Masarautar jordan Book 2 Complete By Mai Dambu

Author :  Mai Dambu Category :  Read Hausa Novels

Chapter   36 / 37

105K to 108K   out of 109.3K words

D'ago jajjayen idanunshi yayi akaina banji komai ba, sai ma kauda kan da nayi....


*Don Allah kuyi hakuri tun jiya rabonmu da wuta! Shi yasa zaku pagen dan mitsitsi idan muka
samu wuta zuwa dare Insha Allah zan yi 48� Wannan labarin yayi tsayi da yawa, da alamu sai
mun shiga book 3 kenan Allah yayi mana jagora yasa mu dace duniya da lahira*
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda
yake a 500fs  +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
   *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne
150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha
Allah*

5️⃣0️⃣
   Ganin har lokacin Aamih tana aman kumfa, na shiga cikin kitchen da mugun gudu na dauko
mangyad'a na d'ura mata, komawa kan Aanih nayi, itama na juye mata, ita Maryamah tana
amai, Husnah shiru, banga Ablah a falon ba.
      "Ablah!!!!!!!"
  "Ummu"
       Naji muryan ta, a sukwane na juya, jikina na rawa.
Ganinta nayi rike da wani apple,  kuka ne ya kwace min, na janyo ta sannan na dauki wayata,
tsabar rawan jiki, dakyar na sami Number shi, yana ɗauka na fashe da kuka.

"Kazo yaran suna cikin hatsari, kowani lokaci zasu iya mutuwa."

         Kashe wayar nayi yi ina kuka, bai yi cikakken minti biyar ba sai gashi. A gigice shida
Ghaniyu, suka dauki yaran. Ni kuma na dauki Ablah har na kwace apple din sai na saka kuka
kuma baci zata yi ba, dole na bar mata, muka bi bayan su.

              Tunda muka shiga motar nake kuka, ina kallon yaran.
     Har muka isa asibitin aka shiga dasu d'akin gaggawa, haka su Dr Fu'ad suka yi takaiwa da
komowa.

              Zuwan wani likita dan kasar Lebanon, yazo wuccewa ya kallemu. Har ya tafi sai ya
dawo yasaka hannun ya amshi, kuka tasaka tana ihun ya bata abinta, tafiya yayi da apple din,
babu wanda yayi Wani yunkurin, dan muna cikin tashin hankali.

     Jaririn Natashah aka fara fito mana da shi, yaron me kyau kamar Ashraf.
Muna cikin wannan halin Dr Fu'ad, ya fito tare da kiran Ashraf zuwa Ofishin sa, yana shiga
yace.
"Fu'ad ya jikin su?!"
      Girgiza kai Dr Fu'ad yayi sannan yace.
"Kayi hakuri! D'aya ta rasu"
    Zaman dirshan yayi a Office d'in, tasirin kiran sunayen Allah ya rike shi, kafin ya d'ago kai
yayi yace.
"D'ayar fa?!"
 
  "Sakamakon bata mai da akayi ya karya ƙarfin gubar, tana nan sai dai ta jikata sosai."

     Bai kuma ce komai ba yafito  daga Office d'in.
     
  Tunda ya fito ya tsare Ni da ido, gabana ke faduwa, kukan da nake toshewa ne na shiga yin
shi sosai.
Kauda kanshi yayi sannan yaje gurin Ghaniyu yayi mishi magana, fitowar Likitan da ya karbi
apple a hannun Ablah yazo zai magana, Ashraf ya hana shi yace yaje yace yaje ya sami Dr
Fu'ad.

Nannah ya gayawa mutuwar Husnah, a fusace ta mike, shi kuma ya bar gurin zuwa
dakin da gawarta take ciki,
Ina cikin damuwa Nannah yazo zata kara min, dan d'aga hannun tayi zata mare ni na riƙe
hannun.

Sosai ta nemi duka na, na hana faruwar, haka Rigima ya kaure a tsakanin mu, fitowa da
gawar na kurawa Yarinyar ido, naje kan gawar na sake wani Irin kuka, me mugun cin rai.

Rike hannunta nayi nace.

"Wani irin laifi nayi haka da nake fuskarta hukunci haka, Ya Allah na tuba ka yafe min zunubi
na."

Fitowar Nurse daga d'akin gaggawar, tace.
"Yallabai d'ayar ma ta cika."

Ji nayi zan fad'i yayi maza ya sake jikin gadon ya rike Ni, gam nake rigarshi ina sauke
ajiyar zuciya, kafin nace.
"Alhamdulillah."
Cak naji hawayena ya kafe, tabbas lokaci yayi da zan bar Ashraf, dan Natashah tana cikin
mawuyacin hali itama, haka suka fidda yaran, muka nufi gidan.

Anan aka kira masu wankar gawa, suka musu shi kuma Ashraf ya kira su Ummi ya gaya
musu, zazzaɓi ne ya rufe ni. Dakyar yasani a gaba naje naga gawarsu, nayi musu addu'a.
Sannan na fita, wani irin dangana nake ji a raina, sai dai bana jin zan cigaba da rayuwa a
jordan. Tun daga ranar ban kuma ganin Ashraf ba, har sai dasu Ummina suka zo naga
idanunshi, abinda nake gani a cikin idanunshi yana kara rikita min lissafi, domin kuwa k'iyayyar
da ban san da ita ba yake nuna min, Ummi da Umma suka zo sai Abba, Dudu yana Ukraine
yana karatun da matar shi.
Kwanansu Ummi biyar suka dawo, ana gobe zasu dawo Abba na yakirani, naje inda
yake duk suna zaune na zauna a gefen Umma. Kallona suka yi sannan Abba yace.
"Kuyi hakuri! Allah zai baki wanda suka fisu! Sannan na fahimci kina cikin damuwa, kiyi hakuri ki
cinye jarabawarki, Insha Allah komai zai zo karshe."

Nasiha suka min, mun jima muna hira, kafin muka yi sallama, har zan fito naji Muryan Ummi
tana cewa.
"Alhaji idan zaman ba me yuwa bane ta dawo gida kawai, na gaji da fitina, nima ina son Y'ata,
ta bar mata D'anta."

"Amma Mariamah me yasa zaki d'aga murya ne! Idan kuma taji fa"

"Ai gwara taji, lokacin da nayo cikinta waye ya tayani sai wasu banzaye su samin yarinya a
gaba."

Ni dai nabarsu ban san ya suka kare ba, sai da asuba da zasu tafi. Dake jirgin biyar da rabi
na asuba, suka samu, ta shigo min, munyi magana sosai wanda naji du duniya bani da sama da
Ummina.

Iyayen Natashah sun zo sun dauketa, inda suka tafi da ita domin sai da suka yi uwaka
ubanka da Y'ar Uwarsu. Tunda Yaran suka rasu Ashraf ya fidda min wani iskanci, da bakar
magana idan yazo shashina, sai ya wucce dakin yaran yaje ya zauna, yayita tuna yaran. Idan

naga ya jima sai na biyo shi, koran kare yake min.

Yau ne dai da ya fara min na dakatar dashi.
"Ban san laifin da nayi ba kake min wannan tozarcin, Ashraf ban maka dole ba, kuma kai baka
min dole na zauna da kai ba. Dan haka rayuwa yana da zab'in shiga ko fita. Amma ba damuwa
gani na da kake a rayuwarka ya saka ke ganin na cutar da kai idan na fita daga rayuwarka, sai
kayi farin ciki."
Ina gama fad'ar haka na fita na bar dakin na koma nawa nayi kuka sosai, yanzun nake jin
mutuwar yaran, had'a kayana nayi dana Ablah. Sannan na dauki wata memo na rubuta mishi
sako.
_Nagode sosai da irin abinda ya faru_

Daga haka na ajiye biron na dauki Ablah,na goya sannan naja akwatina nafito bayanan, duba
agogo karfe goma, na koma na duba jakata, na debi kudi na zuba, sannan na fito na bar cikin
gidan a hankali na bar Masarautar baki d'aya.

★★★
Oman.....
Tunda suka dawo da ita sai yau Allah ya nufa ta bude idanunta, akan likitan da yake
dubata. Sake lumshe idanun tayi kafin ta bud'e tare da juyar da kanta gefe.
"SAFINAH!! Ki koma zasu kashe miki yaranki, SAFINAH ki koma zasu kashe miki yaranki."

Alluran barci suka mata, sannan likitan ya fito, ya sami Iyayenta yace.
"Wacece SAFINAH? Toh ita mara lafiyar take kira ta koma zasu kashe mata yara."

Shiru duk gurin akayi sannan ya kara da cewa.
"Insha Allah zata tashi, sai dai kamar taci wani abu wanda ya haifar mace da kumewar jini a
cikinta bayan ta haihu jinin ya taru, mun same nasarar fidda jinin."

Yana gama musu bayani ya fita.....

★★★
A cikin ɗakin ya kwana, har ya makara ma, fitowa yayi bai ji motsin ta ba, dan haka yayi
wuccewar shi. Abinda Ya bashi mamaki yana murɗa kofar yaji shi a bude, juyawa yayi ya kalli
kofar ta. Sannan ya fita zuwa masallacin sai da garin yayi haske, sannan ya dawo gidan a gurin
Ammyn shi ya tsaya suka gaisa, shiru yayi kan a sunkuye kallon shi tayi cikin kulawa tace. "Kayi hakuri! Allah zai maida maka masu alkhairi."

D'ago kai yayi ya kalleta sannan ya mik'ewa yayi, ya bar falonta. Halayyar shi na baya
yake son dawo da ita, duk yadda kaso mishi magana dakyar yake cire kai ya kalle ka, koda ya
shiga gurin Zoyah ya sameta tana ta barci fita yayi ya koma gurin SAFINAH, koda ya shiga ya
samu bata fito ba, dakin yaran ya koma, ya kwanta a kan gadon su.

Yana tuni ana gobe zasu rasu da yazo kwantar dasu suka fara rigima, akan ya
goyesu, aikuwa ya dauke su, kowa ya dauka sai daya ta fara ihu, a haka SAFINAH ta same su
dams yazo daukar Ablah ce, kuma ba shiri suke dashi ba, har zata fita Aamih tace.
"Ummina kice Appa ya goyi,"
Da sauri na bar dakin tana jin lokacin da suka saka dariya har Aanih nacewa.
"Appa! Ummu tayi nauyi bazaka iya daukar ta ba," cikin dariya yace.
"Ai Ummunku bata da nauyi kamar ku haka nake daukar ta."
Aikuwa suka saka ihu.
"Yeeeeeeee! Appa muje ka dauketa a gaban mu"
Narke fuskarshi yayi dan baya don zuwa gurin SAFINAH dan kartace yazo da laluransa, shine
ya lallaba yaran suka kwanta, a jikin shi, sai da ya tabbatar sun yi barci, sannan ya fita a falo
suka had'u tana sanye da rigar barci sau daya ya kalleta, ya kauda kanshi, dan ganinta sai haka
ba karamin d'aga mishi hankali yayi ba.
Kwallar da suke sauka ne ya an karar dashi halin da yake ciki.
*Taya SAFINAH tabari aka kashe mishi yara?!* Wannan shine tambayar da kullum
yakewa kan shi, kuma har yanzun bai da me bashi amsa,

A sannu barci yayi gaba dashi, me cike da mafarkai marasa tushe, farkawa yayi yana
jin sautin kuka, yunkurin mik'ewa yayi wani irin barci ya kuma ɗaukar shi, dakyar Allah ya bashi
ikon farkawa. Tashi yayi zaune yana kallon d'akin yana son tuna abinda ya gani ya manta dan
haka, ya tashi ya bar dakin. Yadda ya wucce falon haka ya dawo ya samu, anan ne zuciyarshi
ta fara girgiza,. D'akinta ya shiga ya same komai a nutse.

Da azama ya buɗe ban daki, yaga ko dingon ruwa babu, bai gamsu ba, sai da ya fito
zuwa kitchen yaga babu SAFINAH babu labarin ta.

Bai tsaya ba ya wucce gurin Ammyn shi, yace.
"Ammyn ina SAFINAH ta tafi."

Baki sake ta kalle shi, sannan tayi sannan tace.
"Ina zan san inda taje, kaine ka yarda da ita ai nasan komai akayi sai ta nuna maka cewa ita din
Karuwa ce."

"Ammyn ba shi na tambaye ki ba, ina matata tashiga?! Wallahi wani abu ya sameta dake da
Zoyah sai na baku mamaki, ya kuke so nayi ne? Ammyn me kuke bukata na baki ki rabu damu "

Fita yayi daga cikin gidan cikin lokaci ƙalilan kowa yasan Sultan na niman matar shi, cikin
awa gudu aka birkita garin jordan, har babu inda ake wuccewa sai ka buɗe motarshi, tashin
hankali yayi yawa.
Da farko ya zata tana kusani sai tayi fushi sai yaga ba haka bane abun dan har an dauki
lokaci ba a ganta ba, tsabar bai yarda ba da kanshi yaje gidan Ghaniyu da kanshi yaga bata

nan, a nan ne fa yasa aje tasha jirgin sama, da ta jirgin kasa. Sai na Safa safe, aka shiga niman
SAFINAH, har Airport sai da aka je niman nimanta da hotonta ba a sameta ba, sosai ya gigice
tun safiya ake abu d'aya ko ruwa bai saka a bakin shi ba, cikin wuni guda Ashraf ya koma, wani
zararre. A sanadin haka sai da yasa aka rufe masu tsaron gidan shi tare da, zuba wasu.
Gidan shi kuwa yaki magana da kowa, karshe da Zoyah ta dame shi da tambayar ganganci,
kiran wani daga cikin masu tsaron gidan yace.
" A kai ta gidan su, shi zai nimeta"
Kallon Nannah tayi ko zata yi Magana amma ta wani dauke kai kamar bata gurin haka suka fita
da ita ta juya yaje har gaban Nannah tace.
"Wallahi mu zuba dake."

Haka suka kad'ai keyarta....

★★★
"Maah kice SAFINAH ta je karsu kashe mata Yaranta,"
"Toh Natashah za a gaya mata!"

"Maah Ammyn bazata gama da duniya lafiya ba, Ammyn tacutar Da SAFINAH! Maah kice
SAFINAH taje kar su cutar mata da Yaranta."

Iya wannan shine abinda Natashah ke fad'a, kuma idanunta na rufe maganar, duk hankalin
iyayen ta a tashe, ga jaririnta madara ake bashi, sakamakon bata da ruwan nono, idan kaga ta
sai ka zubda hawaye tsabar tashin hankali.

Alhamdulillah book 2 ya kare, cikin yardan Allah,

Ga dai abubuwa sun faru ba a san yaushe suka faru ba,
Tsakanin Nannah da Zoyah akwai alaka me karfi!?
A cikin Nannah da Zoyah wacece tayi nasaran bawa Yaran SAFINAH guba?
Me Natashah ta sani! A pagen baya Natashah ta rike hannun SAFINAH zata mata Magana
Nannah ta fincikota! Me take son Sanar da Safinah?
Kalmar dake Yawo a bakin Natashah, SAFINAH taje karsu cutar mata da Yaranta, iya shi
take fad'a, kenan Akwai wani kulli da tasani.

Na cire muku Abinda baku yi nazarin shi ba.

Duk abinda ke faruwa Sabida Ashraf ne! Sannan Nannah da Zoyah sun taimakawa juna.....
Meye silar taimakon......


Book 3 na hanya......
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda

yake a 500fs  +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
   *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne
150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha
Allah*

4️⃣8️⃣+4️⃣9️⃣

  Juyawa nayi zan bar gurin dan ban ga alamun faduwar da tayi ne ya zubda cikin, kawai dai
akwai abinda ta shirya ne kuma zai koma kanta.

        Fincikoni aka yi lokacin guda aka sauke min wani mari akan idanuna, sai da na daina gani
baki d'aya na tafi zan fadi akan cikina.
"SAFINAH!!!!" Ya kwala min kira, lokacin guda ya ture Zoyah a cinyarsa, kafin ya iso na fadi
akan gwiwata, na dafe kasa da hannuwana biyu.

              Wani irin b'acin rai nake ji, lokaci guda. Mik'ewa nayi tare da juyawa zan bar gurin, ta
kuma fincikoni zata mare Ni ya shiga tsakaninmu.

   "Ammyn ki Kyaleta! Ba ita kadai bace da ciki a jikin ta."

    Cikin fusata tace.
"Ita Zoyah ba cikin ne da ita ba, ta zubda mata,  Muhammad ka farka Yarinyar nan bata kaunar
cigaban ka, amma baka fahimci haka ba, kamar yadda ta zubda mata cikinta itama sai na
zubda nata, idan kuwa baka son faruwa haka sai dai ka saketa na gaji da ganin SAFINAH a
karkashin inuwarka."
             Zubawa Nannah ido nayi cikin bakin ciki nace.
"Wallahi Nannah ke butula ce ke, idan Ashraf ya sake Ni sai ki zau.."

      "Shuuuuu" abinda naji kunne na na cewa kenan, yayinda na taune harshena. Sabida karfin
marin Ashraf yayi min. Sauka kwalla yayi daga idanuna na dama, inda ya mare ni na kura mishi
ido bakina yana rawa nace.

    " Ni ka mara?!"
   Kallon hannunshi yake kamar yaga sabon halitta.
"ASHRAF Ni ka mara?!"
   Dan duk abinda muke yi akan idanun Yaran, lokacin da ya mare ni, k'amk'ame juna suka yi
tare da

36 / 37