Sauyin Yanayi Book Compelet Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   14 / 20

39K to 42K   out of 58.4K words

ta d'ago tana kallon wani rantsatstsan less mai bala'in kyau.

Wani kallo Mama ke bin Less d'in dashi tana cewa "kai Khadija ya kamata ki barmin shi nasa a wajan dinner d'in, aga uwar Amarya ta fita sosai ko?".

Zaro ido Khadija tayi, Maryam kuwa dariya ta saki tana cewa "kai Mama ai wannan, irin na amare ne fa".

"Yo muma manyan ai muna sa irinsu, wai mi kuka maida mune?".

Khadija ta ce "a'afa Mama, wajan dinner d'in nanfa, babu tsofaffi".

Rik'e baki Mama tayi tana cewa "ai wallahi babu d'an kan uban da zai hanani zuwa, dinner d'in nan, Allah dai ya kaimu jibin, ai ita ce kad'ai zani, a cikin duk abunda kuka shirya".

Murmushi Khadija ta saki tana sake cewa "Mama da dai kin hakura kawai, kinyi zamanki a gida, domin duk abunda akeyi a wajan bai kamata ace da manya a ciki ba, duk abun yara ne fa".



"Saifa kiyi al'qur'an sai naje, ko miye ayi a gabana, nima fa uwar zamani ce, kuyi shagalinku babu abunda zance, ai ranar murna ce".

Dariya suka saki kawai Maryam ta kalli Khadija ta ce "nikam Khadija baki kaima Sadiya goran bikinki bafa".

Dafe kai Khadija tayi tana cewa "kin san Allah na manta, komai ne ya fara had'e min fa, gashi gidan nan ya fara cika, kina gani tun ana saura sati d'aya muka fara party fa, shi yasa duk abubuwan suka shige min, amma yanzu kijawo min Halima tana d'akin su Salma taje jin gulma, sai muje tare mu kai mata, daga nan mu wuce wajan inda ake min gyaran jiki, tunda gobe da safe zamu je k'unshi".



"Uhum, kuma fa hakane wallahi, kinga mai k'unshin mafa nake ta kira, kar gobe muje tayi mana akuyanci".

"Yo tama isa, ai tasan damu, tasan kuma amarya ce zatai mawa da k'awayenta".

Cewar Khadija

Tashi Mama tayi tana cewa "kinga ni na fita cikin y'an uwana da abokan arzik'i, da suketa shigowa domin tayamu aiki. Ya kamata ace ma Khadija kin sami gida, inda zaku zauna keda k'awayenki".

Maryam ce tayi saurin cewa "a'a Mama bama son zama gidan kuwa gaskiya a nan dai yafi. Ga d'ayan d'akin can da ba'a shigarsa sosai, tunda akwai komai cikinsa, sai muje can da k'awayen namu mu zauna, koya kike gani Khadija?".

"Keni nama manta da d'akin can fa".

Cewar Mama.

Khadija ta ce "yawwa Mama kisa a gyara mana shi please".

"To shikenan sadda zaku dawo, an gyara zaku iske kayanku ma a can".

Tana gama maganar suka fice daga d'akin.

Suna fitowa waje anata hada-hada a gidan, daka kalli yanayin gidan zaka san cewa biki ne ake.

Mutane sai jan Khadija suke ana cewa "ahhh kaga Amarsu".

Da haka dai suna murmushi suka fice daga gidan.

"Ai wallahi K'awata da nayi fushi, ace ina cikin unguwar nan ba'a kawo min gora ba, har k'awayena sun fara min dariya, inata kod'a bikinki, zaki auri hamshakin mai kud'i, zamu sha shagali a bikinki".

Cewar Sadiya tanayi tana kallon goran da aka kawo mata, na gayyatar bikin.

Dariya Khadija ta saki tana cewa "please kiyi hakuri, kin san idan hidimar bikinki ta tashi, abubuwa had'e ma suke, amma ai gashi na tuna dake, tunda harna kawo miki".

Sadiya ta ce "da nayi sa'a ba aka tuna dani, tunda naji ance har anyi event biyu, cikin abubuwan da kuka shishshirya".

"Hakane anyi, amma ai yau zamuyi K'auyawa day, sai gobe idan Allah ya kaimu, kuma za'ayi dinner".

Cewar Maryam

Sadiya ta rik'e baki ta ce "kai K'awata kefa Allah ya gama dake ta nan wajan, kin wuce raini cikin k'awaye fa".

Sai kuma ta sake cewa "to amma duk anyi anko wadda za'asa a wajan dinner, amma banda ni, gaskiya banji dad'i ba ko kad'an wallahi, yanzu haka zanje dinner d'in nan banda anko?".

Khadija ta dafa Sadiya ta ce "sha kurumin ki, akwai ankon da zan baki kisa, kuma duk iri d'aya ne da wadda za'asa a wajan dinner d'in".

Wata bud'a Sadiya ta saki tana cewa "Wohohooo, kai Allah ya nuna mana ranar dai, akwai cin uwar sabada nake gaya miki".

Dariya suka saki a tare harda su shewa.

Tunda suka dawo daga kaima Sadiya goro, suketa shirye-shiryen tafiya wajan K'auyawa party, gaba d'aya y'an matan da suka halacci bikin Khadijar duk suna gidansu, kota ina hayani ce ke tashi, a d'akin da aka ware domin y'an matan, dukansu sun shirya sun d'au wankan K'auyawa party.

Maryam ce dake danna wayar Khadija, taga kira ya shigo wayar, da sauri ta tab'o Halima dake kusa da ita, sai shafa bak'in kwalli take a fuskarta tana yin irin kwalliyar K'auyawa.

Ta ce "please Halima mi k'ama Khadija wayarta".

Amsa tayi ta d'an mik'e ta mik'ama Amarya wayar, wacce taci uban gayu.

Halima ta dawo ta zauna tana cewa "d'azo kuka manta dani, kukayi tafiyarku gidan su Sadiya".

"Ohh sorry wallahi kuma fa, har cewa nayi dake zamuje, mun sha'afa ne kin..... Shigowar da Sadiya tayi d'akin ne yasa Maryam shuru, ganin yadda d'akin ya d'auki wata shewa had'e da bud'a.

Sadiya ta rungume Khadija tana cewa "kaii kinga kyan da kikai kuwa K'awata?".

Murmushi kawai Khadija ta saki, tana jin kanta a sama.

Maryam ce tajawo hannun Sadiya tana cewa "yanzu muke maganarki ma, ashe kina tafe. Amma ya banga kin shirya bane?".

Kallon jikinta Sadiya tayi tana cewa "hmm, kedai bari, banda zanin K'auyawan ne shine yasa fa".

D'an dafe kanta Maryam tayi tana cewa "kai wallahi na manta har Khadijar ma, kin san ita ta d'au nauyin, duk zanin da y'an mata zasu saka, ko wacce falle d'aya, iri d'aya ne dama, riga kuma sai kasa taka ko wacce iri ce".

"Yawwa d'akko min nawa, naje na shirya yanzu, kamin a fara tafiya".

Mik'ewa Maryam tayi ta d'akko wani zanin atafa, atafar tayi kyau kuwa, ta mik'ama Sadiya.

Baki a washe Sadiya ta ce "shi yasa nake son had'a harka da masu dashi wallahi, ai mu duk inda arzik'i yake to muna nan mak'ale, bama shiri da talauci wallahi".

Dariya kawai y'an d'akin ke yima Sadiya.

Khadija dake waya da Jafar yake shaida mata komai an gama kammala sa a inda za'ai K'auyawa partyn, su kad'ai ake Jira.

Kashe wayar tayi tana cema y'an matan d'akin kowa ya shirya yanzu za'a aiko da motoci domin d'aukar su zuwa party.

Ko wacce ka kalla cike take da zumud'in zuwa wajan party.

*JAFAR* POV

Sauk'e wayarsa yayi dai-dai ya gama waya da Khadija yaji muryar D'an Lami a bayansa yana cewa "kaga Jafar tsaya na ce".

Gaban Jafar saida ya fad'i ganin D'an Lami.

Tunda yaci bashinsa, na zaije ya had'a partyn da akai jiya na arabiyan party, kuma ya ce masa yau d'in zai kawo masa kud'insa.

Da sauri Jafar ya ce "haba D'an Lami sai ka ce wadda yayi maka sata"

"Yo kasan dai ba mutumci ne dani ba, indai akan kud'ina ne ko?, to dan haka maza-maza ka fiddo min da kud'ina, tun kamin naja maka salalan tsiya wallahi".

Zaro ido waje Jafar yayi, Allah ya taimakesa, yana da wasu sauran y'an kud'i a jikinsa, ya ciro su ya mik'a ma D'an Lami.

D'an Lami ya jujjuya kud'in yana cewa "kan bala'i, ban gane ba?, ina sauran cikon kud'in?".

"Kai dai D'an Lami dan Allah ka amshi wannan d'in kawai yanzu, insha Allah bayan auren nawa zan cika Maka".

Sa kud'in yayi a aljihu yana cewa "Kai dai ka fad'i hakan, idan ma baka cika al'k'awari ba, kasan waye ni wallahi. Yo idan banda k'arfin hali ma, ina kai ina k'aryar arzik'i kana talaka futuk da kai, ai wallahi masu baka aron kayan da kake nuna kai mai kud'i ne kana shegiyar k'arya dasu, sune manyan azzalumai, su kuma iyayen yarinya, kud'i ya rufe masa ido, ai maganin y'an iska aka ce Karan maguzawa".

"Kaga D'an Lami, babu ruwanka da rayuwata, tunda na baka kud'inka kawai ka tafi ka bani waje, karma wa'innan maganganun da kake fad'a wani yaji, komai ya kwab'e min".

"Ka bani kud'ina fa kace?, ko kuwa dai ka bani rabinsu?. Ni kaga tafiyata, babu ruwana dama ai. Ai ance rana d'aya ta b'arawo rana d'aya tak ta mai kaya".

Ya idasa maganar ya juya yayi tafiyarsa.

Wata ajiyar zuciya Jafar ya saki, tunda ya fara k'aryarsa, babu wadda ya kawo masa cikas sai D'an Lami.

Domin kuwa hatta kayan lefe arosu yayi, hatta akwatunan, bayan bikin duk zai tattara ya maida mai su.

Gidan da za'ai jere ma, ya samu an ara masa kawai dan ayi jeran a gidan, Allah ya taimakesa ya samu, domin gobe ake yin jere, sunka kirasa wai zasuje ayi jeren gobe.

Komai yana tafiyar mai yadda ya dace. Matarsa kuwa bata san mike faruwa ba, tunda dama ba unguwa d'aya suke da Khadijar ba, kamar ya sani yabar unguwarsu, tafi wata uwa unguwa wacce take nesa da unguwar da yake, yaje neman aure.

*NANAH* POV

A hankali take bud'e idanuwanta, wadda take jinsu sun mata wani nauyi, kamin kuma ta bud'e su duka. Bin inda take da kallo tayi, tana duban akan gadon asibiti da take kwance.

Cike da mamaki zata mik'e da sauri, sai kuma tayi saurin komawa ta kwanta, tana runtse idonta da k'arfi, jin yadda kanta ya sara mata, wani irin ciwon kaine taji lokaci d'aya ya saukar mata, hannunta data sa ta dafe kanta dashi, taji alamar kamar kanta d'aure yake da bandeji. Kallon hannunta tayi ganin duk yadda taji ciwoka a hannu nata harda k'afarta, duk ta gurje.

Maganar data ji a kusa da ita ce, yasa da sauri ta waiga inda take jiyo maganar.

Wata mata ce zaune a bakin gadon nata, ta d'an juya baya kad'an tana waya.

Da alama ma bata lura da Nanah ta farka ba.

Tana ji matar a cikin wayar tana cewa "bari Amma wallahi had'arin mota nayi, na bige wata yarinya, abun tausayi wallahi, da alama ma tana cikin tashin hankali dama, domin bata cikin hankalinta a sadda ta shigo min gaba, harna bigeta bata ankaraba, ni kuma motar ce ta kwace min lokacin, duk na rud'e ganin mutum ya fad'o min ban ankara ba".

Daga cikin wayar aka ce "subhanallahi, amma dai da sauk'i ko?, ya jikin yarinyar?, baki ji ciwo ba dai ko Khalisat?".

Murmushi Khalisat ta saki tana cewa "a'a Amma, ko kad'an ni banji wani abuba, ita ce dai yarinyar da ban san sunanta ba, ta d'anji ciwoka kad'an".

"Kingani ko Khalisat?, shi yasa fa nake cewa, ki rink'a bin motar nan taki a hankali, wai ina mijinki ne, da bazai amshe motar ba?".

Murmushi kawai Khalisat ta saki tana cewa "Amma wai ina Faruk ne?, yaushe wai zaku baro Canada ne haka nan?, munyi kewarku fa wallahi".

Murmushi Amma ta saki wadda Khalisat taji shi daga cikin wayar. Amma ta sani duk dan ta kauda maganar data d'akko mata ne, shine ta sauya maganar da wata. Duk duniya Khalisat ce kad'ai ta rage mata, d'iyace a wajan K'anwar Amma.

Jinye tunanin data lula Amma tayi, tana tuno K'anwata wacce tunda ta haifi Khalisat Allah yayi mata rasuwa, Amma ita ta rik'eta, harta aurar da ita, shi yasa Khalisat bata da uwa kamar Amma, ita ce kad'ai take ma kallon uwa a yanzu.

Amma ta sauk'e ajiyar zuciya tana cewa "Faruk yana nan, kin san Yayan naki, aiki kullum cikin sha masa kai yake, amma mun kusa dawowa Nigeria".

"Hakane Amma, ai yana ma k'ok'ari, kullum cikin hayaniyar jama'a yake, ba'a waya ba, ba'a fili ba, dama duk wadda duniya tasan sa kusan hakan na kasancewa dashi, Allah dai k'aresa daga shirrin mak'iya".

Da amin Amma ta amsa, sun d'an jima suna wayar, kamin Khalisat ta kashe wayar, tana juyowa b'arin da aka kwantar da Nanah.

Da sauri Khalisat ta mik'e tana cewa "kai Masha Allah, kin tashi?, ya jikinki?. Bari naje na kira Doctor, ya k'ara duba jikin naki".



Da sauri Nanah ta rik'e Khalisat ta ce "dan Allah baiwar Allah a ina nake nan?, miya same ni?".



Zama kawai Khalisat tayi ta k'ara damk'e hannun Nanah cike da tausayi ta ce "nan a Zaria kike, jahar Kaduna, kuma nan asibiti ne, dake cikin garin Zariar. Sana na bigeki da mota a sadda kika fito bakin titi, kamar baki cikin hankalinki, domin hawa titin kawai kike a haukace".

Kuka kawai Nanah ta saki, da sauri Khalisat ta k'ara rik'e hannunta tana cewa "mi yasa kike kuka haka?, kiyi shuru dan Allah, kinga jikinki bai wani samu sauk'i ba. Ya kamata ma ki ban number y'an uwanki a kirasu, dan nasan suna can hankali a tashe, domin kin kwana biyu a sume baki farka ba".

Ai wani kukan Nanah ta k'ara saki, tana tuna cewa fa, itafa yanzu bata da kowa, bata da wadda zata nuna a matsayin D'an uwanta, ta zama ita d'aya shikenan ita rayuwarta a haka zata k'are?, anya ma zata ji dad'in rayuwa a haka kuwa?, mi yasa bata mutu ba itama?.

Girgiza kai Nanah take cikin muryar kuka ta ce "ni bani da kowa, mi yasa da kika bigeni baki tafi kin barni a wajan ba?, mi yasa baki barni nima na mutu ba?".

"Subhanallahi, kefa y'ar Adam ce, mai daraja, kuma wacce tayi imani da kaddara, bai kamata kina fad'ar irin haka ba".

Wani murmushin daya fi kuka ciwo Nanah ta saki tana cewa "kayya dan baki san abubuwan dana fuskanta ba a rayuwa, bana jin ko kice hakan ta kasance dake ba zaki zab'i mutuwarki akan rayuwar nan ba".

Tunkan Khalisat taji abunda ya sami Nanah itama ta fara hawaye, tana yi tana sharewa, ta ce "ina son jin labarinki y'ar uwa, kuma zan taimaka miki insha Allah".

Nanah bata da zab'i sai na ba wannan matar dake gabanta Labarinta, gara ta sanar da ita, kota samu nutsuwar zuciya, kota samu ta rage nauyin da zuciyarta tayi mata.

Tun daga farkon rayuwar da suka fara ta farin ciki, da ahalinta, har izuwa sadda aka kashe Baba, har zuwa sadda y'an Ta'adda suka shigo garinsu suka shigo gidansu suka kashe Inna, a gaban idonsu, har zuwa sadda Auta ya mutu cikin jikinta, har zuwa lokacin da data gudu daga hannun y'an Ta'adda.

Sadda tazo k'arshen labarin kuka kawai suke daga ita har Khalisat, kuka suke sosai. Ba k'aramin tausayi labarinta yaba Khalisat ba, tsabar kuka har wani shid'ewa take, da kyar ta samu bakinta ya furta.

"Banma san miye zance miki ba Nanah, hak'ik'a kinga rayuwa, Ubangiji ya baki ikon cinye jarabawar nan, hak'ik'a zan taimaka miki, zansa kema kiyi dariya wata rana, wannan al'k'awari na d'aukar miki".

Girgiza kanta kawai Nanah tayi wasu zazzafan hawaye na gangaro mata ta gefen fuskarta. Magana take a zuci "kayya bana jin zan k'ara wani farin ciki a gidan duniya, bayan babu Inna babu Baba, babu Auta".

Tashi kawai Khalisat tayi ta fice waje.

Tana fita ta sake kiran Amma.

Amma na d'aukar wayar Khalisat ta sakar mata kuka.

A rud'e Amma ke jefa mata tabbayar mike faruwa ne?.

Da kyar Khalisat ta iya tsayar da kukan nata, ta fara ba Amma labarin Nanah.

Ita kanta Amma a sadda akazo k'arshen labarin, saida ta goge wasu hawaye, tana cewa "tsakani da Allah, wasu bayin Allahn suna ganin jaraba a rayuwar nan, hak'ik'a na mugun tausaya mata. To yanzu ke a wajanki zaki rik'eta ko Yaya?".

"Amma zan rik'eta zan sata a makaranta, domin itama ta zama wani abu. Da san samuna ne ma, Faruk ya auri wannan yarinyar, tunda ta gama bani labarinta na yanke wannan hukuncin Amma, domin itama tana buk'atar wani a kusa da ita, wadda zai tarairayeta ya share mata hawaye. Tunda naga shi Faruk bashi da wacce yake so a yanzu, duk wa'inda suke sonsa, Amma kin san ba dan Allah suke sonsa ba, illa dan d'aukakar da Allah yayi masa ne kawai".

Wata ajiyar zuciya Amma ta sauk'e tana cewa "hak'ik'a Khalisat zuciyar zinari ce dake, domin ban tab'a kawo irin wannan tunanin ba, hak'ik'a ba wacce ta dace da Faruk sai irin wannan yarinyar, wacce ba duniya ce gabanta ba. Kuma na amince d'ari bisa d'ari, ina so ayi auran bayan anyi zan sanar dashi, komai kuma insha Allahu sai amince, domin bai tab'a min masu ba".

Sosai Khalisat taji dad'in yadda Amma ta fahimceta, a d'an lokaci k'ank'ani. Khalisat tama kasa b'oye farin cikinta a fili.

Bayan ta kashe wayar, taje Office d'in Doctor, domin zuwa ya k'ara duba jikin Nanah........



P 19-20

*Off Ty D'anjuma, Asokoro District Abuja Nigeria*

Cikin dare Salma ta kasa bacci, sai juyi take bisa gado, tana tuno jiya yadda suka k'ark'e da Salman, yadda take ganin tausayinta a cikin idonsa, murmushi kawai take saki.

K'arar fashewar wani abu data jine yasa ta zabura ba shiri. Tashi tayi tana maganar

14 / 20