Masarautar jordan Book 2 Complete By Mai Dambu

Author :  Mai Dambu Category :  Read Hausa Novels

Chapter   4 / 37

9K to 12K   out of 109.3K words

kai wannan tukunya a matsayin kyautar da ita, Ni kuma zan bata kyautar da na shirya
mata, sai na shayar da ita madaran bakin ciki wanda babu irinsu duk fadin duniya, kamar yadda
suka sashi ya rasa rayuwarsa sai na sadaukar da ita na zubda jininta ga doran kasa, wucce ki
fita kuma ki kawo min kawarki Salmah dan jininta zan sadaukar ga abin da nake bautawa."

Da sauri ta fita tana rike wuyarta tare da shiga ruÉ—ani ganin abinda zata aika ta, jinin Salmah
zata bada Innalillah.
"Na shiga uku! Yau na yadda abin da ya dame ni. Ina zan kai hakkin Salmah."
Haka ta dauki tukunyar tare da barin gidan, jikinta a mace.
Dole haka ta faru da su tunda sun nace sai sun jefa rayuwar wasu a matsala gashi Tun
basu je ko ina ba tasu ce a matsala, garin k'iyayyar SAFINAH ta wulla kanta cikin cikin
damuwa, taya zata kawo karshen bala'in da ta jefa mata rayuwarta, bazata kira haka da zanen
kaddarta bane, sabida shi zanen ƙaddara Allah ne ke zana maka, ita kuma wannan ita ta
zamawa kanta katon layi me girman gaske, ita kuma wannan ita ce ta zamawa kanta, bata jin
badaru da Maryam zasu yafe mata, idan suka ji abinda ta aikatawa yarinyar da sukafi SO duk
cikin yaransu, Domin son da suke wa SAFINAH daban ne a cikin yaransu, suna matuƙa mata
wani irin sone na musamman.
Wannan dalili ya jefa mata k'iyayyar SAFINAH, dan gani take duk cikin Yaran badaru yafi fiffita
SAFINAH akan sauran yaransa.
***
Tun da ta iso gidan dare yayi sosai, dan haka dakinta ta wuce, tare da kwanciya, ko sallah
batayi ba,
Washi gari tana tashi. Ko sallah batayi ba ta fito daga gidan da tukunyar, sai gidan
SAFINAH inda tasami me kula da gidan suka gaisa tace.
"Mutanen gidan suna nan kuwa?"
"Ayya Hajiya jiya sukayi tafiya."
Safe goshinta tayi cike da jimamin gulma tace.
"Ayyana ban sani ba, amma ga wannan a saka a cikin gidan furene me kyau zai kawata mata
gidan. Kace inji Hajiya Kubrah."
Karba yayi tare da godiya, har ta shiga mota sai tayi tunanin kar ya bata matsala ta sai ta
zuge jakarta ta ciro sabon yan dari biyar ta miƙa mishi take ya washe bakinsa, yana ta zuba
godiya. Murmushi tayi tare da samun nasarar, sauran aikin ya ragewa Anim.
***
Yau kwana uku kenan da shigowar mu Poland, duk meeting din da suka shiga baya taɓa bari
ya kai dare dan haka yau ina kwance a jikinshi da wata yakoluelwar riga, hannunshi daya yana
aiki da laptop, daya hannunshi yana cikin rigata dai dai cibiyata, yayinda na Daura hannuna
akan nashi, a hankali nake shafa hannunsa. Sumbatar kaina yace. "Beauty! Kina son jiki kamar mage gaki da mugun tsoro, da zancen zamu haÉ—e yanzun zaki fara
zaro min idanu."
Kwantar da kaina nayi cikin jikin shi ina murmushi mishi Sannan nace.

"My Man! Kaine ai baka da sauki da yanzun zance na amince wallahi da kuka zaka kyaleni, shi
yasa tsakanin na da kai wasan kada kusadashine ruwa ne,"

"Ba wani nan, Beauty kina b'oye min wani abu, baki san Ni likita bane hala ko kin manta ne,
sam baki samun nutsuwa dani, dan haƙa yau sai naga kin samu nutsuwa zan kyaleki."

Rau+rau nayi da idanuna, tare da rike hannunsa nace.
"Wallahi Ni dai ina samun nutsuwa da kai don Allah kar a kuma."
Dariya shi ya gimtse tare da jan hancina, yace.
"Hey! Lady ba zan fasa abinda nayi niyya ba, dan haka ki gama kukanshi an jima sai mun sake
kulawa Sama jannati."
Miqewa nayi zan gudu ya riko hannuna yana dariya yace.
"Duk inda kika shiga zan biki dan Ni É—in ai dai dai dake ne, yarinya ina son ganin yadda kike
jan.."
Kamar zanyi kuka nace..
"Don Allah kabar fadan haka, wallahi kunya kake bani.".

"Wayyo Allah na, Beauty Ni kike jin kunya, lallai kuwa. Toh zo na cire miki kunya tunda ban
cire ba a can rana, yau kuwa sai na cire naga karshe Kunya."
Aikuwa ya shiga min chakulkuli. Dariya nake har da shudewa, gaskiya Dr Zaki karshe ne a
duniyar jiyar da mace soyayya. Bai wani damu da ya nome Ni ba, amma yana nuna a cikin
birnin zuciyarshi nice babu wata umma akwai toh ya cireta, ya kuma bani zuciyar.
"Don Allah Baby! Ka bari zanyi fitsari wallahi."
"Karki damu kiyi sai muje kiyi wanka tunda kin bata mu."

"Wayyo cikina zai fashe wallahi ciwon yake min."
Murmushi ya sake, cikin son sanin inda yake min ciwo yace..
" Ina ne ke ciwon nuna min."
Yana cigaba da min chakulkuli, duk na firgice da dariya, dan ya kyaleni na nuna mishi
gefen marana, bai fasa sai ma sauya salon chakulkuli da yayi ya shiga daura min tashi karatun
zilewa nayi na fadi kasa, ina sauke numfashi.
Kankance idanunshi yayi a raina nace.
*Kai jama'a na hadu da aiki kai kuma naka kalar kenan*
Biyo NI capter din yayi tare da cigaba da murkushe ni.
"Wayyo Dr! Don Allah kabarni bazan kuma ba, wallahi na gaji da salon ka."
"Hmm Ni kuma ban gaji dake ba, ko nace naki wayon, haka kike min kina guduna."
"Allah bani kuma gudun ka."
"Kamar da gaske, Kuma kina ganina zaki fara zare ido kamar mara gaskiya, kawai rufeni
idanunki na baki candy pop."
"Allah na koshi dan wannan candy pop É—in bayi da dadi kai kaÉ—ai kake jin daÉ—in sa, Ni kuwa
bana jin daÉ—in sa."
"Hmm, zan koyar dake yadda ake jin daÉ—in, Allah kuma kika dame ni lokacin da kika
kwarewa

[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna
son Book ɗin Wanda yake a 500fs  +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
   *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne
150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha
Allah*

Oum Muwaddah......

MJ
BOOK-2
19-2-2020

✋🖕
     Shafar fuskana yayi a hankali, lumshe idanuna nayi, tare da kwanciya sosai a jikinshi.
      "Baby baka hakura bane!?"
    Na tambaye shi, muryata na rawa.
        Sumbatar kumatu na yayi tare da gyara min kwanciyata a jikinshi yace.
      "A'ah ai ba zan iya fushi dake ba, kwanta ki huta."
      ........ Wannan halin ko ina kula da Dr yake min ya fara damun rayuwata, dan kuwa a cikin
lokacin ƙalilan na zabge, na fita hayacina, babu shiri muka bar Oman, dan ha fahimci Dr so
yake zuciyata ta buga haƙa muka dawo tattaro zuwa naija.
    Dr Shabhan ne yazo ya dauke mu,  muka nufi gidanmu. Tun daga nesa naga gidan ya koma
kamar irin tsohon gidan nan. Duk wasu flower da aka saka a gidan ya mutu, kamar ba a mishi
ban ruwa, haƙa Dr Shabhan ya shiga da motar shi ciki damu,
    Tunda na kalli gidan sai da zuciyata ta buga, tsabar tsoron da gidan ya bani, bakina dauke da
addu'a na amshi key na nufi gidan. Wanda yayi yanar gizo gizo.
        " Gidan nan naku akwai matsala! Ina shigowa da motana na fahimci hakan."
     Dariya Dr yayi sannan yace.
"Babu komai Wallahi, kawai kana dai tunanin hakan ne."

    Duk yadda Dr Shabhan yaso fahimtar da DR yaki fahimta. Yana fita daga gidan, Me gadin ya
bishi da mugun kallo tare da idanunshi da suka koma ta kare.
      ...... A sannu na shiga gidan na samu yayi kaca-kaca, ga hotunan mu a farfashe. Kome na
gidan a juye fa. Safe goshina nayi sakamakon ganin wulgawar wani bakin kare, cikin yan
second.
          Sunan Allah na shiga kira a hankali har na shiga d'akina. Shima an lalata min kome, Ni
abin ma tsoro ya fara bani,

        Wasu irin abin mamaki nake gani dukda bakina dauke yake addu'o'i.
     Dafani aka yi aikuwa na fasa ihu, da sauri ya rungume Ni tabaya yana cewa.
"Beauty!!! Nine fa"
Da hanzarin na juya tare da shigewa jikinshi, ina rintsa idanuna.

       Ajiyar zuciya nake saukewa. Cikin damuwa nace.
"Nikam,"
       "Ke kam! Me?
    Cikin wani irin murya nace.
"Gidan tsoro yaƙe bani"
  "Kai nifa banga abin tsoro ba kawai idanun ku na nuna muku wani abu na daban ne."

   Duk yadda naso ya fahimta yaki dan haka na hakura muka fara gyaran gidan, sallah ce take
tsayar damu, dake tasowarshi asuba ce sai muka iso karfe sha daya na safe.
Biyar na yamma muka gama aikin har da girki, tare muka ci sannan muka yi wanka gidan
Ammah ya tafi yabarni a gidan, dake Ni É—aya ce sai na kunna ta. Naga ana film din wani horror
bai min  ba sai na mai dashi zuwa, Saudi one sun kuwa saka karatun Alkur'ani. Cikin suratul
ma'edah. A sannu barci yayi gaba dani wajen biyar da kwata.
         Barcin ba wani nisa nayi ba, amma ba fara wani rudaɗɗaɗiyar mafarki na wanan karen da
naga kamar gizo shi na bina da gudu, sai da yayi wuf zai kamani naga anyi sama dani, shi
kuma yana kasa sai haushi yake.
       Cikin salati na farka, dai dai Lokacin da aka wucce wuf ta window na, mikewa nayi naga
ashe ina kwanciyar aka dauke wuta. Fitowa nayi na hango mai gadi yana zaune, amma kanshi
a sunkuye. Kiranshi nayi da cewa,
"Malam Ali!"
     Bai d'ago kai ba, na kuma kiranshi, amma yaki d'agowa sai da na isa inda yake na fara
magana da cewar.
"Malam Ali ya ina magana kaki amsa min ko ba kaji ne?"
                "Bani ne bana ji ba! Kece baki ji! Sai da na gargadi akan kowani namiji Safinah baki ji
ba."
     D'ago bakaken idanunshi yayi baya nayi tsoro ya kamani,
               Horn din Dr yasani manta abinda na gani, dan shima mikewa yayi yaje ya buɗe get din
sam na manta abinda na gani har Dr ya shigo gidan, gabaki d'aya kaina ya kule, ina ƙoƙarin
tuno abinda na gani amma nakasa,
      Jan kafaffuna nayi naje na bude mishi, fuskarshi ɗauke da murmushi ya fito yana cewa.
"Beauty! Ina can zuciyata tana gareki, gaya min keke faruwa?"

    Kallon Malam Ali nayi naga baya gun, rungume shi nayi tare da kwantar da kaina a kirjinshi
nace.
"Babu!"
A takaice, janye Ni yayi ya dawo dani gabanshi, yace min.
"Muna da bakuwa fa"
         Juyawa nayi na hangonta tana zaune, a bayan mota sai wani d'aga hanci take.
   "Wacece ita!?
       "Yar gogg."
     "Goggo Aminah ko? Hmm kace ta fito."
     Magana ya mata ta fito tana yatsina fuska, tabe baƙi tayi sannan tace.

"Toh kayan fa? Waye zai dauka min!"
     Juyawa yayi zai je kamar zan rike shi sai na kyaleshi, ya sauke mata kayanta muka shigo
gidan,
      D'akina na wucce bani takansu ba, dan matukar nayi haka tabbas bani da adalci, kuma
kamata yayi na amshi ta, amma bazan iya ba kuma bazan wulakanta ta ba, nuna Mata dakin
kusada nawa, ta saka kayanta.
           Sannan ya shigo d'akina ya dame Ni na fito daga ban daki, ina tsaye zuwa gabana yayi
ciki  sanyin jiki yace min.
"Kiyi hakuri!"
  Murmushi nayi sannan nace..
"Name fa!?
       D'ago hannuna yayi ya daura a gefen fuskarsa, yace..
"Kiyi hakuri dai, na kawo miki wata gida."
  Murmushi nayi tare da kai ɗaya hannuna din na tallafe fuskarshi nace.
"Ko É—aya idan nayi haka na zama mara imani tamkar butulcin zan kira Kai na tunda ta ko ina.
Allah ya bani nasara yan uwansa nima yan uwana ne, don Allah karka saka komai a ranka ina
tare da kai."
           Jan kumatu yayi sannan yace.
"Allah ya bar min ke!"
  "Tare da kai!"
      ....... Kitchen muka shiga tare muka fara girki abincin dare, muna cikin aiikn muka ji kiran
sallah rage wutar muka yadda abincin zai nuna, a d'akina mukayi sallah sannan muka tare,
bakuwarmu na gani dauke da abincin da ko d'and'ana shi ba muyi ba, ta shake har yayi soro.
   Ban kalle ba , nayi wucce wata kitchen na sauke sannan na juye na fito mana dashi, akan
kafet na ajiye mana, dan jollop É—in taliya ce,
     Gabanshi na shiga na zauna, tare da ɗaukan abincin na kawo gefenmu muka fara ci, tsaki
yarinyar tayi dan bata wucce Sa'ar  Nanah ba,

        Ni yake bawa abincin a sannu ina ci muna hira, yana gamawa ya na juya na fara bashi.
Kamar yadda ya bani, muna gamawa na tashi zan Kai kwanikan ya amsa ya dawo dani, ya
sannan ya dawo tare da tissue, ya goge min hannuna,

   Nan muka cigaba da kallon labarai, har wajen tara sannan muka tashi zuwa cikin, wanka
mukayi sannan ya sani nayi alola muka yi sallar Isha tare da shafa'i da wutir.
      Muna idarwa ya riko Ni tare da zare min hijabi na, rage wutar d'akin yayi sannan muka
kwanta.
   
   "Kiyi hakuri da abinda Sa'ima tayi mana, bana son ace daga zuwanki har an fara samun
matsala daga gareki, zata zauna na wata shida ne, yazo service idan tagama shikenan da."
        Murmushi nayi tare da janye jikina daga nashi nayi rubda ciki, ina Son jin zafin abinda yayi
min amma ba halin haka dole na juya mishi baya, yana tabani nace.
"Please barci nake ji."
    Matsowa yayi ya kwantar da kanshi akan bayana, sannan ya zagaye hannunshi inda ya

turani cikin jikinshi, lumshe idanuna nayi kwallar da nake b'oye suka fara sauka a kan matashin.
           Jin yadda nake jan hancina ya fahimci kuka nake, amma bai hanani ba, sai ma kara
k'amk'ame ni da yake.

          A hankali barci yayi gaba damu.
      00:1am na tsakiyar dare, agogon d'akin ya buga "katttt"
Gyara kwanciya nayi É—an har lokacin ina kwance ne Dr na sama na.
   Juyawa nayi a sannu, sai naji anan magana ƙasa-ƙasa, haɗe da kukan jarirai, abin mamaki
Kuma a cikin d'akin nake jin maganar, sake ware idanuna nayi ina niman inda ake maganar,
kuma abin damuwar sam baka fahimtar Abinda ake cewa. Jin digar abu a kumatuna yasani
shafowa, wani bakin ruwa ne me mugun wari, d'aga Kaina saman nayi.     Wani uban salati nayi gaskiya ban kuma sanin inda kaina yake ba, sai bayan kwanaki biyu,
sannan na farka na ganni a kwance a d'akin Ummina,

     A hankali na bud'e idanunshi, tana zaune akan abin sallah, a hankali nake addu'an tashi
barci... 

  Tasowa tayi tazo inda nake tace.
"Sannu SAFINAH, ya jikin naki."
   Gyada mata kai nayi "da sauki." Nace mata a sanyayye,
      Kallona tayi taga ina son ƙarin bayani, ruwan wanka ta fara haɗa min sannan ta dawo ta
kama hannuna muka shiga ban daki nayi wanka da taimakonta dan zata fita na riƙe hannunta,
shine ta dawo ta cude min bayana tare da kaina Ni kuma nayi sauran ina gamawa ta miƙa min
towel.
         Muna fitowa  ta bani kaya nasaka sannan na zauna, tace.
"Naga kinyi alola a ciki ko Zaki yi sallar kafin na kawo abincin."

"Toh Ummina!"

........ Bayan naci abinci anan na zuba mata ido tace.
"Shekaran jiya! Abdulhameed, ya kiramu wai kumar suma da harbe harbe kamar me cutar
jinmu, kuma daman kafin ya kira Ashraf ya fara mana maganar cewa zai dawo yana jin baki da
lafiya dan yaji haka a jikinshi. Toh da muka ki nashi sai ya tattaro ya biyo jirgi, inda ko tsayawa
ayi bikin shi bai yaƙi, a ranar da ya dawo. Yaje gidanki a daren. Mijinki ya kiramu. Toh a daren
Abbanku ya gayawa Ashraf, shi Kuma dama yana unguwar ku, dan haƙa ya shiga gidan, dan
yasamu Kofar gidan a buÉ—e. Shima yasha wuya sosai kafin ya shiga cikin gidan dan duk jikinshi
ya ji ciwon. Koda ya samu ya shiga tare da mijinki suka fito dake kina fisge

4 / 37