Author : Zainab Idris Makawa Category : Read Hausa Novels
5/18/21, 11:41 PM - Messages and calls are end-to-end encrypted. No one outside of this chat,
not even WhatsApp, can read or listen to them. Tap to learn more.
5/18/21, 11:43 PM - : ♂️ KANIN AJALI NA♂️
1️⃣
BISSMILLAHI RAHAMANIN RAHIM DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI INA
GODIYA GA ALLAH DA YA BANI DAMA DA IKON FARA WANAN LITTAFIN A CIKIN HIKIMA
DA BASIRAN DA YA WADDATANI DASHI DA FATAN SAKON DA KE CIKI ZAI ISA GARE KU A
CIKIN DAUKAKA DA FAHINTA YADDA NAKE BUKATA, , , , ,
WANAN LITTAFIN NA KUDI NE DON ALLAH KI SAYA KI SAURARI SAKON DAKE CIKI BA
TARE DA CIN HAKKIN JUNA BA A TSAKANIN MU
DARI UKU NE KACAL TA BANKI KO KATIN WAYA GA MASU SO ZASU IYA TUROWA TA
WANAN ACCOUNT DIN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KI KIRA
LAYINA 080 36959257 KO 090 26937192 da fatan zamu fahinci juna daku kamar yadda Allah
ya hadamu nagode.
Yau garin ya tashi da matsanancin hadari sakamakon tsakiyan damana da muke ciki na wanan
shekaran zaka iya cewa gari bai karasa wayewa ba a wanan lokacin.
Don yanayin da garin ya nuna na damana a lokacin wanan yanayin bai hana mutanen garin
yin zirga zirga haka a cikin sa ba don neman na yau da kullun.
Hadiza ce tsaye yarinya karama da ita saidai tana da kaifin basiran da tunane don isowar
mahaifiyar ta take jira wacce ta tafi birni tare da yan uwanta dubiya wata yar uwar su a can.
Baya baida kadan don tafiyan ta wata matar kanin mahaifin su tazo ita ma daga lagos ta kawo
masu tsaraba ciki har da ita hadizan ta samu da tan uwanta.
Wanan dokin ne yasa hadiza fita a cikin wanan yanayin tana dakon isowar mahaifiyar ta ta
zabga tagumi tana mai tsura ma hanya ido taga motar da zai iso garin su a cikin dauki.
Wani dan uwansu ne ya biyo a cikin sauri yake yana ganin ta yake tambayan may take a nan a
cikin wanan sanyin ita kadai.
Tace mama nake jira sun tafi birni tun jiya ga matar baffa mu na birni tazo ta bani riga har
yanzu mama bata dawo ba ni idan mama bata dawo ba yaya zanyi da rigar nan kowa ya saka
nashi.
Takaici ne ya kama mutumin ya hau yarinyar da fada yana fadin maza ki bace wurin nan ki
koma gida duk inda ta tafi ai zata dawo riga kuma tunda an baki ai ba kwacewa za a yi ba.
Simi simi ta juya zuwa gida don sanin ko waye a gare ta don baida wasa da yara shi a cikin
yan uwa kaf sun san da zaman shi.
A cikin sanda ta karasa shiga gidan don kada kakanta ta ganta don basu san fitan ta gidan ba
a wanan lokacin.
Kicibis sukayi da kakan da zata fita neman ta a kofar gidan don ta farga da yarinyar bata gida
a lokacin.
Tana rike da kwarya a hannun ta hannu daya tana gyara mayafin data dora a kanta tace suna
arba tace haba kubura ina kika fita a wanan sanyin haka tun dazun nake neman ki ga uwar ki
har yanzu basu dawo ba ni ban san irin wannan tafiyan ba na aje akai wani lokaci a garin
mutane sunyi abinda ya kaisu sai su juyo su dawo gida kuma ba sai sun dora ma mutane lalura
ba ai. Tace umma nima shine na fita ina jiranta don ga rigan ga da matar baffa ta bani ban mama
bata dawo ba ta gani ni yanzu yaya zan yi ?
Umma ta rike baki da mamaki tana kallon yarinyar tace kai kubura akwai ki da shirmay riga
tunda an baki aiba kwacewa zatayi ba duk lokacin da Allah ya nufa uwar ki ta dawo ai gani
zatayi ko ?
Tace to umma kowa ya saka nashi ai amma ni har yanzu bata dawo ba balle in saka nawa a
gani ko tace kai kin faye dumi da shiririta wallahi maza ki shiga daki ki dauki abincin ki kada yai
sanyi in sha Allahu suna hanya tafe.
Shiganta daki ke nan ba a jima ba taji dirin mota ya tsaya ta zabura ta leka a hankali tana
sanda don bata son kakan nata ta ganta don kada ta hana ta fita.
Ta kusa kofan fita taji muryan kakan na fadin ke! ke ! ke kubura tuni ta balla a guje ta fita wajen
gidan don ganin ko mahaifiyar nata ne ta dawo a lokacin.
Bata damu da masifan kakan nata ba akanta ita dai muradin ta uwar ta ta dawo taga sabon
rigar yar kanti da aka zo mata dashi tsaraba ta saka a jikin ta.
Sai dai kasshi ba su bane a wanan lokacin kai kallon ta tayi ga yanayin garin wanda wani
sabon hadarine ake kara hadawa sai wallakiya ke haska ko ina a garin.
Maimakon ta koma gida sai ta samu wuri ta zauna tana dakon mahaifiyar tata a lokacin tunda
kakan tace suna gab da isowa insha Allahu.
Bata jima da tsayi ba a gurin motar ta tsaya dauke da iyayyen nata mata tayi tsalle ta isa gurin
motar tana leken cikin motar.
Nan dai tayi arba da mahaifiyar nata dake kokarin fitowa a motar tun kan ta karasa sauka take
ihun eh mama mama a cikin murna da dauki tana ganin ta diro take fadin mama matar Baffa na
birni tazo ta kawo min riga da, , , ,
Buge bakin ta da uwar tayi tana fadin ke sai yaushe ne zakiyi hankali wai da wanan shiriritan
naki haka ko sannu baki iyawa mutane ba zaki tare mu da bakin dumin ki da kika iya.
Baya taja a cikin fushi tana turo baki uwar ce ta juyo tana fadin zoki daukan min kaya zuwa ciki
da bakin surutun ki na banza ta turo baki ta dauki kayan da uwar ta nuna mata nata zuwa gidan
su.
Sai dai tana kawowa ta tuna da masifan kaka da zata tarar a ciki na hanata fita da tayi ta sa
kai ta fita ba tare da taji gargadin ta ba ga kuma bakin ta da mahaifiyar ta buga don wautar ta da
tace yayi yawa.
Koda ta shiga umma bata tsaya bin ta kanta ba sai fadi take Alhamdullahi masu tafiya sun
dawo lafiya ke nan.
Uwar ta shigo goye da goyon kanwar ta a bayan ta da sallama a bakin ta aka shiga masu
sannu da zuwa tare da gaidasu da dawowa.
Sai lokacin umma ta farga da hadizan take fadin yar nema mara jin magana ga uwar taki ta
dawo sai ki dauko rigar da kikewa dauki da mazari ki saka a daren nan in ga wanda zaki
nunawa shi a garin nan a cikin dare.
Ita dai Allah Allah take kada ta samu wani rankwashe a gurin kakan nasu kuma bayan na
mahaifayar su da ta sha a waje duk wanan zumu din da take tunda taji umma tayi wanan
maganan tasan ba za a barta yau ta saka kayan a jikin ta ba ke nan.
Mahaifiyar nata tace wallahi umma ba hankali ne da yarinyar nan ba a waje ta samay ni ina
fitowa ta tare ni da zancen kayan ashe bayan mu baki mukayi a gidan kuma ?
Umma tace kin san halin kubura ai da wauta kamar wani zai kwace mata rigar ta dauki son
abin duniya ta dora a ranta.
Ai wanan yarinyar girma take tana cin kasa ko yaushe bata abin masu hankali ita, inji
mahaifiyar nata tana fadin cikin takaicin diyan nata da take ji.
Umma tace dazun su Aisha suka iso muna da abin arziki kin san su basu gajiya ko yaushe
zasu zo da irin abin arzikin da zasu kawo muna.
Wanan ma duk mun samu wanan tsaraban sai ita yar douki ta ishi mutane da magana kamar
ita kadai akaiwa tafiyan.
Ai Aisha akwai alheri mama ta kara fadi ni dai ina rakube a kofan dakn mu ina sauraren su
duk raina a bace kan rashin yarda in saka sabon kayana inga yadda zai min kyau a jikina a
lokacin.
Don gani nake kamar gobe yayi nisa a gare ni kaya tun daga lagos ace kuma ba zan saka ba
wai sai wani gobe can haka dai na hakkura dole.
Karshe mama ta baje dan tsaraban data sawo muka lakumay a furin ta shiga ba umma labarin
tafiyan nasu da wace suka je gaidawa din.
Tun da safe hayaniya tsakar gidan su ne ya tada ita tashi tayi tana mustsike isanuwan ta tana
sauraren muryan umma dake zazagawa iyayyen ta masifa.
Kamar ba ita bace suka kwanta lafiya da maman nata a dare jiya wanan abin idan da sabo
hadiza ta saba dashi a gidan su.
Don tun bata san fada ba ta bude ido dashi yadda Umma kan tasa iyayyen ta mata tana
masifa dasu a gidan kan dan abu kadan da bai taka kara ya karya ba a gurin mutum.
Ta kashe kunne tana sauraren umma kakan su ta wajen uban su tana bala,i da iyayyen ta
mata a gidan tana fadin.
Don wulakanci da rainin hankali wanan dan kokon ne za a zubo min shine zan sha in koshi
karshe kuma yaran ku su dawo su sha a gurina.
Taji muryan mama tana fadin kiyi hakkuri umma kullun kokon ne ba yawa iyakar shi ke nan na
dama muna don ba yawa ke da shi kawai kuka samu.
Don ko yaran ban zubawa ba yanzu nake son in dan gwaba muna sauran tuwon daya rage da
gutun raman dana shanya mu karya dashi ni da su.
Tace ai haka zaki ce dama da anyi magana ki wani marairaice wake gata Allah kin sa min da
a gaba kina ta wahalar dashi kullun ku ke nan cikin haihuwa a gidan nan baku san matse kafa
ba ku ko irin dan abin nan na zamani da matan yanzu keyi ku ba a samu a gurin ku.
Ko wace sai kirin tara diya wa mijin ta kullun suna fita suna nema kamar ba nema sukeyi ba
basu da hutu idan sun kawo kuma ku cinye daku da diyan ku.
Fitowa hadiza tayi ta tsaya a kofan dakin su tana sauraren fadan umma din na ba gaira ba
dalili da takewa mahaifiyar ta da ta dawo a daren jiya din.
Bata farga ba sai rankwashen kakan taji ya sauka a kanta tana fadin munafuka kin wani tsare
ni da ido fiki fiki kina kallon bakina don rashin kunya.
Baku da wani amfani sai naci daku da iyayyen ku sai dai in an kawo ku far ma abu da ci ku
taru ku cinye shi a lokaci daya don fitina.
Fitowan kanin mahaifin su daga daki yana fadin haba umma jiya fa saude ta dawo ai kamata
yayi a jika mata kafin ta dawo ta samu sai ayi shi a wadatace yanzun dai wanan fadan da kikeyi
ai ba ta da laifi ita.
Ta juya gurin shi tana fadin to ubana sai kai min fadan abinda ya dace inyi din tunda ni ban san
yakamata ba yanzu ai.
Fitowan wan mahaifi mu daga nashi shiyan yake fadin umma ke da wa da safe haka ya
karaso gaban umma din yana gaida ita da kwana.
Yana fadin umma barka da kwana an tashi lafiya ban san kin fito ba ai sai yanzu danaji muryan
ki a waje.
Ai kasan na tashi tunda kaji murya na din ai kasan garau na tashi ke nan yayi yar dariya tare
da fadin haka ne kuma umma muryan mama ne ke gaida Abba din da kwana.
Ya juya gareta yana fadin saude an tashi lafiya ya gajiyan tafiyan ya kuka bar mai jikin kuma
ta amsa a sanyaye da fadin da sauki yaya mun samu an sallamo ta daga asibiti tana gida.
Umma ce ta katse su da fadin kayi ta kaunar uwarka ka fita zance na ai tunda duk ta hade ku
gidan ta shanye baki daya.
Kuna jina da safen nan ina masifa da ita shi wanan ya fito yana wani juya laifin a kaina kai
kuma ka fito kana wani gaida ita.
Kaga ke nan ta zama lami kanwata gare ku ta juya tana fadan ta dauko ma baba kwano tana
nuna mai tare da fadin ka duba wanan dan kokon da Saude ta zuba min don Allah.
Ita baga nemowa ba sai idan an nemo dafawa yazama rowa a gare ni baba yace haba umma
ai naji abinda kabiru ya fada maki yanzu ina daki.
Yace kiyi hakkuri da abinda kika samu kin san ko banza saude mijin ta baya gari ba wai
abincin suke dashi ba kamar ko wa.
Ki bari idan sauran sun dama a kawo maki nasu tayi mai wani kallo gami da jan tsuki tana
fadin ai gara saude din har naga nata matan ku da suke saraki ko fitowa basuyi ba balle su dora
wuta.
Suna daki sun mike kafa sai idan an kawo min su turo yaran su karya a gurina idan na hana
kuma aji dadin yin gulma na na hana jikokina abinci.
Baba yace haba umma su sun isa ma su zage ki ko suyi gulman ki tunda su basu girka ba sun
baki akan lokaci.
Murya a sanyaye mama tace umma barin in dauko maki na wurin yushau don dama ke dashi
kadai na sawa sai ku kara idan ya fito na diba mai gwaben yaci.
Ta shige daki sai gata da kofin silver mai marfi dan madaidaici da take zubawa baba yushau
kanin mahaifin mu abin karyawa a cikin sa ta kawo gaban umma din ta aje mata.
Ta kalli kofin da fushi ta bude tana dan jujuya kokon dake cikin kofin tana fadin ji wanan wai shi
za a ba mai karfi kamar yushau ya karya dashi da safen nan sai ra dauko wanda aka zuba mata
din ta kara mai kofin ya taso kokon yai yawa ta rufe ta aje a gurin ta.
Bata mika ma mama kofin ba baba kabiru ne yace umma ki mika sauran wa yaran su sha
tunda basu samu ba in yaso ida saura sun dama a kawo maki sai ki, , ,
Bai kai karshe ba ta tare shi da fadin kabiru ka fita idona wallahi kafin in saba maka wanan
kokon na matan ku da suke damawa ruwa ruwa kamar ruwan kasari ai sai ku da yaran ku.
To kuma umma kike mata wanan masifan haka bayan kin san gaskiya idan ba girkin saude ba
baki son na wani.
Ta bishi da harara ya bar shiyan namu zuwa waje bai wani dade ba sai gashi ya shigo da
tuwo irin na sayarwa dinnan ya kwala ba hadiza data gama sallah kira.
Ta fito yace su dauka suje suci da kannen ta a dakin su ta karba tare da godiya don haka
maman su ta koya masu yi din idan an basu abu komai kankantan shi suyi godiya.
Umma hauwa itace mahaifiyar iyayyen mu maza ta haihu da yawa wasun su sun mutu tun
suna yara sai iyayyen mu ne suka rage su kadai a raye su hudu maza mata biyu.
Baba Sahabi baba gwago habiba gwago laure sai mahaifina da baba kabiru sai autan ta baba
yushau da baiyi aure ba.
Mahaifna shi ba mai zama a karkaran mu bane don yafi fita zuwa neman kudi sai ya kwashi
watanni yake dawowa da dan abinda ya samo.
Sai ditan kishiyan kakan mu da suma suna da yawa a dakin su don sun fi iyayyen mu yawa
duk muna zaune ne a gida daya dasu sai wa yanda basu garin ne basu zaune a gidan.
Auren zumunci iyayyen sukayi don hadin gidane da mahaifina da mahaifiyata diyan mace
dana miji suke don haka umma ta zama gwagon maman mu ke nan.
Amma wanan baisa mama ta samu ragwamay a gurin umma ba duk da zumuncin dake
tsakanin su don Umma ta kasance mace ce mai fada da jinini ga saka ido sosai a gareta.
Duk kusan haka take da matan baban nin nawa ko yaushe babu mai fari a gurin ta ita a ko
yaushe kusan kanta ta sani fiye da kowa.
Iyayye na kaf sunyi karatun zamani gaba dayan su sai matan ne basu samu yi ba don akidar
mahaifin su ne mata basu karatun boko a gidan sa.
Bai bari su wani tasa sai yai masu aure wanan dalilin ne yasa yanzu iyayye mu suka fara saka
mu karatun boko mu dake tasowa a cikin su.
Duk wanan fadan na umma tana kokari wurin hada kan diyan ta matsalan ta ya tsaya kawai
iya sarakanta da diyan ta suke aure sai ko mu jikokin ta da bata faye wani wasan jika da kaka
damu