Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
Bata da mai bata amsa bare ya lallasheta. Kukan wani yaro data ji ne a kusa dasu, yasa ta waigawa tana kallon yaron dake ta uban kukan yinwa yake ji. Bata jin tunda suka zo ita taci wani abu ma, tasan dai tana kallo aka rink'a mik'o masu wata bushashshiyar gurasa, guda d'ai d'aya, irin manyan nan, da ruwa fiyowota d'ai d'aya shima, kuma tana ga tun shekaran jiya da safe ne, ai dole bayin Allah suji yinwa.
Maganar da akai ce ta katse ma Nanah tunanin data lula.
"Kai wace uwar yaron nan?".
Da sauri wata mata wacce duk tsufa ma ya fara rufeta, bakinta na rawa, tsabar tsoro da fargaba da kyar ta iya amsawa tana cewa "nin....ni...mi.. ni ce".
Wani dogon tsaki d'an Ta'addar ya saki yana kallonta ya ce "ki lallashi yaron nan naki, idan ba haka ba kuma wallahi yanzu lahira zatai bak'i, dan keda shi zamu kashe, banga ma anfanin zamanku a nan ba, da alama babu uwar da za'a samu da ku".
Da mugun sauri matar ta rungume d'anta tana toshe masa baki. Da kyar wata mai k'arfin hali ta ce "bayin Allah ku tausaya ma k'ananun yara, wallahi yinwa suke ji, komu baku bamu abincin ba, su ku taimaka ku basu dan Alla..... Wani mugun mari da aka d'auke matar dashi yasa ta rufe bakinta ba shiri, tana sakin wani marayan kuka, tana kallon d'an Ta'addar nan daya tsinka mata mari, daga fad'ar gaskiya?.
Ba wadda yayi gigin sake magana, dan sunsan tsaf zasu iya raba mutum da rayuwarsa, yana d'an lallab'ata haka kawai a idasa mutum bai shirya tafiya lahira ba.
Duk abunda ake Nanah tana daga gefe, bata jin zata k'ara saka masu baki, ga duk abunda suka ga damar yi, domin harga Allah ta gaji ta gaji wallahi.
Tunaninta ne ya sake tsinkewa ganin wasu dondozon mutane da suka shigo dajin da suke, had'e da wasu makamai masu yawan gaske, mutanan sun linka yawan y'an Ta'addar da suke a wajan.
Da mugun sauri wani yaje ya sanar da Tajo abunda ke faruwa. Da gudu Tajo ya fito yana kallon mutanan da suka k'araso inda suke yanzu.
Murmushi Audu ya saki yana kallon Tajo kamin ya ce "barka dai uban Daba".
"Miye ya kawo ka daba ta Audu?".
Wata shegiyar dariya Audu ya saki, Tajo cike da fusata ya nunasa da yatsa yana sake cewa "kaiii Audu, tabbayarka neka kawai?, amma zaka tsaya min dariya?, kafi kowa sanin bana son raini a harkata".
Goga dake gefe ya wani zauna ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya, bai tashi daga inda yake ba, yana so yaga ya za'a k'are da Tajon, kowa dake wajan cikin mutanan Tajo sun tashi sun zagaye sa, suna jiran kota kwana, kamar yadda mutanan Audu suka zagaye sa, to amma fa mutanan da Audu ya kwaso Allah yayi yawa dasu, da alama a shiryensa yazo.
"Mi kake ci na baka na zuba Tajo?".
Ya k'are maganar yana kallon cikin idonsa.
Kamin ya sake cewa "abu d'aya nazo ka bani, ko na ce zan iya fansar sa ko nawa ne da kud'i, zan baka ko nawa ne, ka bani shi, a salin alin nayi tafiyata, ba sai mun kai da tashin hankali ba"
Tsayuwarsa Tajo ya gyara yana kallon Audu da mamaki. Shi zaizo yana ma barazana?, dan kawai ya d'ebo wannan uban mutanan?, shi Audu har ya kai ya kalli tsabar idonsa yake gaya masa magana har haka?, anya anya...
Bud'e baki yayi ya ce "ban gane ina maganarka ta dosa ba?".
"So kake na sake mai-maita maka ne?".
"Uhmm ai maganar ce kamar wacce ba mai cikakken hankali ya fad'a ba"
Wani cikin mutanan Audu cikin fushin abunda Tajo ya fad'a zai nufi inda Tajo yake, da sauri Audu ya d'aga masa hannu.
Tajo na kallon komai yayi wani shegen murmushi na gefen baki, yana cewa "da ka barsa ai, yanzu na aika yaro inda ba'a dawowa wallahi".
"Kaga Tajo, bari na fito ma fili, waccar yarinyar nake so ka bani ita, ko nawa ne zan iya sayanta a wajanka".
Da mugun tsananin mamaki Tajo ya waiga yana duban inda Audu ya nuna, yana kallon Nanah.
Nanah da bata san mike faruwa ba tana dai kallonsu ne, da idonta da suka sha kuka.
Tajo ya saki murmushi yana cewa "baka da arzik'i ko dukiyar da zaka iya siyan waccan yarinyar, domin bana jin zan iya bada ita ko duniya zata tashi yanzu kuwa".
Kauda kansa Audu yayi yana wani basarwa kamin ya maido dubansa wajan Tajo ya ce "ka bani ita kawai ta dad'in rai, Tajo, idan ba haka ba kum..... A tsawa ce Tajo ya ce "idan ba hakan ba kuma miye ka isa kayi?, bari kaji Audu, kasan duk d'anyan kanka na takaka na shanye, dan haka tun muna shaidar juna ka tattara wa'innan mutanan naka kubar min nahiyata".
"Kaiiiii Tajo ka tsaya ka saurare ni, idan ba haka ba kuma zata taro da yamutse ne yanzu nan wallahi".
Tajo tsabar b'acin rai bai san sadda ya idasa inda Audu yake ba, yaci kwalar rigarsa ido waje yake cewa "kaii ka isa ka kawo k'arshe na, kai ka isa kazo har inda nake ka ce zaka rink'a min barazana?".
Zai sake magana kawai bai san hawa ba bai san sauka ba, yaji an caka masa wuk'a a bayansa. Wani irin ihu ya saki, yana damk'e rigar Audu da k'arfi, sai kuma ya saketa yana waigowa bayansa. Zaro ido waje yayi ganin Goga ne ya caka masa wata sharb'eb'iyar wuk'a a bayan nasa.
Nunasa yake da hannunsa yama k'asa magana. Shi Goga zai cima amana har haka?, ai ko wallahi saiya kashesa, idan yaso suyi mutuwar gasko.
Mutanan Tajo ne suka harzuk'a zasu fara halbe-halben Bindigogi, kamin su ankara ma mutanan da Audu ya taho dasu sun bud'e masu wuta, ba abunda ke tashi a wajan sai k'arar Bindigogi.
Mutanan da suka sato kuwa kowanan su a mugun tsorace yake, wasu ma har sun fara kuka, sun duk'e a k'asa.
Gaba d'aya wajan ya hargitse da fad'a da halbe-halbe.
Tajo ne ya fiddo da wata wuk'a wacce yake sak'eta a wandonsa. Goga ya juya baya yana inda Nanah take sai faman janta yake yana son d'auketa daga wajan, ita ko sai faman turjewa take, tana wani uban kuka.
Bai ankara ba, yaji saukar yankan wuk'a a mak'oshinsa. Wata irin hautsinawa yayi sai gashi ya saki Nanah yana fad'uwa k'asa, rik'e da wuyansa, yana wani irin tari na magagin mutuwa, yana kallon Tajo da yayi masa aika-aikar.
Da sauri Tajo yaja Nanah yana ce mata "ki gudu kibi nan karki sake ki tsaya da gudun da kikeyi, har sai kin b'illa bakin titi".
Wasu irin hawaye ne suka soma zuboma Nanah, ko kallonsa bata sake yi ba, ta fara wani uban gudu kamar Allah ya aikota, saida tayi nisa da wajan, kamin su Audu su lura da abunda Tajo ya aikatama Goga.
Audu cikin mugun tsanar Tajo ya nufi inda yake, suka ware suka fara danbe duk da ciwon da Goga yaji ma Tajo, ga jini na zuba ta bayansa. Da ciwon da Goga yaji masa dashi Audu ya rink'a anfani yana damk'e wajan, da k'arfi tsabar mugunta, idan ya damk'e wajan, sai Tajo ya saki wata gigitacciyar k'ara. A haka har yaci galaba a kansa, ya fad'i k'asa yana faman juye-juye.
Wata shegiyar dariya Audu ya saki yana cewa "dama na gaya maka sai na kawo k'arshen Dabarka. Ka duba ka gani babu sauran mutananka da suka rage a raye".
Tajo da kyar yake iya bin wajan da kallo, ganin yadda suka maida masa Daba kamar mak'abarta, sun maida wajan duk gawawwaki ne birjit, mutanan da suka rige sune, wa'inda suka sato ne kawai suma wasu sun samu damar guduwa a fakaice.
Tajo na cikin tunani, ga azabar da jikinsa ke masa, kawai yaji Audu ya shak'e masa wuya yana cewa "kaiii Tajo ina yarinyar nan take?".
Duk da halin da Tajo yake ciki, hakan baisa ya kasa sakin dariya ba, dariya yake yana duban cikin idon Audu yana cewa "ai na gaya maka, cewa baka da abunda zaka iya bani na baka yarinyar, kuma bazaka tab'a samunta ba, hhhhhhhhh".
Tajo ya idasa maganar yana dariyar shak'iyanci.
Audu tsabar b'acin rai ya k'ara shak'e masa wuya da k'arfi, yana ji Tajo na shure-shuren mutuwa, bai sake sa ba, har saida yaga Tajo ya daina motsi.
Tsabar b'acin rai ya tattara duk wasu dukiya da Tajon ya tara, had'e da mutanan da suka rige wa'inda aka sato, ya tasa su gaba tare da mutanansa suka k'ara gaba, suka bar wajan, ko gawar Goga basu d'auka ba...
*Off Ty D'anjuma, Asokoro District Abuja Nigeria*
Wajan k'arfe biyu na rana, Salma na kitchen tana kiciniyar d'ora sanwa. Girkinta take hankalin kwance.
A d'an k'ank'anin lokaci ta gama. Dambun shinkafa tayi wadda yaji zogale, had'e da kayan had'i, komai tasa a ciki, sai yayi kamar dafaduka, sai kuma tayi wata y'ar miya wacce tasa nama a cikinta ta yayyanka sa, y'an k'ananu, sai ta had'a Kunun aya wadda yaji madarar iloka, had'e da kwakwa da dabino sosai a cikinsa.
Bayanta gama ta jera komai a darning table, tazo kitchen ta gyara komai data b'ata, a kitchen d'in ta zauna taci abunta, domin harga Allah a tana son dambu sosai, bazata iya wani jira saiya dawo ba.
Tana fitowa daga kitchen d'in ta k'ara gyara parlon, tasa turaran wuta, ya bad'e gaba d'aya gidan da k'amshi, sai ko ina yayi kyau a gidan.
D'akinta ta koma ta shiga wanka, bayan ta fito tasa wata atafa riga da zani, duk da ba wani iya daura zanin tayi ba, to amma tana son riga da zani, dan cikin kayanta suke ma, wadda ta taho dasu daga Hadejia. Zanin ya zauna mata sosai a jiki, hips d'in ya fito sosai, atafar tayi mata kyau sosai ba kad'an ba, wani gyale ta d'akko kalar wadda zaiyi shige da atafar ta d'aura d'ankwali tasa gyalen saman kanta kawai saita d'akko wayarta ta fito parlon ta zauna.
Hajiya ta kira suka fara waya, wani tayi dariya wani murmushi, cike take da farin ciki indai zatai waya da gida, taji lafiyar su.
Tana cikin wayar ne, Salman ya shigo bakinsa d'auke da sallama, amma can ciki yayita ba lallaine ma kajita ba, kaida ke cikin parlon.
Ganin yadda take waya tana murmushi, bata ma San ya shigo ba. Tsayawa kawai yayi yana kallonta, ba k'aramin kyau yaga kayan data sa sunyi mata ba, sosai ya shigala da kallonta.
Ita ko Salma, k'amshin mayan turaransa ne ya ankarar da ita, hakan yasa tayi saurin yin sallama da Hajiya ta kashe wayar.
Da sauri ta waigo, idonta ne ya fad'a cikin nasa, da azama tayi saurin janye nata.
Da sauri kuma ta mik'e tsaye tana wasa da yatsun hannunta.
Ohhh ya Salam. Salman ya fad'a a zuciyarsa, lokacin da Salma ta mik'e tsaye, ganin yadda surar jikinta ta fito sosai shap d'inta da hips d'inta sunyi mugun bayyana a cikin zanin data d'aura.
Shikam dama bata mik'e ba wallahi, kaji k'aramar yarinya na son sashi cikin jidali haka nan kawai.
Tunaninsa ya katse a sadda yaji saukar muryarta tana cewa "sannu da zuwa".
Batai zaton zai amsa ba taji ya ce "yawwa sannu da gida".
Yana fad'ar haka yayi saurin haurawa sama, tabi bayansa da kallo, tana sauk'e wani goran lumfashi.
Zama tayi dab'as akan kujera tana dafe k'irjinta, a fili take cewa "wai mi yasa nake jin haka ne?, a duk sadda zan gansa a kusa dani, mi yasa zuciyata ke bugawa harta wuce misali idan na had'a ido dashi ne?".
Bata da mai bata amsa, sai kawai ta jawo, wayarta wai ko zata koma dai-dai, sai dai wayarma data d'auka hannunta rawa yake, har yanzu yanayin jikinta bai dawo yadda yake ba.
Har saida ta shafe wasu y'an mintina, kamin taji ta d'an samu natsuwa.
Kwana biyu tana so ta dawo da rubutun book, saboda zaman kad'aicin da takeyi, gara ace ta rage da koda rubutun ne, to amma kwata-kwata idan ta d'auki waya da sunan rubutu, komai goge mata yake, koda ta fara saita manta miye ya kamata tasa a gaba, dole tasa ta d'auki hutun typing, ga mutane masoyinta kota ina sai jajanta suke.
Tana cikin wannan tunani ta sake jin k'amshin turarensa, ya k'ara cika parlon, alamar ya sakko yana parlon.
Da sauri ta d'ago tana kallon saitin da yake.
Ganinsa daf da kusa da ita, yasa tayi saurin tashi tsaye ba shiri.
Da sauri Salman ya dafe kansa yana cewa "koma ki zauna".
Komawar kuwa tayi, tana yin k'asa da kanta, jikinta d'au wani sanyi da wani yanayi na daban.
Can ta k'ara jin ya ce "mi kike tunani ne haka?, harna sakko na dad'e a wajan amma da alama baki sani ba".
mamaki ne ya cika Salma, dama ashe yana dogowar magana har haka?, dama ya damu da ita har haka?.
Ture mamakinsa tayi ta basa amsa da cewa "a'a babu komai".
D'aga k'afad'arsa yayi ya fara tafiya ya nufi kan darning yana cewa "akwai wani abu dai. Taso ki zuba min abinci. Sana idan Allah ya kaimu sati mai zuwa, zansa a kaiki wata school dake nan kusa damu, zaki ci gaba da karatunki ne a nan".
Salma saita zama kamar wata sokuwa, itafa da ya bar karatun nan, domin tasan bata iya komai ba, kanmi zai b'ata kud'insa akanta.
Jikinta duk a sanyaye ta zuba masa abincin, ya fara ci tana zaune a kusa dashi, sosai yake jin dad'in abincinta, dan yanzu baya iya cin abincin kowa idan ba nata ba, zai iya aje komai ya dawo gida domin cin girkinta kawai.
Yana lura da yanayin data shiga, daga yin maganar karatu.
Aje cin abincin yayi yana kallonta ya ce "ya naga yanayinki ya canza?. Baki son karatu ne?".
Kawai saita samu kanta da sakar masa kuka, kukan take tana cewa "a'a Ya Salman, bawai sone bana yi ba, ina son karatu sosai, ina da nacin karatu, to amma bana iya gane komai a cikin aji, koda exams tazo itama idan nayi karatu baya zama, zubewa yake, da kyar aka samu ma na gama secondary, shima saida Abba ya biya min aka zana min exams ta fita daga secondry d'in, hatta ita bani ce nayi ba. Na rasa mike damu na. D'azo ma tunanin da nake yi shine, na samu ina rubutun books ne, har mutane sun fara bina, kamar abun arzik'i na rubuta books sun kai biyar, har gasar Hikayata na shiga, amma dai ban sani ba ko zanci, to tsakanin jiya zuwa yau, na nemi wannan basirar rubutun na rasa, domin duk yadda zan d'akko labari, sai naji kwata-kwata ya b'ace min".
Ta samu kanta da bud'e masa cikinta, da bud'e masa abunda ke damunta.
Ba k'aramin tausayi taba Salman ba, gaba d'aya sai yaji abincin ya fice masa a rai. Da sauri ya tashi daga kan kujerar da yake, ya matsa inda take, ya zauna a kusa da ita.
Ya ciro wani kyalle fari ya mik'a mata, amsa tayi ta fara share hawayen dake mata zuba, wani k'amshi daya daki hancinta a jikin Kyallen daya bata, saida taja wani lumfashi, tsabar yadda k'amshin turarensa ke sata a wani yanayi na daban.
Samun kansa kawai yayi da jawota a jikinsa ya rungumeta, yana d'an bubbuga bayanta.
Gaba d'aya Salma notikan kanta ne suka kwance, ji tayi kamar tana shawagi a sararin samaniya, wai ita ce kwance a k'irjin Salman, anya ba mafarki take ba kuwa?, zata tashi taga ba haka bane, kwata-kwata ji take kamar ba'a duniya take ba, ga wani masifaffan k'amshin da jikinsa keyi, ya cika mata hanci, wani irin mugun yanayi ta tsinci kanta a ciki.
Kwata-kwata ta kasa koda motsi na kirki ne a jikinsa.
Shima kamar wadda aka tsikara yayi saurin janyeta daga jikinsa. Shima dai a wajansa wani irin yanayi da bai tab'a tsintar kansa a ciki ba yaji, a sadda ya rungumeta a jikinsa.
Basarwa yayi kamar bashi yayi ba. Sai can ya ce "am sorry, kayi hakuri komai zaizo ya wuce, kamar ba'a yi ba, kuma zansa ki school koda komai nawa zai k'are saboda ke, insha Allah komai zai wuce ne".
Wai kodai bata ji sosai bane?, wai yau ita ce wani ke cewa zai sadaukar da dukiyarsa saboda da ita?, anya kuwa?, taji maganar daya fad'a dai-dai kuwa?. To amma ga fuskarsa nan ta nuna hakan, da gaske yake, da gaske kuma yaji tausayinta. To danmi ita bazata basa kulawa ba?, insha Allah itama zata zama ita silar ciresa daga halin ciwon daya tsinci kansa a ciki.
Yana gama maganar ya mik'e yabar wajan, binsa kawai tayi da kallo..........
P 18
*Unguwar Dubantu Hadejia Jigawa State Nigeria*
"Mama kinga wannan?, shine nake so nasa a wajan dinner d'in nan"
Mama