Author : Zahra Royal Star Category : Read Hausa Novels
yafe min ba keda Salma Allah bazai tab'a bari na haka ba".
Rungumeta Hajiya tayi tana cewa "ko kad'an ni dama ban rik'eki a raina ba, tunda har kin gane gaskiya da wuri na miki barka, Allah ya yafe mana gaba d'aya, Salma kuwa zan fad'a mata ta yafe miki itama, bata da matsala na tabbata zata yafe miki".
Godiya kawai Mama keyi tana share hawaye, harda Maryam dake kusa itama kukan take, da kyar ta iya kama Mama suka shiga d'aki.
Da kanta Mama ta kira Khadija a waya, tana d'auka ta fara jiyo yadda Khadijar ke kuka kamar wacce ake zare ma rai.
Mama ta had'e wani abu mai d'aci a mak'oshinta da kyar ta iya cewa "Khadija kiyi hakuri, hak'ik'a duk abunda ya sameki dasa hannuna a ciki, Abbanku ya ce idan yaga k'afarki kin tak'o kin dawo gidan nan, to bai yafe miki ba".
"Na shiga uku Mama, wai kinga irin gidan daya kawo ni kuwa, Mama hatta lefen daya sa ayi min yanzu yazo aka kwashe su dama ashe na aro ne, hatta kayan d'akina da kuka min ashe saida su yayi, ya sai min wa'inda ba su kaisu ba, ya biya bashi da sauran kud'in, wai har Mari na yayi saboda ina gaya masa maganar cewa ya cuceni, gashi yanzu ya kulleni cikin d'aki saboda yaga zan iya fita na tafi gidanmu, wallahi Mama na tsani Jafar bazan iya zama dashi ba".
"A haka zakiyi hakuri Khadija dan nima nan Abbanku ya ce na sake naje inda kike a bakin aure na, ke gaba d'aya ma y'an gidan nan ya ce idan suka k'ara zuwa gidanki bai yafe ma mutum ba. Ni dai yanzu nayi nadama na rok'i Hajiya da Salma yafiya, k'ila alhakinsu ne ke bibiyar rayuwata da ku kanku wallahi. Abinda nake so dake kayi hakuri Khadija shi arzik'i na Allah ne idan Allah yasa Jafar zaiyi Arzik'i to kamin yabar duniya zaiyi".
"Yanzu Mama haka zan zauna dashi cikin k'uncin rayuwa?, nama fa tsane shi yanzu bana son koda ganinsa ne fa".
Runtse idonta Mama tayi tana sake cewa "Toya kike so nayi ne Khadija?, na ce kayi hakuri ki rungume k'addararki, dama ai bawa harya mutu Allah zai ci gaba da jarabarshi da k'addararori na rayuwa, ki d'aure kawai ki cije wata rana sai kiga komai ya wuce. Baki ga y'ar uwarki ba Salma ita mi yasa sadda Abbanku yayi mata aure da wadda bata sani ba, ta amsheshi hannun biyu-biyu, yanzu ba gashi tana cin ribar biyayyar data yi masa ba, kema kiyi biyayya dan Allah Khadija ko mun samu muma muci harabawar nan da Allah ya d'ora mana ni dake".
Kuka kawai Khadija keyi sosai tana cewa "shikenan Mama zan zauna saboda ke da Abba, Allah ya bani hakurin jurewa".
Tana gama fad'ar haka ta yanke kiran.
Kuka Mama ta saki kawai itama, Maryam ma kukan take sosai tana jikin Mama ba mai iya lallashin wani a cikinsu, ko wanne zuciyarsa cike take da tausayin Khadija.
Da y'ar y'an biki y'an uwan Mama suka tausheta suka k'ara bata hakuri, kwana d'aya y'an biki kowa ya tattara ya koma inda ya fito. Sai y'an unguwar dake shigowa jaje wasu ko tsabar gulma ce ke k'ara shigo dasu, suna son jin a ina aka kwana, shin an sak'o Khadijar ne, wasu abunda suke sonji kenan.
Ga k'ananun maganganu dake tashi a unguwar kota ina, a majalissa da gidajan mutane, sai kaga idan mutum zai wuce ta wajan gidansu Khadijar da wani wadda bai san miya faru ba, sai kaga ana nuna masa gidan ko zund'e da baki ana cewa "kaga wancan gidan, son kud'i ne ya kaisu ga halaka, sunje sun aurawa d'iyarsu fakiri wadda baida komai, saboda tsabar son kud'insu. Yo baka san maya faru ba ashe?".
Irin wa'innan maganganun kawai kake ji a cikin unguwar, shi yasa Abba idan ba dole ba baya ma son fita, so duka mutanan gidan ma haka ne, dan saida Abba ya kai zuciya nesa shi yasa bai saki Mama bama, amma saura kad'an ya saketa domin duk abunda ya same su dasa hannunta a ciki.
Y Ahmed kuwa shima a washe gari ya tattara ya koma Kaduna wajan aikinsa, domin abun shima ya tab'asa, duk inda zai zauna sai anyi gulmar gidansu, shi kuma hakan baya masa dad'i, k'addara ce fa tana kan kowa kuma.............
P 25-26
*Off Ty D'anjuma Asokoro District Abuja Nigeria*
Zaune take a parlo, yau kusan kwana biyu bata samu taje school ba, saboda rashin lafiyar data yi.
Shima Salman d'in da kyar ta lallab'asa ya fita wajan aiki, domin PA d'insa sai zarya yake masa kwana biyu, ana buk'atarsa a company.
Tashi tayi ta d'akko wayarta, tana tunanin fara rubutu, saboda yanzu taji komai ya dawo mata na fikirar rubutun book d'inta, dan har ta fara sabon book nata K'ADDARA CE. Sosai kuma taga jama'a sunyi miss nata, sun fara son book d'in kamar mi.
Tayi nisa cikin rubutunta kawai taji K'arar danna k'ofar parlon nata.
D'an k'aramin tsaki ta saki, domin harga Allah bata son tana rubutu a tayar da ita, shi yasa saida ta tabbatar ta gama komai na aikin gida, ta sallami mijinta ta zauna rubutun ma.
K'ofar taje tana bud'ewa, idonta yayi mata tozali da Momy.
Momy dake kallon Salma sama da k'asa, yasa zuciyar Momy wata bugawa ba shiri.
"Kardai abunda tayi mafarkinsa ne ke shirin faruwa da ita?. Kai ina bazata tab'a bari hakan ta kasance da ita ba, ina hakan ma bazai yiwuba ba wallahi".
Momy ke fad'a a ranta.
Da murmushi d'auke a fuskar Salma take gaisar da Momy, dake aika mata da wani kallo.
Shigowa cikin gidan Momy tayi, tana bin ko ina da kallo.
Salma ta ce "Momy ki zauna, bari na kawo miki abunsha".
"Kinga ni ba zama ne ya kawo ni ba. Nazo ne inji cewa ciwon yaron na k'ara tashi kuwa?, domin kwana biyu bamu ganku a gida ba, Daddynsa kuma yayi tafiya zuwa Dubai, hankalina ya kasa kwanciya ne".
Wani kallon rashin yarda Salma ke bin Momy dashi.
Saita samu kanta da b'oye mata ainafin gaskiyar abun ta ce "eh ciwonsa ya tashi har sau uku ma, muna zuwa asibiti domin har ciwoka yasha ji min, duk sadda ciwon zai tashi".
Ta wutsiyar ido taga yadda Momy ke murmushin gefen baki.
Kamin Momy ta samu nutsuwar zama akan kujera, amma can baya ta kasa zama, duk d'aukarta ko tsawon lokacin nan ciwon nasa bai tashi ba.
Sai dai abunda bata sani ba shine, tun lokacin daya tashi ta karanta masa karatun al'qur'ani mai girma, tun lokacin ciwon bai sake tashi ba, domin kuwa kullum sai Salma tayi masa addu'a a cikin ruwan shansa da abincin cinsa, shi yasa komai yazo ya k'are, kuma abunda ita Salmar bata sani ba shine, makarin asirin Momy indai ya kusanci wata mace to daga nan komai data masa na aikin asiri zai bar gangar jikinsa, to tunda ya kusanci matarsa komai ya riga daya k'are.
A daran ranar Momy tayi wani mafarki mai ban tsoro, wai wasu irin halittu sun biyota suna sun cinyeta. Sana ciwon data d'orama Salman na hauka ya dawo kanta, ita nata ma hauka take sosai, bata ma samu ta dawo hayyacinta wani lokacin, kullum cikin hauka take, ga rabin jikinta dake son komawa na maciji, saita rink'a rikid'a tana zama maciji, mutane da yawa na gudunta.
Shine fa ta tashi hankali a tashe ta nufo gidan Salman taga mike faruwa.
Momy ta saki murmushin yak'e tana cewa "amma dai da fatan babu abunda yake miki ko?".
"Eh Momy domin ma ba waje d'aya muke kwana dashi ba, har yanzu ma ba wata magana ta arzik'i dake shiga tsakanina dashi, muna zauna ne kawai".
Murmushi taga Momy ta sake saki ta ce "ayya ai komai zai zo ya wuce zaku dai-daita ne, karki wani damu".
Shiga kitchen kawai Salma tayi tana tafiya tana maganar zuci.
"Anya matar nan ba ita ce shilar shigar Salman halin da duk yake ciki ba kuwa?, tabbas akwai alamar tabbaya akanta gaskiya".
Momy ma tana ganin shigarta a fili take cewa "yo ai bana fatar ya kusance ki wallahi, domin keda shi har abada keda shi sai dai kallo wallahi, ina ai dama na ce bazan tab'a bari aikina ya kare dan yanzu ba, sai naga bayanka Salman da izinin Allah".
Jin motsin Salma zata fito yasa Momy mik'ewa tana cewa "wucewa zanyi fa, da baki d'akko komai ba, a k'oshe nake, dama akan hanya nake".
Murmushi kawai Salma ta saki ta rakata har k'ofa.
Zamanta da y'an minutes taji k'arar wayarta, da sauri ta kai inda ta aje wayar tata ta d'auka, tana kallon sunan mai kiran, ganin My hayat yasa ta d'auka, da sauri kuma cike da zumud'in son jin muryarsa.
"Kina ina ne haka, nayita kira ba'a d'auka?.
"Ohh sorry Hayat, wallahi bana kusa ne ina kitchen"
"Mi ake dafa mana ne yau".
"Abunda kafi so"
"Wow da gaske Hayatee?".
Zata bashi amsa ta sake jin ana buga k'ofar parlon.
Bata kashe wayar ba tana manne a kunnanta ta nufi k'ofar.
Jasmin dake jikin k'ofar, ganin wata mace ta bud'e k'ofar, sab'anin Salman data yi zaton shine zai bud'e k'ofar.
Ido a waje take kallon Salma, dake mata kallon rashin sani.
Salma na kallonta ta ce "baiwar Allah wani kike nema ne?".
Jasmin a wulakance ta ce "Mai gidan nake nema, da alama ke y'ar aiki ce ba?".
Wani abu mai kama da kishi Salma taji ya tokare mata mak'oshi bata san sadda ta ce "y'ar aiki kuma?, ai sai dai matar gidan".
"Ban gane sai dai matar gidan ba?. Ke karki nemi ki min rashin kunya, yanzu saina tattaka ki a nan wajan, naga uban waye Ubanki a Nigeria. Ke kin san Salman yafi k'arfin irinku, kin kalli kanki kuwa, ai da masu aikin ki kai min maka shi yasa na ce haka".
Rai a b'ace Salma ta ce "a haka da kike ganin ban isa ba, to kuma a hakan na kasance mata a garesa, kuma abar sonsa, ke ya akai duk isar taki bai aureki ba?, ko kuwa isar taki ta banza ce?".
Zaro ido waje Jasmin tayi tana sa hannu zata d'auke Salma da mari. Da mugun sauri Salma ta rik'e tsintsiyar hannunta tana cewa "kinyi kad'an wallahi, kizo har gidana kice zaki dake ni, kuma bari na gaya miki ko mutuwa zakiyi mijina bazai tab'a auran irinki ba, ballagaza dake, dubi kayan dake jikinki, a haka kike kiran kanki a musulma?, ko kunya bakyaji ki kwaso wannan tsunmokaran k'afafun naki kizo gidan namiji?. Ki kalleni da kyau ki gani, babu abunda na rasa, ke kin san idan Salman yana da ni a cikin gidansa, babu wata mace da zai k'ara kalla a matsayin so wallahi, ki dube ni da kyau Hajiya".
Cike da mugun mamaki Jasmin ke kallon Salma, yadda take juya mata jikinta sosai ta kalleta da kyau.
Ta kuwa kalletan, batai k'arya ba, tunda ta ganta ganin farko saida gabanta ya fad'i, domin Salma macece harma ta wuce, babu namijin da zai samu Salma ya k'ara marmarin wata mace kuma.
Ganin ta kasa magana yasa Salma k'ara cewa "tun kan dare yayi miki ki kama hanya ki bar min gidana, kuma ina gargad'inki daga yau karki sake ki k'ara shiga harkar mijina"
Salma na idasa fad'ar haka, ta hankad'a Jasmin ta rufe k'ofar parlon, tana wani huci na b'acin rai, domin harga Allah ta b'ata mata rai ko wacece ma wannan?. Miye alak'arta da mijinta ne?, mi yasa ta biyosa har gidansa?.
Ganin ba mai bata amsa sai shi da kansa, hakan yasa ta koma ta zauna zuciyarta na mata zugi. Magana take ji a cikin wayarta, da sauri ta kai dubanta akan wayar, zaro ido waje tayi, ashe bata kashe kiran ba?, shima kuma bai kashe ba, kenan duk yaji abunda ya faru?. Kashe wayar tayi kawai tayi wurgi da ita akan kujera.
A wajan Jasmin ko tunda Salma ta bugo mata k'ofa, take tsaye a wajan, tama kasa barin wajan. Wata irin shegiyar kunya ce ta rufeta, mi yasa ma tazo wajansa?, ashe da gaske dai baya sonta?, har yaje yayi aure bata sani ba, tabbas daga yau zata fita daga rayuwar Salman har abada, zata lallashi zuciyarta domin ta daina son wadda baya sonta, tabbas yanzu tasan Salman yayi nata nisa, nisan da bazata tab'a samunsa ba, yana da mata irin Salma ita d'in banza ya kalleta da mutumci ma.
Salma ko tunda taga lokacin dawowar Salman yayi ta shege d'aki tasa key, domin wani haushinsa take ji ma.
Salman tunda ya shigo gidan yasan tabbas fushi take dashi, a sadda yaje k'ofar d'akin ta, jinsa a rufe yasa shi girgiza kai kawai ya idasa d'akinsa.
Sai da yayi wanka ya shirya kamin ya nufo d'akinta, yasa wani key dake hannunsa yayi anfani dashi ya bud'e d'akin.
Salma na zaune tana latsa waya kawai sai dai taga an shigo mata d'aki.
Da mugun sauri da mamaki take kallon Salman, tunowa tayi fa k'ila yana da wani key d'in d'akin nata a tare dashi, yasa ta turo baki a shagwab'e ta koma ta zauna tana juya masa baya.
Murmushi Salman ya saki yana takowa a gabanta, yasa hannunsa ya juyo da ita, saiya zaunar da ita akan wata kujera dake d'akin wacce take kallon k'ofa, ya zaunar da ita, kamin shima ya zauna sai ya d'an kwanta akan cinyarta, yasa kansa akan cinyar tata.
Hannunsa yasa ya kamo nata hannun yasa shi a sumar kansa.
A hankali Salma take binsa da kallo, bata san lokacin data fara d'an sosa masa sumar kan nasa ba, amma har yanzu fuskarta alamar fushi take nunawa.
Salman yana kallon kyakykyawar fuskarta ya ce "duk naji abunda ya faru, ashe haka matar tawa take sona?, Wow so nice naji dad'in maganganun da kika gaya mata fa".
Harararsa Salma tayi tana cewa "to amma miye tsakaninku da ita?".
K'ara gyara kwanciyarsa yayi kamin ya ce "babu wani abu dake tsakanimu, illa kawai sona da take, tun acan Dubai take bibiyar rayuwata, kuma tun a can nasha gaya mata cewa bata d'aya daga cikin irin matan da nake so na aura".
Yana jin sadda Salma ke sauk'e ajiyar zuciya, murmushi ya saki kawai domin yasan dama kishinsa ne kawai ke damun Salma.
Ganin bata ce komai ba yasa Salman tashi a hankali ya jawota jikinsa ya rungume sosai, d'agowa tayi tana binsa da wani irin kallo, wadda tunda yake da ita bata tab'a masa irinsa ba.
Lumshe idonsa yayi yana jin sonta na bi masa duka k'ofa ta jikinsa, baiyi aune ba kawai yaji saukar bakinta a cikin nasa, abunda bata tab'a masa ba, sai dai shi yayi.
Sosai Salman yayi fari ciki, dama shi haka yake so, dandanan ya biye mata, ta bada kai bori ya hau.
Bayan komai ya lafa kwance take a jikinsa a parlo, tana basa abinci a baki, shima yana bata, waya yake da abokinsa Faruk dake shirin tahowa Nigeria.
Salman ya ce "wai da gaske kake abokina kaima kayi aure yanzu kana da mata?, anyi aure ba Amarya kamar ni a gari".
Dariya Faruk dake cikin wayar ya saki yana cewa "No ai gara ni da kai, saboda ni mun saba da ita yanzu haka, saboda yawan wayar da mukeyi da ita, har video call muna yi da ita, duk dan mu saba. Kuma abokina nake gaya maka, ka san dama bana son matata ta kasance tana yawan jin kunya ta, nafi son muyi rayuwa da ita kamar wasu abokan juna, to kusan haka na fara koya mata hakan, kuma da alama tana da saurin d'aukar darasin".
Dariya shima Salman ya saki yana cewa "shege friend cewa zakai rashin kunya kawai kake nuna mata, ba wani ku zama kamar friend, nafa sanka Faruk, adai bi d'iyar mutane a hankali idan aka iso Nigeria".
"Ai wallahi babu wannan maganar, kawai dai ayi sha'ani, gobe iyanzu na tabbata muna Nigeria".
"To amma a Abuja zaku sauka ne, gidanka dake nan".
"Sai mun fara zuwa Zaria mun kwana biyu tukunna zamu komo Abuja insha Allah".
"To shikenan ai ko zansa a had'a mana wata y'ar dinner ta bikin naka gaskiya".
"Nasan dama zakiyi abunda yafi haka ma ai, danma ba'a kusa nake ba, da ansha biki na kece raini".
Cike da hara da wasa da dariya suke wayar tasu har sukai sallama kamar kar su rabu.
Salma dake jikin Salman bayan ya tsinke kiran ta ce "aure yayi ne shima?".
"Aure yayi wallahi kusan irin namu da akai mana".
Dariya Salma ta saki tana cewa "baka san irinsa yafi albarka ba?".
"Ohhh really".
"Sosai kuwa".
Salman ya gyara zama yana kallon Salma ya ce "ni ko akwai maganar da nake so muyi dake".
Salma ma gyara zama tayi tana basa hankalinta ta ce "ina jinka Hayat"
"Naji abunda ya sami y'ar uwarki Khadija, na tausaya mata sosai, ina son taimaka ma mijinta domin rage masu rad'ad'in talauci, domin naji Y Ahmad ya ce sosaifa Khadijar tayi laushi, duk ta rame daga ita har Mamar, basa cikin kwanciyar hankali, dama na barta ne ta d'an d'ana taji kuma abunda duniya take ciki, tasan Allah d'aya ne, tun a ranar nasan duk abunda ya faru, da nayi niyar taimaka mata daga farko, sai naji irin abubuwan da sukai masu daga baya, sai na yanke hukuncin, bari na barsu, su gane duniya kowa jiransa take, domin ina da masu sanar dani abunda ke faruwa a gidanku".
Shuru kawai