Kanin Ajali Complete by Zeey Makawa

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Read Hausa Novels

Chapter   3 / 37

6K to 9K   out of 109.3K words

hada tayi masu gori idan bakin halin nata ya tashi.
Kowa a gari yasan halin umma da fitina don haka mutane ke kiyayan ta sai wanda Allah ya
nufa ya fada tarkon ta ranan zai sheda fitinan ta.
Tana matukar son matar baba kabiru da yaran shi duk daba wani dadin take samu ko biyaya a
gurin matar ta baba kabiru ba.
Yau mama wanki take yi don rashin lafiyan shamsiya ya hanata tayi muna wanki kwana biyu
haka yasa mama tayi ranan kare girkin ta da ta saba gamawa a cikin lokaci.
Umma na tashi daga barcin da ta dan yi na rana wanda a saman gira take yin shi don ko kaza
ta gitta ko dogon motsi ta sani balle wani yazo yana magana da mahaifiya ta sai tace gulmanta
suke yi.
Ta fito daga daki tana gyara daurin dan kwalin kanta takai duban ta gurin girkin mama din tace
wai ni ba a aiko min da abinci na bane yau ko ban samu bane don banda hakki a ciki.
Mama ta dago daga duken da take tana fadin umma ban karasa bane yau wankin kayan yaran
nan daya taru nake yi kwana biyu ban samu yin wanki ba don jikin shamsiyan.
A,a dai inji umma don dai ba uwarki nake ba yasa zaki barni da yunwa har wanan lokaci da
kinsan darajana da mutunci na ai ba zaki maida hankali gurin wankin kayan diyan ki ba ki barni
da yunwa.
Murya a sanyaye mamatace umma kiyi hakkuri iccen ne baya kamu sosai taja tsuki tace haka
kuke ai matan yanzu da shegen kiuya gurin aiki.
Kwala min kira tayi in zo in karbo mata goro wurin mai tiredan unguwar mu inda take saya sai
da tayi min kashedi tare da dangwara ta mika min kudin goron.
Illar ya jani ina fita na hadu da kawata hafsa an aketa tace in rakata idan mun dawo sai mu
sayo goron mu kaiwa umma har naso na kiya don tuna halin umma .
Sai dai jin gidan da zata yasa nace muje in rakata din don ina son zuwa gidan kanwar

mahaufiyar hafsa gida ne daya fi ko wani gida a gari kkyau gashi idan munje bamu fitowa sai ta
bamu wani abu da bazamu manta mun je gidan ba.
Mun zauna harda cin abincin mu hankali a kwance kamar ba nice masifafiyar kakan mu ta
aika ba tare da jan kunne kada in dade gurin aiken nata sai gashi duk gidajen dake
makwabtaka damu umma ta shiga nema na ance ban shigo ba.
Sai da muka gama kwadiyan mu muka tun karo gidane na tuna da zancen aiken umma
gabana ne ya fadi na lalaba aljihuna naji gudin suna nan inda na aje su kudin da aka bamu ne
na kara na sai mata goro manya guda uku na tunkaro gida da murna na.
Ina sallama ta lalayo min wani uban ashar sai da na girgiza tazo kamani na gudu ta buge baba
kabiru dake dakin shi ya fito yana asha subbanallahi umma ya akayi haka ya faru kuma.
Ta mike da kyar tana fadin banda yar banzan nan da na aika tun dazun ta sayo min goro nan
da shagon awali mai tireda ta tafi gantalin ta sai yanzu na ganta.
Juyowa yayi gare ni inda nake tsaye ina kyarma cikin sanyin murya yace hadizatul kubura ina
kika je da umma ta aike ki ne tun dazun.
Dan kwala na fara kiu,kiu da idona ina kyarma a cikin inda inda nake fadin hafsa ne tace in
rakata gidan mai kare an aike ta tana jin tsoro shine muka je tare.
Baba yace watau kice baki jin tsoron karen ko hadizatu nayi narai narai da manyan
idanuwana yace kinci abinci kai na gyada mai yayin da umna ke fadin ina fa taci tun kan
muguwar uwata ta kare muna girki na aike ta fa.
Haba umma may ye laifin saude a wanan magana don da zaki tona zuciyar saude da kinga
rashin jin dadin abin da yarinyar nan tayi yanzu.
Kiyi hakkuri umma tunda bata taba aikata hakan ba yau ne ta fara don Allah kiyi hakkuri kada
ki dake ta.
Wani kallo tayi wa baba din dake magana a cikin tsigan lalashi tace gidan uban wa kika ci
abinci bakin ki haka duk maiko.
Na dukar da kaina kasa ta kara daga murya tana tambayana da karfi da sauri na dan girgiza
tare da fadin can ina nunawa da hannu.
Oh kin fara yawon kwadayi gidajen mutane ki nuna wa duniya ubanki ya watsar daku a gari
kuna gararanba kai kai haba umma wanan maganan haka ina yafito maki kuma haka ,?
Dan naki ne yaje yawon gararanba ya watsar da iyalin shi da yawon gararan ba yake zai
dawo muna da abin arziki idan ya tashi dawo haka.
Umma idan wani ya fadi haka yaya zaki ji a matsayinki na mahaifiyar mu duk gari an san ida
yake ansan kuma aikin da yakeyi a can.
Jikin ta ne yai sanyi don itama din dai tuntuben harshe tayi wanan maganan ya fito saboda
masifan ta har ta kai ga fadin hakan.
Ta kama kamay kamay tana fadin bafa haka nake nufi ba yaya zan wa dana wanan kalamin da
ita dai nake da wanan mai manyan udanuwan nake magana tana nunani inda nake tsaye.
Ina aiken da tayi maki baba yake tambayana ledan dana dunkule na saka a aljihuna na ciro
na mika mai ya karba ya mika mata ta karba tare da kutawa tana fadin yau kin kuru wallahi.
Tana magana tana kallon goron nace na hada da kudin da hajiya ta bamu na sayo maki duka
rufa min baki tace cikin tsawa na dan kara ja da baya.
Umma har yanzu fadan bai kare bane duk da kudin da ta samo wurin rakiyan aiken ta nayi da
zata ce ta cika min.

Juyawa baba yayi gurina yana fadin ke kuma daga yau idan kin kara wuce wurin da aka aike
ki sai na yanke maki kaunan ki gidan nan da sauri na daga kaina alaman naji ina kyarma yace
shige shiyan ku maza sai da yaga na shige wurin mu ya ja ya wuce.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:45 PM - : ‍♂️ KANIN AJALI NA ‍♂️

3️⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

MARUBUCIYAR TAKARI TARKO FUREN JUJI SARAUTAR MATA, ALOKACIN MUKE,
MARUCIN KAN DUTSE, BAHAGO, BA MU KADAI BANE, MIJIN BUZUWA, DA KANIN AJALI.

MAI SON NOVEL DINA ZATA IYA NEMA NA A WANAN LAYIN 080 36959257 KO 090
36938192 DON TURA KUDIN NOVEL ZAKI IYA TURAWA A WANAN ACCOUNT DIN
2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KAN DARI UKU KO WANI LITTAFINA
DON FADAKARWA DA NISHADI. NAGODE DA DAMAN KU DA KUKE BANI A KULUN ALLAH YA BADA IKON SHIGA DON
JIN RAYUWAN WANAN BOYAR ALLAH.
WACCE KEDA LABARI DA TAKE SON A HASKA MA YAN UWA MATA SU FARGA ZATA IYA
NEMA NA TA WANAN LAYIN DAKE SAMA DON BANI LABARIN TA IN HASKA MATA SU
FARGA., , , ,


Mama mace ce mai tsabta da tanadi yau ma kamar kulun tana tsakar gida tana gyaran guraren
da take da ikon gyarawa har ma da wanda ba nata ba ta gyara idan gyaran ta ya tashi.
Ta gama ta dora girki ba dai wani girki bane dan kullun ne tuwon masara ko na dawa sai wani
lokaci jumma,a ake girka shikafa da wake muda nama sai idan sallah tazo ko Allah ya tsaga
zamu ci .
Ta kare komai akan lokaci tace zata kitso bayan muma ta sance muna kawonan mu daki ta
rufo muka nufi gurin umma tayi mata sallama.
Don gidan kitson namu a makwabtan mu ne ba wani nisa sosai a kofan shiga wurin umma taja
ta tsaya tana mata sallama kamar ba zata amsa mata ba sai can tace a dawo lafiya.
Kitson shuku akaiwa maman mu inda mu kuma akai muna zanen yawo na hannu ta biya kudin
kitson muka dawo gida.
Lokacin har anyi sallah azahar ko a gagauce mama tayi sallah don ta makara saboda kitson
da aka tsaya mata.
Sai da ta idar da sallah ta bamu abinci muka fara ci tare da ita muna tsaka dacin abincin ne
mukaji muryan umma da itama shigowan ta gidan ke nan daga makwabta.
Take fadin umma mun dawo tun dazun sai yanzun kuka shigo kamae kitson wata mai miji a
kusa mama dai sai murmushi tayiwa umma din ta fara aikin ta na tsakar gida.

Kafa dare yai mata kuma ya zama matsala gurin umma da bata raina laifi mutum gare ta gab
da zata karasa aikin ne muka ji sallaman mahaifina da isowan shi ke nan garin sai shigo mashi
da kaya akeyi wanda wanan karon yafi na kulkun zuwa da kaya masu yawa.
Murna da farin ciki muka shiga yi na zuwan shi duk gidan in ka debe mama da take kawaici
kada umma tace bata da kunyan idon su.
Baza ka iya gane farin cikin mama ba duk yadda ka iya fahintar ta don kawaici irin na
mutanen karkara da kawar da kai ga komai.
Dakin umma ya fara shiga ya dade a gurin umma din don kayanshi da komai da komai da
yazo dashi , yana dakin umma din son irin karfin da take dashi akan diyan ta.
Kira ya kwalawa maman mu dake kara gyara dakin ta don taron baban mu da ya iso garin a
bazata sai gata ta shigo da saurin ta .
Ba tare daya kalli fuskan umma ba ko jin wani dar din ta irin da yace kwashe wanan kayan da
yaran nan suka tara min a nan kikai daki mana.
Dan darr mama tayi don jin abinda umma zata iya fadi a lokacin sai dai taji shiru bata ce kalla
ba har ta duka ta fara kwashe kayan zuwa dakin mu.
Sai dai fuska da umma ta bata gashi babu halin magana don yadda mahaufin namu yai mata
kwarjini a idon ta sosai ya waye ya zama dan birni babu alaman kauyanci a tare dashi.
Tana kallo ba yadda ta iya haka mama ta kwashe kayan kaf zuwa dakin mu karshe ya mike
yabi bayan ta zuwa namu shiyan .
Zaune muke inawa shamsiya wasa ya shigo na mike da murna ina taron shi yace a, a hadiza
kina gidan nan dama baki fita ba shine ban gan ku ba ?
Banji nauyi ko kunyan idon shi ko kurciyane sai bude baki nayi ina fadin idan naje umma zata
kore ni ne baba na bashi amsa da hakan.
Kai ya jijiga shigowan mama dakin dauke da ruwan sha a kofi da ta kawo mai ya samu yin
shiru daga ni har baba din ta aje a gaban shi tana mai sannu da zuwa.
Kiran da umma tayi min ne yasa na bar dakin da sauri zuwa amsa kiran nata da fadan nan
nata ta tare ni wai na fado mata daki kamar an koro ni saboda gulma.
Aikena tayi sayen goro na fita da sauri nan na samu daman fada ma kawayena da ma wasu
da ba sa,a naba da naga suna mutunci da iyayyena ina fada masu zuwan mahaifina.
Ko da na dawo na samu baba ya bude tsaraban shi ba abinda ya dauke min hankali kamar
lemo da ayaba dana gani a cikin kayan anfitar daga cikin buhun da suke.
Mama tana ta famsn kakasawa mutanen gida ina shigowa tace in dauka in kaiwa inna da
sauri na shiga kawai inda take fada min sai godiya sukeyi zan kai na karshe ne umma ta
dakatar dani da kuma kwala wa mama kira.
Mama ta fito da sauri tana fadin gani umma tace yanzu dan tsaraban da mijin naki ya kawo ne
mu tada komada kike kwashewa mutanen gidan saboda neman suna.
Eh ai ki kwashe tunda ganin abin kiyi daga sama baki san wahalan da yayi ya sayo ba a can
muryan mshaifina ne daya fito daga wanka yake fadin.
Haba umma waye bare a gidan nan ina duk a yan uwana ta raba wanan abin dai don Allah ki
bar yin haka mana umma kamata yayi ki godewa Allah daya bani halin sayowa ai.
Baki umma ta tabe ta shiga gyara goron ta da ta mayar kamar abincin ta ta saka a baki ba tare
da tace mai komai ba.
Yan gidan mu sai shigowa suke gaida baba da masa godiyan tsaraba wanda hakan yake

mashi dadi sosai mu kan muna cin abinci barci ya kwashe ni a gurin .
Washe garine ya zauna da yan uwan shi da umma din yake fada masu zancen aikin daya
samu na dan sanda sunyi farin ciki dajin wanan labarin sosai sai umma ta tuma ta kafe da ita
bata yarda da wanan aikin ba.
Baba kabiru ne yayi karfin halin yin magana tare da katse umma din yana fadin umma da wani
ya fada min wanan zancen ba zan taba yarda ba.
Sai gashi a gaba Allah ya nuna min akayi ashe wanan ba bin farin ciki bane a gurin ki garin
nan kaf babu wanda ya fara wanan aikin sai tsatson ki ashe haka ya zama abin alfari a gare ki.
May ye amfanin yin karatun da kika jajirce muyi Allah ya fara kawo muna mafita da bakin ki
zaki fadi wanan maganan yanzu.
Kamata yayi ki sa mai albarka da fatan alheri Allah ya tsare ya kare ya ba da sa,a ya kamata ki
fada mashi.
Umma da bakin ki fa kike kokarin fadin rashin aikin shi takamaimai a can yanzun Allah ya
kawo mai mafita zaki kawo wani magana kuma umma.
Jikin ta ne yayi sanyi tace idan haka ne Allah ya tsare ya bada sa, a kowa a gurin yace amin
nan yake fada masu bai dawo ba sai da komai ya kammala a gare shi hae gidan da zai zauna
sai da ya samu a can .
Da sauri umma tace amma kai kadai zaka zauna a can din ko baba kabiru ne ya karba da
fadin haba dai ai gara dai yaje da iyalin shi a kusa dashi zaifi mai sauki da kwanciyan hankali.
Baba yushau yace nima dai haka naga yafi mai sauki kaga muna mun samu wurin zuwa a
birni ke nan .
Kai rufe muna baki da wanan shirmay yana nufin da saude duk da yaran zai tafi ke nan baba
kabiru yace kwarai kuwa don ya kama inda zasu zauna ma a can tun kan yazo din.
Don haka tare zasu tafi ke nan idan zai koma baba yushau tace kai amma naji dadin
Wanan maganan don ko ba za a barni a nan ba nima kafan ku kafana.
Da sauri umma tace babu inda zaka tafi shidai din da iyalin nasa Allah ya sa aje a sa,a yakai
lafiya .
Sai dai zanso ku barmin kubura a nan mu zauna tare wanan karon mahaifina ne yayi magana
yace umma zan so mu tafi da ita don su samu karatun zamani mai kyau a can don rashin
karatun da basu samu a nan yana damuna.
Wanan mara makarin wani karatu zata gane ko sunje can kayi fatan Allah ya baka diya maza
su samu ilimin kamar yadda kuma kuka samu.
Kowa cikin iyayyen nawa maganan yayi mai zafi sai dai babu yadda zasuyi da mahaifiyar tasu
baba kabiru ne ya murje ido yace dani mahaifa na zasu tafi.
Tunda aka fadawa mama zancen tafiyan mu take jin dadi a ranta ta shiga sallaman yan uwa
da bokan arziki suna mata fatan alheri da murnan fita cikin kangin umma da suke kallon tana
gallaza ma rayuwan auren ta.
Mama bata dauki wasu kaya ba sosai don baba ya hana yace ko can din basu da tabbas din
zama za a iya daga su ko wani lokaci don haka aikin su ya gada kamad fulani suke su.
Wanan shine fitar mu daga kauyen mu asalin garin mu na iyayyen mu ka shigo birni sai dai
idan munje ziraya kuma.
Mun isa birni kano unguwa madawari baba ya kama dan gida madaidaici mai dakuna biyu da
falo sai kicin da makewayi, sai dan tsakae gidan ba wani mai girma ba sai dai duk an shafe shi

da suminti kamar dakunan.
Kauyawa muka zama a gidan don har kayan kallo a falin an shimfida ledan kasa a ko ina na
gidan ga yan kayan aiki da baba ya sayawa mama na amfani irin na yan birni da alama bada
itace zata dinga girki ba a garin.
Murna fal a zuciyana muma mun zama yan birni ina kallon yadda baba ke koya wa mama
yadda zatayi amfani da resho da karamin gas din da ke kitchen din.
Satin biyu aka sani makaranta sai dai ta gwaunati ce amma duk da haka akwai banbanci sosai
bisa

3 / 37