Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
zance ya tashi karshe sai fita daga
gidan nayi don ban iya sauraren maganan su.
Dama baba ya saya min set din akwatuna da yan tufafin da yai min da zan saka aka kara
zuba kayan da suka kawo a cikin akwatin.
Shi dai baba sai fadin Allah dai ya bamu zaman lafiya ace gara da akayi albarkan auren ake
nema ba kyalekyalin auren ba.
Ga gida ya cika da yan uwa da abokan arziki ta ko ina a gidan don bukina kawai suka hallara
wasu tsakani da Allah suka zo wasu kuma gulma aga karshen abin ne ya kawo su daga kauyen
mu.
Shiko gogan sai waya muke a tsakanin mu inda yake kara karfafa min yadda nake a rayuwan
shi da irin taimakon da nayiwa rayuwan shi din.
Anje an gyara min dakina komai tsone gwanin ban sha,awa dai kowa ya dawo yana yabawa
irin kokarin da baba kabir din yayi don ba a ma maganan matan shi duk da suma sunyi iya
kokarin su kan sha,anin.
Party kan har kala biyu aka sha don jin dadin buki wanda ya shirya da abokan shi yan karya
anci ansha an gwangwaje a gurin an dawo ana bada labarin komai.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:55 PM - : ♂️ KANIN AJALI ♂️
1️⃣4️⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
LITTTAFIN KUDI NE IDAN KIN SAYE KIJI TSORON UBANGIJI KADA KI FITAR MIN DASHI
DON AMANA NE A TSAKANIN MU KI GUJI NAUYIN AMANA A KANKI YAR UWA IDAN KIN
GA MARA TSORON ALLAH TA FITAR KI GUJI SHIGA HAKKIN WANI YAR UWA DON NA BIKI
DARI UKU AKAN NOVEL, , , , , , , , , ,
Duk wani abin al,ada na buki angama lafiya sai fatan Alheri ga auren mu da yan uwa da abokan
arziki ke gabatarwa a gare ni.
Abokan ango sun rako ango daki daya sha gyara sai kyali yake don katan alatun dayaji
wanda a kauyen mu kaf idan da ca muke nabar tarihi a kauyen namu don haduwan dakin
namu.
Sai dai may bayan tafiyan abokan ango da kamar minti goma Jamil ya dawo daga rakiyan su
yace hadizatul kubura yau dai Allah ya cika muna gurin mu akan jajircewan mu da juna.
Ina dan murmushi na bude fuskana ina fadin bisa ga taimakon baba kabiru bawan Allah muka
samu wanan cikan gurin namu da yake Allah yace ni matar kace jamil.
Banda abinda zance da baba kabiru sai fatan Allah ya saka mashi da alheri yadda ya rike
zumuci Allah ya bashi ladan zumunci kamar haka.
Duk maganan da nakeyi jamil sai bin dakin da wani irin kallo yake wanda ba zan iya fassara
shi a lokacin na burgewa ne ko na wani abu ba.
Budan bakin shi bayan na gama magana sai cewa yayi dani amma dai ke har yanzu yarinya ce
khadija wani kokari sukai maki a nan daki kamar na kauyawa.
Da mamaki na juyo ina kallon shi ya ce eh duk irin dukiyan da mahaifin ku ya bari da wanda ya
tara maku wanan abin zasuyi maki ga auren ki ?
Yanzu dai ai kinga abinda nake fada maki ko da ina fada baki yarda yanzu don Allah wanan
kayan yan kauyen tsohon yayi ya dace ace sunyi maki ?
Tsaye nayi galala ina kallon shi don jin abinda yake fada a lokaci wanda ban san amsan da
zan bashi ba kan maganan da yakeyi din.
Yace eh na fada kuma gaskiya nake fadi da ke yar su ce wallahi ba zasuyi maki wanan
wullakancin ba haka da komai na zamani zasu kawo muna.
Amma da yake ke baki da wayau har wani addua kike kokarin zabga mashi irin haka ni har
kunya naji da abokai na suka shigo suka samu dakin namu a haka.
Yanzu jamil duk wanan uban kayan basuyi maka ba kake nufi yace wallahi basuyi min ba
hadiza duk sake su zamuyi musai na zamani da ake yayi mu saka don abin kunya ne a gurina
abokai na su zo suga dakin matana haka a wullakance bayan sun san yar gidan wanda na
aura. Na fada maki ba son ku suke da zuciya daya ba kece baki yarda kin kasa fahinta na duk
lokacin da nake fada maki sai ki dinga daukan magana kamar ina son hadaki dasu ne.
To ai yanzu kin gani da idanuwan ki abinda sukai maki yar bare kike a gurin su kin fi nan gare
su jima wani karamin tv da wasu kujeru na raini da suka saka maki a daki don Allah.
Yar su da suka aurar haka kikaga sunyi mata ke baki tunanen haka da bakin ki ke fada min
irin tsaruwan dakin hajara yadda suka gyara mata dakin.
Kasa magana nayi sai tsayjn danayi galala ina kallon shi don yau na tabbatar mutum bai da
kunya shi da ko pant ya kasa saya ya kawo min a matsayina na wace zai aura da kowa nasa ya
kasa yi mai wani abin azo a gani a matsayin shi na dan su.
Sannan iyayyena sunyi min abin arziki zai zo ya rena mamakon ya yaba da kokarin su a kaina
da yake dan duniya ne sai yace koda yake ke har yanzun baki san komai ba ai.
Don wallahi wanda suka sayar da gidan mahaifin ki a abuja ya fadi inda ba a karya kudin da
aka sai wanan gidan naku zai iya sai maku ukun wanan ma don girman gidan mahaifin naku.
Kuma kin san gida a abuja tsadane dashi nina dauka ya aje sauran kudin ne ai don laluran ku
kawai wallahi nan hankalina ya daga sai dai ina tuna zancen baba kabir akan maganan baba na
bashin da banki ke binshi sai nace niko ina ganin baba kabiru ba zai muna haka ba gaskiya.
Ya bata rai sosai yana fadin ke may kika sani don Allah an barku a duhu ana cutan ku ya ja
tsuki yana cire tufafin dake jikin shi fuska a daure.
Idan akwai abinda naki baga jamil ya daure mun fuskan shi shima yasan da hakan yaune
daren auren mu dashi duk da ba farkon kasancewar mu tare ke nan ba.
Amma sai na koma fadin sun cuci kansu wallahi don mu basu cuce mu ba don amana muke a
gare su dan uwansu ya haifa ya bar masu amana duk abinda sukayi mun barsu ga Allah.
Wanan maganan da nayi yasa ya dan sassauta daure fuskan dayayi da farko don ya fara
shawo kaina ke nan don duk takona ya sani kamar yunwar cikin shi.
Mun raya dare mu kamar na sauran ango da amarya sai dai da safe kuma ya tashi yana cika
yana batsewa duk a kan maganan dai dakin baiyi mashi ba.
Ban fito ba sai da gari ya dan haska zuwa gaida iyayyen shi dake cikin gidan inda na zube
daga kofan su ina gaida su da kwana ban san jamil yana dakin zaune ba tare da mahaifi nasa.
Jin muryana mahaifin nasa yace in shigo daga ciki yana fadin ashe kuma haka mayaudaran
ubannen ki sukai maki ya tabbata ke nan sun cinye maku gadon ku ko ?
Nace baba basu cinye ba har yanzu kudin bai fito bane na baba yace sunciye mana waye bai
san wanan maganan ba ya ta.
Yanzun dai kuyi hakkuri da dan abinda suka kawo maku din tunda kin shigo cikin mu komai
zaizo da sauki don ba zamu saka ido muga ana cutan ku ba haka ai.
Nayi maki alkawarin zamu tsaya maki akan komai dake da yan uwan ki muddin muka samay
ki a yadda muke son ki mai biyayya a gare mu.
Nace insha Allahu baba mun gode yadai dan muna fadan zama tare da nusar dani akan
saurin yarda da iyayyen nawa da nakeyi.
Nayi godiya na bar sashen nasu don tsakanin mu dasu ba wani nisa bane kusan ma dakunan
a hade suke sauran yan hayan da ba a tayar ba suna a dayan bangeren su uku.
Ya ganin amarya suna ta zuwa daga gidan mu wasu kuma suna zuwa yi min sallama don
komawa gidajen su an bude dayan buhun shimkafan da iyayyenba suka kawo na gara a gidan
suna dafa ma yan uwan su da suka zo gurin buki.
Sai dai abinda ke ban mamaki duk wanda yazo yana yaba kyawon dakin nawa in ka debe
daidaikun yan uwan jamil dake tabe bakin su.
Dangin mahaifiyar shi da suka zo buki a wurin su nake jin ashe su suka zo da turamay nan da
aka kai gidan mu ke nan, nan iyayyen shi su basu kashe mai komai ba kenan.
Ranan dai wuni nayi ina taron baki a gidan sai dai yakan shigo jefi jefi yana wani cika yana
batsewa na rasa gane kan shi a gidan ga baki daya.
Zaman sati dayan da mukayi kullun a cikin korafi yake akan shi shirin dakin bai mai ba har dai
na hakkura na tambaye shi yanzu yaya kake son ayi ke nan yace yanzun kikai magana dai.
Abinda nake so shine mu sayar da wanan kayan a sai wasu wanda ya dace damu a dakin ina
ganin haka zaifi bada ma,ana sosai nace kana ganin haka zai yuyu tun ban kai wata daya da
aure ba ace na sayar da kayan dakina.
Baka ganin zasu ga na rena da abinda sukai min a baya yin hakan zai kawo wani rigima a
tsakanin mu nan gaba a hasale ya furta ina ruwan su dake yanzu ina sun sauke nauyin su da
ke kansu suke gani da wanan abin da sukai maki suna ganin burgewa ne a gurin su.
Yanzu muke da ikon ki basu ba don nauyin ki ya dawo gare mu ke nan ba ruwan su da abinda
zamuyi maki anan kuma yanzu.
Nace to shike nan yace da kaina zan kai kayan nan can kauyen mahaifiyana a sayar muna
dashi muzo mu cika kudi a sai maki na zamani wanda ake yayi.
Nace idan kana ganin haka zaifi a kai a sayar din na kuma gode da kaunar da kake mun din
dani da yan uwa na ya saki wani shu,umin murmushi a fuskan shi.
Bai bar dakin ba nan ya zauna muna hiran yan uwan mahaifina na zage ina fadin karya da
gaskiya ga irin rikon da suke muna a gidan baba kabiru din.
Yana ta faman zugani ina hawa ina ganin gaskiya yake fada min don banda masoyi bayan shi
a duniyan nan kaf baki daya.
Washe gari ya bude kofan falona ta baya ashe tare da motar daukan kaya yake ina ji ina gani
Jamil da wasu mutane suka kwashe kayan falon nan kaf suka fice dashi a gidan.
Sai da yai kwana biyu bai dawo ba a cikin kwana na uku ne ya dawo garin fuska a daure ya
shigo min ina jin muryan shi yana gaisawa da iyayyen shi bayan ya gama dasu ne ya shigo
yana kara sha min kanshi.
Ba daman in tambaye shi zancen kayan don banga fuskan haka ba a gurin shi abinda ban
sani ba ashe ya fita yaje gidan wata dillaliya ya juye mata kayan ta bashi kudin shi ya biya
bashin da ake bin shi na party bikin daya hada sai sutura na alfarma da turararuka daya kara
saye. Sauran kuma ya hole da yan matan shi sai da kudin suka kare ya dawo gidan a lokacin shine
yake cika yana batewa don kada inga fuska shi in tambaye shi yadda akayi da kudin kayan.
Sai da yaga ban tambaye shi zancen kayan ba wanda ni a zahiri tsoron haka nake ji yasa ban
tambaye shi ba amma zancen kaya yana a raina.
Don ina jin kunyan mutane suna shigowa suna ganin dakin haka ba komai a cikin sa alhalin
kowa gari yasan amin kayan daki na alfarma.
Matsalan farko dana fara fuskanta shine akan ibada sam Jamil baya sallah ko wani iri da safe
sai sha dayan rana zai tashi daga barcin jiya da muka kwanta yayi wanka ya shirya ba
maganan yin sallah.
Idan nayi mai magana sai ya hauni da fada yana fadin kin san ni bansan Allah ba sai kin koya
min may zaki nuna min akan addini kin dai san na fiki sanin hakan.
Ni da na tashi a gida cikin hausawa yan uwana kuma musulmai na san Al,Qurani nasan hadisi
don haka bake zaki nuna min yin sallah ba inda yake shiga ba nan yake fita ba.
Ni dai na samu gefen gado nayi tagumi ina kallon shi sai ruwan bala,i yake min kan kawai
nace dashi ya tashi rana nayi yayi sallah.
Har ta gaji ya mike ya dauki buta ya kurkure bakin sa ya dawo yana tambayana idan na gama
abin karyawa in kawo mashi fita zaiyi.
Na mike jiki ba karfi na fita na dauko mai kayar karyawan shi da na aje mai ya zauna sai da
yayi kat ya fice daga gidan.
Mikewa nayi na kwashe kaya raina ba dadi ina tunanen maganan umma a karo na farko a
raina ashe abinda take hango min ke nan wanda na kaaa hangowa kaina shi.
Tun ba,a je ko ina ba zaman ya fara ban tsoro da Jamil don babu wani dadin auren da zance
naji wanda amare suke ji idan anyi aure a farkon aure.
Ga tsoro shi da yake kokarin cusawa a zuciyana dan abu kadan zanyi yanzu ya hauni da fada
na fitan arziki yana zagi iya son ranshi ni dai babu zancen wani amarci a gurina sam.
Iyayyen shi kuma da muke zama dasu da akace wai zasu zauna ne don barin iya mu yara a
gidan baiyi ba shine suka ga dacewan zaman mu tare dasu din.
Ni dai banga wani amfanin su ba a gidan asalima kamar tsoron dan nasu suma suke ji don har
su yakewa wanan tsare gidan nashi da yake min sai dan jefi jefi zakaji yana hira da mahaifin
nasa.
Ko idan yana min fada mahaifin nasa ya karbe ya goyi bayan dan nasa kirikiri yana fadin nice
banda gaskiya banda mutunci.
Sai dai idan sunga yana cikin dadin rai da nine nake samun sakewa dasu a gidan har zamu
dan zauna muyi hira da matan amaryan baban nasa da muke zaune a tare.
Duk wanan baya damu na nidai buri na inga munyi zaman lafiya a tsakanin mu dashi kamar
na sauran ma,aurata don sam banda wani walwala balle har in dan fara cikan daki da akeyi
idan anyi aure.
Ranan da yan gidan mu suka zo gani na na rasa yadda zanyi akan rashin kayan dakin da
babu dakina wanda akai min daga gida da Jamil ya sayar din.
Suna shiga dakin maganan farko da sukai min shine anty hadiza ina kayan dakin ki nace ku
zauna mana in fada maku komai a tsanake.
Zama sukayi suna saurarona don jin abinda zance din bayan sun zauna ne muka gaisa nake
fada masu sai da aka jera min kayan naga basu min kyau ba na bayar a hurhura min ne za a
kawo min wani sati in Allah ya yarda.
Badon sun yarda da magana ta ba don yarda naga suna min wani irin kallon na tuhuma a
ransu sai da mukai hirane zasu tafi nake rokon su akan don Allah su rufa min asiri kada su fada
a gida sai idan an kawo min kayan zanje in fada a gida.
Sukai min alkawarin ba zasu fadi ba kuma hakan ne don naji shiru ya tabbatar min da basu
fadi din ba a gida don banga kowa yazo min da maganan ba.
Jin shirun yayi yawa ne kan kayan yasa ranan na tambaye shi labarin kayan fada ya fara yi
abinda yasan ban so ke nan fada yana fadin idan ta ban ai zan kawo maki tunda kin nuna min
banda iko a kan abinki yanzu.
Da har zaki bude baki kina tambayana kayan ki kamar wanda baki yarda dashi ba ya fice yana
fada kamar yadda ya saba yi idan zaiyi yaudaran nasa a gurina.
Tun ranan da nai maganan kayan ya shiga fushi dani sai ya shigo fuska a murtuke yayi
abinda zaiyi a dakin ya fice daga gidan idan ya gama.
Da abin ya ishe gani ban iya gaba ba a rayuwana ranan dai na kudirta a raina zan mashi
magana idan yashigo gidan don mu fahinci juna dashi.
Dama ni tsoro na kada yan gidan mu su sanda wanan zancen a dauki mataki a kaina shine
kawai damuwa na a lokacin.
Can cikin dare ina barci ya shigo dakin ina jin motsin shi na bude idanuwa ina kallon shi filo ya
dauka ba tare da yai min magana ba zai nufi falo dashi da sauran abinda yake bukata a