hmm Hajiya duk zata nuna haka, amma in gaya miki babu uwar data iya, a karatu bare harna addini babu abunda ta sani, domin shi kanshi Abbansu abunda yasa ya tsaneta kenan, kwata-kwata a makaranta bata da k'ok'ari, kullum cikin musguna mata yake, shi yasa ma naga ba wacce ta dace sai ita. Dama ita haka take bata da kwaramniya kwata-kwata".
Wata ajiyar zuciya Momy ta sauk'e har Asiya na jinta ta ce "kai wallahi har hankali ya kwanta, dana ji hakan, ai na d'auka komai ta iya ne".
"A'a wallahi ko kad'an Hajiya, ba abunda ta sani, bare ma ta b'ata miki shiri".
Sallama sukai Momy ta kashe wayar.
*Unguwar Dubantu Hadejia Jigawa State Nigeria*
Asiya na sauk'e wayar ta kalli Mama dake zaune kusa da ita, har yanzu Asiyar na gidan bata tafi ba.
Mama ta kalleta ta ce "anya wannan matar bata fini son duniya ba, da shaid'anci?".
Dariya kawai Asiya ta saki, domin ita tasan Aysha itama muguwa ce, cikinsu ta kasa gane waye yafi iya had'a munafurci da mugunta, tsakanin Mama da Momy.
Asiya ta d'an gyara zamanta ta ce "kinga na zafga mata k'aryar cewa, Salma bata da ilimin addini, shin da gaske ne har a Islamiya bata da k'ok'ari ko kuwa bokon ne kad'ai?".
Mama ta tab'e baki ta ce "ai kuwa tsakani da Allah Salma indai ta b'angaran Islamiya ne, sai dai ta koyar da wani, domin har sauka tayi kusan sau biyu ma, kuma tasan littatafan addini sosai, dan dai gaskiya bata wani rik'e addu'a sosai, saboda duk aikin da nake mata da kyar ake samu ya kamata, wani lokacin ma sai idan tana jinin haila".
Zaro ido waje Asiya tayi tana cewa "ke yanzu to ya za'ai da Momy idan taji haka?".
"Kinga kawai ki share, Momy bama zata tab'a ganewa ba, ke kuma saiki fad'a mata cewa tana da rik'o da addu'a?, wani lokacin kuma ai tana wasa da addu'ar, kin san D'an Adam, yana da shagala da duniya. Ki barsu can saji da juna, nidai tunda burina ya cika akanta ai shikenan, na kusa rufe babinta ma ni".
Dariya kawai Asiya tayi tana cewa a zuci "kaii lallai Hajara kin taki abunda kika taka a gidan nan, keda Momy komai sai abunda suke so shine akeyi a cikin gidajen ku, itakam bata jin zata iya yin abunda sukeyi, ta dai biye masu abi yarima asha kad'a, kallo ne nata idan ansa da ita ta biye a aiwatar, amma bata jin zata iya cutar da wani d'an Adam, abisa ra'ayin kanta dai, an dai had'a baki ko asata aiki ta aiwatar.
(Kaji wannan matar, anyi ba'ai ba kenan?, tunda aka had'a baki aka cuci wani dake, ai kamar kema kin aikata laifi ne irin nasu).
*KHADIJA* POV
Tsaye take rik'e da leda a hannunta, tana d'an jujjaya jikinta, ledar dake hannunta na d'an motsawa. Sai Jafar dake jingine da mota a k'ofar gidansu Khadijar.
Kallonta yake yana ta shararo mata k'aryar daya saba mata ai koda yaushe, yana cewa "ai nake gaya miki My Khady dole ne ma, ranar bikin nan namu a kama wajen dinner mai kyau mai tsada, za'ayi biki ne wadda ba'a tab'a yin irinsa ba".
Dariya ta saki tajin dad'i tana cewa "Wow da gaske My love?".
"Wallahi kuwa, ai babu abunda za'ai na k'aranta a bikinmu".
Murmushi ta sakar masa tana sake cewa "amma kuwa da ka gama min komai a wallahi, ina son harkar girma, a rayuwata, bana son harkar k'aranta".
Murmushi ya saki shima yana cewa "harkar k'aranta ai sai talaka shine ke yin wannan".
"Hakane kuma fa My love, shi yasa a rayuwata na tsani talaka wallahi".
Kallonta yake yana murmushin yak'i a zuci yake cewa "uhum lallai ma wannan ajawon yarinyar, kajita wai ta tsani talaka, ai ko baki san nima nan talakan bane fotuk ma kuwa. Ai ko duk abunda na kashe miki tun daga had'uwarmu harna hidimar biki, da zanyi, saina fanshesa ta hanyar saida kayan d'akin da za'a miki, tun kan a kaisa gida na, zansa a saida shegu na biya bashi dana ci dasu, idan yaso na sai miki dai-dai wadda zasu iya shiga d'aki d'aya a gida na dam..... Maganar zucin da yake ce ta tsinke jin Khadija na cewa "kayan lefe ma ina son irin akwatunan da muka tab'a gani da mukaje shopping da kai a ranar nan, ka tuna?".
Dariyar zuci yayi yana cewa a ransa "ni ko nasansu, ai hatta lefe auro akwatunan zanyi, danma ki sani, komai zanyi shine ta hanyar ba yacce za'ai ki gane ni talaka ne, har sai an kawo ki gida na, tukunna za'ayita ta k'are".
Sai can kuma ya ce "na gane irinsu ai, duk abunda kike so dole ne nayi k'ok'arin siya miki a cikin lefen, duk wasu abubuwa da kike so asa a ciki kawai kiyo min liss nasu, duk zaki gansu a ciki, karki wani damu".
Murmushi tayi tana k'ara jin son Jafar d'in a ranta, tana k'ara jin dad'in yadda komai sai abunda take so shine yake yi. Da yanzu fa duk wannan abun Salma ce zata samu ba ita ba ko?, kai ta gode Allah lokacin daya zo Salmar ma bata gidan, ai da rabo ya wuce ta tana zaune sake da baki.........
P 14
*Off Ty D'anjuma, Asokoro District*
Tunda suka shiga gidan Salma ta zama bak'auyar k'arfi da yaji, domin da gani take gidan Daddy mai kyau ne, ashe na Salman d'in ya ci uwarsa a wajan had'uwa da tsaruwa.
Ba wadda yayima wani magana cikin ita dashi, ya dai nuna mata d'akin da take da tabbacin yana nufin shine zai zama nata.
Bayan ta shiga tana bin d'akin da kallo, ya had'uwa sosai. Cire hijab d'inta tayi ta shiga toilet ta watsa ruwa, tawul ne d'aure a jikinta, bayan ta fito, ta hangi akwatin kayanta, da murna ta matsa ta bud'e ta ciro wata riga marar nauyi ta ajeta bakin gado.
Da sauri ta bud'e d'ayar jakar tana fiddo da wayarta, Hajiya ta kira, kwalla na taruwa a idonta. Ai Hajiya na d'aukar kiran, ta sakar mata kuka.
Hajiya dake cikin wayar ta sauk'e ajiyar zuciya tana cewa
"Haba Salma, ai saiki tayar min da hankali. Y kuke?, ya mijin naki?".
Turo baki Salma tayi kamar tana gabanta ta ce "hmm Hajiya yana nan, ya samu sauk'i mun dawo ma gida".
"To ki nutsu Salma ki rungume mijinki Salma, bana son abunda zaije ya dawo ace kinyi, kin san halin Mahaifinki, karma ya ce ni ce ke zugaki kiyima mijinki rashin d'a'a, dan Allah ki bisa sauda k'afa, ki gama lafiya dashi, sana ki kula dashi, ki kula da cutar dake damun mijinki, ki rink'a masa addu'oi. Sana kema ki kula da shan magungunan ki, ki kula da abunda zaki rink'a ci".
Sauk'e lumfashi Salma tayi tana d'an gyara zamanta akan gadon data ke, kamin ta ce "insha Allahu Hajiya, zanyi duk abunda kike ce, sana Momynsa ta ce ai ciwonsa wai bana asibiti bane".
"Bana asibiti bane kuma?, amma naji kince ta ce idan ciwon ya tashi yana wasu surutai yana kawowa mutane bugu ba?".
"Hakane Hajiya, kin san jiyan da muka iso muna waya dake, ina zaune ne ma a tare dashi a asibiti, kuma ita ce, ta ce min haka, amma gaskiya ni Hajiya ban yarda da Momyn nan ba, saboda ta ce min wai kamar uwa take a wajansa, kenan ba ita ce Mahaifiyarsa ba?".
"Tabbas Salma sai kin iya takunki a wajan matar nan, tunda zuwan farko take iya bud'e baki ta ce miki wai ba ita ce uwarsa ba, ki iya bakinki Salma, ki san ya za'ai ki zauna da ita, kuma bance karki fasa masa addu'a ba, idanma tana da wata manufa akanki taje can aniyarta tabi ta, kedai ki kula kawai".
Sun dad'e suna magana kamin suyi sallama. Salma na aje wayar tana niyar tashi ta shafa d'an mai a jikinta tasa rigar bacci.
Taji kamar k'arar bud'e k'ofar d'akin data ke.
A zabure ta d'akko hijab d'inta ta zura, tsabar sauri ma bata sata dai-dai ba. Salman ne ya shigo hannunsa rik'e da wata leda dake shik'e da abinci.
Kallo d'aya yayi mata ya d'auke kansa. Taso ta basa dariya ma, ganin yadda dukta rud'e tasa Hijab d'in a karkace, tana kallonsa idonta a zare.
Baice mata komai ba, illa d'an murmushin gefen baki da yayi, wadda ita kanta Salma bata isa ta ce ta ga yadda yayisa ba. Aje mata ledar yayi akan gado, ya juya zai fita, Salma harta d'auka bazai ce mata komai ba, har ya kai k'ofa, ya kama hannun k'ofar, sai kuma ya d'an tsaya, bai waigo ba, ya ce "ga abinci nan".
Abinda Salma ta iya ji kenan daga bakinsa, taga ya juya ya fice.
Wata wawar ajiyar zuciya Salma ta sauk'e tana dafe kanta. Wayyo Allah wannan mutunin zai kasheta wallahi, duk sadda zata gansa a gabanta, zuciyarta ta kama bugawa kenan, kamar zata fito daga k'irjinta, har sai ya matsa yabar inda take ne, take samun natsuwar zuciya, amma indai yana kusa, ita kanta Salma neman natsuwar take ta rasa.
Jikinta a sanyaye ta cire hijab d'in, taje bakin k'ofar ta kulle d'akin, kamin ta dawo tasa kayan, ko mai d'inma bata shafa a jikinta ba. Bayan tasa rigar ta matsa jikin waduraf d'in d'akin, taja jakar kayanta ta bud'e waduraf d'in, zaro ido tayi tana bin waduraf d'in da kallo, ganinta shak'e da kayan mata, su Hijabs ne da y'an Dubai gasu antanfofi kala-kala duk d'inkakku ne, su las su ne su shadda matiril ne, kuma duk d'inkakku ne suma. Zaro d'aya tayi ta d'an gwada a jikinta, ga mamakinta dai-dai cif da ita, kai kardai ace duk wa'innan kayan nata ne?.
Kai a'a badai ita ba, sai dai ko wata. Take tabbayar kanta, tana girgiza kai, daga k'asa ta samu wani waje ta jera y'an kayanta daba wasu bane, tana gamawa ta rufe waduraf d'in.
Ta dawo inda ya aje mata ledar ta bud'e, wani k'amshi taji ya bugi hancinta, harsai da ta lumshe idonta, da sauri ta idasa bud'ewa, tana kallon abunda ke ciki, kaza ce babba sai wani lemo mai kamar Madara. Sosai Salma taci dama rabonta da abinci tun a Hadejia, ko a asibiti bata wani ci abinci ba, lokacin duk damuwar barin gida ta hanata iya komai, har saida sukai waya da Hajiya ta k'ara kwantar mata da hankali, har taba Ahmad suka sha fira harda su Ismail dake ta cewa wai yaushe zata dawo idan zata zo tayo masa tsaraba.
Murmushi ta saki sadda ta tuno ahalinta, farin cikinta.
Tashi kawai tayi bayan ta gama ci, duk da akwai sauran Kazar da bata cinye ba, saboda harga Allah tayi mata yawa, wannan katuwar kaza haka.
Fita tayi daga d'akin nata, tana sakkowa k'asa, kitchen ta nufa inda take da tabbacin shine, tana bud'e k'ofar kuwa taga kitchen d'in ne. Sakin baki kawai Salma tayi tana bin k'atoton kitchen d'in da kallo, babu abunda ba'a zuba masa ba, na anfanin yau da kullum, babu ce kawai babu, wani irin murmushi ne ya sub'uce ma Salma, tana ta bin kitchen d'in da kallo, domin harga Allah tana son taga kitchen haka, tana mugun farin ciki taga tana sanwa da kanta, shi yasa da yawa babu abincin da bata iya sarrafasa ba, shi yasa ko a wayarta da yawan videos na ciki duk na girke-girke ne, abinci kawai na sata farin ciki, tana son abinci a rayuwarta, shi yasa ko a Instagram wa'inda take following duk masu koya girke-girke ne, irinsu Maryaamas kitchen.
Ci gaba tayi da bin ko ina da kallo, tana bud'e wasu abubuwa dake kitchen d'in, bud'e sito tayi ganin babu abincin sarrafawa yasa ta d'an saki tsaki, itafa gaskiya bazata juri abincin saye ba, zatayi k'ok'arin gaya masa ya sayo mata kayan abinci zata rink'a yi da kanta, ina dalili ga kayan sarrafa abinci a kitchen da yawa amma babu abincin da kansa. Bud'e wata k'atuwar firiza tayi, ganin firizar ta aje nama ce da kayan miya haka dai, amma itama duk babu wasu abubuwa a cikinta, wani tsakin ta sake saki, ta juya d'ayan sayins d'in da take, ta k'ara bud'a wata k'aramar firiza, ta tsaye, sab'anin d'ayar data kwance ce, tana bud'eta ta gane cewa ita kuma ta aje lemoka ce, domin taga wani lemo daya rage guda d'aya, shima kamar a lalace yake. Maidawa tayi ta rufeta itama, bayan ta aje sauran Kazar da bata cinye ba, tana cewa a fili "matsala d'aya ce babu kayan masarufi, amma zan gwada cewa ya sayo, domin ni nafi jin dad'i nayi girki da kaina", yo ko a gida indai girkin Hajiya ne ita ce take amsa tayi komai Hajiya bata komai sai dai ta zauna.
Can kuma saita tuno Hajiya yanzu fa ita ce zata rink'a komai da kanta, wasu y'an guntun hawaye ne taji sun cika mata ido.
Da sauri tabar kitchen d'in ta koma d'akinta.
Kwanciya tayi kan gado, tana tunanin yanzu fa ita d'aya zata rink'a kwana wannan uban d'akin. Gata da d'an banzan tsoro kamar farar kura, k'udundunewa tayi waje guda, bayan ta kashe fitilar d'akin, wani tsoro ne ya rufeta, domin ita harga Allah bata saba kwana ita d'aya ba, a d'aki, juye-juye ta kamayi abu kad'an ta d'akko wayarta ta haske ilahirin d'akin wai ko zata hangi wani abun tsoro, motsi kad'an zataji ta mik'e tana haske-haske.
Sai gabanin Asuba wani bacci yayi gaba da ita.
Yauma taso ta makara, sai da taji ana buga k'ofar d'akinta ne, yasa ta tashi da sauri. Mik'a tayi tana dafe kanta jiya da batai baccin k'irki ba, kanta harya fara ciwo. K'ofar d'akin ta nufa, tana bud'ewa taga babu kowa, d'an lek'awa tayi k'asa, ta hangesa ya bud'e k'ofar waje ya fice, da alama Masallaci zai tafi.
Tab'e baki tayi kenan tada ita yayi kawai?, bama zai mata magana ba kenan?,
Ke Salma ya kamata ki tsaya iya matsayinki, ai baki kai ya tsaya yana miki wata dogowar magana ba, ki shiga hankalinki Salma.
Wata zuciya ke gayama Salma.
Tab'e baki tayi tana nufar toilet.
Bayan tayo alwalla ta fito ta gabatar da sallarta kamar yadda ta saba, kamin ta d'an gyara zamanta akan sallayar bata tashi ba, ta d'an jingina da bakin gado, ta rufe idonta ta fara karantu karatun al'qur'ani a kanta, tunda taga babu al'qur'ani a d'akin, dama kuma ta iya ko babu shi.
Cikin muryarta mai dad'in sauraro take karatunta, idonta a rufe.
*SALMAN* POV
Waya ce rik'e a hannunsa bayan ya fito daga Masallacin dake manne da gidansa. Ya kira PA d'insa yana basa umarnin cewa da safe ya sayo masu abun k'aryawa, baya jin yau zai iya fita wajan aiki, companynsa dake nan Abuja yake son lek'awa, domin tunda yazo bai samu damar zuwa ba, ciwonsa ya tashi, shine duk ya hanasa komai, ya shaida masa idan zai fitan zai nemi sa kawai.
Tunda ya bud'e k'ofar parlon ya shigo, yake jin saukar karatun al'qur'ani a kunnansa. Cike da d'an mamaki yake k'ara baza kunnan nasa domin ya k'ara jiyo daga ina wannan karatun ke fitowa ne?. Mamakinsa ne ya k'aro jin kamar daga sama