Kanin Ajali Complete by Zeey Makawa

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Read Hausa Novels

Chapter   4 / 37

9K to 12K   out of 109.3K words

ga karatun garin mu.
Baba bai dauki wani lokaci yana kaini makarantar ba har na gane hanya don baida isashen
lokacin da zai rika kaini ya dauko ni.
Da yake mama ba karatun boko tayi ba sai hakan ya rage ma karatuna gudu don babu mai
taimaka min a gida idan an bamu aikin gida muyi.
Sai dai hakan bai hanani kokari ba don Allah ya bani kokari sosai na fahintar abu hakan ya
jawo min farin jini ga malamai da yan ajin mu.
Idan na dawo gida da yamma nake zuwa islamiyan uguwar mu gurin daukan karatu sai
shidda na yamma ake tayar damu.
Mama ma ta shiga wani islamiya a nan unguwar suje goma na safe su dawo da sha biyun
rana wanan karatun da mama ta shiga ba karamin ci gaba ta samu ba sosai.
Don ta fara koyon rayuwan yan birni tana fahintar zamantakewa da mutane zan iya cewa mun
dai fito birni ne don a nan ma ba ganin mahaufi mu muke koda yaushe ba.
Haka na dai yafi muna zaman can din da fitinan umma sai da muka share shekara daya a kano
baba kabiru ya kawo muna ziyara.
Ranan nayi murna sosai da ganin kanin mahaifina ya kawo muna ziyara na farko a gidan mu
wanda tun tarewa mu kanon zance bamu taba yin bako ba a gidan mu.
Sai faman rawan kai nake mai yana dariyan jin dadi da ganin yadda muka sauya a dan lokaci
mama tayi kyauta kamar ba ita ba ga dan matashin cikin dake jikin ta daya fara tasawa yanzu.
Yana fada ma mama zai dan kai sati daya a wurin mu mukai ta murna da zuwan shi sai dare
baba ya dawo daga gurin aiki.
Yana shigo ya samu da uwanshi yazo duk da yarinya nake a lokacin naji mamakin kalami
mahaifin nawa a lokacin don cewan da yayiwa baba kabiru lafiya dai kazo kabiru ?
Walwalan dake fuskan shi ta sauya yace lafiya kalau nazo in ganku ne kawai mu sada
zimunci da kuma zancen siyasan da zan fara.
Maganar baba ya girgiza mama don cewa yayi ashe kana da kudine da har zaka fara siyasa
dashi ya danyi murmushi yana gyara zama yace.
Ina dai da rufin asirin Allah dana yan uwa don ko ina noma da kiwo sai ko dan aikin da nakeyi
yanzun kuma na sake.
Baba baiyi magana ba ya mike ya shige daki ya dauki lokaci a dakin ya barshi nan suna hira
da mama a dan falon mu.
Ya fito ya samay su hiran gida da mutanen kauyen mu sukeyi haf barci ya dauke ni a gurin a
falo baba kabiru ya kwana.
Nidai washe gari na tafi makaranta na dawo na samu wai baba kabiru ya tafi nace mama ba
yace sati zai muna ba tace dani kin san halin mahaifin ku ai haka yake kamar umma idan halin
shi ya tashi.

Ban san lokacin da hawaye ya fara zuba min ba don har ga Allah banji dadin wucewan da
baba kabirun ba mutumin kirki mai kaunar mu da gaskiya.
Ranan haka na wuni sokuku har zazzabi yaso kamani da wuri na kwanta tun kan baba ya
dawo gida ya shigo yayi abinda zaiyi ya kai kallon shi a inda nake yana tambayan mama har
nayi barci ne yau da wuri haka ?
Mama tace fushi nake babana ya suce bamu yi sallama dashi ba ya ja tsuki tare da jawo
kulan abincin shi gaban shi ya fara ci.


Kuyi hakkuri yau ban da caji yanzu na samu na dan tubuta wanan .
..

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:46 PM - : ‍♂️ KANIN AJALI ‍♂️

3️⃣


A cikin dare ba dinga jin kukan mama sama sama tana magana abinda ban taba jin ya faru da
ita ba sai yau ban san abinda ya falkan dani daga barci ba a lokacin.
Sauraren maganan mama da na sama tayi a lokacin shine dan uwanka yazo gurin ka don ka
taimaka mai koda da shawara ne.
Zaka rufe ido kayi mai cin mutunci irin wanan ka tuna kabiru shine jigon mu a lokacin da ka
barmu gida banda wanda nake dafawa inji sanyi sai yan uwanka.
Tsawan da baba ya daka yasa na runtse ido daga inda nake ina ci gaba da sauraren fadan da
suke wanda akan zuwan baba kabiru ne gurin mu.
Yace ke ki rufa min baki don ba kece ke nema min abinda nake nema din yan uwana ne ba
naki ba don ba a canzawa tuwo suna.
Tana dina a iyalina nake yin shi ban sa rai ga abin wani don haka kowa tashi ta fitar dashi duk
da fadin hakan da baba yayi bai sa mama tayi shiru wurin nisan dashi nauyin zumucin ba.
Taci gaba da fadin idan baka nuna wa diyan ka tan uwanka ba sai yaushe zasu fahinci
muhinmancin zumunci icce fa tun yana danye ake lankwasa shi.
Mudin ya bushe ba zai taba lankwasuwa ba sai dai ya karye don bushewan shi duk abinda
kake yi suna hankalta dashi suke koyi.
Idon baba suka kankance kalamin mama yana mashi zafi a ranshi yasa gaskiya mama ta fadi
yasan bai kyautawa baba kabiru ba don yasan dan uwa ne na gari a gare shi .
Lalai ya tafka kuskure sosai wanda bai dace ace yayi shi ba ga dan uwan shi yadda ya fito fili
ya nuna ba zai taimaka mashi ba.
Ni dai har na sake komawa barci ban san lokacin da suka kare fitinan ba a kan baba kabiru din
wanda duk da yake ina da karancin shekaru na gane abinda mama ke son nuna ma mahaifin
mu din.
Tun wanan lokacin ba wani dan uwan mu da ya kara zuwa inda muke mu din kuma ba gida

muke zuwa ba tunda muka baro gida.
Tun ina kewan mutanen gidan mu har nazo na saba da rashin su a tare dani yanzu har kakata
duk da fadan ta sai ya kasance ina kewan ta yanzu sosai.
Washe gari ta fito kamar ba ita ba ni kaina ban nuna mata naji abinda ya wakana a tsakanin
su ba a daren jiya din.
Sai dai har wanan lokacin akwai damuwa a tare da ita sosai bata da yadda ta iya kasancewan
mahaifin mu mutum ne mai riko sosai akan akidar shi da aikata duk wani abinda yayi niya idan
har ya fada hakan yake nufi har a cikin ranshi.
Aikin hada abin karyawa take tana hawaye hankalinta duk a tashe yake tasa mijin nata yana
tafka kuskure a rayuwan shi.
Sai dai babu yadda ta iya da wanan halin nashi na nuna son kai ga yan uwan shi yanzun ne
ya kamata ace ya saka masu da abinda sukai masu a baya sai dai wannan mumunan halin
nasa ya hana shi hango haka din yanzu.
Hawaye ne masu dumi suka kara zubo mata a gurin gaskiya ce yanzu daci ne gare ta don
wanan abin kunyan da mijin nata yaiwa dan uwanshi da wani ido zasu kalle shi dashi.
Murya na ne ya katse ta ina fadin mama ki bar kuka ki kyale baba ai baba kabiru ba zaiyi fushi
damu ba don yasan bamu ne da laifi ba laifin baba ne daya kore sa.
Ta kai idon ta kaina tana nazarin magana na ni dai din duk da karanci na nice abokiyar firan ta
a gidan don baba ba mai zama gida bane shi.
Tace yi maza ki shirya kada ki makara kin tsaya fadin abinda ba a tambaye ki ba don iya
surutun ki simi simi na koma falo ina saka sock a kafana don karasa shirin da nakeyi wanda
yanzu ni ke taimaka ma mama da shara da sauran yan aiyukan gida.
Nagama daidai lokacin da ta fito dauke da kulan abincina falon da wanda zan dan karya kafin
in fita zuwa school din don duk saurin da nake mama bata bari in fita gida ban karya ba.
Don munhinmanci da yin hakan ke dashi a cewan manya fita gida baka saka wani abu a baki
ba yana kawo wa mutum rashin sa,a.
Ina isa cikin makaranta na a buga muna assemble don haka ban makara ba duk da ganin da
nake da farko na makara din.
Muna shiga aji ne zazzabin dake damuna a daren jiya ya dawo min sabo duk kokarin danayi
na kannewa dashi sai da ya kada ni a school din haka yasa jikina ya dauki kyarma har mutane
suka gane hakan.
Dole aka bugawa mahaifina waya akan yazo ya dauke ni don banda lafiya ba, a dauki lokaci
ba baba ya iso school din akabashi ni muka tafi.
Bai kaini gida ba ya tsaya dani wani asibiti na karbi allura da magani ya wuce dani gida mun
samu gidan a rufe mama ta tafi islamiya wurin daukan darasi.
Waya ya kirata do ya sai mata dan karamin nokia don kira idan baya gida sai gata tana gani
na cikin yanayin ciwo tace.
Kin dauki tafiyan baban ki kin sa a ranki kamar wata babban muta ga shi har ciwo ya kama ki
yanzu.
Baba dake jin mu kala bai ce ba ta bude gida muka shiga ya shimfide ni a falo ban dade ba
barci ya dauke ni a gurin.
Sai da mahaifina yaga na samu barci sosai yake tambayan mama abinda ya jawo min
zazzabin da nakeyi.

Mama bata bashi amsa ba don zuciyar ta dake tafasa a lokacin maimaita tambayan yasa ta
bashi amsa da fadin don babanta kabiru daya wuce bata sani ba.
Kukan tafiyan shi ya haddasa mata zazzabi tun jiya take fama dashi ai, magani na bata taji
sauki a she bai tafi ba.
Batare da ya tsaya jin karashin maganan ba ya fice daga gidan sai karan tayar da mashin din
shi taji ya tafi.
Wasa wasa na kwana biyu ina fama da jikin sai da nasha allurai na mike tare da fadan baba
dayai min idan na kara saka abu haka a raina sai ya yanke min kauna.
Na koma makaranta naci gaba da karatuna yayin da cikin jikin mama yake girma bata kai ga
haihuwa ba akai muna transfer muka koma katsina.
Acan mama ta haifi danta na miji mai kama da mahaifin mu sak aka saka mai suna wan
mahaifin mu daya rasu muna kiranshi da baffa.
Mun samu sauyin makaranta don da za,a saka Shamsiya makaranta boko sai ka maida mu
guri daya makarantar yana da tsada sosai.
Hakan yai ma mama dadi sosai don ita batayi boko ba tana da gurin taga mu mun samu ilimin
zamani don mu samu na dogara da kan mu.
School bus ke daukan mu ya dawo damu a can ne na fara kawa bayan kawayena su hafsa
dana bari a kauyen mu.
Baba ya shigo gida ranan da fara,ansa sabanin yadda yake shigo muna fuska a murde wanda
mun saba da hakan yanzu.
Tundai ni da nake yar fari a gurin a gurin duk abinda nayi ba daidai bane a gurin shi zai rufe
ido yayi min fada sosai kan abu dan kankani.
Sunan mama yake kira sauden ta don basu iya saya suna kamar yadda mazan birni sukewa
matan su ba duk da wayewan da yayi yanzu.
Daga kitchen ta amsa mai da gani baban shamsiya don itace ta biyu da bata kunyan kiran
sunan ta ya taka har zuwa kofan kitchen din.
Bata kai ga fitowa ba ya samai ta a gurin tana tsane hannun ta dake da ruwa yayin da ni
kuma nake a kitchen din ina rufe abincin da ta zuba a kula.
Daga cikin kitchen din na gaida shi da dawowa da sannu da dawowa baba ya amsa min da
yauwa hadiza maman ta ina mamakin farin cikin mahaifina a yau.
Yace yanzu ina offoce din mu na samu sakon ashe kabiru sun lashe zaben da akayi a gida
yanzu ya zama kansilan garin mu.
Ba mama ba har ni dake duke ina aikin ban san lokacin dana sake ihun murna ba duk da a
lokacin ban san kan aikin da ake fadin baba ya samu ba.
Yaci gaba da fadin zaki sha mamaki isan kinji wa yanda ya kara dasu ya kuma lashe zaben
mama tace lalai abin farin ciki ya samay mu.
Ta juya da fadin kaga abin Allah yafi gaban mamaki wa zaice zaici wanan zaben haka a
sauwake tunda bayi ya saba yi ba can.
Ya gama bata labari ya fita ya barta nan tana mamakin shi kamar bashine dan uwa yazo wurin
shi neman shawara ya muzanta shi ba a lokacin.
Abinka da dan uwa bayan kwana biyu sai ga baba kabiru ya kawo muna ziyara har inda muke
gurin aikin su baba ya tafi inda suka dawo gida a tare.
Mama na daki tana gyara baba ya shigo gidan yana fadin ina maman yara take ne yau kina

da bako a gidan fa ta amsa da gani nan baban shamsiya.
Yace yau kina da babba bako da ke da yara mama ta kalle shi cike da kulawa tace bako daga
ina kuma yace kabir ne yazo gashi nan falo a zaune yana jin ki.
Cikin mamaki mama ke dariyan jin dadin ganin na gida a karo na biyu da baro gidan mu tun
zuwan
Shi na baya da suka rabu da mahaifina babu dadi sai yau da ya sake dawowa da uwa ke nan .
Ta fito falon a cikin fara, a don ta tare shi da zuwa yana zaune yaci shadda dan uban su ya
sauya sosai a yadda ta san shi a da can baya.
Nan suka kaure da hira da tambayan ya bayan rabo tana mashi murnan samun karuwa da
yayi sun dan jima tana tambayan shi mutanen gida.
Kafin ta koma ta hada girki lafiyayye da cafanen da baba ya fita ya sawo don kanin nashi da
yazo inda baba kabiru ke falo zaune da baffa daya sake dashi kamar ya san shi.
Mun dawo daga school muka samay shi nan na hau murna sai shamsiya ne da bata waye shi
ba s taki zuwa wurin shi ta make gurin mama.
Kiran da mama ta kwala min ne yasa na bar falon zuwa gurin ta kitchen inda take aikin abincin
abinci na samu tana hada masu.
Ta nuna min tire tace in hada abinsha a cikin dan karamin fridge din mu dake aiki a kitchen din
na shiga hada kayan data umurce ni akan tire din tana gyara min.
Lemu su zobo mai sanyi sai ruwan sha na leda shima dai mai sanyi sosai kofina na dauko na
jera na dauka na kai masu a falon namu.
Inda na samu suna magana akan umma nayi sallama suka amsa mun cike da fara,a a
fuskokin su a gaban su na kawo na aje.
Baba kabiru ne ya dube ni yace masha Allahu diyar tawa tayi wayo sosai wallahi ai umma bata
gane ki idan ta ganki yanzu.
Kunya naji na dan tsone kaina na dago ina fadin baba umma ta bar fada ne yanzu cikin
yarinta zalla nake mashi tambayan.
Mahaifina ne yayi min dakuwa a inda yake tare da fadin tabar ma furera fadan cewa yar shi
watau gwagona shigowan mama bayana dauke da kayan abinci ne ya katse maganan.
Sai da ta aje take fadin wai yaya ake magana baba yace wai tambaya take idan umma ta bar
fada yanzu.
Juyawa tayi tana fadin ga mara kunyan banza idan bata bar fada ba ke nan baki zuwa idan
mun tashi tafiya da sauri nace wallahi ina zuwa mama suka sa min dariya.
Muryan baba kabiru naji yana fadin idan kin gama aiki sai kije kiga mota dama ita nazo in
nuna maku kusa min albarka.
Mama ta fadada murmyshin ta tana murnan jin abinda yace din da sauri ta koma daki ta
dauko hijja din ta zuwa waje inda muka mara mata baya zuwa ganin motar.
Munyi murna sosai da ganin motar baba kabiru din sai albarka mama ke sakawa tana taya shi
murna yana jin dadi har cikin ranshi.
Sai lokacin ya sauke muna tsaraban da ya kawo muna abin kamar da gayya sai da babana ya
sauke kai ya dago yana fadin kabiru may yasa kai muna haka.
Yana dariya tare da fadin wanan ba komai bane ai nan dai baba ya rasa abinda zaice ya shiga
yi mashi godiya.
Sunyi hira sosai ranan kafin ya tafi masaukin daya sauka ya kwana a can din bai sauka a

gidan mu ba kamar yadda ya saba.
Sai washe garine da yazo ya karya yake fadin a ranan zai koma mama bata

4 / 37