Sauyin Yanayi Book Compelet Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   7 / 20

18K to 21K   out of 58.4K words

da iliminki na ganki ba, miye karatun bokon baiyi miki ba, hatta aikin hajji da kika je, ba ta dalilin karatun bane?".

Ganin maganar naso tayi tsayi yasa Hajiya tashi domin tasan ko kwana zatai tana gaya masa gaskiya tofa ba yarda zaiyi ba.

Tashi tayi tana cewa "Allah ya baka hakuri, amma gaskiya ka rink'a kamanta adalci a cikin y'ay'anka"

Tana idasa fad'ar haka ta fice daga d'akin.

Wani tsaki Mama taja tana cewa a zuciyarta "kinyi ki gama Hajiya, amma Salma ba ita ba auran wani wadda zata huta a rayuwa, sai nasa ta auri wadda zai ida nakasa mata rayuwa, wannan al'k'awari ne wadda na d'aukarma kaina"

Abba ne ya katse mata tunani, suka ci gaba da maganar Khadija da Jafar yadda komai zai kasance.

Washe da safe. Salma ce ta fito daga d'akinsu tana k'ok'arin shiga babban kitchen d'in gidan. Fitowarta ta hangi su Maryam da Mama dake zaune k'ofar nasu d'akin.

Fitowarta taji tsakin da sukai mata. Mama ce ta kunna redio, kawai taji suna karanto wani littafi waishe KADDARA CE, abunda ya k'ara hargitsa ma Mama da Maryam kwakwalwa shine yadda sukaji wacce ta rubuta book d'in.



Salma duk da taji abunda yasa su firgita sai tayi shigewarta kitchen d'in ta nuna kamar bata ji ba. Duk da tasan book d'inta ne, to amma cikin gidan nasu babu wadda yasan tana rubuta book's daga ita sai y'an d'akinsu. Ita kanta bata san gidan redio na karanta book nata ba, amma taji dad'in haka.

A rud'e Maryam ta ce "wai baku ji wane suna naji ana kira bane?"

Dariyar rainin wayo Khadija ta saki tana cewa "naji mana, zai wuce wata ce can sabuwar marubuciya akai, dan naji wani book ma abokiyar hira ta karanta na marubuciyar yadda kaddara taso, duk ita tayi shi".

Maryam ta ce "to amma ya akai sunan marubuciyar yake kama dana wancar Salman"

Mama ta tab'e baki ta ce "ke kuwa Maryam da abun dariya kike, idan banda abunki ina Salma ina iya rubuta wani littafi, yarinyar da bata san komai ba, sai jakanci kwakwalwata babu komai ciki sai dusa"

Dariya suka saki tare Maryam da Khadija har suna tab'awa. Dai-dai lokacin da Salma ta fito daga kitchen d'in.

Duk taji abunda suke cewa, sai kawai ta girgiza kanta tana murmushi ta shige d'aki.

Tana shigewa Mama tabi bayanta da harara tana cewa "yo yama za'ai hakan ta kasance, ai da nayi kukan bak'in ciki kuwa, ai insha Allah haka zaki k'are a gantale Salma keda uwarki"

Bayan kwana biyu Mama na zaune kan gadonta taji Maryam ta tab'a ta, ba shiri ta tashi zaune tana kallonta.

Ganin kamar gulma ta kawo mata yasa ta tashi da sauri tana cewa "ke lafiya na ganki haka?, kamar wacce aka biyo tayi sata"

Maryam tama kasa zama, ta had'e hannayenta waje d'aya, sai kuma ta kama baki cike da tsananin mamakin abunda kunnuwanta suka jiyo mata a k'ofar d'akinsu Salma, sakin bakin tayi ta dafe kanta. Mama ganin cewa kamar fa Maryam d'in a kid'ime take yasa ta jawota ta zaunar da ita a kusa da ita.

A hankali Mama ta waiga k'ofar d'aki wai ko wani abu ne ya biyo Maryam d'in, daya sa ta zama Haka.

Ganin babu alamar komai yasa Mama cewa "wai minene naga fuskarki ta cika da mamaki?"

Sauk'e wani goran lumfashi Maryam tayi kamin ta ce "yo ba dole Mama ki ganni a haka ba, ashe duk littatafan da muke ji a redio da You tub channel, wadda abokiyar hira take Karantawa, ashe duk na Salma ne, mu duk d'aukarmu ai suna ne kawai yazo d'aya ba ita ba ce, ashe kuwa Salmar gidanmu ce ba wata ba"

A zabure Mama ta mik'e tana cewa "keeee Maryam bana son maganar banza kinji"

"Na rantse miki Mama ita ce"

"Ke ta gidan Ubanwa kika sani to?"

"Mama ki natsu dan Allah kaji"

Jawota Maryam tayi ta zaunar da ita tana cewa "Mama nazo shiga ban d'aki ne, kawai kamar ance na matsa k'ofar d'akin su Salma, sai naji Hajiya na cewa. "Salma ya kamata fa ki aje typing d'in nan haka nan, ki d'an huta, idan kika gama littafin nan, ki d'an huta, kamin ki d'ora wani"

Sai kuma na sake jin Salma ta ce "Hajiya ai hutu ba yanzu ba, tunda ina da lokaci yanzu so nake sai nayi littafi kusan goma ko biyar tukunna zan huta. Dan har gasar Hikayata nake so na shiga shekarar nan"

A haukace Mama ta mik'e tana cewa "kutumar Ubancan, ai ko bazai tab'a yiwuba wallahi, dole na d'au mataki, dole ne gobe naje garin Hayin fari, wajan Mlm, dole ne sai Salma ta nemi wannan basirar rubutu littafin ta rasa, dani suke zancan wallahi".

Maryam ta sake kamo hannun Mama tana cewa "Mama kiyi a hankali dan Allah, kar wani yaji, nasan dama zaki d'au mataki ai, shi yasa zuciyata ta kasa yarda ba Salma bace tunda naji sunanta, na ce ni ko saina binciko, ashe-ashe b'oye mana ake dankar mu gane",

"Hmm dole zasu b'oye mana, amma yanzun ma ba makara nayi ba wallahi".

*Gurbi K'aramar Hukumar Jibia Katsina State Nigeria*

Tagumin da Nanah ta zafga ne, tun fitar Saminu take jin wata fad'uwar gaba, Allah ya sani tunda Baba ya rasu take jin irin haka, kuma har yanzu bata sake ta ba.

Inna dake mata magana tun d'azo, ganinfa kamar bama jinta take ba, yasa Inna mamakin miye Nanah take tunani har haka ne?. Ace duk uwar maganar nan da take bata ma jinta ashe?.

Saida Innar ta dafa kafad'arta, ta d'ago a d'an zabure tana kallon Inna.

Inna tana kallonta, ta nisa ta ce "Nanah lafiyarki kuwa?"

Ai kawai Nanah saita fashe mata da kuka. Tana jin wani abu ya tsaya mata a wuya.

Hankali a tashe Inna ta ce "Subhanallahi ke Nanah miye hakan kuma?",

"Inna tsoro nake ji wallahi. Inna ina tsoron mutuwa yanzu wallahi, bana son k'ara rasa kowa Inna"

Wani murmushin manya Inna ta saki tana cewa "haba ke kuwa Nanah ai mutuwa dole ce, ga duk mai rai. Ki kwantar da hankalinki insha Allahu sai Kinga y'ay'anki harma da jikoki, kinji bana son ganinki cikin wannan halin kinji?"

Goge hawayenta Inna tayi. Nanah ta sakar mata murmushin yak'i wadda bai kai zuci ba.

Cikin dare Nanah ta kasa runtsawa ko kad'an ga Auta dake kwance a jikinta, sai Inna dake gefensu. Tana baccinta hankalinta kwance.

Murd'awar da cikin Nanah yayi ne tasa ta sauk'e Auta daga jikinta, domin zuwa ban d'aki, haka nan taji wani zawo-zawo ya kamata.

Da sauri ta nufi ban d'aki.

Tayi mamaki ba abunda taci amma cikinta ya b'aci domin zawo tayi mai ruwa ma kuwa.

Bayan ta koma ta kwanta bata fi minti biyar da kwanciya ba, ta sake jin cikinta ya katsa.

Wani d'an tsaki taja tana dafe cikin nata. Fitowarta kenan zata d'auki buta, ba zato ba tsammani kawai taji K'arar halbe-halben Bindigogi kota ina suna tashi a tsakiyar garin nasu.

Cikin Nanah ne ya k'ara hautsinawa, ji tayi tana niyar sakin kashin a wando tsabar tashin hankali.

Zaro ido tayi hankalinta a mugun tashe tama k'asa koda motsawa a inda take. Sai da taji saukar maganar Inna itama hankalinta a tashe tana cewa "keee Nanah kinji abunda naji kuwa?, kodai kunne na ne kawai ke jiyo hayaniyar mutane da halbin Bindigogi?"

Nanah ji tayi kamar bacci take Inna ta farkar da ita. Bakinta na kyarma wajan cewa "mun shiga uku Innna, inama yau muka bar garin nan, na shiga ukuna, bana son mutuwa yanzu, bana son rasa kowa yanzu, wayyo Allah Inna ki taimaka mana, Inna ina zamu gudu?, Inna kina jifa gida-gida suke shiga".

Ai kawai Inna itama saita ji wasu zafafen hawaye na zubo mata. Auta dake gefen Inna ya rungumeta yayi shuru kamar wadda baida baki, shima kansa hankalinsa a tashe yake.

Banko k'ofar gidan da akai ce tasa Nanah da Inna zabura suna curewa waje d'aya. Ba abunda ke fita a bakinsu sai Addu'a, sosai Nanah ta rungume Inna da Auta.

Abunda ya shigo gidan nasu ne ya k'ara hargitse masu kwakwalwa.

Nanah kuwa zawon data ke rik'ewa ne ya samu damar kufce mata a wando. Zubewa kawai sukai a k'asa su duka. Ba abunda jikinsu yake sai rawa.

Ganin wasu Y'an Ta'adda sun kai su biyar fuskokinsu duk a rufe rik'e da wasu Bindigogi wadda tunda aka haifi Nanah bata tab'a ganinsu da idonta ba, kai hatta Inna ma, sai dai su kallesu a cikin Film.

Wata tsawa aka daka masu yasa su Inna runtse idonsu ba shiri suna fashewa da kuka.

"Keee ina mai gidan nan yake?"

Bakin Inna na rawa take cewa "mai gidan nan ya rasu da dad'ewa"

Zagaye gidan suka farayi suna bincika ganin babu wani namiji cikin gidan yasa wani Babba cikin y'an Ta'addar ya ce "kaiii Tajo, ka kashe min matar nan, yarinyar nan kuma ku taho min da ita, da wannan yaron"

Wata irin kururuwa Nanah ta saki tana ihu iya k'arfinta take cewa "na shiga ukuna, na lalace, dan Allah karku kashe min Innata, gara ni ku kashe ni, daku kashe ta, wayyo Allah dan Alla...... Maganar Nanah ta tsaya cakkk sak'on d'aya biyu...... Jin saukar k'arar Bindiga a kunnanta, kamin ta gama tantance waye aka halba, taga Inna ta zube a jikinta babu alamar sauran rai a tare da ita. Domin a saman kanta Tajo ya saita bindiga ya halbeta nan take.

Yadda kasan batun-batumi haka Nanah ta koma. Hatta da d'an yatsan hannunta baya motsi. Tana iya jiyo kukan Auta yana girgiza Gawar Inna dake yashe a k'asa.

Tana dai jin sadda wani ya sab'eta a bayansa, daga nan bata sake sanin mike faruwa ba.

Shima kansa Auta tasa k'eyar yaron sukai suna zaginsa suna turasa da bakin Bindiga.

Auta yana gani aka tasa su gaba aka bar gawar Inna. Auta yana ganin yadda y'an Ta'addar suka kaso mutane da yawa, dake cikin garin naso. Wasu suka d'ora su a Mashina, wasu a mota, wasu ma a k'asa, an d'aure su da igiya, kamar wasu dabbobi, yana gani akasa Nanah kan wani mashin, shima aka jefasa cikin wata bayan mota, suka fara tafiya cikin dokar daji mai duhun gaske, sunyi tafiya harta wuce hankali, tun yana iya gane ina suke har ya rasa ganewa, tun idonsa biyu suke tafiya har wani wahalallan bacci ya d'aukesa............

*SAUYIN YANAYI*

Share Fisbilillahi

*©ZAHRA ROYAL STAR 🌝*

*ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION*

*EPISODE* 9-10 END OF FREE PAGES

*MAMA* POV

"Mlm so nake a lalata mata basirar rubuta littafin data fara. Ina so asa mata rashin kwanciyar hankali tare da farkai masu ban tsoro, ta yadda bata da wata natsuwar rubutun bare harta k'irkiri wani labari"

Mlm dake kallonta da jajayen idonsa, ya saki wani murmushi yana cewa "wani hanzari ba gudu ba Hajara"

"Ina jinka Mlm"

"Akwai wata k'awarki Asiya hakane?"

"Kware kuwa Mlm Asiya k'awarta ce Unguwa d'aya ma muka taso da ita ai"

"Yawwa to zata kawo miki ziyara a yau d'in nan. Zata zo da wani fahimmin zance, duk yadda zakiyi kiyi domin aba Asiya aurar Salma. Indai kina son ganin bayan Salma, to ki tabbatar Abbansu Maryam ya amince da abunda Asiya tazo dashi"

"Mlm na kasa fahimtarka fa?"

Murmushin gefen baki ya sake saki kamin ya d'akko wata kwarya cike da ruwa ya nuna cikinta, yana cewa "ki kalla tsakiyar kwaryar nan"

Da sauri Mama ta kai dubanta a cikin kwaryar abunda ta gani ne ya bata mamaki.



Da d'an mamaki take kallon Mlm.

Mlm ya ce "miye kika gani ciki?"

"To Mlm mutum na gani, kwance bashi da lafiya, kamar mai shirin komawa maciji, jifa fatar jikinsa yacce take komawa tana sabulewa kamarta aljanin maciji, masu komawa mutane, irin wadda nake kallo a cikin fina-finan India"

"To kinga wannan mutunin shine za'a aurama Salma shi, zata zauna da mahaukaci har rayuwarta ta lalace, bata tsinana komai a duniya ba, tazo a wahale zata koma a wahale".

Wata shewa Mama ta saki harda su bud'a tsabar dad'i.

Ta k'ara duba cikin kwaryar tana cewa "ai Mlm dole ma Abbansu Maryam ya amince da wannan batu. Abu d'aya zaka min kasa shi ya amince kawai idan na masa zancan, karma yayi min gaddama".

Mlm ya d'akko wani k'ulli ya mik'a ma Mama yana cewa "kinga wannan?, ki tabbatar kin sa masa a abinci yaci, kamin ki kai masa maganar, na tabbatar zai amsa bai shirya ba. Sana ita kuma zamu sa mata rashin natsuwar zuciya bata da lokacin ma rubuta wani littafi"

"Idan kamin haka Mlm ka gama min komai ai"

Mama ta fad'a tana bud'e jakarta ta fiddo da wasu kud'i, tana dank'ama Mlm sai washe baki yake.

*Unguwar Dubantu Hadejia Jigawa State Nigeria*

"Hajiya yau ne fa na tura labarina na gasar Hikayata, kimin addu'a"

"D'iyar albarka Allah ya bada sa'a kinji"

"Amin Hajiyata"

Cewar Salma tana kallon Hajiya da murmushi kwance akan fuskarta.

Ahmad ne yayi sallama ya shigo hannunsa rik'e da wata leda.

Zama yayi kan d'aya daga cikin kujerun parlon yana kallon Salma dake mik'a masa gaisuwa, ya amsa yana cewa "Salma kina shan magungunan ki kuwa?"

Murmushi ta saki tana jin dad'in yadda Yayan nata yake bata kulawa sosai. Ta ce "eh man Y Ahmad Ina sha"

"To amma naga kwayar idonki ta canza kala tana son komawa d'orawa?"

"To nima ban sani ba, amma dai duk ina sha akan lokaci yadda ya dace"

"Abinci fa kina kiyaye cinsa?, kin san fa ba kowane abinci ne ya kamata ki rink'a ci ba?"

Hajiya ce tayi gyaran murya tana cewa "Ahmad kenan, kaima kasan ba komai take samu ta ci yadda ya dace ba, kai dai kawai Allah yasa mu dace ya bata lafiya kuma"

Shima ajiyar zuciya ya sauk'e yana mik'a ma Salma ledar hannunsa ya ce "anshi wannan ki samu kici, ki ajema Ismail sauran"

Da murmushi sallama ta amsa tana godiya.

Tashi yayi ya fice daga d'akin.

Bayan fitarsa Salma ta bud'a ledar tana kallon abunda Yayan nata ya sayo mata. Su kankana ne dasu Ayaba, da dai sauransu.

Sosai Hajiya tayi murna dan ya kamata Salmar ta rink'a shan abubuwa irinsu dama.

Sallamar da ake rafkawa a tsakar gidan ce, sawa Maryam fitowa daga d'akinsu.

Ganin k'awar Mama Asiya ce yasa ta cewa "Inna Asiya sannu da zuwa, ai ko yanzu Mamar ta dawo daga unguwa, Allah yasa zaki tadda ita, bari na kira miki ita, tana d'akin Abba"

"Yawwa y'ar albarka kira min ita, akwai magana yau ai",

Bata tsaya jiran jin sauran abunda Asiyar ke cewa ba tayi gaba ta shiga d'akin Abban.

Zaune ta iske Mama sai wani iyaye take ma Abba yana biye mata.

Ganin Maryam ta shigo d'akin yasa Mama dubanta tana jiran jin miya kawota?.

Maryam ta ce "dama Mama Inna Asiya ce tazo ",

"Kai ai ko nasan da zuwanta, bari jeki gani nan zuwa",

Maryam na fita Mama ta dawo da dubanta wajan Abba tana cewa "kaji abunda nake gaya maka ko?, dama na ce ma zata sake dawowa ne, domin tana so ayi abun da wuri"

Abba ya nisa ya ce "kin ce yaron bashi da lafiya zata je kula dashi ne, za'a d'aura auran domin gudun faruwar wani Abu?, to amma a can zatayi karatu ne ko kuwa?",

Kallon takaici Mama ke aikama Abba, yadda yake shirin mata musu, duk da ta basa abinci da abunda Malaminta ya bata, kuma ya ci, dan yana kanci ma.

Ta ce "eh man zasu sata mana, babu abunda zata nema ta rasa. Ai kaga gara ma taje can tayi mai dalili, kai ka huta da kashe kud'inka akanta. Kuma tazo karatun ta kasayi kayi asarar kud'i akanta, tunda kasan ai ba k'ok'ari gareta ba, asarar kud'i kawai zakai, gara can taje tayi karatun acan"

"Kuma fa hakane Hajara. Ai kawai na amince, ko gobe suka zo za'a iya d'aura auran babu wata damuwa"

Wani almurin murmushi ta saki. Tana cewa "yawwa Abbansu Maryam shi yasa fa nake k'ara sonka, akwai saurin fahimtar mutum. Bari naje wajan Asiyar na sanar da ita abunda ake ciki"

Tana gama maganar ta fice daga d'akin.

"Ahh ahh Asiya yada zama waje kuma?, ga d'aki"

Cewar Mama data fito daga d'akin Abba, ta iske Asiya zaune a waje.

Asiya ta ce "wallahi kawai zama nayi nida Maryam muna d'an tab'a fira, ina Khadija ne ni kam?, ban ganta ba"

Mama ta ce "wallahi Khadija sun fita ita da wadda zata aura sunje wata sayayya ne"

"Ahh kai Masha Allah, kice an samo mana siriki kenan?"

"Ai kuwa dai, na nunawa a sa'a kuwa"

"Ayyiririiii, kice mun kusa zuwa aikin hajji?".

Dariya Mama ta saki tana kamo hannun Asiya suka shige d'aki Mama na cewa "ai kuwa dai, gamu can a k'asa mai tsarki"

Zama Asiya tayi tana cire gyalanta ta k'ara natsuwa ta ce "kinga akwai fa magana a bakina sosai",

Dariya Mama ta saki tana cewa "tunkan kizo na riga da na gama da matsalar, domin nasan zancan daya kawo ki"

Cike da d'unbin mamaki Asiya ke duban Mama, ta kasa hakuri ta ce "kamarya ban fahimta ba?"

"Hmmm Asiya kenan, Malami na nasa yayi min duba, har ya sanar dani zuwanki, da abunda zaki zo min dashi, tunkan kizo, na riga da na sanar da Abbansu Maryam, akan wannan zancan, kuma na

7 / 20