Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
ya rungumay mu tsakani da Allah.
Sai dai zugin Jamil a kanshi yana aiki a kaina don duk wanan kokarin da yake muna sai jamil
din yace wai bai da hali bai taimaka muna don bai bamu kudi .
Ko yace wai sun haye muna kudin gadon mu sun barmu muna wahala sun saka muna ido don
basu suka haife mu ba idan da badon yana gudu mutane su gane ya cinye muna kudi ba ba
abinda zai sa ma ya kula damu.
Ire iren wanan maganan da yakeyi tun bai tasiri a zuciyar mu har ya fara nan zamu taru a
gidana da yan uwan haihuwana mu kulla mu warware a tsakanin mu.
Gashi kamar kudin uban shi ko da mahaifin shi ne ya mutu iya abinda zai iya ke nan a kan
kudin mu gashi ban taba jin yana ma mahaifa addu,a ba a gaba na koda na rana daya ne.
Karamin mu ne da aka samu kudin nan anty tasa ya sai tabarmi da butoci ya baya a
masallatai sadaka mukan ta bimu har ta gaji bamu sai komai mun bada sadaka ba.
Ni ina ma naga kudin tunda banda ta cewa alan kudin sai yadda akayi dani dasu yanzun ko
ancinye an koma jin haushina.
Ni dai ga wautana burina shine a zauna lafiya a tsakani na dashi na dauka yi hakan shine zai
kara sa muna yarda da kauna a tsakani mu dashi.
Ashe van san ba duka maza ne suka san hakan ba a rayuwan su don ba zance ba za, a rasa
wanda keda rikon amana ba sam.
Don girman Allah kuyi hakkuri ba laifina bane haka Allah ya tsara ma lamarina wallahi wallahi
wutane bamu da har yanzu nakai caji wayata ta samu matsala dole yau sai da na sayi wata still
bamu da wuta har yanzu don trasfomer din mune ya buga.
5/18/21, 11:57 PM - í ¾í´”í ¾í´”í ¾í´”: Na samu wannan kawana dake makwabtan mu tasa mijin ta ya
dauko muna manja da garin rogo a can inda yake da zai dawo.
Ita nata zata aika dashi ne gidan su a sayar ni kuma tace in saida nawa a nan cikin unguwar
mu din tabar min sai idan mun sayar zamu tura mai kudin ya kara sayo muna wani.
Alhamdullahi don sana,ar ta karbu min a cikin unguwar tamu da farko da Jamil ya gani ya fara
tambaya a ina na samo kudin da na sai wanan abin ?
Ban so in fada mai ba amma danaga matsin yai yawa yana tambaya don zargina yake ko na
samu wasu kudine naki fada mai don har bugun cikin baffa kanina yayi a waje bai ji komai ba.
Dole na fada mai inda na samu kayan ina sayarwa din nan ya hau fada wai yarabani da wanan
matar don ta fini wayewa shi bai son rikici da dauko magana.
Na dai kyaleshi yayi fadan shi ya gaji ya sa mun ido mutane sai shigowa suke dare da rana
suna fadin abasu manja ko gatin kwaki da sugar.
Dadi dadi na hada kudin farko don a cikin sati biyu komai ya kare muka tura ya sake turo min
da wani don ita ma an sayar mata da nata acan gida da ta kai.
Wanan ma yayi saurin karewa da wuri don yanzu mutane sun sanda ina sayarwa kuma a cikin
sauki na hada kudin mijin kawata cif da sunan washe gari in kai mata ta tura muna wurin mijin
nata.
Washe gari tun da safe Jamil ya fita kan zai tafi wani kauye yace min a can zai kwana don
haka sai dana gaba duk aikin gida na shirya na nufi inda na aje kudin don in shiga in mika mata.
Kudi yace dauke ni inda kika aje sai da na dafe kirji na nakai kasa don capert nake dagawa na
aje ba wanda yasan inda nake aje kudi a dakin idan na hada su.
Don gudun haka tunda nasan halin shi da kudi ni kadai a daki sai zufa ke karyo min a lokacin
don nasan babu wanda zai dauki kudin nan sai Jamil din don ba mai shiga dakina har kurya.
Ko baki nayi a falo nake ajesu basu shiga min daki, don kunyan dakin da nake ji ni kaina ban
son wata mace yar uwana ta shiga min dakin.
Don haka ban zargi kowa ya shigo min daki ba na rasa yadda zanyi a lokacin sai daukan
diyana nayi na nufi gidan da mahaifi shi yake.
Duk da nasan abu mawuci ne ya goyi bayan dan nasa a lokacin sai banda yadda zanyi dole in
je gurin shi da wanan maganan.
A gigice na isa gidan muka gaisa dasu sai na fashe da kuka na fara fada masu halin da ake
ciki budan bakin mahaifin nashi tun ban karasa ba shine.
Kina nufin Jamil ke nan yai maki sata ko wa da kika zo nan din ranan matar mahaifin nashi tayi
min abin kwarai don kafin in magana tace .
Haba malam idan bata zo nan ba ina kake son taje da wanan abin kunyan kai kullun danka bai
laifi itace mai laifi haba a rika yin abu don Allah mana.
Yarinyar ga dai tana iya kokarin ta wurin ganin ta kyautata mashi amma hakan bai isa ba sai
an hada da dauke na mutane da ta dauko kuma yanzu mai kake son tace ma mai kudin do
Allah.
Ai sunan danka ne zai baci a unguwar tunda kowa yasa halin shi a gareta ido kawai mutane
suka sa masu hakanan.
Naji dadin wanan maganan har cikin raina don yau ta fadi alheri a gamay dani bayi son
zuciyan da suka saba ba.
Fada ya hau yi da ita amma bata barshi ba dole tsohon ya sauko tare da fadin nawa ne kudin
na fada mai yana gyaran zama yace sai dai ayi raba daidai kije ki nemi saura ki cika masu kudin
su.
Ya kirga rabi kamar yadda yace din ya bani na fito ina share hawaye ina zan shiga cikin garin
nan in samo rancen kudi in ba mutane kudin su.
Ko dana koma yan gidan mu ke fadin matar tazo nema na sai da gaba na ya fadi lokacin
haka na daure na shiga gidan ban boye mata komai ba na fada mata halin da nake ciki da kudin
na bata rabin da mahaifin shi din ya bani.
Na bata hakkuri kan zan nemo sauran in karkare mata in an kwana biyu hakkuri ta bani na fito
ina hawaye gidan zuwa gidana.
Bai dawo ba sai bayan kwana uku ya dawo in da ya samay ni zaune a cikin tagumi ban ko iya
mai sannu da dawowa ba don zakace ba kauye ya fito ba da yace yaje.
Shi sai wani fresh yake karawa ni ko ina figewa banda wani kumari a jikina ko kadan daka
ganni, kasan damuwa ya samu gurin zama a zuciyana.
Ganin yadda na fuske shima ya fuske ya shiga daki ko may yayi a ciki can ya fito yana fadin
ke lafiya kuwa mutum ya dawo ko sannu da zuwa ba zaki mai ba.
Wani kallo na watsa mashi tare da kawar da kaina daga kallon shi ina fadin azzalumi baiji dadi
ba wallahi.
Ka rasa wanda zaka yaudara sai matar ka ta gida mai dawainiya da yayan ka duk wani nauyi
da hakkin ka ka rataya a kaina .
Haka bai ishe kaba sai ka hada da kudin mutune ka kwashe ka tona min asiri a gari.
Ya zaro ido yana fadin wa kika mayar barawon ki gida nan nace kai tas ya kwashe ni da mari
sai da ba dafe wurin don zafi.
Hakan bai sa na fasa magana ba nace ka kashe ni ka huta dama nasan mutuwa ta kake son ji
macuci kawai azzalumi.
Ba wanda zai shigo ya daukan min kudi dakin nan sai kai ba zan zargi kowa ba wallahi don
kaine ka kwashe su .
A harzuke yace an kwashe din kiyi abinda zakiyi in zaki iya wawiyar banza kawai kan wasu
raggan kudin ki zaki dinga kirana da macuci can kudin da ko mota basu isheni shiga ba.
Nace baka nayi da zakace kada in kiraka da macuci ya kara daga hannun zai mare ni na sa
mai ihu sai ga yan hanyan gidan a sukwane sun shigo suna tambayan ko lafiya ?
Ina kuka na fara fada masu abinda yai min don duk cin kudina da jamil keyi wanan din yafi
bata min rai sosai wallahi.
Don ya nuna min bai damu ba duk halin da zan shiga da mutane ni na sani ke nan shi ba
damuwan shi bane hakan.
Bayan sun gama ji ba mai shiga tsakanin miji da mata sai cewa sukayi inyi hakkuri in kyaleshi
mu san yadda zamuyi kudin mutane ya fito.
Haka suka dinga fita daya bayan daya suka barmu a dakin dagani sai shi ya shiga kuryan daki
ya fito yana fadin wawiya da bata san ciwon kanta ba.
Da kika fada masu kwatar maki zasuyi ko may ai na dauka zasu sa in biya ki ne dole ina kuka
nace Allah dai zai kwatar min hakkina ba wani ba.
Mu kai ta yada ma juna bakaken magana har ya gajibya fita daga gidan ya barni nan ina
tukukin bakin ciki da na daman auren shi.
Sai mutum daya ne cikin yan hayan mu ya iya mai magana kan abinda yakeyi din bai kyauta
ba gaskiya kudi mutane ne fa ya dauka kuma ya sani yaya yake son inyi.
Don Allah Jamil idan ka samu kudi kaba wanan yarinyar kudin ta don hakan zubar mutunci ne
a gurin mace wallahi .
Kaga dai duk cikin matan mu tafi kowa hakkuri yau gashi kakai har ta tona maka asiri a
bainan jamma,a haka ai irin haka babu dadi.
Jamil din yace ta dai tona ma kanta tunda bata da wayau don kawai na dauki kudin ta zatai
min wanan tonon asirin haka a idon jamma, a.
Mutumin ya sake fadin ai abin ne da cin rai jamil yace malam naga fa kana son shiga hurumin
da ba naka ba gaskiya yace a, a niba haka na bane ina dai guje maka hakkin marainiya ne a
kan ka.
Kada ka manta matar ka marainiyar Allah ce ta gaskiya kowa kuma nan yasa tare kuke cin
kudin gadon ta idan ya samu aiko kaga hakan tayi kokari wallahi.
Don ba ko wace mace bace yanzu zaka samu haka nan yace kada ka fada min maganan
banza Nasir ina ruwan ka ne da zancen mu wai da matana.
Basuji dadin juna ba da mutumin nan kowa ya fadawa dan uwan shi bakaken magana ya kulla
da wanan mutumin da yake gani wai ya raina mashi wayau shi.
Tun wanan lokacin ya sa wana mutumin da matar shi agaba gidan da anyi abu zai fara fadin
ba mutumin arziki bane dama ya kamata su tashi su bamu gida.
Sai dai wanan karon baiyi nasaran haka ba kaina don ban bashi hadin kai yadda yaso ba yake
min a baya kan yan hayan mu.
Sannu a hankali na samu na biya kudin bashin da ake bina koshi da taimakon dan abin da
nake samu a wurin baba kabiru aboye bai sani ba na biya.
Don daya sanin karbe kudin zaiyi ba wani wuyan aiki bane a gurin shi don haka yanzu na fara
boye mashi komai nawa nima saboda yanzu na fara fanhintar shi.
Don a gaba shi maman jinior zata aiko batun kudin ko tazo da kanta yana ji bai cewa komai
idan kuma na mashi magana sai yace idan ta samu zai bayar.
Ko hakan da yake fadi don mahaifin shi wanan karon ya fita bayan shi yayi mashi fada sosai
har ranshi ya baci shine yake fadin wai zai biya da baki don baida niyar biya din.
Tun da yaji baba yace yana nema na yana daki kwance yaron yana fita zubur ya fito daga
dakin yana tambaya ko lafiya baba ya aiko yans nema na ?
Nace ban san ko may yake nema na dashi ba in dai na gama zanje in ji dalilin kiran yace ki
tafi ni zan karasa sauran akin daya rage din.
Ban ki nasa ba na gyara jikina na nufi gidan namu inda na samu baba na gida bai fita ba baya
mun gaisa ne yake fada min zancen kudin mu ne ya taso bayan long proces da akayi yanzu
ranan monday zamu je muyi signing din documents din a Abuja.
Wani irin farin ciki ne ya turnuke min zuciya ta idan mai karatu bata manta ba na fada maki
kudin an kasa su uku ne kadan kadan suke zuwa muna ke nan.
Murna a gurina ba a cewa komai hakama dana koma gida da zumudi Jamil yake tambayana
lafiya dai ko ?
Ba bata lokaci na labarta mai abindake faruwa ya wani washe baki yana murna tare da fadin
wai Allah dai ya jikan baba.
Karo na farko danaji yayiwa mahaifina addu,a ke nan ita mahaifiyar mu ba a magana kanta.
Nan wuyan talaucin da muka fito ne a ciki yasa yai wanan addua,an haka da bai ma san yazo
mashi a baki ba a lokacin.
Nan ya fara haba haba dani bai fita yawo sosai sai lokaci lokaci yakan dan fita ya dawo ana
jiji dani da yarana lokacin har fita yake da yaran wurin fira kofan gida inda suke taruwa.
Yanzu idan mun zauna baida magana sai na tsara yadda za,ayi idan kudi sun shigo hannun
mu har da fadin zai fito dani gari don zai sai min babban waya irin na kowa ni da ko nokia banda
shi.
Sai yan uwa idan sunji haushi rashin wayana ya damay su zasu dan sai min yar nokia in rika
bai kai wata daya a hannun na idan matsi ya kama mu in sayar in sai wani abin.
Gashi nima bakina yasaba da dadi irin na jamil yanzu ba ko wani abinci nakan iya ci ba in ba
yan kayan kwalama ba da sauran su.
Ni dai ina jin shi yana ta tsara yadda yake so abin ya kasance wanan karon dariya nakan yi a
raina kawai do ko da tsiya sai na gyara dakina wanan karon.
Nagaji da rufe kofa da boye boye wa kawayena idan sun zo gidana har kunyar yadda dakina
yake nakeji don ko na wata tsohuwa yafi shi dadin kallo.
Ranan mondaya shi da kanshi ya rakani gidan baba kabiru tunda asuba don asubanci zamuyi
mubar garin don mu isa da wurin during warking ahours.
Sai dai bai yarda mutanen gidan mu sun gashi ba yana isa kofa saida yaga na shiga ya koma
shi bai shiga ba lokacin.
Nasan nasa wayau do kada aga zalaman shi a fili ne yasa ya boye hakan ya labe daga kofan
gida yaki shiga daga ciki.
Mun isa lafiya mun samu wanan kudin a yadda sukai muna bayani suna da yawa sosai don
haka zai fi na farko dana baya yawa ke nan .
Murna fal a zuciyana baki har kunne muka dawo gida da farin ciki zuciyar mu fara kal da jin
wanan zancen.
Na samu ya gyara daki ya dafa abinci ya jera min yana jiran dawowana kamar ance mai da
kudin zamu dawo dayani daga zuwan mu.
A gidana baba ya sauke ni suka tafi ina shiga na samu yana zaune yana jirana a cikin duhu
duk da babu wuta a lokacin amma haka yake zaune kamar maye shi kadai a falon mu.
Nan yai muna sannu da zuwa ya karbi goyo na yana tambayan ta ya hanya kamar yarinyar ta
iya magana lokacin.
Yace bari yai mata wanka don kada gajiyan hanya ya hanata barci shi yai mata wanka ya bata
abinci taci ta kwanta tunda dama a gajiye muke.
Ya fara tambayana yadda akayi ina labarta mashi yayi wani irin ihun murna tare da fadin kice
zamu faso gari ke nan sosai wanan karon.
Da yakw dan duniyan namiji ne bai barni na huta ba duk ko da gajiyan dana debo a hanya sai
da ya kusanceni ranan .
Don kawai ya kara gyara min rai niko ina jin dadi a raina ga miji na tatali na ana sona don sai
ka dauka ya daina halinshi ne yanzu na bariki.
Tun wanan ranan suka shiga yin meeting dashi da mijin kauwata wai idan kudi sun zo ga
yadda zasuyi muna dashi .
Zakace abin na Allah ne ake shiryawa lokacin don sunce bazasu yarda su baba kabiru suna
muna wayau ba ko wani lokaci duk da fa su baba basu karban ko kwandala