Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
dai ba wani kyawun fuska gareta ba sosai, amma na jiki kam ba'a magana.
Da kyar ya iya danne zuciyarsa suka fita, domin baya son rusa mata farin cikinta na fitar da ya ce mata zasuyi.
Kai tsaye wata jami'ar dake kusa da unguwar da suke Salma taga sun nufa. Tunda suka shiga school d'in take faman binta da kallo, domin ba k'aramar makaranta bace, kai da ka kalli yanayinta zaka shaida ta kud'i ce, sai wane da wane da y'ay'an masu hannu da shuni ne kad'ai ke iya shiga irin wannan makarantun.
A sadda suka tsaya dai-dai parking lot na school d'in, da kansa ya fito ya bud'e mata ta fito, da mamakinsa again take kallonsa, kamo hannunta yayi suka fara tafiya. Tunda motarsu ta tsaya har iya zuwa sadda Salman ya fito ya bud'e mata ta fito, hankalin d'alibai Maza da Mata ya dawo kansu, sai y'an maganganu ke tashi a cikin school d'in, ko ina suka gifta sai anyi maganarsu, domin sunyi wani irin kyau sun dace da juna sosai.........
P 21-22
*Unguwar Dubantu Hadejia Jigawa State Nigeria*
Tun daga k'ofar gidansu Salma zaka shaida cewa hidima ce ake sosai, domin kuwa motoci ne sun kai guda biyar ajere a k'ofar gidan, ga y'an mata ansha wanka na kece raini, ko wacce ta ci gayun zuwa dinner. Kaya iri d'aya ne sanye a jikinsu, d'inki kowacce da irin nata, sun tsaya gaban motocin dake parking a k'ofar gidan.
Ana jiran fitowar Amarya, ango kuwa yana d'aya daga cikin motocin dake jere a wajan.
"Khadija kinga yadda kikai kyau?, kamar a sace ki a gudu wallahi, sai san barka".
Bud'ar da aka saki ce a gidan. Y'an jere ne suka dawo daga gidan Amarya. Da gudu Maryam ta fita tana tabbayar ya jeran ya kasance?, taso zuwa gidan Khadijar to hidimar dinner d'in da za'aje ta hanata zuwa.
Wa'inda sukaje kuwa ba abunda suke sai san barka, masu wayoyin ciki da suka je, harda masu yin video na gidan. Sai nunama mutane suke, mutane sai san barka suke had'e da santin gidan, domin gida yayi sosai, irin na masu hannu da shuni ne.
Maryam dake kallon yanayin gidan Khadija sai sakin murmushin jin dad'i take, da gudu taje inda Amarya take ta nuna mata videon gidanta.
Ita kanta Amarya sai wani sakin murmushi take na tsabar jin dad'i, ji take kamar ta kai kanta gidan nata.
Mutane fa sai maganar gidan suke, hatta y'an unguwar taso wa'inda sukaje ganin kwaf sai baza maganar suke kota ina, kamin kace mi gidan ya k'ara cika, wasu dansu tabbatar shin maganar da suke ji hakane?, wasu kuwa dan abincin biki ya kawo su.
Maryam ita ta kamo Amarya aka fita da ita waje, aka sata cikin wata mota wacce tafi sauran motocin dake jere kyau da had'uwa. Khadija data zauna cikin mota ta waiga taga Jafar angon nata, yasa wata d'anyar sadda yayi kyau harya gaji, sai sakar mata murmushi yake, itama murmushin take mayar masa.
Maryam ta koma cikin gidan nasu, tana sanar da duk wadda zaije wajan dinner to yayi hanzarin fitowa domin tafiya za'a farayi.
Ai ko jin haka, yasa da yawan y'an bikin suka kwaso suka fito, aka rink'a jidar mutane ana tafiya dasu inda za'ai dinner, ciki harda Mama ba'a barta a baya ba, domin dama taci babu abunda zaisa bazata je dinner d'in nan ba.
Mutanan da aka biri y'an kad'an ne a gidan.
Hajiya kuwa dama tana cikin d'aki abunta, tana dai fitowa wani lokacin ta d'an kama masu aiki, idan ta gama ta koma d'akinta, hatta Ismail jawosa d'aki tayi ta hanasa zuwa ko ina a ranar, Y Ahmad ko yana wajan aikinsa ma Kaduna, sai gobe zaizo d'aurin aure.
Wajan dinner fa yayi kyau ba k'arya yayi armashi, dinner ake cike da kwanciyar hankali komai na tafiya dai-dai, anci ansha anyi rawa yadda ya kamata. Su Mama ba kunya ta kama tikar rawarta, ana mata lik'i. Sai hotona ake d'auka y'an mata kowacce ta fiddo da wayarta ana kashe hotona. An d'au lokaci anata shagali sai wajan goman dare tukunna aka tashi daga wajan dinner d'in, aka fara jidar mutane ana mayar dasu gida.
"Wash Allah wallahi na gaji nidai Kam".
Cewar Khadija bayan an dawo daga wajan dinner, tana cire kayanta, take fad'ar haka.
Duk y'an mata ne cike da d'akin da suke.
Sadiya dake kusa da ita, wacce ta dawo gidan saboda hidimar bikin komai sai an sata a ciki, shi yasa ta d'ebo kayanta ta dawo gidan bikin kawai.
Ta ce "ai dole ne da gajiya, keda samun hutu yarinya ai sai an kaiki gidan mijinki. Kamin kuma ya sauk'e gajiyarsa a kanki shima ba".
Wata shewa y'an matan dake d'akin suka saki, Khadija tayi dariya tana cewa "kefa y'ar iska ce wallahi Sadiya".
Dariya Sadiya take itama tana cewa "yo ai gaskiya ce, dan kin san Mazan zamanin nan ba hakuri garesu ba, ta wannan fannin, zaki gurzu ne yarinya, bana jin zai iya d'aga miki k'afa a daran farkon ku".
Wata dariyar aka sake saki had'e da sakin bud'a, anata raha da jan Amarya, abokan wasanta y'an mata kamarta sai tsiya suke mata suna janta da wasa, tana biye masu, su Sadiya na k'ara tayasu.
Washe gari, gida fa ya sake hargitsewa da jama'a kota ina hayaniya ke tashi ta y'an biki, sai shiga da fice ake a gidan.
Amarya a ranar ta rasa inda zata sa kanta kota ina mutane zuwar mata suke, daga ace wannan yazo yana son ganin Amarya su gaisa, sai ace wancan yazo.
Amarya sai shan wanka ake, a shiga wannan a fita wannan.
Su Maryam ma an kasa zaune an kasa tsaye sai shige da fice suke ita da K'awayen Amarya su Sadiya.
Wajajen k'arfe sha biyu, mutane suka fara tafiya wajan d'aurin aure, duk mazan dake waje da wasu dake cikin gidan bikin ana gaisawa da y'an uwa da abokan arzik'i, duk sun tafi wajan d'aurin aure, sai lokacin aka samu y'ar ragewar hayaniya a gidan.
Da gudu Ismail ya shigo d'akinsu yana nishin gudun da yayi yasha wasu sabbin kaya. Hajiya ganinsa da gudu ya shigo yasa ta ajiye abincin da take shirin d'iba a cikin wasu kuloli wadda aka ciko mata su da abinci, saboda nata bak'in na hanyar zuwa, zuwa can yamma, ta ce "kai lafiya zaka shigo ma mutane da gudu cikin d'aki?".
"Hajiya wai kin san wa na gani kuwa?".
"Ya za'ai nasan waye ka gani, baccin baka fad'a min ba".
"Hajiya Salma fa na gani, ita da mijinta ya sauk'eta a k'ofar gidan nan, shi kuma ya wuce wajan d'aurin aure shida Y Ahmad".
"Kai bana son maganar banza kaji. Yaushe kaga su Salma?, yama za'ai suda suke Abuja harsu samu damar zuwa d'aurin aure?".
Ismail zaiyi magana saiga sallamar Salma a k'ofar d'aki.
Da sauri Hajiya ta waiga tana duban k'ofar d'akin. Ita ce kuwa ta shigo.
Sanye take da wani less wadda ya k'ara mata kyau, ta k'ara haske tayi k'iba abunta.
Hajiya bakinta yak'i rufuwa, tsabar murna da jin dad'i.
Salma ko rangume Hajiya tayi cike da tsananin farin cikin ganinta.
Tofa tunda akaji Salma tazo ko wanne dake cikin gidan zuwa yake ganinta.
Mama ko sai sakin tsaki take, tana yada habaici tana cewa "aikin banza aikin wofi, yo aikin banza mana, duk wannan gayun a banza ne tunda mijin nata ma ba cikakken mai hankali bane".
Haka Mama tayi ta, yayatama mutane.
Duk abunda take fad'a a kunnan Hajiya, Salma ce ta tausheta ta hanata fita, saboda gidan biki ne, karsu yada hali a gaban jama'a. Tasan ba abunda ke damun Mama sai bak'in ciki da hassadar yadda ta ganta tsaf-tsaf, ba haka taso ta ganta ba, dad'in dad'awa ma ance ai da mijinta tazo, mutane sai kuranta mijin Salmar suke, suna cewa "wai kin gansa kuwa, kamar balarabe, kamar shi yayi kansa".
Wasu y'an matan ma cewa suke, ai wallahi ba hauka ba, ko yankani zai rink'a yi, wallahi na yarda na zauna dashi a haka, kai ko kallona zai rink'ayi na amince a hakan.
Kai magana dai kota ina jinta kake, daga kaji wancar magana sai kaji wannan.
Salma dai ta toshe kunnuwanta kawai bata kula duk wasu y'an maganganu na mutane, duk da wani kishi data ke ji, yadda y'an matan ke yaba mijinta.
Haka nan dai ta shiga har wajan Mamar tayi mata Allah yasa alkhairi had'e da bata wasu kud'i masu yawa na gudunmuwa, da kyar Mama ta amsa saida Asiya ta warce kud'in tanama Salmar godiya.
Harta fice daga d'akin Mama, Mamar na jefa mata wani shegen kallo.
Data je inda su Khadija suke kuwa, ba wacce ma ta kalleta bare har suyi wata magana mai tsayi. Salma bata ji dad'in abunda sukai mata ba, amma ta danne ta koma d'akin Hajiya.
Hajiya ta lura da sauyin yanayin fuskarta, saita share kawai ta d'akko mata wata maganar suka fara fira, suna raha suna dariya, harta manta da abunda su Maryam sukai mata.
A sadda aka dawo daga d'aurin aure, Salman suka gaisa da Abba tun acan ya basa gudunmuwarsa, kud'i ne masu yawa, ya kuma taho masa da kayan abinci buhu-buhu, ba k'aramin dad'i Abba yaji ba, sai sa masa albarka yake, ba k'ak'k'autawa.
Yasa a kira Salma itama ba kunya sai albarka yake sa mata, harda wani cewa ta yafe masa, abunda yayi mata ita da Hajiya. Murmushi kawai Salma ta saki, tana ce masa, ita babu abunda yayi mata, idanma akwai ta yafe masa.
Ana d'aura auran, Salma tayi sallama dasu Hajiya domin a ranar zasu juya, domin a mota sukazo daga Kano zuwa Hadejia, ta Kano zasu hau jirgi zuwa Abuja, yana da gida a Kano da motoci shi yasa daga Abuja suka hau jirgin Kano suka sauka a gidansa dake Kanon, suka hau motarsa suka kamo hanyar Hadejia. Ita kanta Salma bata san cewa gida zasu zo ba, saida taga sunzo Kano sun d'au hanyar Hadejia, ta gane cewa gida zasu je.
A lokacin bata san sadda ta rungume Salman ba tsabar murna harda sakar masa kiss a kumatu, saida tayi abun ta rink'a jin wata kunya ta rufeta, shi kuwa sai sakin murmushi yake, yana kallonta, tun lokacin har yanzu ta kasa had'a ido dashi.
Taso ya barta ta kwana biyu cikin y'an uwanta, shi kuma baya jin zai iya barinta tayi nesa dashi yanzu, ya saba da ita, sosai, ya saba da girkinta, baya jin zai iya jure rashinta yanzu.
Salma badan taso ba, suka kama hanyar Kano, bata samu damar zuwa gidan Amarya Khadija ba, ko sallama batai dasu ba, dominta lura ko san ganinta basayi ma.
NO. 14 Sultan Road, Zaria, Kaduna State Nigeria*
Ba'a dad'e da sallamo su daga asibiti ba, har yanzu Nanah ta kasa sabawa da Khalisat, duk da kullum cikin jawota take a jiki, domin dai ta kawar mata da damuwar dake damunta.
Nanah ko, ko bacci take saita rink'a wasu mafarkai, duk abubuwan da suka faru da ita take Mafarkinsu, idan tana Mafarkin kuka kawai take a cikin baccin nata. Damuwa na son mata yawa, duk ta rame ta fige ta kasa sakin zuciyarta ta manta komai. Ya za'ai ta iya manta abubuwan da suka faru da ita?, ai ba abu bane wadda zatai saurin ciresa a ranta, ya za'ai ta iya mantawa da cutar da rayuwarta da y'an Bindiga sukai, har duniya ta nad'e bazata manta dasu ba kam.
Abinci Nanah take ci, amma chakalin da take cin abincin dashi ya fad'i k'asa, saboda ta d'ebo abincin zata kai bakinta kawai ta tuna Auta, a sadda yake kukan yinwa yake ji, a sadda suna hannun y'an Ta'adda.
Wasu zafafen hawaye ne suka fara bin fuskarta, sai had'eyar zuciya take, ji take kamar zata had'iye zuciya ta mutu, kota huta da wannan duniyar.
Har Khalisat ta zauna a kusa da ita bata sani ba.
Dafata Khalisat tayi tana cewa "Nanah, kiyi hakuri komai zai zama tarihi insha Allah, kema wata rana zakiyi dariya kuma kiyi murmushi".
Sauk'e lumfashi Nanah tayi ta ajiye abincin tana kallon Khalisat, hawaye na mata zuba har yanzu ta ce "bana jin zan sake yin farin ciki a rayuwarta, bana jin zan sake samun kamar y'an uwana dana rasa".
Rungumeta Khalisat tayi itama wasu y'an hawaye na cika mata ido ta ce "na sani tabbas da wuya, wani ya iya maye gurbin y'an uwanki da kika rasa, amma na miki al'k'awarin sama miki abokin rayuwar da zai cike miki gurbin abunda kike rasa a rayuwa, ki bani dama Nanah bazan tab'a cutar dake ba. Zan baki Yayana sunansa FARUK GALADIMA, Yayana bashi da matsala ko kad'an zaki ji dad'in zama dashi, yanzu haka bai k'asar shida Amma, amma sun kusa dawowa insha Allahu, ina fatan zaki amshi auran Yayana?".
Cike da tsananin mamaki Nanah ke duban Khalisat. Har takai matsayin da Khalisat zata ce ta auri d'an uwanta?, anya kodai bata ji sosai bane?, ai ita yanzu ta yanke tsammani da sake yin farin ciki, bare wani aure kuma, kai gaba d'aya duniyar ma ta sare da ita.
Saida Khalisat ta girgiza ta, kamin ta dawo hayyacinta.
Khalisat ta sake cewa "ki amince dan Allah, nasan bazaki tab'a yin nadamar auran Yayana ba, ni a nawa tunanin yanzu kinfi buk'atar abokin rayuwa, wadda zai baki kulawa sosai, kema zaki haihu ki hayyafa, ki sake gina wasu ahalin naki na kanki".
Kuka kawai Nanah ta saki ta sake rungume Khalisat cikin muryar kuka take cewa "ban ma san miye zance miki ba Khalisat, hak'ik'a ke mutum ce harda rabin mutum, kinfi k'arfin komai a waje na, na amince wallahi, koda kuwa shi ya kasance baya sona, zan iya zama dashi, har sadda zai fara son nawa, zan koyi sonsa nima".
Hawaye itama Khalisat keyi tana d'an bubbuga bayanta alamar tayi shuru haka nan.
Hatta mijin Khalisat d'in Nanah ta lura shima ba k'aramin mai kirki bane, bashi da matsala ko kad'an hannu biyu ya amsheta. D'aki d'aya aka ware mata a gidan Khalisat.
A d'an lokaci Khalisat tasa Nanah school ta gaba da secondary, ta kuma sata a Islamiya, ta fara zuwa lokaci guda. Duk da makatar bokon saida akai cuwa-cuwa aka mata takardun gama secondary school, kamin ta samu gurbin shiga Jami'a, kuma duk mijin Khalisat d'in ne, yayi k'ok'arin hakan.
Tunda Nanah ta fara zuwa school sai ta d'an fara rage damuwar dake addabar zuciyarta, cikin kwanciyar hankali take zuwa school da Islamiya. Duk sallar da zatai saita sa ahalinta a cikin addu'ar samun rahmar Ubangiji, duk irin halin da take ciki bata tab'a mantawa dasu ba, koda da rana d'aya ne, koda da sak'on d'aya ne kuwa.
*FARUK GALADIMA* POV
"Ka zauna Faruk magana zamuyi da kai, mai mahimmanci".
Faruk ya kalli Amma dake maganar, yaga fuskarta ba wasa, hakan yasa shima zama yana bata dukkan hankalinsa.
Amma ta k'ara cewa "Faruk kasan ban tab'a rok'on alfarma a wajanka ba ko?, ban tab'a cewa kamin kaza ka musa min ba hakane?".
Jikin Faruk yayi sanyi yana kallon Amma, kamin ya ce "Amma ai umarni kawai zaki bani nayi, bawai ki rok'i alfarma a waje na ba, ai kinfi k'arfin ki rok'eni alfarma Amma".
Amma ta gyara zama tana jin dad'in ubanda Faruk ya ce. Ta fara basa labarin Nanah gaba d'ayansa duk abunda Khalisat ta sanar da ita, shine ta gaya masa.
Faruk tunda ta fara basa labarin Nanah idonsa suka kad'a sukayi jawur tsabar tausayin Nanah da bai sani ba.
A hankali Faruk ya ce "Amma yanzu so kike na aureta na dawo mata da farin cikinta?".
"So nake ka aureta ne, domin ta cancaci hakan, domin ita ce matar dana dad'e ina maka addu'ar samu. Duk da nasan ba lallai ka iya dawo mata da farin cikinta ba duka".
Faruk yayi k'asa da kansa yana cewa "Amma na amince indai hakan, zai saki farin ciki, to na amince, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi".
"Allah yayi maka albarka Faruk, Allah yasa yadda kayi min biyayya yasa kaima Y'ay'anka suyi maka, kamar haka".
"Amin ya rabb Amma".
"Amma wani sauri ba gudu ba Faruk, ka tabbatar dai babu wacce kake so a cikin ranka, kar mu tauye maka hak'k'i?".
Murmushi Faruk ya saki yana cewa "ko kad'an Amma, babu wacce nake so har zuwa yanzu".
"To Masha Allah, tashi kaje Allah yayi maka albarka. Sana ka kira Khalisat d'in, idan ta sai ma Nanar waya ta baka numberta ka rink'a kiranta ku d'an fahimci juna, kamin mu koma Nigeria. Amma fa ina so a d'aura auran muna a nan, idan yaso muna komawa ka d'auki matarka kawai".
"Yadda kika ce Amma haka kawai za'ayi".
"To shikenan Allah dai yayi maka albarka Faruk".
Da amin yake ta amsawa, ba abunda yake sashi farin ciki kamar albarkar da Amma d'in ke sa masa. Harya fita murmushi ne d'auke akan fuskarsa. Baiji wani haushi ba dan Amma tayi masa mata wacce bai sani ba, albarka da take sa masa kad'ai ta ishesa farin ciki, kuma yasan Amma bazata tab'a zab'a masa abunda zai cutar dashi ba, dan haka baiji komai ba, illama tausayin yarinyar daya