Kanin Ajali Complete by Zeey Makawa

Author :  Zainab Idris Makawa Category :  Read Hausa Novels

Chapter   21 / 37

60K to 63K   out of 109.3K words

samu ya kimtsa min ita don bai bari na tafi da ita ba.
Ina shigo jikin shi har rawa yake wurin tambayana to yaya zancen kudin ne komay ake neman
mu dashi kudin dake a jikina na fitar ina nuna mai take ya washe baki yana fadin alhamdullahi.
Allah ya rufa muna asiri dama ko barcin kirki ban samun yi kan rashin samun mafita da banyi
ba yanzu kin ga Allah ya rufa muna asiri.
Nan ya shiga lissafin irin karyan da zamuyi idan na haihu yake fadin in kawo kudin tun yanzu
yakai na mai shagon da yake sayayya da na haihu daukowa kawai zamuyi a gurin shi.
Ina kallo ya lissafa kudin da yake so ya kuma fitar da wanda zamu sai abinci har na suna idan
na haihu din da za,a dafa gurin taron suna.
Da kyat da boni na samu yabar min wanda zan dan rika a hannu na don lalurori irin na mata
sai cewa yayi dani ba ga baba kabiru nan ba yasa zai min idan na haihu.
Ni don sanin yadda muke da mutanen gidan mu yanzu sama sama yasa hankali bai kwanta
da zasu yi min ba idan na haihu din ganin na na matsa mai ya firar da dubu talatin ya bani a
cikin dubu dari tara da kyat ya mika min a hannu na wai sakaci gare ni kada in aje a wurina a
kwashe. Nasan abin da yakewa shine ganin haihuwana na farko an min abinda ma bai zata zasuyi min
ba ga kuma kanwa ta data haihu itama an mata sha tara na arziki ya gani.
Ban san baida kunya ba sai da ya miko min kudin yana wani shan toka a fuskan shi tare da
fadin ni ke nan naga kudi na daure fuska may zanyi dasu bayan baba kabiru yana muna komai
idan mun haihu mafarin in koyi kashin kudi ke nan jifa.
Baba kabiru da ya gama zagi yana batawa a gurin mu ne yake kuma tunanen zai muna abin
arziki yanzu saboda son banza daya iya a rayuwan shi.
Ni gani wawiya ta karshe ban koyi tunanen irin sakin da yake min ba a lokacin ni dai bukatana
da tunane na dani kadai zai zauna ba wata mace da zaice zai kara aure nan gaba.
Don sam bani irin wanan tunane a raina saboda son shi daya rufe min idanuwana a lokacin
har mutane na fadin wai ko asiri yai min ne haka wana abin ga kowa don sanin halina an kawo
ido ansa min dashi banda makwabi a rayuwa na.
Don kowa yasan da ya fada min gaskiya zan kwashe in fada mai ya dora gaba da mutum har
illa masha Allah.
Yanzun kan muna da abinci ga kudi don shi Jamil mutum ne da bai ci ko wani irin nau,in
abincin daya danganci tuwo a rayuwan shi sai dai dan taliya makaroni shimkafa da miya ko tea
kamar ba haihuwa kauye ba shi.
Sai daga kai nake wa mutanen gidan mu don komai ina dashi yanzu ban dan murya gun kowa
don neman wani abu don tunda anty tai min fadan haka ga yan hayan gidana na daina
tambayan su wani abu.
Da yake ni sakarai ce sai wanan samun yasa ina daga masu kai har suka fahinci hakan gare
ni kowa ya jaye min daga harkana sai ni dashi da yan uwan shi muke bushashan mu a gidan.

Daka ji sallama yan uwanshi ne ba dai nawa ba yanzu zan hada masu delicious ko a sawo
masu kayan sanyi susha su wuni suna cin dadi a gurin mu.
Sati kaman uku da haka na haihu na kara haihuwar diya mace ba laifi don yan uwa da matan
baba suna asibiti a tare damu har na haihu aka dawo dani gida.
Tun yanda suka ga ni kaina da Jamil din muna masu kowa ya dauke kafan shi a gidan tun
ranan matar mahaifin shi ce tazo ta zauna damu na satin da akeyi inda Jamil sai dadi yake cika
mu dashi.
Niko ban tunanen komai a raina don sai fadin ake yarinya tazo da goshin ta don muna cikin
wadata inji yan uwan shi suke fadin haka gare mu.
Ban wani damuwa ba na rashi ganin dangina basu tsayawa a gurina ni tunda ga dangi jamil
sun tsaya min akan komai ai ya waddatar dani nake gani don haka ne ban nemi shawaran kowa
ba.
Da anty ta kara shigowa duba mu take kebewa dani irin yadda akeyi din nan tana tambayana
mai muka shirya ma bukin don sunji shiru ban tuntube su ba har yanzu.
Sai budan baki nayi nace kada su damu ai mun gama shirin komai da zamuyi tace kai madalla
Allah ya raya muna bata dade ba ta fita .
Sam ban kawo magana na wani katobara bane a lokacin don haka na shiga harkokina ba
wani damuwa don ina ganin ai muna dashi.
Summaiy kanwata ce tazo tana tambayana nake fada mata yadda mukayi da anty tace kai
amma ke anty hadiza wai wata irin wawiyace haka don Allah.
Anty ce zaki fadawa kun kun gama shirin komai da mijin ki kina ganin ke yanzu baki da
bukatan komai a wuri su ke nan ?
Nace may zamu bukata tunda muna da kudi a hannun mu yanzu tace to shike nan ita yanzu
gida zata taji irin shirin da akeyi a gida don tasan yau ya kamata ace anyi su cicin da sauran su.
Nace sai ta dawo ta fita zuwa gidan mu niko ban wani damuwa ba a raina don nasan zamu
burge kowa da wanan haihuwa ko suyi ko kada suyi ban damu ba ni.
Da ta shiga gida sai ganin gidan tayi wayau ba kowa anty ma tana dakin ta tana barcin ta a
lokacin don tana up a wurin aiki.
Bayan sun gaisa ne take tambayan ta ko akwai wani abinda za a yi a gidan sai take cewa ai
mai haihuwa tace ta hutar damu don sun gama shirin komai.
Tace a ina ta shirya anty har gashi gobe suna ni banga wani shiri da takeyi ba tace summaiya
kin san shirin da sukayi ita da mijin ta ne ki sa masu ido aga ni mana.
Abinka da dan uwa sai hankalin ta bai kwanta ba ta kara dawowa gidana tana fadin ita fa taje
gidan mu bata ga wani shiri da akeyi ba a can yanzu idan mutane sun taru mai zan raba masu
na buki ?
Nan dai dabara ya fado min nace buta zan sayo sai alale da taliya da zan dafa kuma da
dambu .
Tace duk a ina za ai maki wanan aikin to nace a gidan yaya sani wanan Jamil din nan da suke
kamar abokai wanda ya tilasta min kiran matan shi da anty.
Wani tsoki taja tana fadin yanzu ke a can za ai maki aiki sai kace wace bata da gata a gari
gaskiya bai kamata mu nuna wa baba kabiru da matan shi haka ba anty.
Fada mukayi da ita sosai a gurin don ta fahinci ina haka ne don gyarawa Jamil dina rai kawai
ban damu da abinda dangi zasu fada ba a kaina.

Nan na fitar da kudi cikin wanda ya dan rage min na bashi ya sawo min buta sai gashi da
kananin butoci kuma dozen uku ni da na bashi kudin dozen biyar yana fadin.
Wai ya samu sun tashi shine ya sawo min wa yan nan nace ai ba zasu isheni ba yake fadin
wai har wasu mutane zasu zo da zan saye da yawa don barnan kudi kawai.
Dinki kala uku yai min duk a cikin kudina shiko ya dinka sun kai kala goma sha kamar shine
mai haihuwan da zai fita bani ba.
Washe gari a gidan su aka yanka katon ragon da ya sayo aka gyara sai dan hanjin da aka
aiko min dashi wai sun raba a can suma zasuyi amdani dashi ne.
Sannu sannu gida ya fara cika da mutanen arziki yan uwa da abokan arziki suka fara zuwa
min suna gashi ba a kawo min abinda zan ba su ba.
Yan uwana da suka zo tayani aikin suna daga gidan mu sai tambayana sukeyi mai zasu yi
nake cewa ba wani aiki a can gidan su Jamil ake abinci.
Koda za a kawo min sai ga taliya wani iri dashi ba mai kuma dan kadan kasan kula sai dana
dafe kaina don takaici da bakin ciki ga alale shima kamar hakan aka kawo min din.
Haka na aka raba ma wa yanda ke gidan a lokacin aka barni ina kamay kamay idan mutane
sunzo mi don ba abinda zan basu anan.
Yan uwana suka kwasa suka wuce gidan mu don a can suna nasu dahuwan don dangin mu da
suka zo daga wurare anan suka sauka.
Dama kuma a ka,ida hakan yake ga al,adan bahaushe yan uwan mai haihuwa zasu taru ne a
gidan mahaifanta har zuwa wani lokaci kafin su zo gidan ta da dan abinda suka tanada don ta.
Sai da sukaci suka sha a can suka dauko dan turamay dana samu wanan karon turmi hudu
ne kawai daga gidan mu sai buhu biyu na abinci gero da masara da baba kabiru ya saka min.
Aka nufo gidana dashi tun da naga haka naji raina ya baci dasu a zuciyata fadi nake aiko in
haka ne zasu sha kunya don ni dama a shirye nake abina don haka.
Nan gidan su Jamil suka shigo da akwatinan daya gabatar masu a ranan don ba wanda yai
tsammanin haka daga gare mu.
Sai wani washe baki nakeyi ina sallo ni adole mun faso gari muma sai fadi mutane ke yi basu
taba ganin itin set din akwatinan ba a gurin.
Da aka bude kuma sai da kowa ya kama baki don kyawon kayan dake cikin akwatinan danawa
dana baby duk abin kallo ne a gurin.
Aka kwasa zuwa gidan mahaifana kamar yadda akeyi a wuri mu sukai ta sa albarka suna
fafin yarinya tazo da goshin ta inda yarinya taci sunan mahaifiyar Jamil data rasu watau
maryam.
Kayan basu dauki lokaci ba aka bayar aka dawo min dasu kamar dai yadda akeyi idan an
haihu ga al,adan gidan mu idan ka haihu zaka cire wa mahaifiyar ka da mahaifin ka turmi ka
basu su saka maka albarka.
Amma haka nayi mirsisi na hana ma kowa wanan irin al,adan na hana masu ban basu komai
ba nace nima na rama ai haka dai dan kudin da ake kawo min gudun mawa .
Na fitar nake bayarwa ana sawo min biscuet da butan da nake rano ina ba mutane don wanda
ya sawo min ko dangin shi bai isa ba lokacin.
Na dai samu aka watse lafiya duk dan abinda na samu ya tafi gurin mutane sai dai ban damu
ba don ni Jamil ya gama min komai tunda ya fitar dani a kunya.
Na gyara dakina da taimakon yar uwana data kai har dare a gidan mu ta soya min nama tare

da wasu aiyuka muka gyara ko ina na gidan .
Muka gyara akwatin tsab har ta roke wani zani nace ta bari sai Jamil ya dawo naji kudin shi
zan bata shi mijin ta yazo ya dauke ta suka tafi.
Gidan ya rage sai ni da yan hayana wanda suke part din su Jamil ya dawo abinda ya fara
tambayana shine ina naman da aka kawo na mike na dauko mashi.
Ya karbi roban ya dan jujuya ya girgiza kai tare da fadin wanan naman za a bar muna duk
rago dayan nan kato daya yanka sai wanan zamu ci.
Nace gidan ku fa sun cire nasu ankai nawa kason gidan mu suma sun cire na iyayye kamar
yadda akeyi baiga laifin wanda yan uwan shi sukaci ba sai wanda yan uwa na sukaci ya hashi
haushi.
Ya dan tsince tsoka daga ciki ya zauna yaci da drinks mai sanyi ya kora ya kwanta na dauki
roban na duba babu komai sai kasusuwa suka rage.
Dole haka na fara amfani dashi wa gida dashi nake muna girki ina watsawa a cikin abinci
idan zanyi.
Kwana biyu da suna tun da safe da yake ba sallah nakeyi ba ina barci ban ko tashi ba sai
hayaniyar kattai naji suna fita da buhun abincin da baba kabiru ya aiko min na kunu da tuwo.
Don shine abincin da mace da ta haihu ya kamata taci nasan shine dalilin da baba kabiru ya
saka min su don samun sauki a gare ni.
Sai gashi Jamil ashe ya sayar ya soke kudin shi bai min maganan komai ba ina kallon shi
yana kallona ba dama inyi maganan komai ya hauni da fada kuma.
Kafin kwana uku da suna duk Jamil ya zauna ya tsotse kasusuwan nan daya rage ya cinye
komai dana tanada wa kaina don haihuwa na in samu inci in sha indan na haihu din.
Ranan muna zaune dashi muna dan hira duk akan wa yanda suka zo min gun suna muke
hira sai na jefo mai zancen ina son in danyi dinki daga cikin turamay nan daya saka min .
Sai cewa yayi idan ya shirya kai mun dinki shi zai kai da kanshi don haka in saka mai ido
kawai yace tun wanan lokacin ban kara mai magana ba ni kuma.
Haihuwa na da sati biyu matar wani wanshi da suke zaune a gidan da wansu ya gina tare da
mahaifiyar shi ta haihu .
Tun haihuwa da kwana uku ya turani wai in je in kama masu aiki nace kada ka manta nima
haihuwa nayi ai waya zo ya kama min aiki lokacin har ya tare haka a gurina cikin su.
Yace ra,ayin shi ke nan shi don haka in shirya kawai in tafi in ba bacin ranshi nake son gani ba
ba wanda ya sani haka na shirya na tafi ina mai jin kunya yadda zan tare wa mutane a gida
nima da jego na haka.
Da zan tafi yasa na dauki turmi daga cikin wanda na samu buki a gidan mu nakai wa mai jego
cewan in ji shi nashi gudun mawan ke nan.
Na Kai ba wani godiya suka karba a na wani yatsune baki don gaba dayan su ba sona sukeyi
ba a gidan don karara ake nuna min bambamci ba boyo.
Ina gidan har sati daya don ko bayan da akai suna sai da ya yasa na kara kwanaki a gidan
kuma ranan dai da dare yaje ya dauko ni na dawo gida.
Na samu dakin yayi kaca kaca kin san yarda daki keyi ida an kwana biyu ba,a cikin sa dole na
zage na shiga gyaran dakin kamar yadda ya kamata sai dai sama sama nayi aikin ba ko ina na
gyara ba lokacin.
Sai waini faman daure fuska Jamil ke min wanda ban gane hakan ba a raina nace ai dole kai

bakin ciki da dawowan mu tunda zamu hana ma jin dadin da yakeyi idan bamu nan.
Ban bi ta kanshi ba sai da muka cika kwana uku da dawowa ne nace bari dai in gyara dakina
da kyau don har lokacin banga ya koma min daidai ba a idona.
Na shiga gyara inda na fara da falo ganin na gama da wuri yasa na shiga kuryan dakin don in
gyara sharo nan kwakwalo nan har nakai wurin akwatuna na sai kawai naga sun biyo ni alaman
dai babu komai a cikin sa ke nan.
Ban san lokacin da na yarda tsintsiyan dake hannu na ba na shiga bude akwatunan na sama
na bude wanda kayan baby na ke ciki babu komai a cikin sa hatta permpers din ciki an kwashe.
Da sauri na jawo wanda kayan nawa ke cikin sa shima dai hakan na samay shi wayau ba
komai a cikin sa hannun na dora akai na zurma ihu ni kadai a dakin.
Ba wanda ya jini jiki na rawa da makyarkyata na fito falo na zauna ina tunane kala kala
idanuwana suka birkici a lokaci guda.
Sai wani zufa ke yanko min ta ko ina tunanen duniya na yishi a lokacin yafi a kirga a cikin dan
lokaci kada ni kadai a daki ina jin hayaniyar matan gidan daga bangaren su.
Sai nake jin dariyan su kamar dani sukeyin shi sun san abin da ya samay ni ne suke rahan su
a cikin gida.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
5/18/21, 11:56 PM - 🤔🤔🤔: WORLD


Zaman mu ya koma lafiya da kowa a gidan sai kuma fitina ya taso tsakanina da Jamil akan
yadda nake shiri da yan hayan mu yanzu.
Yana

21 / 37