Masarautar jordan Book 2 Complete By Mai Dambu

Author :  Mai Dambu Category :  Read Hausa Novels

Chapter   6 / 37

15K to 18K   out of 109.3K words

Yau aka shirya dinner kuma a cikin babban filin masarautar, za ayi dan haka Kowa zai.

Karfe tara aka fara hidimar, dukkanmu mun shirya cikin wasu gown Ni bawa dark green, sai
Dr da yasaka suit ashe colour, muka fito.
Hannunmu sarke da juna, muka je inda aka ajiye abin zama muka zauna. Amarya ta riga
Ango fitowa.
Yana can ya saka tarukan hannunshi, a fuskar shi yana tunani. Sau uku Nannah tana zuwa da
kanta, Amma yana kin buɗewa. Duk wandaake tunanin zai masa magana yaki fitowa, ba dan
me Dudu ya gayawa Dr ba sai dai ya tashi ya riko hannuna, muka nufi part dinsa.
Umarni Dr ya bani na buga, amma yaki budewa sai da nakiya aunanshi sannan ya bude
kofar, ya fito cikin shirinsa.
Mikawa Dr hannu yayi, suka gaisa sannan muka fito, ina manne da Dr. Kamar bai ga
abinda muke ba, nan kuwa idanunshi na kanmu yake. Ranshi na kara ɓaci sam baya jin zai iya
yafewa zuciyarshi akan katsalanda da tayi mashi na rabashi da abar kaunarshi,
Har muka zo inda zamu zauna, shi kuma ya wucce gurin zaman shi, hankalin mu kwance
muke hira da Dr tare da Dr. Kowa yaga yadda muke cikin farin ciki sai mun burgeshi.

Anyi nisa a shagali na zare jikina zanje ban daki.
....

Har na isa na gama uzurin nafito, a baƙin kofa na ganshi tsaye, tamke fuskana nayi cikin sauri,
yayi maza yasha gabana.
"Meye laifina! SAFINAH! Kawo hannunki kiki, SAFINAH mutuwa zan."
Matsowa nayi zan wucce yayi sauri zai tabani nayi, na matsa cikin zafin nama ya kai

hannu zai tabani a karo na biyu kafin yayi yunkurin tabani na Kifa mishi mari, wanda yayi
sanadin zubda kwallana, shi kuma hancinsa ya fashe har yana zuba da jini.
D'ago kai yayi cikin izza hadi da mugun mulki, jinin sarauta na yawo a jikinshi, chafko
wuyata yayi ya matseni a bango, kafin yayi kokarin haɗa jikina da nashi na kuma zuba mishi
wani mari, na kuma marin shi.
Zare hannunshi yana kallona, zuba gwiwarshi muryanshi na rawa, yace.
"Ki min kome SAFINAH! Kawai ki dawo garemu"

"Kai jahili ina ne? Da aurena kake bina, Muh'd ka gaya min meye nayi maka da zafi haka
ka rabu dani mana, don Allah ka barni nayi Rayuwata da mijina."
Tunda muka fara rigimar Dr yake tsaye, bai iya motsawa ba, sai da yaga zan fito ya
juya da sauri ya koma inda ya muke, ina zuwa gurinshi na zube a jikinshi ina kuka nace.
"Baby! Mu bar garin nan."
Rintsa idanunshi yayi zuciyarshi na zafi, ji yake kaman ya an cimma mishi wuta, ji yaƙe
kamar ya rufe Ashraf da ya fito jikinshi ba laka, yaƙe ya zauna yana goge hanci sa da jini yake.

Kukan da nake sosai nake ganin kamar hankali mutanen zai dawo gare mu ya mike dani
muka koma masauki sa, muna shiga cikin d'akin na ajiye Ni. Ya juya abinshi.

Wannan shine karon farko da ya fara jin ciwon akan aurenta, bai ga dalilin da zai bar Ashraf
yana tun kara matarsa. Dole yau zasu bar garin dan.

....... Nayi kuka har na godewa Allah, banga Dr ba, har kusan Asuba, da nafito na hango
shi zauna a kan kujerar, takawa nayi gabanshi, tare da saka hannuna akan gwiwarshi nace..
"Hameed! Nasan kaga abinda ya faru tunda kaki zama kusa da ni Hameed do.."

"Don Allah karka juya min baya ko? Safinah da tun farko kin nuna min Uban yaranki SAFINAH
da ban shiga rayuwarki ba, Safinah abinda kika min baƙi kyauta min ba, amma banga laifinki
ba, nine me laif.."
Rufe mishi baki bayi da hannuna, a hankali na shige jikinshi, ina kuka.
"Don Allah ka yafe min wallahi kai nake so, Hameed daka rabudani gwara ace bana numfashi.
Don Allah kabar Mutuwa ta rabamu, karka.".

Haɗe bakinmu yayi, nima na riƙe kanshi. Shi kuka Ni kuka dan mun fahimci rabuwa da juna ba
abu me sauƙin bane, tun daga wannan kiss din abubuwa suka sauya, sosai ban taba jin dadin
kasancewa da Dr ƙamar yau, shima ya fahimci haka, kwantar da kaina nayi a kirjinshi, ina
sauke ajiyar zuciya, a hankali yake shafa bayana, a Sannu har barci yayi gaba dani. Leka
fuskana yayi a hankali yaga yadda yanake barci, shafa fuskana yayi a hankali don da tausayi, ji
yayi zuciyarshi tayi mishi nauyi tausayin kanshi yake ji, wani iri yake ji. Bakin yanayin da yake ji
a jikinshi. Musamman mugun ganin da yayi ya kuma karya mishi zuciya.

Lumshe idanu yayi a sannu barci yayi gaba da shi, bamu farka ba sai karfe shida na safe
da sauri muka shiga wanka a tare, muna fitowa sallar muka gabatar, sannan muka koma gado

Dan barci bai ishenmu ba.
Ina manne cikin jikinshi, kaina yana kirjinshi, dan haka fitar numfashinsa yana sauka a
kirjinsane, shafe kaina yayi cikin jin kunci irin na wanda yake jin zai rabu da abinda yafi so a
rayuwar shi, damuwa ce ta ƙara mishi yawa. Mikewa yayi zai fita daga d'akin, yayi maza tare da
riko hannunshi, nace. "My Man! Ina zaka je i need you."
Haurowa gadon yayi cikin sanyin jiki. Ya janye bargon ya shiga min tausa, juyar dani yayi
ya zuba min ido, ganin yadda nake mika yasashi shiga cikin bargo a sannu ya cigaba da min
tausar tare da salon shine me taba zuciya, lumshe idanuna nake ina bud'e su, shigewa jikinshi
nake sosai yasashi fahimtar ina bukace dashi........
Kuyi har maneje
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: *Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna
son Book ɗin Wanda yake a 500fs  +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
   *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne
150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha
Allah*

Oum Muwaddah......

MJ
BOOK-2
19-2-2020

️✌️

   "Hameeed! Karka juya min baya, a lokacin da nake bukatarka, Hameeed!"
              
      Cak ya tsaya hannayen shi duk suna cikin aljuhun wandonshi.
          D'aga kanshi yayi sama cikin jimamin hukunci da ya yanke, karshe yasa kai ya fita, wacce
itace fitar da yayi a rayuwata.

      *(Tabbas nayi rubutu akala goma sha tara a rayuwata, Masarautar Jordan yasani jin kaina
wata daban ban wannan shafin ya ƙaryata min da zuciya ya sani jin kamar nice jikina yayi sanyi,
ban taba duban rayuwar macen da ta rasa mijinta da yardanshi ba amma yau naji ina
tausayawa matan da aka shiga tsakaninsu,Labarin Sadaukarwa ce garesu)*
              Yana fita yaga Ashraf jingine da bangon, murmushi yayi sannan ya dafa kafadar shi,
yace.
"Yanzun na sauke nauyin da yake damun zuciyata, na bar maka baiwarka, amma kayi ƙoƙarin
janye tunaninta. Iya haka ne zai sa ta fahimceka, Don Allah nan gaba ka gaya mata gaskiya aiki
kasani ba yin kaina bane."

       Gyada Kai yayi tare da mai da kwallar da yake ciko mishi idanu.
"Nagode sosai Dr Abdulhameed! Tun daga haduwarmu kake taimaka min, sai dai bana jin
zan Safinah zata yafe mana, sabida munyi wasa da hankalinta."

"Toh! Wallahi kai da ita nikam aiki kasani, kuma nayi maka, bani da niyyar aurenta kasani.
Dan haka ya zama maka wajibi ka."
Cikin tsare gida Ashraf ya kalli Dr.
"Kayi hakuri! Yallabai."
Fita yayi daga ware din zuwa inda motarshi yake, ya zauna tare da kallon Sa'imah wacce ta
cika ta batse.
"Ayya na zata kwana zaka a gurin ta!"

"Bazai yi na kwana ba, sabida iya abinda aka dauke Ni nayi da akwai wani abu bayan haka da
zanyi."

Cikin jin ba dad'i tace.
"Ban gane ba!?"

"Eh zaki gane"
Nan yaja motarshi ya bar asibitin,
***
Kuka nake me mugun cin rai ji nake kaman na had'iye zuciyata na huta, ina jin aka bud'e kofar
ban daina kukan ba, jan kujerar yayi ya zo dab dani ya zauna, yana kallon yadda na fita
hayacina, amma dan jaraba shi kukan da nake dad'i yake mishi sai wani lumshe idanunshi
yake, tare da gyada kanshi,
Shigowar Dudu bai sashi d'ago kanshi ga kallona da yake ba. Sai ma kura min ido da yayi, da
sauri Dudu ya iso gurina yace.
"Didi! Kiyi hakuri don Allah. Wallahi banda Ashraf da yaje gida dazun ba Allah."

Zuwa yayi ya tsaya duba ruwan da aka saka min. Kallon takardan da yake hannuna yayi, a
hankali ya zare a hannuna, tare da warwarewa.
*Ni Dr Hameeed nasaki SAFINAH saki d'aya."

Rintsa idanunshi yayi cikin zafin zuciya, yafi minti biyar a haka, Sannan ya buɗe idanu ya,
"Safinah me kulawa Hameeed ya sakeki"

"Sabida yagama yayinshi da ita, kamar Gwanki"

Cikin mugun fusata yayi kan Ashraf wanda yayi fuska kamar bashi yayi magana ba, dan dama
tsakanin dudu da Ashraf bawani jituwa bane, kawai suna dan zumunci ne sabida, yaran dashi
suke tsakani.

Kwalar rigar Ashraf ya cukumo ya kawo shi bakin kofa ya watsar cikin gargadi yace.
"Kar na kuma ganinka a rayuwata, ka kyalemin yar uwa ta huta."

"Idan zaka wulakanta Ni sau dubu bazan daina ba, sabida ita ta koya Min kome, zaka iya
sawa ayi min kome Ni dai don Allah ko sau ɗaya ne kabarni na dinga ganinta"
Banka mishi kofa yayi tare da komawa gurina. Zama yayi yana son sanin abinda ya faru.
Amma na kasa cewa kome sai kuka, Banda kuka.
Har dare Dudu yana tare dani, duk wani kulawa shi yake bani.

***
A hankali sauki yake samuwa, gefe kuwa Dudu. Na kaftawa Ashraf wulakanci, kuma yaki ya
barshi ko sau daya ya ganin, har ofishin Dr Dudu yake, sukayi fada sosai karewa ya ajiye musu
aikin su, babu abinda ya ƙarya musu zuciya akan Dudu sai kukan da yake tare da cewa.
"Nan ka bada lokacinka akan SAFINAH, ashe shigo ba zurfi kamata, tare da cutar da zuciyarta.
Meye laifin yarinya da ta mutu akan ka, ban taba jin tsanar kowa a duniya sama da kai ba,
yarinyar da ta hadu da jarabawar Rayuwa zaka wulakanta. Ba kome mun gode sosai ai kayi
namijin kokarin, ga takardanku. Na ajiye muku aikinku."
Yana gama gaya musu haka ya juya yabar Office ɗin, yana zuwa d'akin da nake, yaja
kujera ya zauna yana kallona, na cusa kaina a cikin cinyata.

"SAFINAH! Haka zamu cigaba da zama baƙi ce min kome ba, aiko sau daya ne zaki ce min
wani abu."

Duk maganar da Abdullahi yake naki d'ago kaina, banda zubda kwalla da nake bana kome,
sam bana iya cewa kome.
"Toh tashi mutafi gidana."
A sannu na d'ago kaina. Na sauko daga gadon, na dauki hijabi na nasaka sannan na jira
shi ya gama hada kayanmu, haka muka fito jikin Dudu na koma tare da rike rigar shi, ina b'oye
fuskana a jikinshi.
Muna zuwa gun motarshi ya buɗe min na shiga tare da kira kaina.
"SAFINAH!!!"
Muryar Ashraf naji, sake rintsa idanuna nayi, yazo da gudu zai buɗe Kofar, tureshi Dudu
yayi ciki masifar da dama abokin mutuwa yake nima.
"Wai kai wani irin masifa ne haka? Ka rabu da ita dole."
"Don Allah ka barni na ganta ko sau ɗaya n"
Wanka mishi mari Dudu, bai damu ba ya kuma zuwa zai buɗe motar, Dudu ya sake
tureshi. D'ago kai nayi naga yadda dudu yake dukan Shi.
Wani irin tashin hankali naji ban san lokacin da na buɗe kofar motar Ba.
Zuwa nayi na riƙe hannunsa, ina girgiza mishi kai hawaye na zuba daga idanuna bakina
na rawa nace.
"Toh meye amfanin haka, kamanta waye shine? Ko dan baka san irin Daular da ya fito bane,
masu tsaro dari biyar suke tsaron lafiyar shi, kartine majiya karfi, yafito ta gidan da ko karar

sautin faduwar abu akaji mataki ake dauka, shugaba ne na al'umma guda. Kabilu uku ne a
karkashin mulkinsa, kimanin yan majalisu dari da goma ke, bashi goyan baya, hatta manyan
attajiri da yan kasuwa suna bayan shi, shine zaka dake shi, yaushe ka zama mara tausayi da,
da zaka dake shi, badan Kowa ba kodan su Mariamah da Husnah Zaka daga mishi kafa, kazo
mujee yanzu ba lokacin rigima bane."

Jikinshi yayi sanyin yabi bayana, muka shigo motar, kauda kaina nayi dan bana son na
cigaba da ganin jinin da ke zuba a fuskar shi. Tunda muka fara tafiya, babu wanda ya iya cewa
kome. Banda kwalla da ya ɓalle min a idanuna babu abinda nake, tissue ya mika min na amsa
a hankali. "Kiyi hakuri! Amma wallahi matukar zai zo inda yake zan wulakanta shi, gwara ya
nisanceki shine zaman lafiyar shi"
"Toh meye yayi maka?"
Na tambaye shi muryata na rawa.
"Didi na tsaneshi! Sabida shine mafarin matsalolinki"
Murmushi nayi dan ya bani dariya da tausayi.
Ban kuma ce mishi kome ba, sai dai fuskar Ashraf yaƙi fita a cikin idanuna, ina masifar jin
zafin digar jininshi, kurawa hanyar ido nayi.
Wasu abubuwan na tuna kuka ya kwace min, yama rasa tacewa.
A haka muka isa gidanshi, dan yasan koda ya kaini gidan mu akwai matsala.

***
"Amma me yasa ka bar shi ya dake ka haka?"
Goge fuskar shi yayi. Sannan yace,
"Bazan rama ba, sai dai nafison duk lokacin da zai min haƙa yayi akan idanun ta, so nake na
suna girma matsayina a zuciyarta, kamar yadda ta same matsuguni a zuciyata so nake naga
haka a cikin idanunta, duk abinda ya faru itace ta kirkiro shi, amadadin ta tsaya kome yazo
karshe sai taki, Nima kuma ban fahimci ma'aukin abun ba, sai yanzu dan haka ku barni da su."
"Amma naga dai, kana da Matarka toh ka rabu da Safinah mana."

"Hmm! Dr Fu'ad bai gaya maka waye Ni bane? Ni ba a bani umarni, umarni na iya
haɗawa."

Kura mishi ido yayi sannan ya janye daga gareshi. Dan shegen kwarjinin Ashraf yake
dashi kana ganinshi kaga jinin sarauta, amma ba daga nan abin yake ba, sai ya kalleka kukayi
ido biyu dashi anan zaka fahimci karfin mulkin a idanun sa, domin. Tsakarka yake babu tsoro a
cikin ta sai tarin izza. Kome girmaka da zaran kunyi ido biyu toh gabaki d'aya dole kayi ladab,
mafi akasari da idanunshi kawai yake horasu Ghaniyu.

***
Tunda na dawo gidan zancen da sauki kenan, amma batun aljanu nan

6 / 37