Kanin Ajali Complete by Zeey Makawa

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Read Hausa Novels

Chapter   16 / 37

45K to 48K   out of 109.3K words

Jamil yayi min.
Nan dai aka kirashi akai mai fada sosai aka shirya mu ba tare da gida sun sani ba ya kuma ce
ba tare dani zai koma ba sai dai idan ya koma da kwana biyu in koma.
Hakan akayi ko da na dawo ina shan kamshi dashi kan sakin dayai min din ko may ya gani ya
sauko da kan shi ya bar fushin da yake yi din dani.
Ashe abinda ban sani ba bayan tafiyana Jamil mata yake daukowa ya kwana dasu har dakina
ya bude ta baya inda iyayyen shi basu ganin abinda yakeyi don muna da kofan baya a cikin
falon mu ba lalai ne su san abinda yakeyi a gidan ba.
Kanne na duk sun san wanan labarin suna kallo na ne kawai an rasa wanda zai iya fada min
don gudun tashin hankali sai dai su basu sani ba aikin gama ya gama ko in ma har saki suke
gudu a gare ni.
Don haushin cewa da nayi zan koma gida yasa shi ya sake ni a kauye don zan bata mai jin
dadin shi da yake a nan din.
Jamil yakai dan duniya sosai don har abokiyar ta gwaicin yar hayan gidan mu ashe wata yar
duniya ita batai aure ba kamar yar uwarta ya samu suna shedan cin su a dakina da ita.
Na dawo ina hura hanci wai ni ga mai miji suna kallona sara mai bisa ruwa duk da dawowan
nawa bai rage shi da komai ba don sai ya raba dare a waje suna iya shegen su can da ita wai
shi auren ta zaiyi a cewar shi kuji fa yan uwa.
Na dawo ban dade ba Allah ya ban ciki dama a can kauye nasha maganin gargajiya na mara
wai mara ne ke damuna sukace wai shiyasa har lokacin aure da shekara ban samu haihuwa ba.
A fili ya nuna min farin cikin shi na samun cikin da mukayi sai dai a can kasan zuciyar shi ba
haka yaso ba don yace shi bai shirya ma haihuwa ba yanzu.
Daga yin aure ace wai an fara samun ciki mafarin a tara iyali ke nan da wuri tun muna da
kurciyar mu ke nan zamu fara tara iyali.
Nikan dadin samun cikin nakeyi sai faman planning nakeyi ni da yan uwa na dake tayani
murna na gaskiya kan cikin da na samu din a yanzu.
Lokacin da kanwata Saadatu ta samu ciki ta kusa haihuwa ta danyi tanadin ta takai gida don
taimakawa iyayyen mu dashi duk da baba yayi fadan haka yace ta bar shi tayi laluran gaban ta
ai itaka tana da hidimar da zatayi na kawayen ta.
Sai dai ni ba wani labari kan hakan don ban aje ba ban ba wani ajiya ba ko turmin zanin da
baba kabiru ya aiko min dashi da sallah yaso ya lalashe ni ya karbe sai dana nuna mashi hakan
ba mai yuyuwa bane don tare da sauran yan uwana dake aure baba din ya saya muna kayan .
Dole yana kallon abin kudi a wurina ya kyale ni ba yadda zaiyi yayi fushin shi ya gaji har ya
sake don yasan na fishi gaskiya a kan zancen zanin.
Iskanci ko yanzu baijin kunya a gabana zai dinga waya da yan mata suna hira da farko naso in
sa mashi ido sai naga zanja wa kaina damuwa gurin kyale hakan.
Ranan ina zaune wata ta kirashi ya dauka sun fara fira ke nan na wauce wayan daga hannun

shi na fara dura mata ashar cikin dakiyar fuska ya dauka zanji tsoron shi dana saba ji ne ya fara
daka min tsawa akan in bashi wayan har yana fadin you very stupid ki ban wayana nace.
Nima tsawa ba daka mai take na birkice mashi a dakin yana gudun iyayyen shi suji ko daya
daga cikin yan hayan mu suji.
Girman shi ya zube a gurin su don idan zai shigo gida sai ya daure fuska kamar hadarin
marance fuska ba annuri ko kadan.
Zakace shine maigidan da muke cikin sa yadda yake basu doka da iko a gidan nasan badon
baba yasa yan hayan ba da zai iya koran su ma.
Ganin da gaske ina shirin tona mai asiri yasa ya sauko yana fadi amma ke baki da wayau
dafa budurwan yayana sa,idu nake waya kin dauka ko budurwa tace.
Da yake wawiya nake sai na yarda da maganan shi na miko mai wayan yayi saurin kashewa
ya kuta ya fita daga dakin bai dawo gida ba sai da dare ya raba sosai ya dawo.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:56 PM - 🤔🤔🤔: ZIM


Ina zaune ina kare mai kallo yana shirin fita da yamma don duk yamma haka yake wanan
al,adan ya tsala ado a jikin shi ga kamshin turare mai tsada yana tashi.
Sai daya gama shirin shi yana batun fita nace gida nake son zuwa in duba su yau kamar baiji
abinda na fada ba ya kara dauko kwalban turaren shi ya kara fesa ma jikin shi yadda yake so.
Bakajini bane na fadi daga inda nake zaune ina kallon shi cikin tagumi yace najiki mana sai dai
ban san abinda zaki je yi gidan bane.
Zuwa zanyi in gaida su kawai don nasan in ka fita ba lalai ne ka dawo da wuri ba yace ni na
rasa ma may zance maki hadiza .
Wai da kike dadin zaki ki duba su ina ko dazun naga shigowan Baffa gidan nan shekaran jiya
kuma summaiya sun zo nan gurin ki.
Nace su kadai ne a gidan halan yace ke kika damu dasu su basu damu dake ba ni dai da zaki
bi shawarana ki hade kan uan uwanki kuzama tsintsiya daya madaurin ku daya ku hudu da zai
fi maki alheri.
Nace ban gane may kake nufi ba har yanzu yace eh bazaki gane ba muddin baki kwantar da
hankalin ki yanzu kin fahinci magana na ba.
Don yawan zuwa gidan nan da kike yi ko wani lokaci yana daya daga cikin daman da zasu
samu su cinye maku kudin ku idan ya fito nan gaba.
Wani kallo na watsa mashi tare da fadin kudin ina baba kabiru ne mai muna fafutukan fito
dashi yace ko yanayi ai da wata manufa yake yin su don shima ya debi rabon shi daga ciki.
Kara mai kallon mamaki nayi don jin furucin shi akan baba kabiru din yace yes waye bai san
da dukiyan ku yake tunkaho ba a garin nan.
Sai ku da har gobe baku wayau da zaku gane hakan sai idan sun gama maku barna zaki
dawo kina fadin dama na fada maki kinki ji a baya.

Ni fa ban fahinci inda maganan nan naka ya dosa ba har yanzu zama yayi a kusa dani don ya
fahinci banda saurin zurmawa idan ya tsarani da magana.
Yace ni abinda naga yafi maku shine kiyi kokari ku hade kai da yan uwan ki tun yanzu ta inda
bakin ku zaizo daya a kasa gane tsakanin ku.
Nace ai muna hakan ko yanzu wani shu,umin kallo yayi min tare da fadin ke har yanzu dai
yarinya ce hadiza ana gabas kina yamma ni zan fita idan na samu lokaci zan maki bayani a
tsanake.
Daga haka yasa takalman shi ya fita kallon inda yaci abinci nayi naga ledan kazan daya shigo
dashi da rana yaci yashe saman dan table din da muke cin abinci a falon namu.
Naja tsuki tare da mikewa ina duba ledan kazan na samu ya rage dan guntu a ciki zama nayi
na karasa cinye sauran tare da sude kasusuwan da bai karasa cinye tsokan su ba na gama na
kwashe kayan na fita dasu.
Gyaran daki nayi na fita gurin girki na don kada yamma yayi min don nasa a raina yau zan
shiga gidan mu da dare.
Da sallama na na shiga gidan namu inda na samu yan gidan mu a dakunan su suna kallo da
murnan ganina kowa ya tare ni muka shiga gaisawa dasu.
Sai da nabi da kunan matan baba na gaidasu na dawo dakin yan matan gidan mu na zauna
muna hira sai tsokanana sukeyi wai ciki yasani muni.
Anty ne ta shigo dakin ta zauna don ganina a cikin dakin tana fadin wai ke haka zaki haihu
daki ba komai a cikin sa har yanzu hadiza.
Ko kun gyara dakin naku ne yanzu muzo musha kallo mu kan tana fadi a cikin zolayata don
takanyi wasa damu wani lokaci.
Fadin haka yasa kanwata fadin wanan shegen macuci ai itace ya samu har ta yarda da hakan
idan da nice wallahi sai ya fito min da kudin kayana wallahi.
Take na daure fuska don jin ashar din data dura ma Jamil dina alhalin yanzu ya gama
maganan alheri a kan mu.
Sai anty ne tace kuna zagar mata miji a gaban ta yanzu kuna samun sabani a gidan nan
bandai sake fuska ba har lokacin har ta gama dan hiran da mukeyi sama sama da ita a dakin ta
fita.
Can takira yarta dake dakin tare damu tayi mata wani abu lokacin na samu fadin yanzun ke da
kanki kikewa Jamil haka idan wani yai min ashe ba zakiji haushin sa ba summaiya.
Tace wallahi halin mijin nan naki yana ban haushi anty dubi yarda kika koma don Allah kamar
wata bakauya dake don babu mai kallon ki ya dauka wai kin yi karatun boko.
Nace to ki matsa kowa bada yadda Allah ke masa tsarin rayuwan sa ba ko kin naso ne in
dawo wanan gidan ne kuma mu kama ganin laifin juna daku.
Nan dai na nuna mata bacin raina akan abinda tayi min din har sai da ta bani hakkuri na sauka
nace da ita ta samu lokaci ina son ganin ta ita kadai idan zata zo kuma ta zare jiki tazo ita kadai
tace min taji.
Ina shirin komawa baba ya dawo do yayi tafi ashe kwana biyu bai gidan yana dawowa muka
fita muka gaida shi yake fadin a,a hadiza kin shigo ne ?
To ya kuke ya mijin naki na amsa da suna lafiya suna gaida ku baba yace lafiya dai ko nace
lafiya baba na daizo gaida ku ne kwana biyu ban shigo ba na duba ku.
Yace cikin nuna jin dadin shi ga hakan mun ko gode naji dadin hakan sosai adaita hakkuri don

Allah komai na duniya sai da hakkuri ake cin riba nace na gode baba daga inda nake tsugune.
Har na mike ya sake fadin ina ganin kwanan nan zancen kudin ku zai tashi don munyi magana
da wanan mutumin dake muna hanya kudin su fito a cikin jin dadi nace Allah ya nufa baba na
kara mai godiya.
Na fito ban dade kwarai ba don daren da yayi na yi masu sallama na nufi gida sai da yan gidan
mu suka rakani har gida muna hira suka juya suka dawo gida.
Har lokacin na sami Jamil bai dawo gida ba nima ban sa rai da zai dawo haka da wuri ba don
sai dare yayi sosai yake shigowa gidan.
Washe gari ya gama barcin shi karfe goma da wasu mintina ya bukaci ruwan wanka na kai
mashi bandaki kafin ya fito na aje mai abin karyawan shi ko a inda na saba aje mai ina gyaran
gida ne ya kwala min kira.
Nazo yake fadin wa zai sha maki kunu haka babu sugar ko kosai nace yau baba bai sawo
muna kosai bane kuma sugar ya kare tun jiya na fada maka.
Ya ja tsaki tare da rufe kwanon kunun ya dan mayar da kan shi saman kujera fuska a daure
nace jiya naje gida baba yana gaida kai ya mace wai kudin mu ya kusa fitowa.
Wani irun dagowa yayi daga yadda yake kwance yana fadin saboda Allah nace wallahi ko jiya
baba yake fada mi hakan da naje yace ashe mun kusa warkewa ke nan nace insha Allahu.
Nan ya fara sake min hira a ciki sakin fuska inda yake shiga ba nan yake fita ba jin dadin hira
yau yasa na sako mai zancen da anty tayi min.
Take ya bata rai ya fara fada yana fadin ina ruwan ta da rayuwan mu ne nifa kwata kwata
wanan matar batai min ba a rayuwana nasan duk wani cin amana da baba keyi da zuginta ne
yakeyin shi.
Nace niko banga hakan ba gaskiya don bata saka kanta a cikin maganan mu yace ke may
kika sani so take kowa ya koma yadda take wai ita ta waye din nan .
Ranan kan hirane zamzam dashi ba wani nuna bacin rai a tare dashi fitan da baiyi ba ke nan
har mahaifin shi yana tambaya ko lafiya yake gida har yanzu.
Yace lafiya yana dai hutawa ne a gida yau tun wanan ranan muke zamzam dashi kanwata
tazo na danyi mata nasiha kamar yadda Jamil din ya lurar da mu muyi din.
Bata ki ba sai dai cewan da tayi amma kada mu nuna yadda har za a fahince mu a gida tun
daga wanan ranan muka dinke tam dani da yan uwana da muka fito ciki daya.
Babu mai gane jan mu komai namu a hade mukeyin sa a gidan ga summaiya Allah ya dora
ma anty sonta a rayuwan ta komai ta samu ko zatayi sai tace summaiya dai har yan uwanta
suna sata gaba akan hakan da take nuna ma diyan cikin ta bata damu dasu ba sam.
Bayan kamar sati uku dayaji shiru shi da kansa yace mu shirya muje mu gaida mutanen gidan
namu nayi mamakin haka sai dai naja bakina nayi shiru tunda gidan mu zamu tafi.
Mun samu baba a gidan ya tare mu a cikin fara,an nan nasa suka dan taba hira da Jamil din
ina gefe ina jin su sai dan zungura na Jamil keyi akan inyi maganan kudin mu mana a gurin
baba don ya gama kitsa min abinda zance tun a gida gamay da kudin da mukaji shiru.
Can nace baba har yanzu dai wanan mutumin bai kira ba ko cikin mamakin wani mutumi nake
nufi baba ya tambaye ni nace wanan mutumin da zancen kudin mu ke gurin shi baba.
Baba yace wallahi har yanzu banji wani abu a guri sa ba amma dai barin kira shi muji yanzu
komay ake ciki akan zancen nan ya daga waya tana ringing gab da ta katse ya dauka.
Suka gaisa a cikin harshen turanci suke magana baba yace yaji shiru yace eh kasan abin da

wuya amma dai insha Allahu ana sa ran fitowan shi a cikin wanan shekara din sai dai kasan ba
duka yake fitowa ba za a kasa shi kamar kashi uku ne haka.
Baba yace haka abin yake yace yadda tsarin namu yake ke nan ai dama sukayi sallama
bayan baba yayi mashi godiya ya katse layin tare da dubo mu yace kunji ko.
Abin sai kaman za a kama sai kuma aji shiru duk dai wani abinda suka bukata na riga dana
gabatar masu dashi ko akan takardan nashi.
Ya kare da fadin Allah dai ya jikan wani yai masa rahama muka ce amin don ni nama manta
rabon da inwa mahaifina addua irin haka yanzu idan ba raina ne ya baci zan tuna dasu ba.
Nan dai mukai wa baba sallama muka fito tare da yiwa sauran mutanen gida sallama ganin
tare da shi muke yasa yau ban samu rakiyan yan gidan namu ba har gida.
Tsuki yai ta ja har muka kawo gida yana dura ma wanda bai sani ba zagi wai sallon suci
kudine yasa suka rike kudin har wanan lokacin ace mutum ya mutu har kusan shekara biyar
kudin shi bai fito ba.
Ni dai ina jin sa sai jefi jefi nake saka mai baki a zancen nasa sai kawai kwana biyu angulu ta
koma gidan ta na tsamiya ya tayar da halin shi na yawon dare da yakeyi sosai.
Nan dai nayi ta zaman hakkuri ban faye damuwa da halinsa ba sosai a cikin haka maganan
kanwata da wanan mai nemanta usman magana tayi karfi sosai akai masu baiko a tsakanin su.
Don yafi jamil dina hali ta ko ina bama za a hadasu ba kuma ya dan girmay ma Jamil din ga
shekaru shi karatun shi yasa ma gaba sosai don gidan su suna karatu har nisa .
Ba irin Jamil ba da yasa karyan duniya a gaba kuma a haka nake son abina kamar in hade shi
ba dama wani dan gidan mu ya fadi maganan shi a gaba na koda kuwa mahaifan mu ne.
Sai dadin hira yasa na kwashe na fada mashi abinda kace mai wani fa mai miji don a yadda
mukai alkawari a tsakanin mu sai nake ganin ni kadai zai zauna dani har tsufa

16 / 37