Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
daga cikin kason
mu din.
Amma sun ce wai wayau suke muna kawai don sun dauke mu yara kanana suna yi muna
yadda sukaga dama da hakkin mu .
Muko mun hau munga ga masoyan mu na asali masu kaunar mu da zuciya daya don Jamil
yana cewa.
Da ke nan da baisan ciwon kan shi ba suke cinye kudin ba abin kwarai da mukeyi dashi
yanzun kan tanadi sosai za a yi muna gaskiya.
Fadin haka da yakeyi yasa na kara yarda dashi sosai don na dauka talaucin da muke ciki yasa
yanzu yayi hankali ne.
Mun dauka wani sati kudin zai fito a yadda aka nuna muna a can da mukaje abuja sai gashi
shiru har mako uku ya share ba wani labari kuma na kudin .
Nan dai ya shiga kuma sake magana yana fadin kila ma su baba ne da sherin su kudin an
sako basu fada muna ba kai ba dai abinda bai fadi kan kudin.
Har turani gida yayi in koma in tambayi baba cewa munji shiru baba dai yayi dariya yace
hadiza banda abinki ko wancan karon ai haka akayi ko ?
Sai lokacin da muka ji su kin san gwaunati ba ayi mata dole tunda ba abin mutum daya bane
abu ne na taro kowa dake cikin system din jira yake yi kamar mu.
Na dawo gida na fada mai abinda baba yace ya ja tsuki don takaicin da yake ji a lokacin yana
fadin wanan shegen gwaunatin basu da tausayi wallahi.
Yakan yi maganan kudin nan kusan sau uku ko hudu a wuni shi dai ina ganin lokacin
damuwan shi bai wuce yaji ance kudi sun shigo muna ba shine nasa.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU.
5/18/21, 11:57 PM - í ¾í´”í ¾í´”í ¾í´”: Ranan dai ban iya aikata komai ba a gidan ko abinci ban dafa ba
duk jikina ya mutu ina jiran shigowan jamil din gidan inji inda kayana suke.
Wanda nasaye da hakkina na rufa mai asiri dashi na dawo yanzu ban samay su dakin ba
kuma ai dole hankalina ya tashi sosai fiye da tsamani.
Kamar yasan ina jiran shi sai ranan kuma bai shigo gida da wuri ba sai can cikin dare sosai ya
dawo lokacin har barci ya fara sata na a inda nake zaune a falo.
Jin karan bude kofan shi na mike zubur dani yace may ye haka ban bari ya rufe baki ba nace
Jamil ina kayana suke don babu komai a cikin akwatunan ga baki daya dana bude.
Yace cikin dakewa wasu kaya kuma nace kayan sunana da muka saye yace suna ciki mana
ina ruwana da kayan ki tunda muka saya.
Nace abar maganan wasa ina kayana suke yace wai bai sani ba yana kokarin shigewa daki
na mike da sauri nasha gaban shi ido rufe na kara tambayan shi.
Yace wai kina haukane ko may ko kin mai dani barawo ne da zaki tsare ni kina tambayana
kayan ki ko kinga ina zama a gidan ne ni ?
Hannu na dora a kai na fara zunduma mashi ihu a dakin ina fadin wallahi ban yarda ba don
babu wanda zai shigo min daki bai bar alama ba.
Ganin zan tayar da mutane gidan yasa yace ki bari zan maki bayani da safe don Allah yana
fadin haka ya shige daki ya kwanta abinshi .
Haka na kwana ina juyi duk tunane ya hanani barcin kirki washe gari ma da wuri na tashi don
kada barci ya dauke ni ya gudu.
Ina cikin aiki ya fito na bar abinda nakeyi nace Jamil ina sauraren ka yayi kamar bai jini ba
yana kokarin ficewa dakin.
Nayi sauylrin tarewa ina fadin wallahi ba inda zaka sai ka fada min ko inyi karan ka ya wani
juyowa yana fadin ni zakiyi kara akan kayan ki hadiza ?
Nace wallahi kuwa idan baka fada min inda kakai min kayana ba yau a gidan nan ganin da
gaske nakeyi yasa shi fadin suna wurin dinki.
Cikin zaro ido nace duka kake nufin kakai dinki turmi talatin da wani abu , yace bake kika ce
a dinka ba shiyasa na kai dinki duka.
Wani wawan ajiyan zuciya na sauke ina fadi yanzun naji magana dai sai dai har yanzu
zuciyana bai yarda cewa duka kakai din ki ba gaskiya.
Yace yanzu dai na gane abin hannun ki ya fara rufe maki ido da har kike son tayar min da
hankali akan zanuwan banza naki ki jawo min mutane.
Nace ai dole don kudin nan kaima kasan ban ci komai a cikin su ba don may ko ba zan tayar
da hankalina ba akan su.
Kowa ya sai abin kwarai da kudin shi sai nice zan banzatar da kudina a sakani a baki gashi
dama mutane na fadin nice banda arziki cikin mu da an bani kudi ka cinye.
Yace inji uban wa ke fadin haka ya wani gayayyako ni yana fadan karya har ya samu ya fice
daga gidan dama abinda yake so ke nan ya samu hanya ya sulale ya fice.
Ashe shi wayau shi daya kwashe kayan ace sata aka shigo akai min da bana nan shine hikima
shi na turani gidan su in yi kwanaki acan.
Sai kuma wani abinda ban sani ba mai ban mamaki da daure kai da lamarin Jamil shine ashe
wai hayan kaya nan sukayo dashi da Ruth a shago.
Sukayi alkawarin zai dawo masu dashi da zaran an gama suna danawa da na baby din ga
baki daya har akwatinan gaba daya na hayane.
To ina yakai min kudin da ya karbe a hannu na din daya karba wanda yasa na sayar da filin
mu a wani gari daya matsa muna sai da muka sayar.
Duk abinda nakeyi yin shi kawai nakeyi hankalina bai kwanta da zancen kayan ba don tun
ranan da mukai maganan ya shiga wani tsare gida yana daure fuskan shi gare ni.
Kyale shi nayi sau da aka cika sati biyu na kara tuntubanshi kan zancen dinki yace yaji kawai
ya fita bayan kwana biyu mm a sake tambayan shi kuma.
Ranan dai fada mukayi dashi sosai kan kayan inda nasha kuka na sosai don na fahinci babu
dai kayan kwana kwana kawai yake min kan kayan.
Washe gari tun da safe na shirya sai gidan mu gurin iyayyena inda na samu dama irin ranan
da suke jira gare ni ke nan yazo.
Sai da suka gama saurare na suka dora a inda na tsaya baba bai gida a lokacin sai da ya
dawo ne anty ke fada mashi ina nan na zo gida mun samu rikici da Jamil.
Yasa a kirani nazo ina kuka nake fada mai komai har na gama murmushi baba yayi tare da
fadin ni dama ban shirya ma zuwan irin ranan nan bane a rayuwana.
Ko ban san wanda na nace sai na aura din bane wai dama sin san abinda zai je ya dawo ke
nan sai dai a lokacin da suke kokarin nuna min hakan ganin su nake a matsayin makiyana a
gare ni.
Ina kuka nace baba nayi nadaman auren Jamil a rayuwana don ya gama dani gaba daya a
rayuwana wallahi.
Baba yace hakuri zanyi in koma don ga zuria a tsakanin mu yanzu sai dai in koma inyi hakuri
da halin mijina don su ba zasu taba kashe min aure ba in dawo ina kuka dasu daga baya.
Naji haushin wanan maganan na baba gaskiya sai nake ganin don mahaifan mu basu da rai
ne sukai min hakan.
Kwanana uku a gida kafin Jamil yazo da yannan shi maza inda suja samu baba ya aika a
kirani da su anty muka samay su a falon shi.
Baba ya bukaci in fadi magana na nan dai na shiga jero magana yan uwan shi sai assha suke
fadi tare da fadin su basu san komai ba a kan wanan abinda na fadi jamil din yana min.
Ranan dai ya jishi ba dadi do a gurin yaso yai ma anty da ta zake tana kokarin kwatar min
incina a gurin shi don shi baba yana sakaya wani abu don shima nashi ne.
Nan dai anty tayi mashi tas ta zage shi sosai saida ya raina kan shi sosai a lokacin suka dai ba
da hakkuri tace zai karbo dinkin idan tellan daya kaiwa ya dawo.
Aka ba da hakkuri ban koma ranan ba sai washe gari inda anty ta saka ai min kitson kaina da
kumshi ta bani kaya masu yawa .
Irin su zanuwan gada da kayan aiki da tufafi masu yawa da dare suka mayar dani dakina mun
samu bai gidan har suka tafi bai dawo ba.
Sai dare can ya dawo bai kwanta ba yai min dadin bakin shi daya iya yana fadin ya dauka ni
mai rufa mai asiri ne ba zanje gidan mu da wanan maganan ba.
Lokacin ne yake ban hakkuri kan kayan nan dai babu su inyi hakkuri idan ya samu hali zai
saya min wasu da yardan Allah ya kare cikin dadin baki da bani hakkuri.
Haka na hakkura na shanye zancen kayan a raina na dogara ga dan albashin dake zuwa min
wanda yanzu munyi wata uku ba a bamu ko sisi ba na aikin mu.
Haka nake ta faman kama kama ina juya rayuwa a yadda yazo mi din sai daga baya nake jin
gaskiyan maganan a makwabtan mu .
Wurin wanan kawar tawa take fada min yadda zancen yake inda take fada min itama a gidan
da taje kitso don kawar matar ce bata san suna tare ba take bata labari na.
Inda take fadin maza suna cuta wallahi don abinda akai min din ko da bata sanni ba na bata
tausayi sosai raina naji ya baci sosai kafin ta gama bani labarin a gidan ta.
Inda nayi mata sallama na fito ban zamay ko don ko gida ban shiga ba sai gidan da mahaifin
shi yake na samay su da kuka ina fada masu abinda naji a gari dan su yayi min don ni yanzu
kunyan in koma gida da wanan maganan nakeji.
Budan bakin mahaifin nasa sai fafin yayi ina da aiki idan zanyi amfani da jita jita a rayuwana su
masu fadin haka kyashine da hassadan dan shi yasa suke kulla mai sheri.
Don kawai su bata wa dan baidai goyi bayana ta ko ina na fito sai ya tare dan nasa ya kare
shi haka na taso da bacin raina na dawo gida naci kuka na ba wanda zan fada ma wanan
zancen na takaici ya saurare ni.
Haka ya dawo gida ya samay ni yana wani cika yana batsewa don ma kada inga fuskan yi
mai magana ban kula yadda ya dawo min ba.
Na shiga fada mai duk wani kalma daya zo min a baki akan indan har maganan dabaji gaskiya
ne na roki Allah ya dubi maraicina ya saka min a gare shi shi da Ruth da duk wani wanda ke da
hannu a cikin cutana din da sukayi.
Ruth kan itama bai barta ba don tatsanta yake sosai yayi mata alkawarin zai aure ta idan ta
musulunta duk da kusan haihuwan shi da tayi .
Amma haka munafukin yayi mata alkawarin aure a tsakanin su take bude mai bakin aljihun ta
yake shagali shi dashi don iya yaudaran shi da karyan shi.
Da farko yaje gun Ruth ne ya tatsi banza ya gudu sai ya hadu da yar duniya dama tana neman
wanda zata kama sai ta daure shi har kafa baida daman dogon motsi ya gudu gareta.
Don ta dade da asirice shi yaje cin banza banza ta ciyo shi ga masifana a gida da nake aza
mai tunda nasan bai rabu da ruth din ba na sashi gaba da fitina.
Har ya fito fili ya nuna min ban isa in rabashi da ita ba wallahi haka muke zaune bani na samu
kaina ba dashi sai da kudin da muke bin gwaunati ya fito na wata hudu sannan ya nemi shiri
dani don yaci kudina.
Ya ko ci don nan ya kawo min kabali da ba,di bamu da kaza ya kamata mu sai kaza na
amfanin mu shi nashi bana lalurar gida bane sai nawa idan sun zo ake sakawa a gaba a cinye
anga banza.
Niko ban gane shi ba har yanzu ina dauka sona yake tsakani da Allah sai nake sakar mashi
komai idan yai min dadin bakin su na maza.
Na ramay na lalace ni ragga diyana ragga duk mun bi mun kanjamay don wahala gashi dan
aikin da nake kuri dashi an dakatar da yin shi yanzu.
Sai abin ya taru yai min yawa sosai a kaina dole naje gida wurin anty don ta taimaka min tasa
baki ga kanne na su bani dan wani abu in sai ko kura na ruwa dan kwabo ya dinga shigo min.
Da kyat da boni anty ta yarda zata sa mun baki gare su duk ko da tasan abune mai wuya a
banbare su kudin da nake so.
Amma haka ta daure zatayi masu magana idan sun shigo shikan baffa tana tun karan shi da
zancen yace ba zai bayar ba.
Sai dan karamin mu ne da anty ta titsiye yace zai bani dubu goma tace bai yi ba don Allah su
tausaya min idan basu koyi bani ba yanzu yaushe zasu koya.
Haka dai har ta ciwo kanshi yace zai bani sha biyar lokacin daidai kudin baron ke nan nayi ta
murna da ta fada min.
Inda ta zaunar da kanne na tayi masu nasiha sosai mai ratsa jiki duniya ke nan wace Jamil ya
cusa muna ra,ayi mu guje ta itace kuma yau na komawa ta taimake ni.
Ba tare da tayi duban baya ba ga komai ta tausaya wa hali da nake ciki tasa ai min wani abu
a tallafa ma rayuwana don Allah.
Baron ruwan da na saye baiyi wani tasiri ba duka duka baifi wata ba na kadar dashi na fara
sana,an kayan mata da dan kudin.
Wai ni a gani na zaifi sana,an ruwa kawo min kudi a cikin lokaci kwana biyu muka turmushe
kudin babu ko labarin su kuma.
A cikin haka ne su maman Ahmed yan hayan gidan mu suka tashi don zaman mu yaki dadi
dasu ga matsin jamil akan shi fa sai dai su bar muna gida.
Do sune ke zugani ina wani abin don shi bai kaunar yaga nayi wayau a rayuwan shi yafi son
ya gannin ko yaushe kamar wawiya yana juyani yadda yake so.
Tashin su ba a dade ba aka sa wata amarya a dakin da suka tashi ciki amaryan matar abokin
Jamil ne yasa muke kuma dan shiri da ita.
Wanda hakan yasa na dan samu sauki wasu abubuwa a gidan yanzu don yana ganin yadda
abokin nasa ke kula da matar shi.
Sai dai abinda ba halin mutum ba bai iyayin kamar kowa don bai saba yin hakan ba tun farko
ina dai zama zamana hakkuri dashi.
Shiko yana holewar shi waje da matan banza yau ma kamar kullun na tashi babu ko sisi a
hannuna ga yara na har sun fara min kukan yunwa.
Na rasa yadda zanyi dasu a daki can dai dabara ya fado min wanka nayiwa yaran babu ko
sabulu na shirya su muka nufi gidan mu dasu.
Bayan mun gaisa ake tambayana inda na fito da sanyin safiyan nan nake cewa gida ganin
yanayi na baisa sun matsa da dogon bincike a kaina ba sai abin karyawa aka gabatar min
dashi.
Na dan tsaya basarwa mama ta matsamin akan in dai karya din don ban samu anty a gida ba
lokacin tana gurin aiki sai mama ne a gida kawai.
Nan dai na fara labarta mata halin da muke ciki a gidan ina kuka tace in daina kuka nawa
kaddaran auren ke nan yazo min a haka.
Hadiza kina da hankali da ilimin ki zaki zauna kullun miji yana cutan ki kin kasa wayau ki
fahinci abinda yake nufi dake.
Fada sossi mama tayi min ban iya magana ba sai kukan da nakeyi har barci ya daukeni a
gurin ban koma gida ba anan naci na safe dana rana har anty ta dawo daga aiki ta samay ni a
gidan.
Kallo daya taimin ta gane halin da nake ciki bayan ta idar da sallah la,asar ta fito ta samay mu
nan dai ta shiga min nasiha inda duk laifin a kaina ta dora inda ta kare da fadin idan naga dama
in koma in kara bashi kudin don yanzu ba abinda ma yarage ai.
Na samu ta hada min abubuwa na koma gids na girka muna abinda zamuci da dare dani da
yaya na sai gashi ya shigo dauke da dan leda a hannun