Author : Mai Dambu Category : Read Hausa Novels
nasara"
'''' Tunda ta bashi zoben ya saka a cikin aljuhun rigarshi, bai kuma bin takan zance ta
ba.
Mata da yawa an kawo su cikin masarautar musamman bangaren shi aiki, bai taɓa ganin
wacce ta iya kallonshi ta gaya mishi magana sai Safinah, ita ce ta an karar dashi dukda yana
sane, dan Bayan abinda Kakan Ghaniyu ta gaya mishi, Baban Ghaniyu ya bashi shawaran ya
tafi niman ilimi Addinin, shine dalilin da ya sashi tafiya Saudiyya karantan Islamic law, a
shemaranshi na biyu ne, ya dawo samu labarin mutuwar Hakeem, lokacin Ghaniyu yana
shekarar shi ta karshe a makarantar horan Yan sanda, amma haka aka yanke mishi karatunsa,
ya dawo yana kula da lafiyar Ashraf,
Abinda Ya fahimta shine ba mutuwa Hakeem yayi ba, kashe shi akayi, dan haka ya shiga
bincike amma bai samu kome ba, da zai koma ne yake Ghaniyu suka tafi,
Bayan ya kuma nimawa Ghaniyu damar karasa karatunsa. Na dan sanda a nan
Saudiyya, sai da suka kwashe shekaru uku, sannan suka dawo, rana da suka iso suka haɗu da
Fahad.
Shima Fahad Baban shi yayi aiki da Sarkin Abdullahi mahaifin Ashraf, wani ziyara da ya
taɓa kawowa Ashraf, har yaso gaya mishi wani magana, bai samu damar haka, toh a hanyar
komawarshi gida aka sami gawarshi.
Dan haka Fahad ya basu shawara su shiga aikin tsaro kasar, amma dole sai Ashraf yayi
amfani da ƙarfin ikon shi dan a basu aikin sirri,
Fahad ya karanci ilimin kimiyya computer, dan haka Ashraf da kanshi yaje har ofishin
ministan tsaron da shugaban kasa, aka basu iznin shiga aikin.
Kuma dake suna da goyon bayan shi basu wani gardama ba, inda a ranar aka kirkiro, Jordan
26 Agent, inda suka sami wasu tsofin sojojin da yan sanda, da kuma masu aiki a lokacin, aka
shiga basu hoto na musamman,
Sun same shekara biyu suna samun horo, kafin suka gama, Ashraf ya dawo ya cigaba
da zama a matsayin Sarki, a idanun jama'a. A gefe guda kuwa yana aikin bincike sosai.
Babbar matsalarshi yana niman inda mahaifiyar shi take, tunda yana zuwa Oman kuma
suma suna zuwa masa, kwatsam sai ga Alie ya kai Safinah zai sayar da ita, daga cikin mutanen
da suka ja motar, har da Fahad shine Yaron kazab, shi yasa biya kuɗin ta.
Hotonta ya ɗauka ya turawa Ashraf, yana ganinta. Ya fara binciken akanta anan ya fahimci
yar jarida ce, kuma ta b'oye bayyanta. Sake turawa Fahad sako yayi akan daga wani yanki
tafito.
Shi kuma ya turo masa da cewa.
Daga Senegal, murmushi yayi bai kuma bin takanshi ba,dan shi yasan koma a binciken da
yayi dukda rufe information ɗinta, sai da yasan yadda yayi hanking ɗinta ya fidda kome akanta,
printing din hotonta.
Tunda ta shigo gidan yake jiran ta inda zata fito mishi, bata fito ta ko ina ba sai ta masa
katsalanda a cikin al'amuran shi, haka yayi mishi dad'i, ita ce mace ta farko da ta sanya shi farin
ciki ta hanyar gaya mishi gaskiya, taurin kai, kafiyarta haka ya matuƙar burgeshi.
Gabaki d'aya rayuwarshi babu mace dan shi abinda ke gabanshi ya hana shi fahimtar wata
mace.
Sannan shi bai fara sonta bayan ya sameta ba a'a sonta ya fara ne daga lokacin da Fahad ya
turo mishi hotonta, Dan Koda ta fara aikinta da gaya yasa aka ki bata d'aki, kuma ya shiga bata
aikinta wahala, kuma sai yaga bata damu ba.
Da kuma tasowa tsoma kanta Cikin sha'anin shine ya sa ake ta bata wahala, dan Ghaniyu
yasha mishi magana da a sassauta mata, akan haka sai da ya bawa Ghaniyu hutun sati biyu,
dan haƙa ya cigaba da zuba mishi Ido,
Abubuwa da suka faru daga farkon labari har zuwa, rape ɗinta da yayi. Lokacin da
Ghaniyu yazo ya samesu fita yayi yaje ya tawo da Fahad da kuma, Azrah ita tazo ta sanya
mata kaya, Ghaniyu ya dauke ta zuwa can shashin bayi, Fahad kuma da wasu kartin maza
suka riƙe Ashraf wanda suna tashinsa ciwon ya kuma tashi, Danne shi sukayi aka fara aikin, basu fadi wanda ya turo su ba, a haƙa suka fita.
Bayan ya farka ne yake gaya musu mafarki da yayi, sunkuyar da kai yayi tare da rike
kanshi.
"Na cuci kaina na zalunci yarinyar da bata zo dan cutar dani ba."
"A'a Sultan ka bar fadan haka, kaddara ce kuma babu wanda yafi karfin haka "
Sun ɗauki lokaci suna nuna mishi yarda da suka yi da shi.
Sai abubuwan suka faru daga lokacin har zuwa yanzu.
Tunda da abin ya faru ya shiga damuwa, a hankali ya fara fahimtar sauyi daga gare ta
musamman yawan amai ko tayita amai, dukda yaso ta bashi haɗin kai a dubata taki, karshe har
ta zuba mishi guba, a cikin abinci.
Bayan an rufe ta yasa aka dauko mishi kayanta nan yaga passport ɗinta, wani abinda
Safinah bata sani ba, ai Ashraf yasan cewa guba zata sa mishi, dan haka da ta kawo shayin bai
sha ba, sai ya zubda a kasar table, sannan bakin shi dama ya kuntso kumfan brush ɗin da yayi
( mugu) da taga yasha dan har kekenshi take, shi kuwa bayan wasu lokuta ya fara
fidda kumfan, ganin haka ai kuwa ta fara ihu, kuma dama sunganta. A Cctv shi da Ghaniyu da
Fahad, ganin yadda ta rude ga Ashraf a kwance, su Ghaniyu suka fita da ita zuwa gidan kaso.
Shima ya tashi yana wani murmushi miskilancin, sannan yace.
"Zan kwanta dan nasan yanzun motar asibiti zasu zo, Kuma Hikimarku tayi dan bansan iya
mutane da aka kashe sabida Ni ba."
Yana kwanciya sai ga Ukshe da Abu Zarri
A hanzarince suka nufi dashi.
Daga nan har abinda ya faru na barishin Masarautar da ita,
Lokacin da yaji labari bata da lafiyarta, yasa aka dubata nan suka tabbatar da tana da ciki na
kusan sati Uku shi kuma yana don maida Ita gaban iyayenta, gashi ya son zuwa amsar
takardun shi a Saudiyya. Kafin su bar kasar sai da yayiwa Dr Fu'ad magana, shi Kuma ya haɗa
shi da Hameeed. Da farko Hameeed yaso bayyana mata gaskiya amma ganin tana cikin damuwa yasa shi
yasa bai fada mata aiki aka sashi ba.
Koda Ashraf ya dawo ya samu tayi nisa a soyayyar Dr, abin ya bashi haushi, duk
yadda Dr yaso mishi bayani yaki sai da ita ta nuna bata yinshine, yasa shi hakura.
Amma maganar gaskiya Ashraf bai so ta auri Dr ba. Amma ganin haka zai iya haifar
mata da farin ciki ya sashi, hakura sai zamanta da Dr shima dai ya kai zuciya nesa ne, amma
kullum sai yaje Asibiti jin yaushe zai sake ta. Abinda basu saka shi cikin tsarin ba Anim wanda
fatalwansa ya sabbin rayuwarta.. .....
Ajiyar zuciya ya sauke tare da gyara kwanciyar shi.
Yana tsananin kewar tsiwar rigimarta yanzun yasan tunda tace sai ta nime shi.
***
Ina kwance inda nayi sallah ban kara motsawa ba, barci yayi gaba dani. Saboda jiya ban
samu barci ba.
Shafa min kan da ake ne ya taddani a barci, a sannu na buɗe idanuna, Ummi na gani tana
zubda hawaye.
Tashi zaune nima ina kallon ta, yadda take kuka taba bani hakuri, murmushi nayita na ciwo,
sannan na shiga labari abinda Hameeed suka min, ita ma kuka take ta bani labarin haukacewar
da Mamie tai sakamakon Kama aljani ta.
Hakuri tayi ta bani tare da gaya min sharrin Mamie ce.
***
Lokacin ya tafi dan har na koma gida, na cigaba da zaman idda, sam bana jin daɗin kome.
Kwanciyar tashi asarar me rai, yau nice saura wata ɗaya na gama idda.
***
"Don Allah idan laifi na maka ka gaya min. Kusan wata uku da zuwa na amma kamar wa."
Mika mata hannu yayi, ta tsaya tare dayi ƙaramin tunani kafin ta taka zuwa gabanshi, sanya
hannunta tayi cikin shi sannan ya ajiye ta bisa cinyar shi..
"Natasha ba lallai bane ki gane halin da nake ciki ba, saboda ke Ni kike so? Ni kuma
zuciyata yana gareta, taya zaman mu zai haifar da da mai ido.
Gashi ta kusan gama iddarta ina so samu ne, zan sawwak."
Rufe mishi baki tayi da hannunta.
"Wallahi zan iya zama da kai Indai zaka rike aurena, ka rufa min asiri, kasan ba karamin abu
bane zai sa miji ya saki mace, a cikin tarihin masarautar mu ba a taba samun ba, don Allah
karka sa a min kallon wacce bata san darajar kanta ba, don Allah kayi hakuri Ni na yafe ma
bazan kuma maka magana ba tunda ba kaso, Allah ya baka Safinah." Yadda tayi maganar sai da tsigar jikinshi ya miqe, sabida muryanta rawa.
A hankali yake kewaye hannunshi a tsakanin k'uib'inta zuwa shafafeffen cikinta tare da
manna mata, kasancewarta me karancin shekaru, dan haƙa ya dauke ta zuwa other room
( Yau ma nasan haushi zai kama wasu naki leka d'akin Don Allah ku rabu dani bazan leka
ba wato kai ena Kubar turani )
(A fito lafiya AshTash)
***
Muna zaune a falo yau na tashi da kewar Yarana da suke gurin Nannah, kamar wanda aka
wurgoshi na ganshi a kaina!
Waye kenan
Assalamu alaikum
_kuyi hakuri ina ta zirga zirga ne Insha Allah zaku samu zuwa dare Nagode _
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda
yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne
150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha
Allah*
Oum Muwaddah......
10.A firgice na tashi ina kallon shi.
"Don Allah ki yafe min! Safinah nayi da nasanin biyewa Ashraf."
Ban kalle inda yake ba na yi zama na ina gyara farcena, ganin baki kulashi ne yasa shi
matsowa kuwa dani zai tab'a Ni na saka mishi tsawa tare dace.
"Wallahi ka kuskura ka taba sai na baka mamaki. Kuma ka fita mana a gida Hameed ko nasa a
fitar min da kai, kaje Ashraf ya cigaba da juyaka."
Ya kasa bani hakuri haka yaja tsunami rayuwar shi ya fita daga gidan mu.
Kwallar da suka tawo min na maida dan nayi alkawarin bazan kuma wani kuka ba, kuma
dole nima na rama duk iskancinsa da suka min.
***
Rub da ciki yayi bayan ya gama turmusa Natasha wacce take matsar kwalla, idanunshi jajjur
ajiyar zuciya yaƙe saukewa,. tsabar damuwa da bakin ciki bawai dan bai same yadda.yake so
bane kawai kishin Dr yake
Musamman yadda ya fahimci mata daban daban ne,.wasu duk gyara da zasu yi bazasu kai
wasu bata tabbas SAFINAH mace sama da kasa, mace da duk namiji da ya rabu da ita sai ya
fahimci haka, sau d'aya ya makale mata ya fahimci ita tana cikin mata na musamman.
_Yanzun haka Hameed yaji lokacin da ya aureta?_
Haka yayi ta sakawa da kuncewa.
Tashi yayi tare da saka kayan shi ya fita daga d'akin.
Binshi tayi da ido kwalla na kuma sauka a idanun ta.
***
"Hameed! Baka kyauta min ba, karasa wacce zaka yaudara sai Safinah yarinyar da ta yarda
da kai sama da kome shine ka zauna ka cutar wai kana gaya min maganar banza."
Haka Ammah tayi mashi wankin babbar bargo.
Ya Kuma tashi ya bar gidan likita ba sauki ba, shi kanshi ya san yayi kurakurai amma dole
ya nemi ya yafer Safinah.
***
Wani abin takaici shine jinin karshe da zai tsarkake ni daga rayuwar Hameeed yaƙi zuwa
dan har kowa ya shiga tambayata ko na gama idda, shiru nayi ban kuma cewa musu cikanku
ba.
Duk yadda bawa yaso da rayuwarsa ya kasance sai kasamu matsala, rayuwar da babu tsarin
Allah a cikin sa shirme ne, kuma duk rayuwar da babu jarabtar banzan rayuwa ce, kai kanka
kaji cewa Allah ya halicci kane dan ya gwada ƙarfin ikonsa da buwayarka, shi yasa a cikin
Alkur'ani (Allah subhanahu wata'ala Yace ku zaga duniya kutafi kuga abinda baki taba gani ba, tayi hakan ya zame muku Aya
da izinin.)
Ai basan munje da nisa ba ko a iya inda muke munji kuma mun bika, don koda a Film ban
taɓa kawowa Ashraf zai buga wasa dani ba, shine coach din, shine reapre, sannan ya haɗa
team. Ba kome ya janyo haka ba, sai dan ya fitowa cikin mugayen mutane.
Sam babu tausayi ko imani sai tsantsan son kai, da mulki, indai har na sanya shi ya bar wasu
dabi'a tabbas dole na gama idda domin na saita shi yadda zan zan ji daɗin. Ya ajiye izza da
mulki,
*Ta ya?*
Na tambayi kai na! Lumshe idanuna nayi kafin na kuma buɗe su, akan window d'akina.
Hanyar sanya shi fita niman kuɗin aurena, matukar Ashraf ya iya kawo Sadakina a cikin
wata uku, zan iya auranshi, amma dole yayi wasa da hankali shi nima, yadda zai fahimci nima
ba saukine dani ba.
Lumshe idanuna nayi tare da gyara kwanciyata, ina jin na kama Ashu dam a hannuna zan
amince masa ne bawai dan ina sonshi bane, sam bana sonshi sai dai ya zame min dole na
gyara halayyar shine.
Sai da nakusan cinye watan baki daya sai ga bakona tsabar murna sai da nayi kuka.
A hankali na fara har na gama cikin kwanaki biyar, ina gamawa. Kuwa sai da kowa na
gidan ya fahimci haka domin dai da a takura nake, yanzu kuwa na fara walwala kamar bani ba,
dukda kulawar da nake samu. Daga Ummina da Abba.
Ina tsinci wake dan Yau fara da mai muke don ci, tunda nace ina so kowa ma yace zai ci dan
sun san cewa in dai nice zan yi abinci toh zamu ci dad'i, idan Ummi ce zata ce so fito suyi kome
da kansu. Ni kuma ban cika don nayi aiki da kowa ba.
Dake na maida hankalina tuni na gama, sannan Batul da Khalilah suka yanke ganye da
kwai, Ni kuma na fita na bar musu kitchen ɗin, naje nayi wanka.
A falo na same shi da Ummi suna gaisawa, sam Ashu babu yarinta a tare da shi ko nace
kuruciya dan duk lokacin da zaka gashin kwarjinin da kima ne ke kwance a fuskar shi, mulki ya
b'oye ya kuruciyar shi.
Kanshi a sunkuye yaƙe magana, Ummi kan banda murmushi babu abinda take, juyawa tayi
cikin harshen shuwa tace min.
"Baki ganshi bane,?"
Shiru nayi tare da bata rai nace.
"Sannu"
D'ago kai yayi ya kalle inda nake, tabbas nice nayi magana, take abinda yayi min lokacin da
muka je gurinshi a gidan yarin ya dawo mishi.
Juyawa tayi zata balbaleni koda fada taga wayam kwafa tayi. Irin zata gamu dani sannan
suka cigaba da hirar su.
Wanka nayi nasaka riga da zani, zangon anyi shi kamar skirt. Dan har da tsagu a baya, sai
daurin dan kwalin Maryam Babangida da nayi wanda aka mai dashi Zahra Buhari. Fara hoda da
kuma, da man baki da nashafa, sai dan kwalin da na zizara a idanuna, na Humra na shafa na
fito a sannu nazo na wucce su, kitchen na shiga na samu har sun gyara kome, Sannan na zuba
abincin nake table na fara ci, na samu Ummi bata falon. Hango yayi ina cin abincin a nutse.
Miqewa yayi ya tawo dinner area yaja kujera ya zauna, kallon yadda nake ci