Author : Nana Kanwar Soja Category : Tknovels
Hajiya Hauwa kuma tun tana ciwo a kwance har tagaiga an killace ta a asibitin mahaukata lokacin da ZALFAT ta yunkura da maganar samun lafiyar ta domin tune tune asirin ta da takiye yasa suka nema wane malami donyi mata ruƙiyya tunda ga wanna lokacin wane aljani ya fito da musu bayanin cewa layar da sukawa a bakin ƙadangare to shine ba lizard ba ne hakan yasa ya shigo jikin ta ya samata ciwo amman bashida alaqa da hauka a sannu a hankali ya fitta jikinta yayi sauki sosai sai dai taɓin ƙwaƙwalwa da bai samu maganin su ba.
AFTER 3 YEAR'S
"Abban Majhat kasan me kuma " matsowa kusa da ita tayi tare da zagaye hannun sa akan West nata "a'a Umman Majid sai kin gayyamun " murmurshi tayi ta sumbachi shi a kan hannun sa "ina sonka miji na nagode sosai da kulawar ka tabbas nayi dacen samun miji irrin ka gani naki duk duniya babo wacce ta kaine dacen miji irin na" ah haba dai to in kuwa hakani zaki kawo wa Majhat ƙanwa "
Ido ta zalzalu waje "wa don girman Allah ka rufamin asiri shifa haihuwar nan ba rigi bindiga ce ba" kumatun ta yaja " fisabilillahi haka zamuyi dake to yanzu muje ciki muyi magana "a'a wayo zaki min ko to bazan yarda nayi ciki yanzu ba gadon ka daban nawa daban sai Majhat tayi shikara gom" bata gama magana ba ya ɗaga ta sama nan ta fashi dariya
"Ummm ummm nashigo ne " da sauri suka juya " ta wai kai doctor meyasa kakison takura rayuwa ta ne yanzu da sanyin safiyar ma sai ka takur" ganin ZALFAT a bayan sa ne ya sauki HABLAT " doctor kazama mara kunya fa "dariya yaye to baby sauka kinji ko " duk ido suka biso dashi " Wallahi wai ZALFAT ce yau bazata taka ƙafar ta ba rigimar ai duk wanchan yarinyar ta koya mata yana nuna HABLAT
" Wa ni kuma yaushe "look doctor kar ka kuma cewa matata yarinya "na faɗa yarinya" da gudu yabiyo sa suka fara gujil gujil sukaye waje HABLAT ce ta hurgawa ZALFAT pillow '" aikin banza yanzu na samu ya fita aikin ke yayi kyau tashi mu tafe meeting kinsan time na gudu kar muyi late "wa ai ne wallahi bazan taka ƙafata ba HABLAT sai dai doctor ya goya ne "
Baki ta buɗe " Waiyo ne HABLAT wai kima fa akaiw rikici ashe don baki samu fili ba ne ko "duk dariya sukayi nan suka fitta cikin annushuwa da farinciki ciki ,
" Ku gyara zamuyi hoton " cewar photographer da sauri ANBAR ta kuma gyara mayafinta don duk kunya takiji ganin cikin ta ya fara girma Abba ne yayi murmurshi nan Alhaji Imam ya zauna kusa dashi sai Hajiya Khadijja a ƙifi sa daga hannun Abba kuma ANBAR ce da Lattu sai Zayyan da Hafeez da matan su kusa dasu Amrat ce da Afra sai Ikram sai Inna da Malam Daga ɓangaren guda kuma Baffa ( mahaifin HABLAT) da sabuwar matar sa Salma ,
PAYAM ne yaga ba Majhat " Majid ina Majhat " ta bai rufe baki ba ta taho da gudu da waya a hanunta duk ta hargitsa screen nin wayar "subhanallahi shikkinan ta fasa min waya " da sauri ta faɗa jikin PAYAM tana ɓoya" Allah sai na daki ke Abba kuna gani ta fasamin waya yarinya sai fitina"
" A'a HABLATU gado tayi kinga laifinta ke lokacin dakike yarinya Form na farko na tafiyar yayanki makarantar soja kika yaga ranar ba burin da baiyeba don tafasa waya ba'abin mamaki ba ne " duk dariya suka sa harda ita cliiiipppooo photographer ya ɗauki su family picture.
Alhamdullah!!!
Alhamdullah!!!
Alhamdullah!!!
Godiya ta tabbata ga Allah da ikon sa na kamalla wanan littafin lafiya kuskure da na aikata a rashin sani sanadiyyar wanan litattfin Astangafurallah abinda ya zama Alkaire Allah ka kai ladar kabarin mahaifina ,
Amince da tsira su tabbata ga Annabi Muhammadu S A W 💞 da Sahabban sa da mabiyan sa har zuwa gidan Aljanna maɗaukakiya.
Godiya ga member's na sirrin ƴa mace Allah ya bar ƙauna da zumunci 💖
Godiya na musamman ga group na MAI CIKI CE da lokacin ku da adu'a ku garine Allah biya mana buƙatun mu na Alkaire 🙏💖
Jinjina na musamman gari ku mai commenter's Allahu ya barmu har a gidan Aljanna 🥰🙏
TAMMAT BI HAMDULLAHI
ALƘALAMIN NARNAH ƘANWAR SOJA ✍️📝
ALƘALAMIN ƘANWAR SOJA 🖋️💞🌹