Sauyin Yanayi Book Compelet Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   12 / 20

33K to 36K   out of 58.4K words

baki ta ce "eh na iya, tun ina k'arama nake girki".

Ta fad'a har yanzu bata kallesa koda sau d'aya ba, a hakanma bata kallonsa jikinta na rawa, inaga kuma tana kallonsa sun had'a ido.

Tab'e bakinsa yayi, yana d'aga kafad'arsa, ya haye sama abunsa baice mata komai ba. Bin bayansa tayi da kallo, tana mamakin rashin son maganarsa. Itama tab'e baki tayi, tana addu'ar Allah yasa ya sayo mata d'in.

Bata wani ji wani abuba, dan zuwa yanzu ta fara sabawa da rashin maganar tasa.



Idasa sauka k'asa tayi, ta zauna kawai a parlon taci abincin, bayan ta gama ta nufi kitchen ta kai sauran data rage a cikin firiza, domin dama itama ba wani cin abinci take da yawa ba.

Saida ta k'ara gyara kitchen d'in sosai, duk da safe data tashi ta gyara komai na gidan.

D'akinta ta koma, ta zauna tayi shuru harga Allah bata son rayuwa ita d'aya irin haka, duk sai taji ta takura, tafi so taga wani zaune kusa da ita, ko suna labari, hakan na mata dad'i, kai koma basu wata magana sosai, tafi so dai taga mutum a kusa da ita.

Lumfashi ta sauk'e ta jawo wayarta, kawai ta samu kanta da kiran Ahmad.

Ai ko yana d'auka ya fara mata tsiya yana cewa "Ohhh y'an Abuja, kwana biyu ba'ama nemanmu, an samu duniya".



Dariya kawai Salma ta saki, tana cewa "kai Y Ahmad, wallahi kana raina, ai ko jiya munyi waya da Hajiya nake tabbayar kana ina?".

"Allah sarki, toya kike?, ya Abuja kuma?, zaman kad'aici?".

Ya tab'o mata abunda ke mata k'aik'ayi ta turo baki cike da shagwab'ar data zame mata jiki, indai tana gaban Hajiya ko Ahmed d'in ta ce "uhum bari Y Ahmad zaman duk ba dad'i, bana ganinku duk bana jin dad'in rayuwar ma gaba d'aya".

Murmushi Ahmed ya d'an saki yana cewa "ke tafi daga can, ba wani nan. Muna fa waya da mijinki, kuma sosai nake ganin yana da kirki wallahi".

Ido waje Salma ta ce "kai Ya Ahmed da gaske kuna waya da Miskilin nan?".

Wata dariya Ahmed ya saki yana cewa "ke mijinki kike cema Miskili?, Allah ya shiryaki Salma".

"Yo Y Ahmad dan baka sansa bane, na rantse ban tab'a ganin Miskili irinsa ba".

"Ni kuwa kinga lafiya lau muke waya dashi, dan har Hajiya naba suke gaisawa dashi".

Salma ta rik'e baki, kamar yana gabanta ta ce "amma Y Ahmad ya akai ka samu number sa kuke waya dashi?".

"To sarkin tabbaya, shine yasa akai masa binciken ko wacece matarsa, had'e da son sanin y'an uwanta, kuma cikin sauk'i ya samu number na, dandanan muka saba dashi ma, domin indai ka fahimce shi, yana da sauk'in kai ga iya ma'amala da mutane, sai dai idan baka fahimce sa bane, zaka rink'a masa wani kallo can na daban, domin in gaya miki har aiki ya samar min a garin KADUNA, wani company nashi dake can Kaduna, ya bani Babban matsayi, ki masa godiya dan Allah. Ammafa ba wadda ya san shine ya samar min aiki, daga Hajiya sai ke da nake fad'amawa yanzu, ko Abba bai sani ba, domin idan yaji, saiya sanar da waccan matar Mama. Yayi bincike ne, sosai nake gaya miki, yasan komai yanzu, da abunda muke fuskanta a cikin gidanmu, shi yasa yafi tausaya mana, kullum Hajiya cikin gode masa take, tana addu'ar Allah shima ya saka masa da alkhairi".

Salma ta rasa bakin magana, dama haka yake ashe?, dama haka yake da zuciyar zinari?, tabbas shi yasa kenan Hajiya kullum idan zasuyi waya take cewa, tabi mijinta ta faranta masa, ta kawo mai farin ciki a rayuwarsa, ta zama ita ce mutum ta farko da zata sauya rayuwarsa. Tabbas zatayi iya bak'in k'ok'arinta domin basa farin ciki, zatayi iya iyawarta domin sauya rayuwarsa daga bak'in tabon dake bibiyar rayuwarsa, zata sauya komai, zata kawo mai farin ciki insha Allahu.

Nannauyar ajiyar zuciya Salma ta sauk'e tana cewa "Allah sarki, Y Ahmad zanyi k'ok'arin hakan, sai inda k'arfina ya k'are wajan basa kyakykyawar kulawa. Amma mi yasa Hajiya bata sanar dani duk wannan ba?".

"To kin san Hajiya da zurfin ciki, inaga shine kawai. Kuma kinga yau ranta duk babu dad'i saboda an kawo lefen Khadija ne, Mama tana yada mata habaici kala-kala, danma ina gidan, nina tausheta da bata hakuri, har masu kawo lefen suka tafi".

Murmushi kawai Salma ta saki tana k'ara tausayin Mahaifiyarta kamin ta ce "Allah sarki to Allah yasa alkhairi, karma ta damu kanta wallahi indai akan Mama ne, ai zatayi abunda yafi hakama".

Sun dad'e suna magana daka k'arshe Salma ta sauk'e wayar, bayan sunyi sallama.

Sosai taji dad'in waya da Y Ahmad, ko banza ta d'an rage kewar gida dashi........

P 16

*Off Ty D'anjuma, Asokoro District Abuja Nigeria*

Yinin ranar a d'aki ta yisa, bata k'ara fitowa ba. Taji dai motsin bud'e k'ofar parlo, alamar fitarsa taji.

Da dare, ma dai cike da tsoro ta kwana, kamar dai jiya, dan har Allah-Allah take safiya tayi, Allah ya zuba mata tsoron dare sosai ba kad'an ba.

Yauma da kansa ya buga mata k'ofa, ta tashi tayi sallah. kamar jiya ma haka ya dawo ya iske tana karatun al'qur'ani.

Allah ya sani ba k'aramin dad'i yake jiba idan tana karatun nan.

Gari ya d'an fara haske, Salma ta tashi ta sakko k'asa, kitchen ta nufa, tana addu'ar Allah yasa an sayo komai da take buk'ata.

Wani murmushi ta saki lokacin data bud'e firiza taganta shak'e da kayan anfani, babu kalar naman da ba'asa cikinta ba, d'ayarma shak'e take da lemoka kala-kala, bud'e suto d'in tayi, shima an cikasa da kayan masarufi kala-kala, harda ma irin wadda bata tab'a gani ba, harda na turawa.

Murmushi kawai ke fita daga fuskar Salma. Cike da nishad'i ta fara, fera doya. Sai da ta fara dafata kamin ta sauk'e ta d'akko wani k'aramin turmi tasa doyar a ciki, sai kuma ta d'akko kayan miya, tayi giretin d'insu, da kayan k'amshi, kamin ta d'akko magi, ta aje shi gefe, wata y'ar babbar roba, ta d'akko ta aje k'asa, inda ta aje turminta, ta d'an jawo kujera ta zauna, ta fara daka doyar dake cikin turmin, saida da take ta sosai kamar za'ai sakwara, kamin ta juyeta cikin robar nan, ta d'akko kayan miyanta data markada su, ta juyesu a cikin doyar data daka, magi ta d'akko tasa a ciki, sai kuma ta rufesa da murfi. Ta tashi ta bud'e firiza ta d'akko naman kaza tsokar Kazar kawai tayi anfani da ita, ta yankata k'anana, kamin ta yanka albasa tare da kayan k'amshi ta zuba a tuk'unya ta kunna gas, ta d'ora. Minti kad'an Kazar tayi, ta sauk'eta, sauran ruwan Kazar daya rage bai tsotsu ba, ta juyesa a cikin doyar nan, da yake ruwan Kazar d'an kad'an ne ya rage bai tsotsu ba. Kazar data dafama, ta juyeta cikin doyar, d'akko wata ledar hannu, ta zurata a hannunta yadda bata so tayi anfani da hannunta, ta fara motsa doyar nan data daka, da kayan had'inta, sai da suka game jikinsu gaba d'aya, kamin ta fara luliyata kamar kwallo, a haka tayita har ta gama luliyawa, kamin ta tashi ta d'akko wani bushashshan biredi wadda ya koma kamar gari, ta ajesa daga gefe bayan ta juyesa a wani faranti, sai kuma ta fasa kwai guda hud'u ta yanka albasa, tasa magi ta juyasa. Kasko ta d'akko tasa mai a ciki dai-dai yadda zai isheta ta soya, ta d'orasa saman gas. Sai da ya d'auki zafi, sosai ta matso da doyar data luliya, ta fara tsomata a cikin bushashshan biredin nan, kamin ta fiddo ta tsoma a cikin kwai, sai tasa sa a man dake kan gas, haka tayita yi harta kamalla soyawa. A cikin kula mai kyau tasa masa nasa, ita kuma tasa a cikin wani filet.

Wanke kayan data b'ata tayi nan take, kamin ta duba taga akwai zob'o, dandanan ta dafa zob'on, ta had'a komai tasa sa a firiza yayi sanyi.

Minti kad'an kuwa sob'on yayi sanyi ta fiddosa, ta d'auka ta fito parlo, ta jera su a darning table.

Komawa tayi kitchen d'in, ta k'ara gyarasa, kamin ta d'akko nata, tana niyar fita.

Ta fito parlon kenan, taji k'amshin turaren Salman d'in ya cika parlon. Da kyar ta iya d'aga kai ta kalli saitin da yake, yana parlon tsaye da alama bai dad'e da sakkowa ba. Ganin ita yake kallo yasa da sauri har tana shirin sakin abunda ke hannunta, tayi azamar rik'esa a hannunta k'arfi, da kyar ta iya saita kanta ta ce "ina kwana?".

"Lafiya, kin tashi lafiya?".

Da sauri Salma ta d'ago tana dubansa, ko dai bata ji da kyau bane?, yau wai ita Salman ke tabbayar yaya ta tashi?, anya ba jine batai ba sosai kuwa?.

Ganin kallon da yake mata yasa ta d'an daburcewa ba shiri ta amsa da cewa "lafiya Lau".

Bai k'ara magana ba, ganin yana niyar fita baici komai ba, yasa Salma tayi saurin cewa "gafa abincinka akan darning table, na aje maka".

Tsayawa yayi yana duban kan darning table d'in. Shi dama ta ajema abinci?, anya ma ta iya wani abinci kuwa?, amma bazai iya y'arfata ba, bari yaje yaci yaji, da dad'i idan babu baya jin zai iya ci gaba da cin abincinta. Tabbas ya dai ji k'amshi ya cika gidan, na girki, amma babu tabbas d'in zaiyi dad'i ai.

Ganin ya tsaya tunani yana kallon kan darning d'in, yasa Salma jikinta yin sanyi ta d'auka ko cewa zaiyi ya k'oshi.

Sai kuma taga ya taka ya nufi kan darning table d'in.

Da kanta Salma ta matsa wajan darning table d'in ta fara zuba masa abunda ta girka, duk yadda zuciyarta ke bugawa saboda kusancin da suka samu ita dashi, gashi motsi kad'an take jin idonsa akanta.

Tana gama zuba masa zata juya ta tafi, taji saukar maganarsa yana cewa "dawo ki zauna"

"Am... Amma ga nawa can abincin fa".

Bai kalleta ba ya sake cewa "ki d'akkosa a nan zamu ci tare, ba'a zuba min abinci a tashi ban gama ba, kin gane?".

Tab'e baki kawai Salma tayi tana jinjina k'arfin hali irin na wannan Salman d'in. Shi komai nasa daban yake da kowa wai?.

Take tabbayar kanta.

Ganin tunanin bazai kaita ga komai ba, yasa ta d'akko abincin nata, duk da tasan ba wani cinsa zatai yanzu ba, tunda dodon nata na zaune a kusa da ita.

Da kyar taja kujerar dake kusa da tasa ta zauna, amma akwai wata a tsakaninsu, duk da haka Salma bata da wata natsuwar cin abinci a gabansa, bata jin zata iya hakan.

Shi kuwa k'amshin abincin ne ya fara masa maraba, tun sadda Salma ta bud'e kular abincin, k'amshin ya cika masa hanci, dan har wani miyau ya had'iye ba shiri. A hankali ya fara cin abincin, wadda tsabar yadda abincin ya mai dad'i, bai san sadda ya cinye duka wadda Salma ta zuba masa ba.

Har yana neman k'ari.

Ganin kamar bai ishesa ba, yasa Salma ta d'an kalli saitin da yake zaune ta ce "akwai, a k'ara maka ne?".

Da kyar ya motsa bakinsa ya ce "Ohh akwai ne?".

Wani murmushi Salma ta saki tana tashi ta bud'e kular, ta idasa juye masa na ciki daya rage, tana yi tana maganar zuci "shifa wannan bawan Allahn d'an rainin hankali ne wallahi, yana fa jin sadda ta ce masa, akwai, yana son a k'ara masa ne?, amma ji wata tabbaya da ya k'ara mata".

Zama Salma tayi har yanzu bata jin ta cinye guda d'aya ma, saboda wasa kawai take da abincin dake hannunta, tunda ta kai abincin sau d'aya a bakinta bata k'ara ba.

Tana gani ya cinye tas again, yasha zob'an. Yana gamawa yayi mata sallama, harda wani cewa "Thanks, na gode da abinci".

Bata ce masa komai ba har ya fice daga parlon gaba d'aya, tana jin tashin motarsa har ya bar gidan baki d'aya.

Sauk'e lumfashi Salma tayi tana girgiza kanta, ta d'ansa tafin hannunta ta kaima goshinta wani d'an duka, tana cewa a fili "kai Salma mike damunki ne haka?, idan kina gaban mutunan nan ne?, mi yake shirin faruwa dake ne haka?".

Wani d'an k'aramin murmushi ta saki, sai yanzu ne ta samu natsuwar fara cin abincinta.....

*FARUK GALADIMA* POV

"Faruk ka zauna mana, ka natsu dan Allah"

"Amma, ya za'ai na samu natsuwa, ace tun sadda mukai waya da PA d'insa, ban k'ara samunsu a waya ba, ya kamata ace nasan halin da abokina yake ciki"

Dafasa Amma tayi tana mik'a masa ruwa, sha ya d'anyi yana sauk'e ajiyar zuciya.

Amma ta ce "inshallahu lafiya yake Faruk addu'a kawai zaka masa kaji?".



Zaiyi magana kenan yaji wayarsa dake hannunsa tana k'ara. A zabure ya mik'e ganin sunan mai kiran.

Wani haushi ya rufe masa zuciya, saima aje wayar yayi kawai, sai yanzu ne zai nemasa?, au wato dama yana lafiya kenan?, damuwa ne baiyi dashi ba?.

Amma dake dubansa ta saki murmushin manya ta ce "haba mana Faruk, ka d'auki kiran mana, tun d'azo fa dama jiran kiran nasa kake, ya yanzu kuma ka samu ya kira ka zaka wani maze haka ne".

D'an k'aramin tsaki Faruk ya saki yana shafa kansa ya ce "Amma dole nayi fushi, yasan irin tashin hankalin dana shiga ne a kansa?, saura fa kad'an na tafi Nigeriar da kaina".

"Yanzu dai please d'an albarka ka d'auki wayar nan".

Amma na gama fad'ar haka ta shige kitchen d'in dake parlon gidan, k'ofin data kawo masa ruwa rik'e a hannunta.

Bayan wucewar Amma Faruk ya samu ya d'auki kiran.

Yana ji Salman nata masa magana, yayi shuru dashi, shi kad'ai ke yima Salman haka ya zauna lafiya, ya sani kuma, shi kad'ai ne Salman ke iya doguwar magana dashi, ko su Daddy, ba wani sosai ya cika sakewa dasu kamar yadda suke da Faruk ba.

Salma dake cikin wayar ya ce "haba mana My friend, ya kamata kamin uzuri, ka tsaya ka saurare ni kaji abunda yasa, duk na kashe wayoyina"

Sauk'e lumfashi Faruk yayi yana cewa "amma ko zaka kashe wayoyinka bai kamata ka kashe wacce y'an uwanka ne kad'ai ke iya samunka ba, mi yasa kayi haka?, kasan irin tashin hankalin dana shiga kuwa?, nida Amma, har muna shirin baro Canada mu taho Nigeria, hatta da aikina dole na barsa na kwana biyu, saboda bana da natsuwar yin wata wak'a"

Murmushi Salman ya saki yana jin Faruk har cikin ransa, Faruk ya kasance kamar D'an uwa ne a garesa, kai yama fi wani d'an uwan nasa, Faruk ya wuce duk yadda kake tsammani a wajan Salman.

Ya ce "am so sorry My friend na tuba kaji?. Abunda yasa na kashe wayoyina shine, ina cikin ciwon nan, ban san inda kaina yake ba, kawai su Daddy da Momy suka je wai aka d'aura min aure, auran ma da k'aramar yarinya, wacce kamar an bani rainonta ne".

Dariya Faruk ya shek'e da ita, har yana kwanciya, tsabar dariya har wasu guntun hawaye na neman zubo masa.

"Kaifa d'an rainin wayo ne Faruk, miye abun dariya a nan kuma?".

"Sorry Abokina, ai ji nayi wai an maka aure, kamar wata mace, su Daddy sun maida kai mace wallahi, sau nawa suna ma hakan. Abu na biyu daya ban dariya shine, wai k'aramar yarinya kake cewa an baka, wai rainonta zakai. Kai yanzu fa babu abunda yaran nan basu sani ba, kallonka kawai suke, ba wani rainonta da zakai, nasan ma bata wuce shekara ashirin ko k'asa da haka, to wallahi irinsu babu abunda basu sani ba in gaya maka. Allah dai yasa daga wannan kayi dacen mace, bana son wannan aura-auran da ake maka, Allah yasa dai mai addini ce, wacce zata kawo k'arshen ciwon nan naka, wacce zata kawo maka SAUYIN YANAYIN da kake ciki".

Can k'asan zuciyarsa Salman ya amsa da amin. Kamin ya ce "hmm to ya zanyi, ai dole nayi masu biyayya, dole ko Khare suka ce na zauna dashi, zanyi domin ina so na gama lafiya dasu".

"Hakane abokina Allah dai yaja da rayuwarsu".



Sun dad'e suna magana kamin suyi sallama, inda Faruk yake shaida masa insha Allah ya kusa dawowa Nigeria, Canada sai dai ko su rink'a zuwa akai-akai.

Salman yaji dad'in hakan, duk da shi ba wani zama Nigeriar yake yi ba sosai.....

P 17

*NANAH* POV

Wani irin masifaffan sanyin Asuba ne yasa Nanah farkawa daga suman data yi jiya. Aka rasa kum d'an iskan dazai wasa mata ruwa ta tashi. K'udundune jikinta tayi, tana wata irin rawar sanyi, har hak'oranta na gamewa waje d'aya. Wasu irin hawaye ne taji suna niyar zubo mata, barinsu kawai tayi suka cigaba da shatata a fuskarta.

Kallon b'arin data ke tayi, ganin babu mutanan nan, daya mata sharri jiya, saima wani jini data gani a inda yake zaune. Karda kashesa sukai?. Ta samu kanta da jefa kanta tabbayar.

Girgiza kai kawai tayi, hawayen data ke suna k'ara gudu sosai, sosaifa rayuwar nan ke bata tsoro, yanzu shikenan sun rabasa da rayuwarsa, akan d'an wannan abunda yayi masu?.



12 / 20