Author : Mai Dambu Category : Read Hausa Novels
takewa Ashraf sai gashi tana marin shi, tare da gaya mishi cewa ya ajiye
Ni. Ko tagaya mishi magana, ganin haka Ummi tazo zata janye Ni daga jikinshi, ya kara
runguma na yana fad'i.
"Don Allah! Karki rabani da ita, ita ce gatana! Ita ce duniyata! Ita ce Alfarma ta! Ita ce suturata!
Sirrnina da halayyata ya gurinta! Na had'i da wanda rayuwar mu da mutuwarmu ke hannushi ku
hukuntani amma karku ce bazan zauna da ita ba."
Kura mishi idanu Ummi tayi jikinta na tsuma, ga Nannah ita ma, tana jan Ashraf. Tare da kifa
mishi mari,
"Dole ka rabu da Ita! Yarinyar da bata ji maganar iyayenta ba yaushe zata ji maganar ka!?
Yarinyar da bata ɗauki zina a bakin komai ba yaushe zata zauna iya kai ba tare da tafita niman
wasu ba!? Me zakayi da mace mara daraja ga mata bila adadin idan don mata kake muje ka
nemi a gidajen alfarma."
Kallon Mahaifiyarshi yayi jin abinda take fad'a.
"Ke Mahaifiyata ce!? Tayani niman auren SAFINAH zakiyi ki bar tozarta min uwar
Y'ay'ana Don Allah Ammyna."
Kallon Ummi tayi cike da bakin ciki tace.
"Nawa ne kuka kashe gurin shanye min D'ana!?"
Murmushi Ummi tayi sannan tace.
"Idan shanye shi muka yi, toh bazamu tab'a barin shi ya kalleki ba. Tabbas idanunmu sun rufe
da kaunar da muke miki muka gaza fahimtar meye a ranki, wancan ranar! A wancan lokacin da
Badar ya barki a can jordan da kaddararta bata sauya ba! A lokacin da kika fahimci in ba ita ba
burinki bazai cika ba, da ban bata kwarin gwiwa ba, da haka bazai faru da ita ba! A lokacin da
ban barta a jikinki ba da yau baki raye! Amma ba damuwa! Dan Ni a tunanina idan sadaukarwa
da tayi zai iya sayan soyayyar da kika mata ashe ba haka bane, dukiyar da kika bamu shine
fansar duniyar Y'ata."
Juyawa tayi gurin Abdul tace.
"Kaje kasan gado! Zaka ga jaka ka dauko mata! Karki manta baki da dukiyar da zata fanshi
SAFINAH, tuntuni dukiyar ki na zaune, wanda muke ciki rufin Asirinki daga Ubangijin, a lokacin
da kika bamu naki a lokacin nima mahaifina ya bamu dan ya rike mu."
Fitowa yayi da jakar ya mikawa Ummi ita kuma ta ajiye a gaban Nannah.
Sannan ta juya ga Ashraf tana murmushi tace.
"Tunda ta tambaye ni Ummi na! Meye Ake nufi da Hulu'e!? Na fahimci ta fad'a komarka, sannan
dan ta guje min jin ɓacin rai take niman hanyar rabuwa da kai badan bata sonka ba sai dan
soyayyar iyayenta! Ashraf indai Ni da Na haifi Safinah zan zuba mata ido naga gudun ruwanta
ai kai da ka mata roman baka me sauki ne!? Ina sane da abinda ka mata ranar da ka aureta,
amma dake Ita wawuya ce bata ji zafin ka ba saima kara mika maka rayuwarta da tayi. Duk
abinda kake ina kallonku, dan haka yau badan Ni ba badan mun isa ba, kamar yadda ta dawo
maka da dukiyar Aurenka, yau ma zan dawo maka da ita, yana cikin takardan da kabata, dan
na ɗauki asalin na kuɗin na bar mata wanda babu kome a cikin sai takardun. Karka manta Ni
uwa ce."
Juyawa tayi taje d'akinta ta ja wani durowa ta ciro farin ma kunshi kudin ta fito dashi sannan
ta kai mishi, cikin wani Irin yanayi amsa yana kallon Nannah da Abba, sannan ya kalli Dudu, a
sannu ya cire ni daga jikinshi.
*(Hulu'e kuɗin fansar kai ne ko nace kuɗin wanke muni da kotu take niman mace ta biya idan
tace bata son mijinta! Sannan wasu sukan biya idan zama yaƙi dadi sabida rabuwa! Sai dai a
wannan rayuwar ina son nayi jan hankali gare mu mata, sam ba dad'i kam amma shi rayuwar
aure dukkanshi ibada ce, idan muka dauke shi a hakan zamu rabauta, sannan idan kika ce sai
abinda mijina yayi min ke naki mijin zai miki wallahi kin fad'i ba nauyi, sannan bamu amfanin
kiran Namiji da suna mara fahida, su kanin Ajali, su buhun kaya, su hankaka, Wallahi a wannan
rayuwar kina zaune cikin gidanki kika b'allo aurenki ko!? Wallahi sai kin yi dana sani,
bawai nace ki zauna ayita cutar ki ba ki nazarci rayuwarki meye yasa Bawan Allah yake miki
wani abu!? Idan kuskuren nakine better ki gyara, zaki samu kwanciyar hankali. Wallahi ina
Alfarma da Iyayena, dan lokacin da aka zo niman aurena, abinda suka ce shine sai kayi hakuri
da ita dan fitinanniya ce, amma tana saukin hali idan Kabi da Ita sannan tana karanta labarin
kanzon kureje dan karka sameta tana karatun tana wasu dabi'u kayi tsammanin haka muka
tarbiyyar ce ta. Alhamdulillah now ina niman 10yrs, ba yaji ba raba faɗa. Har mahaifiyar ta rasu
ban taɓa kai mata matsalar aurena ba, abin mamaki a wannan duniyar aure yana fuskarta
barazana, su iyayen suna jiran giredi ita ma yarinyar haka, shima mijin haka, yau abin haushi
namiji dan ashirin da daya zai fito ya nuna aure yake so ki hana, Shin zaki hana shi matse yar
mutane a lungu!? Haka ma yarinya ta nuna tana son auren kin hanata zaki iya hanata bada
kanta a matseta ki kuma fad'awa lesbian. Don Allah domin kare kananun yaran mu daga sharrin
fyade, luwadi, madigo, muyi ƙoƙarin bawa mutane kirki aurensu, Heeeeeeyeee Sai kuma Matan
auren kina Ruwa idan kika ce baban yaro sai yayi miki irin cin da Ashraf yayiwa SAFINAH
kin kama gaibu, wallahi kin fad'i ba nauyi. Dan Ni mijina kullum kallon zaki nake mishi
ba mijin novel ba, saka sex ko Romance bawai dan a kwadaitar daku haka yake a zahiri, a'a
akwai ƙalilan, amma rashin sa yafi yawa, ki kalli mijinki kamar Tiger shruff ko sharukhan ko
Ashraf sai kin wahala, amma kika mishi kallon abokin rayuwarki sai kinfi samun nutsuwa.
Banda lalacewa kina tare da shi kina tunanin ai ba haka mai lucky yayiwa Maryam
Sajida ba, bayan Itama a cikin labarin sai da ta hadu da kaddararta, wallahi mu ji tsoron
Allah...... Sannan nasan maza biyu da suka sayi wannan book ɗin kuyiwa kanku adalcin da
matayen ku. Ko sau daya ne ka nuna mata so zatayi alfahari da haka, bawai dan kun tara Yara
soyayya ya kare ba, Yana daga cikin soyayyar da bazai kare ba shine soyayyar gidan Abu
Alkassim Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, don Allah ku sanya mu a hanya
idan.mukayi kuskure duk abinda zamu aikata duk sabida kune ku k'iyayye nuna mana abinda
idanunmu bai gani ba, sannan ku girmama soyayyar mu. Yanzun da zaka taɓa wata rabonki da
mijinki yace yana sonki tun yaushe Allah sai kaji tace i heard that since 1948 Why sabida bamu
daraja kanmu ba mun maida kanmu wasu dabbobi zamu hadu a Next pag)*
Ku gafarce ni Ni yarinya ce dan ban rufa 27yrs nasan kuma na tara iyayena da yayuna a cikin
grps ɗin ga kanena yan mata da matan aure, sa'o'i na dole sai da tunatarwa ku gafarce ni abisa
kurakurai na
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda
yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne
150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha
Allah*
Oum Muwaddah......
2️⃣2️⃣
Gaggara motsawa yayi hannunshi daga nawa, yana kallon Ummi.
"Tashi ka tafi amma ya batun sakinta fa."
"Wallahi bazan iya ba! Bana kuma fatar haka, Ni na saki mata ta! Matar da nake So! Nake
kuma alfahari da samunta a matsayin mata ta! Wallahi gwara na mutu da naga wani ya rab'e
mata ta, wallahi bazan iya ba! Gwara na mutu da na saketa."
Yana fadar haka ya juya ya fita, juyowa Ammyn tayi zatawa Ummi tijara, ta nuna mata hanyar
fita dole tafi.
Sannan suka dawo kaina, Dudu ya dauke Ni da sauri, suka fita dani Abba ne ya tadda motar,
aka nufi asibiti dani.
Abin mamaki Dr Hameeed shi ya karb'eni amma Dudu ya hana shi min kome karshe Dr
Muhsin da Dr Azeemah.
Cikin gaggawa suka shiga bani taimakon, sai da suka shafe awa d'aya cur sannan Dr
Muhsin ya fito shida Dr Azeemah, suna share gumi. Dafa Dudu yayi cikin damuwa yace.
"Am sorry Dr Kyari mun rasa babyn."
Lumshe idanu Ummi tayi cikin damuwa.
Hawaye ne ya zubo mata tace.
"Ya ita SAFINAH! Da fatan babu abinda ya sameta"
Girgiza kai Dr Azeemah tayi cikin sanyin Murya tace.
"Babu Wata matsala Mah idan ta farka zata warware."
Hawaye ne ya shiga zuba ita tayi dukar ne bawai dan ta daki cikin. Tayiwa Yarta Asarar
gudan jininta, ba zata kuma barin SAFINAH zubda hawaye ba, goge kwalla tayi tace.
"Zamu iya ganinta!?"
"Eh! Mah zaku iya ganinta amma banda hayaniya."
Mikewa tayi ta shiga dakin ta zauna a kujeran. Tana kallon yadda na firgice, duk na
zub'e.
★★★
Koda Nah ta fita babu Ashraf babu me kama dani da shi, abin ya kad'ata tambayan Drivnta tayi
ya gaya mata ai ya fita a guje.
Haka ta shiga motar aka kaita gidan shi babu labarin shi.
Dole aka nimo mata Ghaniyu, ta saka shi gaba da masifa, dake yaji abinda ya faru kememe
yaki gaya mata inda yaƙe.
Kamar zata yi hauka, sai da ta kwana ta wuni sannan tattara ta koma.
........
"Ya jikin Nashi Dr."
Murmushi Dr Hameeed yayi cikin nutsuwa ya kalli Fahad yace.
"Da sauki! Zaku iya ganinsa, amma don Allah karku takura mishi dan ya bugu sosai a kanshi."
Gyad'a mishi kai suka yi, sannan suka shiga yana kwance idanunshi a rufe, zama kura
mishi ido suka yi. Duk ya zauce ya koma zararre, a cikin wuni daya ya koma wani irin halin,
Abinda Ya faru bayan fitar shi da mota, a guje garin ɗaukar waya ya kira Ghaniyu ya fitar
mishi da Passport dinshi, wata mota ta daki nashi take motarshi ta fad'a cikin rami.
Dr yazo wuccewa yaga lambar motar. Ashu shine ya kawo shi asibiti.
★★★
Bayan awa hud'u na farka, ganin Ummi ya sani razana zan tashi.
"Koma ki kwanta,"
Komawa nayi nayi na kwanta ina lumshe idanuna.
Riko hannuna tayi tace.
"Kiyi hakuri! Na miki asarar babynki"
Kwalla ne ya zubo min, a hankali nace.
"Ummina! Ki gafarceni cin amanar ku da nayi."
"Ni dai da baki sabawa Allah ba shine farin cikina."
....... Haka muka cigaba da jinya kwana uku suka sallame ni, sai dai na kara komawa wata
irin, dukda nasami Yarana a gidan, haka ya rage min damuwa sosai, kuma ina ƙoƙarin fitowa ayi
wasu abubuwan da Ni, sai dai Aahu ya zame min bugun zuciyata, tabbas ya zame min farin
ciki na.
★★★
Shima ya warke sumul, sai dai ya tafi Oman sakamakon kiran da aka yi mishi Nannah ba lafiya.
Ta asibiti ya fara bi, ya sameta da sauki ba wani ciwon da kawai dan ya dawo suka ce bata da
lafiya.
Tunda ya shiga d'akin shi ya rufe bai fita sai lokacin Sallah.
Duk sun damu da rashin kulawar da yake nuna musu.
Kara Smartphone dinshi yayi da sauri ya shiga dakin ya haɗa da laptop dinshi.
Sanye take da wani pink towel, tana tsane gashinta ta da Towel Dan Karami, yaran suka
shigo da gudu suna faɗa, duk sun rud'ata sai ƙoƙarin kunce mata towel ɗin suke,
Tsawa ta daka musu suka fita da gudu, tana dafe goshi tayi a dame.
A hankali bakinta yake motsawa, murmushi yayi cikin nutsuwa yace.
"Madarata ina kewarki sosai."
Kamar wanda aka tsikare shi ya shiga had'a kayansa a cikin jakarshi, ya ɗauki Passport
dinshi, ɗaukar takarda yayi dan yi rubutu sannan yasa kai ya bar musu gidansu.
★★★
Kusan wata uku kenan da faruwar rabuwarmu, duk lokacin da begen mijina ya taso min daki
nake komawa nayi ta kuka ina masifar Son mijina, a yanzun da baya nan na fahimci cewa nima
jarababbiya ce irin shi, duk lokacin da na kwanta sai nayi mafarkin shi, idan zan zauna gizo
yake min.
★★★
Yau ake sunan Asma'u ta haihu, ina ta sauri zan je gidan sunan duk sun tafi sun barni tsabar
nawa.
Mota ta nake ja da sauri, tsayar dani akayi kamar bazan tsaya ba, dan har na wucce sai
na dawo da baya.
Ina zuwa nayi parko tare da sauke glass.
Matsowa mutumin yayi sai a lokacin naga bashi d'aya bane.
Nuna min bindiga, a rud'e na kallesu bakina na rawa, nace.
"Lafiya!? Me na muku!?"
Shigowa mutumin yayi tare da cewa.
"Muje"
Zan bud'e gefen ya jefa min hanky, kifa kaina nayi sai da jera Atishawa uku sannan
barci yayi gaba dani. Fitowa yayi sauran suka fito zasu fitar dani, sai ganin mutane sukayi sun
zagaye motar, Ghaniyu yace musu.
"Me kuke bukata!?"
Babban zai magana Ghaniyu ya daga mishi riga dole yayi shiru suka fita daga motar, a
motar su Ghaniyu suka tafi, Shi kuma ya tura mishi sako.
A rikicin ya zo gurin tare da yan sanda, tun kan su iso su Ghaniyu suka bar gurin.
.......
Dukar Babban barayin yake zuciyarshi na ta fasa.
"Mata ta! Zaku tab'a saboda wata yar iska."
Shigowa da Kidaya akayi suka watsar da ita kamar kayan wankin.
Takawa yayi har gabanta ya take ƙafarta ihu tasaka, sannan ya durkusa yana tauna
toothpit, kallon irin shigar jikinta yayi, ya kauda kanshi.
"Wato kika ce idan suka kama Safinah su keta mata haddi sannan su saka a intanet, yadda
sunan ahalinta zai ɓaci, Mata ta da igiyar aurena, mata ta mace me daraja da kima zaku lalata
min Ita saboda son zuciyar ki, ki godewa Allah ina da yara mata, da wallahi sai nasa yarana sun
miki wulakancin da ko biyanki akayi ki tab'a sunan Safinah gudu zaki yi dan mata ta."
Gyara suit din jikinshi yayi bayan, ya cigaba da gyara button ɗin, rigarshi tafiya ya fara
Ghaniyu da Fahad suka rufa min shi baya, kamar bazai magana ba, ya isa jikin window ya dafe
hannun damansa yana kallon waje.
"Razana min ita Yadda ko sunan Safinah aka kira sai da suma, so nake naji ihun da taso
SAFINAH tayi, ita nake son jin tayi."
Kwashe mazan Ghaniyu yayi shima ya dawo, Fahad tsaye A gabanta.
Yana ɓalle rigarshi, tsorone ya cika mata ciki shiga ja da baya jikinta na cikin harshen
turanci ya.
"Abinda kika saka a mata shine Ni zan miki kiki irin ciwon da kike so taji kunga gobe koda kuɗi
aka had'aki bazaki cuci kowa ba"
Gashin an daure ta, ba halin gudu. Duk ya taso kaucewa barazanar sai da Fahad ya gigita
mata lissafi, bata kara fita hayacina ba sai da ya fisge hannun rigarta, taga yayi mata runfa. Nan
ta kara kidima taba basu hakuri, a zuciye Ashraf yazo yayita kifa mata mari sai da suka riƙe shi
yace. "Irin kukan da kika so tayi kenan ta gigice ta firgice tayita baku hakuri kuna mata dariya, ashe
mutunci bai fi mutunci, koda yake idanuna suna kanki ko a mafarki kika ga fuskar Safinah ki
nemi tsari da ganinta."
★★★
Barcin kwana uku nayi sakamakon shaka min cocain, sabida rashin karfin jini na, a hankali na
bud'e idanuna akan Ummina, mik'a naso yi amma na kasa, dole na koma na kwanta a hankali
nace.
"Ummina! Lokacin Sallah ya wucce ni!"
"Eh SAFINAH! Yau kwananki uku kina kwance, dan ma Allah ya taimaka kin fad'a hannun na
gari da bamu san me zasu miki ba."
"Ummina!?
Taimaka min nayi wanka!?"
Haka Ummina ta taimaka min nayi wanka da sallah, sannan ta bani abinci na tab'a ina kara
zurfaffa abinda na gani lokacin da suka watsa min abin.
"Ummina!?"
Na kira sunanta a hankali, kallona tayi cikin nutsuwa.
"Ummi! Na ganshi! Yana raye."
"Waye!?" Ta jefeni Ni da tambaya,
Sunkuyar da kaina na yi,nace.
"Shi d'in!"
Ta fahimce Ni sarari so take taji daga bakina.
"Abban su!?"
"Toh waye kenan! Kin sani a rud'u."
Sunkuyar da kaina nayi