Sauyin Yanayi Book Compelet Zahra Star

Author :  Zahra Royal Star Category :  Read Hausa Novels

Chapter   17 / 20

48K to 51K   out of 58.4K words

ji ya rufe masa zuciya. Hak'ik'a zai koyi sonta, zai bata kulawa, zai nuna mata so kodan ya samu ladar marainiyar Allah, daga jin labarinta tana buk'atar mai share mata hawaye.......

P 23-24

*Off Ty D'anjuma Asokoro District Abuja Nigeria*

Tsaye take a parlo, yau tunda ta dawo daga school take jin kwankwatsar k'ashi alamar ciwonta na son tashi, da kyar take iya komai, da kyar ta lallab'a ta masa abincin rana. Sadda zata gama tayi wanka ta kwanta a bisa gado jikinta yayi zafi, kwankwatsar k'ashin data ke ji ta k'aro sosai, k'udundunewa tayi da bargo sai rawar d'ari take, ga kwankwatsar k'ashin nan shi ke wahalar da ita, ga k'afarta data ke ji ta rik'e kamar ba tata ba, wasu hawaye ne take jin suna bin gefen fuskarta, tsabar yadda take jin azaba cikin jikinta.

Salman tunda ya shigo parlon bai ganta ba, sai k'amshin turaren wuta da yayi masa maraba, kallon parlon yake wai ko zaiga daga inda zata b'illo, ganinfa bata a parlon kwata-kwata yasa shi nufar kitchen, duk da yaga an jera komai a bisa darning table.

Kitchen d'in ya shiga ganin babu alamarta yasa shi juyowa ya fita daga kitchen d'in, yana mamakin ina tashi ga?, ko tana d'akinta?, amma ai zuwa yanzu bata cika zama a d'aki ba, yanzu tafi zama a parlo.

Bashi da mai bashi amsa, hakan yasa shi haurawa saman kai tsaye kuma d'akinta ya nufa.

Tura k'ofar d'akin yayi ya shiga, yana faman baza idonsa. Hangota yayi bisa gado ta k'udundune sai rawar sanyi take.

Bai san sadda ya wurgar da key d'in motar da ke hannunsa ba, ya hau bisa gadon.

Hankali a tashe ya yaye bargon data rufa dashi, ya rungumeta a jikinsa yana jero mata tabbayar lafiya take kuwa?.

Ganin batai magana ba yasa shi k'ara rud'ewa yana cewa "Ya salam Hayatee miya same ki?, please kimin magana mana".

Duk da irin halin ciwon data ke ciki hakan baisa ta fahimtar halin tashin hankalin da yake ciki ba, sunan daya kirata dashi ne ya tsaya mata a zuciya. Hawaye ne suka zake gangaro mata a k'unci wani irin dad'i take ji dama haka Salman ya damu da ita kamar haka?, tana iya hango tsananin tashin hankalin daya shiga a cikin idonsa.

Da kyar ta bud'e baki ta ce "bafa wani ciwo bane, Sikilata ce ke son tashi".

"Subhanallahi, dama kina da Sikila?, mi yasa baki sanar dani ba?".

Shuru kawai Salma tayi, ya bata damar sanar dashi ne, kuma ai Momynsa ta sani, mi yasa bata sanar dashi ba?.

Salman ya sake cewa "da jinina ba O bane, da shikenan sai ace dole sai na rabu dake, bayan munyi sabon da bazan iya koda nesa dake ba, Why Salma da bazaki sanar da mijinki abunda ke faruwa dake ba, yanzu fa baki da wadda yake da kusanci dake sama dani"

K'ara k'ank'amesa Salma tayi, tana jin wani sabon farin ciki na rufeta, jin cewa zasu iya zama dashi, su haifi raya masu lafiya, shi yasa tunda akai auran bata da wata natsuwar zuciya saboda ita tasan Sikila ce da ita, amma yanzu da yake gaya mata kilar jininsa sai hankalita ya kwanta.

Salman ya ce "mi yasa kike dafa abinci da maik'o?, kuma kin san anfi so kuna cin Manja, da abubuwan gina jiki?, kinga illar rashin sanar dani miya kawo ko?".

Bata tab'a tunanin zai nuna damuwarshi har haka ba akan ciwonta. Da kansa yasa mata Hijab ya d'auketa kamar wata jaririya ya nufi k'asa da ita, bata iya ce masa komai ba, sai kallonsa da take kawai.

Har cikin mota saida ya kaita, kamin ya koma yana duba key d'in daya wurgas a d'akinta, can ya gansa ya kusa shigewa k'ark'ashin gado ya d'akko ya dawo cikin motar, ya tayar suka nufi asibiti.

Asibitin da aka tab'a kwantar dashi nan suka je.

Ganin shi da kansa ya kawo matarsa, hakan yasa aka tarbesu cike da girmamawa, aka fara bata taimakon gaggawa.

Doctor ne ya kira Salman bayan an gama duba jikin Salma, sunyi mata komai yadda ya kamata.

Sosai Doctor yayita fad'a akan danmi za'a bari bata shan magungunanta yadda ya dace, da rashin bata kulawa da ake na cimarta.

Shi dai Salman shuru kawai yayi shima abun ya bashi haushi, danma rashin lafiyar data ke ciki shi yasa ya sassauta mata. Sosai Doctor ya k'ara ba Salman shawara akan abincin daya kamata mai Sikila ya rink'a ci, da dai sauran bayani.

Sosai shima Salman yaji dad'in hakan.

Kwanansu d'aya aka sallamesu. Ba laifi jikin nata yayi sauk'i sosai.

Amma fa a kwana d'ayan nan, Salma taga Salman baya mata magana sosai, kamar ma fushi taga yana yi da ita, shi yasa duk ta kasa sakin jikinta, duk wata y'ar damuwa tasa ma zuciyarta.

Koda suka dawo gida ma hakane, da kansa ya shiga kitchen ya dafa mata abincin da doctor ya ce ta rink'a ci.

Koda ya kai mata d'akinta, ajewa kawai yayi zai juya ya fita. Salma tayi saurin rok'o hannunsa.

Tsayawa yayi kawai, shi bai juyo ba shi bai waigo ba, taga bashi da niyar waigowa hakan yasa Salma tashi, ta bayansa ta rungumesa tana sakin wani irin kuka mai zuma zuciya.

Domin harga Allah bazata iya jurar wannan shashsharetan da yake yi ba.

Runtse idonsa yayi da k'arfi, yana jin yadda kukan nata ke sa zuciyarsa yi masa zafi sosai, kwata-kwata baya son ganin hawayenta.

Juyowa yayi kawai ya juyo da ita ta dawo tsakiyar k'irjinsa yasa hannunsa ya k'ara rungumeta.

Ganin har yanzu bai ce mata komai ba yasa ta cewa "please mijina dan Allah kayi hakuri, wallahi na tuba, bazan sake b'oye maka komai nawa ba kaji?".

Wani irin murmushi ya saki, yana k'ara sata a jikinsa kamin ya ce "shikenan ya wuce, dama ni ba fushi nake dake ba, kawai ina nuna miki cewa abunda kike bai dace ba, kawai ina d'an horanki ne akan gobe karki sake min irin haka, amma komai wuce".

K'ara rik'esa itama tayi tana jin wani sabon farin ciki na rufeta, harga Allah tana son mijinta, ba tun yanzu ba, d'an zaman da sukai dashi kawai ya isa ko wacece sonsa ya d'arso a ranta.

D'agota yayi, ya kamo fuskarta goshinsa da nata na gogar juna, idonsu a cikin na juna, duk da Salma sai wani kyafkyafta idonta take, saboda idonsa yana da wani kwarjini da baki isa ki kalli tsabar idonsa ki dad'e kuna kallon juna ba, dole kallo d'aya ma ki d'auke naki idon daka kallonsa, to amma ita wani maganad'ison da babu yadda za'ai ta iya janye idon nata a cikin nasa, ji take wani maganad'iso ne ya rik'eta.

Batai aune ba ya had'e bakinsu waje d'aya. Da sauri Salma ta damk'e gaban rigarsa da k'arfi, jikinta ya fara d'aukar rawa, a sadda taji ya kamo harshanta yana tsotsarsa kamar alawa, bata san sadda ta saki gaban rigar tasa ba, ta sak'alo da hannun nata a wuyansa ba, kamo kansa tayi da hannunta ta rik'e, bata san lokacin da ta fara basa had'in kai ba, ta fara maida masa martanin kiss d'in itama, hakan yasa Salman fara fita daga hayyacinsa.

Bai san lokacin daya d'auketa kamar baby yayi bisa gado da ita ba.



A daran ranar komai ya faru a daran ranar duk wani k'ulli da mak'iya da y'an hassada, suka dad'e suna shukawa a daran ranar komai ya kwance komai ya warware.

Kwance take a bisa k'irjinsa, sai kukan shagwab'a take narka masa, sai cewa take "shine kamin wayo, banda lafiya fa amma kamin mugunta irin wannan, wallahi Allah saiya saka min, ko tausayina baka ji ba".

Ta k'are maganar had'e da tab'e baki alamar zata k'ara sakin kuka.

Da sauri Salman ya k'ara had'e bakinsu waje d'aya.

Zaro ido waje Salma tayi, ai ko ta fara turesa daga jikinta, domin bata gama dawowa dai-dai ba, da irin azabar data sha a hannunsa ba.

Dariya ya saki a sadda ya cire bakinsa daga nata.

Turo baki Salma tayi tana kallonsa.

Ya ce "bafa wani abu zan k'ara miki ba, matsoraciya kawai. Danma Allah ya taimakeki na gasa ki sosai ai da yarinya kasa tafiya ma sai kinyi".

B'are baki tayi kawai ta sakar masa kukan sangarta. Da sauri ya jawota jikinsa ya rungume, ita ko dukan k'irjinsa ta farayi da hannunta.

"Wash Allah na, haba My Hayatee nahh, na tuba indai ni ne bazan sake ba kinji?".

Da sauri Salma ta d'ago daga jikinsa tana cewa "da gaske baza sake min irin wannan abun da kamin jiya ba?".

Salman ya zaro ido waje yana maganar zuci "abunda bazai tab'a yiwuba ba kenan ai Hayatee, d'aukar al'k'awarin da bazan iya cikawa ba".

Ganin yadda take kallonsa, yasa kawai ya d'aga mata kai, alamar tabbatarwa.

Komawa tayi cikin jikinsa, ita nan duk a tunaninta bazai sake ba ta yarda kuma.

Yadda take motsi a jikinsa, dukiyar Fulaninta na gogar masa k'irji, ji yake kamar zai mutu, tsabar yadda taushinsu ke saukar masa da wata muguwar sha'awarta,

A haka take cewa wai karya sake?, tab abunda ma bazai tab'a yiwuba kenan ai.

Salman yake fad'a a zuci.

*Unguwar Dubantu Hadejia Jigawa State Nigeria*

"Waini abunda ban gane ba shine, ina kukai min yarinya da har kuke cewa wai wani gidan k'asa ba suminti ko d'aya sai a k'asan d'akin da kukai Khadija keda suminti, na kasa fahimtarku fa".

Cewar Mama dake tsaye a tsakar gida, ga y'an biki zagaye da ita, wa'inda suka je kai Amarya ne suka dawo, suke shaida ma mutanan gidan abunda suka gani da idonsu.

Domin kuwa sunje kai Amarya motocin da Jafar ya aiko akai Amarya, ba gidan da akai jere suka ga an nufa dasu ba, wasu daga cikinsu tun a cikin mota suke fad'a suna cewa "su za'a raina hankali, ina za'a kaisu baccin ga gidan Amarya an wuce za'a nufi wata unguwar talakawa dasu kuma?".

A sadda motocin suka tsaya bakin wani gida wadda daga kallesa zaka san na talakawa ne futuk kuwa, yaran unguwar sai fitowa suke suna kallon Amaryar Jafar, da mutanan da suka kawota.

Amarya Khadija fa tsabar tashin hankali ma yaye gyalen dake rufe a fuskarta tayi, tana bin gidan da aka kawota da wani shegen kallo.

Wa'inda suka d'akko su kuwa haka suka ce masu, sudai nanne inda ango ya ce su kawo Amarya.

Tofa waje ya hargitse da k'ananun maganganu, Matar Jafar kuwa tana jin duk abunda ke faruwa tun ranar daya zo akayi sabon fenti aka jera wasu kaya y'an dai-dai a d'ayan d'akin dake kusa da nata, sai ranar yake sanar da ita cewa shifa aure zaiyi, ko a kwalar rigarta bata ce komai ba sai da ya fita ta ce "Allah yasa alkhairi, ido ne nawa, yanzu haka k'aryar daka sabayi ce kaje kayi, wajan auran nan, nima baccin Ubana ya ce na sake na dawo masa gida da aure na saiya tsine min, ai da wallahi nafi k'arfin na zauna da kai a haka, amma itama tazo ta d'ana ko wacece nima son kud'i na da son duniya shine yaja min".

Haka dai suka shiga gidan, da kyar Khadija ta shiga gidan sai wani uban kuka take a sadda taga d'akin wai da yake mallakinta, kayan da Iyayenta suka sa mata, ba sune ta gani a wannan d'akin ba.

Cewa take "wallahi Allah bazan zauna dashi ba, na rantse sai ya sake ni yanzun nan, ashe dama macuci ne maci amana, wallahi Jafar na tsane ka".

Kuka kawai take yi tana fad'ar haka, da kyar cikin y'an uwan Mama suka tausheta, suka ce mata "ki rufa mana asiri ki zauna a d'akinki, idan yaso zamu koma gidan mu sanar da iyayanki, duk matakin da suka d'auka shikenan, na tabbatar Hajara bazata kyale wannan Jafar d'in ba, kedai ki d'an bamu lokaci mu koma gidan".

"Ni wallahi bazan zauna a gidan nan ba".

"To ya kike so muyi, so kike ki tuno mana asiri y'an unguwarku suyi miki dariya, kibi komai a hankali mana Khadija".

Maryam dake kuka ta ce "yo dariya ta nawa kuma, dubi fa wajan nan, cike yake da k'awayenta wasu dama y'an ganin kwaf ne, zuwa kawai suke suga inda aka ajeka suje suyita yad'awa a gari, ai jin kunya dai munjita wallahi, Allah dai ya tsinema Jafar d'in nan wallahi".

Su Sadiya kuwa tsabar mamaki sai kallon gidan suke, suna rik'e da baki, abunfa yafi k'arfin tunaninsu ko hasashensu, sai y'an maganganu ke tashi a tsakin y'an matan dake wajan, ko wacce da abunda take fad'e.

Da kyar ta yarda suka baro ta a wannan gida.

Suna gama ba Mama labari ta yanke jiki ta fad'i.

Tofa gidan biki sai koma na zuwa jaje, da kyar aka samu Mama ta farfad'o.

Sai wani abun kuka take kamar wacce aka ce mata mutuwa zatai.

Hajiya ma fa abun ya girgiza ta sosai, rayuwar sai taji ta k'ara bata tsoro, tana tabbacin Allah ne ya maida ma Mama magana, tasan cewa alhakin Salma ne da ita kanta ya fad'ama Mamar ita da Y'ay'anta.

Mama sai kuka take tana cewa "wallahi koda ubanwa yake yawo Jafar saiya sakar mata d'iya, bazata tab'a yarda ba".

Hijabi take niyar sawa wai zata fita taje har gidan da aka kai mata d'iya taje ta ce ya sakar mata Y'a, bazata tab'a yarda ba wallahi. Kuma kayan da akai mata saiya gaya mata gidan ubanwa ya kaisu tunda ba ubansa yayi mata su ba.

Duk abunda ke faruwa Abba ya sani, jama'a sai samunsa suke suna tarbarsa da zancan, ya rasa inda zaisa kansa dan kunya, abun duniya ya taro yayi masa yawa, y'an unguwar mata da Maza sai shige da fice suke a gidansa suna jiyo labari, suna zuwa suna yad'ashi a gari, kamin ka ce mi ko ina na unguwar ya d'auka, wasu ma harda k'ari abunda bai faru ba, saida aka k'ara wani abun akan wadda bai faru ba.

Koda Abba ya shiga gidan, jin cewa Mama ta yanke jiki ta fad'i, ta farfad'o tana niyar fita taje gidan sirikin naso, yasa shi shigowa gidan badan yaso ba, sai dan ya jama Mama kunne.

A bainar jama'a Abba ya nuna Mama ya ce "idan kike sake kika fita daga cikin gidan nan, bada izinina ba to a bakin auranki".

Da mugu mugun mamaki Mama ke kallon Abba ido a waje. Bakinta na rawa wajan cewa "Abbansu Maryam anya kaji abunda ke faruwa da y'arka kuwa?, kake fad'in wannan magana, ni zatona ma zaka ce zaka makasa a koto ne ya sakar maka d'iya".

Murmushin daya fi kuka ciwo yayi yana cewa "nasan komai, kuma duk kece kika jawo ma Y'ay'anki haka, dan haka ban amince kowa ma ya sake zuwa gidan Khadija ba, kuma zansa a gaya mata idan ta sake ta baro gidan mijinta ban yafe mata ba".

"Innallihi wa'inna alaihir raju'on, na shiga ukuna, anya Abbansu Maryam kene a tsaye a nan kuwa?, kai ina bakai bane wallahi, idan kuwa kai d'in ne, to wallahi asiri akai maka domin dai a raba ka da Y'ay'ana, kuma wallahi bazan tab'a yarda ba".

Mama ta k'are maganar da hargagi har jijiyoyin kanta na tashi.

Y'an biki suna tsaye suna kallon ikon Allah, wasu ma so suke a ci gaba da yin diramar kar a daina, wasu a b'oye suke ma Mama dariya.

Abba ya sake nuna Mama da yatsa yana cewa "nidai na gaya miki, idan kinfi son auranki ya mutu to ga hanya nan ki fita kije gidan Khadija amma daga nan ki wuce gidanku, karki sake ki sake dawo min gida, kuma gaba d'aya Yara na ban amince su sake zuwa gidan Khadija ba. Komai ya faru kece sila, kice kika ce kar ayi wani bincike ai kinsan Jafar d'in, ai kamar D'an uwa yake a wajanki, ni kuma lokacin kamar wani abu ya shiga kaina na biye miki, to daga yau insha Allahu zansa ido akan Y'ay'ana, da bana tunanin ina cikin yaccina, amma yanzu na dawo cikin hayyacina, na dawo daga rakiyarki, ko acan da inaga wani abu kikai min harda yasa bana iya musa miki ga duk abunda kike so ayi a cikin gidana".

"Wayyo Allah na shiga uku, Abbansu Maryam ni kake tonawa asiri a gaban jama'a a gaban duniya, wai mike faruwa dani ne yau?".

Tofa kowa kallon Mama yake wasu har sun fara yada mata maganganu barkatai.

Abba zai sake magana Hajiya ta fito ta janyesa ta kaisa d'akinsa, ta fara ce ma jama'ar da suka shigo jin gulma, "dan Allah idan sun gama jin gulmar kowa na iya wucewa sun gode".

Mama tana kallon Hajiya tana kuka hak'i K'anin gaskiya ta fara hango yadda akai auran Salma, sai gashi babu abunda ya faru cikin auran nata, gashi dai ba abunda akai d'aura aure kawai akai, Salmar ma bata san waye aka aura mata ba, amma ta amshesa hannun biyu-biyu. Sai gashi ita da aka d'ora dogon buri akan bikin tata d'iyar ayi waccan bidi'a ayi wannan bidi'a, sai gashi abunda ta Allah ta kasance da ita da tata d'iyar.

Kuka take ta d'uke k'asa a sadda taga Hajiya ta matso inda take tana bata baki. Kallonta kawai Mama keyi tana cewa "dan Allah Hajiya ki yafe min, na rantse nasan alhakinki ne ke bibiyar rayuwata data Y'ay'ana, idan baki

17 / 20