Author : Mai Dambu Category : Read Hausa Novels
yana fushi dani
ya koma gurin Yarta sai ta same nutsuwa, bazan iya kwatanta muku halin da na tsinci kaina a
ciki ba, amma wallahi uwar mijina tana jin zafina da ciwon kasancewata rijiyar D'anta.
A sannu ciwon kai ya fara sani a gaba, me had'e da jiri. Ranar da bazan manta ba, sun
dawo daga yawon shakatawa, shine a gaba table da yaran a kirji ko nauyin su baya ji, ya shigo
gidan,
D'akina ya kaisu sannan ya shigo nawa ya dame Ni ina kwance a kasa jini ya b'ata ko ina,
d'aga Ni yayi yaga na koma. Da gaggawa ya fito dani zuwa asibiti, wanda yake a lekki d'in.
Kamar zautacce yake tuki har ALLAH ya kaimu asibitin, nan dai aka shiga Bani kulawa
cikin aka samu bai fita ba.
Kwanan mukayi Ni dashi, washi gari basu san zai dawo ba, a lokacin yazo ya same
Natashah ta zane yaran tare da sheka musu ruwan sanyi, Nannah kuwa tana d'aki tana barcinta
wai dan sun tashi suna kiran Didih dake yaran sun bi bakin Yaran gidanmu suma Didi suke
kirana da shi da, shine suka yita kuka daga fitowanta ta zane su, da wayar Usb kuma ta watsa
musu ruwan sanyi, shine Uban yana zuwa.
Bai bi ba'a si ba, ya rufe ta da duka, yadda yake shiga banan yake fita ba, sai da Nannah ta
mare shi ya Kyaleta.
Sukan yaran ganin yadda babansu ya haukace yasasu komawa guri guda jikinsu na rawa,
dan dama matsorata ne.
Kwashe yaran shi yayi ya kaisu sama ya musu wanka, daga nan ya wucce dasu Our daily
meal, inda ya saya musu abinci har dani ya kawo min asibiti.
Suna isowa suka zo guna da gudu, tare da fashe min da kuka, kallon shi nayi yadda yake
cikin rashin walwala. Ga fuskarshi a daure.
Ina cikin damuwa sosai, domin fushin da Ashu yake yana tab'a zuciyata, ina son sanin
meye matsalar na kasa, kwana na uku aka sallame ni, tare da gargad'in banda aikin ƙarfi banda
dogon tafiya. Banda Sex!?
() Wallahi a take Ashraf ya dallawa likitan harara yace.
"Ina zan kai bukata ta! Ko ce maka aka yi Ni d'in mazinacine!? Tun wuri kusan abinda zakuwa
cikin, dan tabbas sai na sauke nauyin dake kaina."
Kallonshi likitan yayi cike da damuwa yace mishi.
"Me Oyinbo! Zakayi hakuri har cikinta ya shiga wata shida!"
Tsuke fuska yayi cikin masifa ya riko hannun yaranshi.
★★★
Koda ya bar gidan da Yaranshi, zuwa Nannah tayi ta d'ago Natashah daga ƙasa tace.
"Matuƙar kika ce zaki saka kishin ki a kan yaran zaki wahala! Ni dai kisan yadda zaki yi ya dawo
gare ki dan matuƙar yana tare da SAFINAH! Shima zai iya bada rayuwarshi dan ita da
Yarantaka! Domin haka Kakansa da Mahaifinsa sukayi.,"
Kura mata ido tayi cikin kuka tace.
"Ke bata Ni ma kike ba!? Ta d'anki kike! Sai dai SAFINAH ta gama da shi amma ba makawa
bazan kuma taimaka miki ba, dan nima mijina nake buƙata. Kuma sai na haifi Yaron da narasa."
Tabbas rayuwar da ka ganshi nan, a shirye kome yake. Musamman idan ya shiga
zanen Kaddara, toh haka zaka ga komai na zuwa maka ba zato ba tsammani. Zaka ga komai
na faruwa da kai, tunda muka dawo Ashraf ya tsiro min iya shege, dan ban san meke faruwa
ba, sai dai zai gayyato min Natashah zuwa falona suyi rashin kunyar su, dake cikin ya sanya
min rashin son magana ko kallo basu ishani ba, ban kuma tab'a gayawa koda Ummina, dan ban
ga abinda zan gaya mata ba, kusan me yasa sabida ita d'in Mahaifiyata ce! Zata iya yuwa na
manta abinda aka min, amma ita har duniya ta tashi bazata manta ba, shi yasa wani lokacin
bana son nace Ummina wane ya min kaza ya min kaza( wallahi akwai kuskuren da muke
aikatawa, dangane da iyayen, Yarone yayi miki laifi sai ki hukuntan shi, indai akwai Fahimta da
iyayen shi, karki fad'awa Iyayen shi laifin sa, ba dan kome ba sai dan ita Uwa takan ajiye duk
wani kalubalen D'anta a cikin wani cantainer na daban, a duk lokacin da ta gana zata bud'e tana
jiran yau ma dame kazo dashi, idan alkhairi ne ta saka a ciki ta rufe, idan sharri ne ta addana a
ranta, a duk ganinka da ita zatayi toh da wannan tunanin ne a ranta, ta riga cewa toh yau wane
da mai yazo, kai wane baya ji! Don Allah ko sau d'aya ne karki kai yaro kara gurin Mahaifiyarshi,
ki kai gun Mahaifinsa haka zai ragewa Uwar damuwar da take ciki Allah ka bamu ikon
tarbiyyarta da yaranmu takan dai dai Amin Ya Allah)
Dan haka naji a raina zan iya fuskarta abinda yafi haka idan takama na kuka da bakin
ciki ne, zan had'iye saboda gidan Aurena. Babbar matsalar da muke fuskanta, shine na
ƙarancin zaman lafiya a gidanjenmu sabida munyi imani wani zai iya haifar mana da matsala
bayan mun manta cewa a kowace rayuwa akwai mujarabbi, dan haka na dauki mahaukaciyar
soyayyar da nakewa Ashraf ta zame min rawa Jarabawar, shi kuma Mahaifiyarshi ta zame
mashi jarabawa, domin duk abinda yake min daga Mahaifiyarshi ce, itama kuma ban ga laifinta
ba, dan na fahimci halin da take ciki, A duniya kowa yasan Balarabe ana iya kashe shi sabida
abu uku, Matar su! Yaran su! Dukiyar su! Sarkin Yasir Alhashmiyya, an kashe shi akan mulki ba
mulkin nace tasa aka kashe shi sai dan sun nemi ya sadaukar da Matar shi da kuma Yaranshi,
sai ya tafi bayan ya bada mulkin shi kuma ya duge yaki shine suka sukayi ta saranshi har sai da
ya mutu. Sarki Abdullahi Alhashmiyya, shima Marhum ya nemi ya bar mishi Nannah yaki,
amincewa har ya kai ya fitar da su ta bayan gidan suka kashe su, dan sunyi imanin duk wani
sarki baya auren macen da bata da juriya da tsayawa akan gaskiyar ta, sai gashi duk na had'a
juriyar da kafiya, uwa uba soyayyar mu, ta gaskiya da take gauraye a cikin zukatansu.
★★★
Zama yayi yana kallona, bs tare da yace komai ba. Kafin yace,
"Ba zaki sunan Matar Dudun bane!?"
Murmushi nayi cikin nutsuwa nace.
"Zani mana! Amma dole sai an bani izinin ko zan tafi babu izinine!"
Kauda kanshi yayi sannan yace.
"Kwana nawa zaki yi "
Cikin son jan hirar nace.
"A ranar ma idan kace na dawo zan dawo."
Kallona yayi a kaikaice sannan ya maida hankalin sa kan tv falon kafin yace.
"Me kika fuskanta a zamanmu na kwanan nan!?"
Murmushi nayi sannan nace.
"Me kuwa na fuskanta bayan kana jin mulkin ka, sai yan damuwar da baza a rasa ba, kuma
kaga Ni ina fama da cikina! Bazan aro damuwar wani na kara da nawa bazan indai ba son nake
zuciyata ta buga ba, dan kasan yanzun ina fama da......
✋✋ Assalamu alaikum
(Yana da kyau da Muhimmanci mu nunawa Yaran mu, Darajarmu ta iyayensun Mata har da
Mazan ma! Dan nayi Imani duk cikin ku babu wacce zata so ace wancar yarinyar Y'arta ce, don
Allah mu nunawa Namu yaran mu iyayensu mata muna da daraja da kima! Dan duk Yar da
tasan Wahalar daukar ciki da Wahalar Shayarwa toh bazata tab'a zagin Uwa ba, Toh Allah ya
shirya mana yaranmu baki d'aya ya bamu ikon sanin meke cikin rayuwar su, dan matuƙar mace
tayi irin wancan shirmen, kamar Yadda wasu suka ce wai Yar tasha ce toh Tabbas ta fad'a
d'imuwar Rayuwa, dan abinda kayi a kuruciyar ka itace Tsufarka, kuma duk rayuwar da babu,
Tarbiyya toh akwai nakasu a cikin sa, Ya Allah Ka shiryar mana da zuri'anmu baki daya don
Allah Auntys Mummys, ku kula da kanena Yan matan nan kar asamu wasu daga cikin b'ata
garin Kawayen masu halin banza su b'ata mana su)
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda
yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne
150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha
Allah*
Oum Muwaddah....
2️⃣7️⃣
"Kuma naga abin naku na dangine, kaga aba ni da ikon shiga hurumin kowa gwara na tsaya
a matsayina na baiwarka"
Hannunshi ya tura cikin rigana, yana shafo cikina. Lumshe idanuna nayi sannan na buɗe
akanshi.
"Me yasa baki damu da halin da nake ciki mu, don Allah ki saka ido sosai akan abinda yake
faruwa."
Yana gama fad'ar haka ya bar Ni zaune a gurin ina tunani, abinda ya gaya min, tabbas akwai
abinda ke faruwa wanda Ni ban sani ba, kuma ban tab'a zarginshi ba, dan duk macen arziki
bazata tab'a zargin mijin ta ba, dan haƙa bana zargin Ashu dan nayi a manna da son da yake
min. Ba zai tab'a cutar dani ba,
Fitowa yayi zai sauka kasa, yaga yadda na zurfaffa tunani, dafani yayi tare da cewa.
"Karki manta da halin da kike ciki karki takura kanki da damuwar wasu."
Tun daga rana na zuba idona sosai, sam bana gane kome tunda ban san abinda ke ransu
ba, sai dai rashin fahimtar da na gano a tsakanin Nannah da Natashah.
Abin ya bani mamaki taya haka ya faru ban sani ba, karshe na tattarasu na watsa gefe,
sabida yawan tunani akan su ciwon kai yake sani.
Dan haka da na tashi tafiya Abuja daga Ni sai yarana sai Shi, dan ya zame min jela. Duk
inda zabi muna tare, har takaici yake bani.
Tunda muka shiga gidan Sunan ake min tsiya Musamman Nana Asma'u, har cewa take.
"Wallahi Ummi tayi farar dabara da ta barki kika koma d'akin mijinki, da wannan babyn a
gidanmu za a dame shi, tunda Sultan ya lalata mana ke da rashin ta ido Didih"
Pillown kujera na wurgata mata ta tashi a guje tana min dariya.
Wato Ni dai ban san ya zanyi da Kanena ba, sun ishe Ni da fitina.
Sai dare muka koma gidan Iyayena, na shiga d'akina na fara had'a kayana da zan koma dasu
Lagos, ina cikin haka naga kwalbar da ya bani, ranar da ya shigo gidan Dudi. Kallon kwalbar
nayi yana wani irin hayaki, ajiye shi nayi a cikin handbag d'ina na, shirya kayan.
Ina gamawa na shiga d'akin Ummina, nan muka baje hira, har sha biyu sannan ta Kore Ni
d'akin sa, yana zaune a bakin barandar shi, nazo na wuce shi.
Koda muka kwanta, hakkinshi ya nima. Kuma ban hana shi ba, dan nima kwana biyu ina
yawan jin haka sosai, sai da ya sami nutsuwa sannan yace min.
"Ina son Rabuwa da Natashah, amma ban san ya zanyi."
Nutsuwa nayi ina jin abinda yake fad'a min a zahirance shawara yake nima, dan alamu sun
nuna min yana cikin damuwa.
"Idan na fahimta, baka son Rabuwa da ita sabida wasu dalilin, Ni a nawa tunanin ka
hakura da ita. Sannan idan ka rabu da Natashah, amadadin ka samu sauki a rabuwar ku zai iya
zama tashin hankali, sannan zumuncin dake tsakanin iyayen zai lalace, sai abu na gaba wanda
dole ka hakura da ita, shine aurena da kai, Yau kana sake Natashah. Duk danginka sai sun
tsanani, sannan k'iyayyar danginka zai iya kasara rayuwarmu, ga kuma Nah ya zakayi da ita.
Don Allah kayi hakuri ku zauna da ita ka kuma bata hakkinta. Idan kayi haka tabbas zaka sama
min zaman lafiya."
Sumbatar goshina yayi tare da gyara min kwanciyata, dake yana jingina da jikin gado, Ni
kuma ina tsakanin cinyarsa.
Shafa bayana yayi cikin jin dad'i yace.
"Nagode da Allah yabi ke a matsayin matata jakadiya ta gari, mace me hangen nesa da tunanin
gaba."
Kwantar da kaina nayi a kirjinshi ina shakar kamshinsa.
★★★
Jordan...
"Abu Zarri! Ya kamata Ku sanya mutane na ko ina na duniya, su fita niman Sultan Ashraf.
Dan na lura Wancan azzalumi ba kyalemu zai ba."
Inji wani daga cikin manyan Fadar Salman bini Abul Bashari,
Ajiyar zuciya Abu Zarri yayi cikin damuwa, sannan ya koma ya zauna. Yana kallon
Salman kafin ya had'iye yawu, cikin damuwa yace.
"Babu inda ban tura ba niman shi, har yau ina alakanta kaina da son zuciyata, dan haka muyi
hakuri. Lokaci na zuwa da zamu kwaci kanmu, Insha Allah."
"Toh haka zamu bari yana cutar da kowa, talakawa sun fahimci cewa ba Sultan Ashraf
bane, dan yanzun basu da yanchin magana basu da ikon magana kome sukayi sai an azabtar
dasu, shima Ukshe ance bai da lafiya dan ya kwace komai na shi, Allah ka kawo mana mafita."
Haka suka yita tattaunawa, har wani lokaci sannan suka bar falon.
★★★
Lagos....
Saukowa muke daga jirgin sama nisa shi sai yaran da yake rike dasu, Ni kuma ina rike da
handbag d'ina, fuskana a tsuke nake tafiya kamar zan fashe da kuka, kuma ba kome ya had'a
mu ba, sai akan abincin da aka kawo mana ina ƙoƙarin daukar meatpie, kawai ya buge min
hannuna, ya dauki cake ya ajiye min, tare da b'ata rai. Ni kuma nace bazan ci ba, shine fa nake
ta fushi, shi ko a jikinsa sai murmushi yaƙe, muna fita muka same Ghaniyu da Fahad suna jiran
mu,
Kallona Ghaniyu yayi yace.
"Ranki shi dad'e lafiya kike fushi!?"
Aikuwa bahaushe yace.
*Me niman kuka aka jefa shi da kashin Auwal*
Kawai na b'are baki sai kuka,( saura wata tace hmm Yo haka nake nifa bana
rena abin kuka musamman kukan banza✋)
Aikuwa me Ashu zai banda dariya ya d'auka da wasa nake, sai da yaga jikina arawa, ya
fahimci dagaske ake, cikin airport d'in yaje ya amso min meatpie, ɗin ya kawo min. Tureshi nayi
ina fad'in.
"Jeka dashi bana so bana so"
Rungume Ni yayi cikin damuwa yace.
"Wallahi ban san zaki yi kuka ba, da ban hanaki ba, akiyi hakuri kinji"
Dakyar suka samu nayi shiru, a take na cinye,na fara zare ido ina niman kari, b'ata rai yayi
al'amun babu wasa, haka na hakura amma dan niman fitina na kwanta a bayan mota na fara
rera musu baitotin kuka.
Haushi kamar ya rufe Ni da duka, Ghaniyu bai kai mu gida ba, sai gidan abinci ya fita shi da
Fahad da yaran nan Ashraf ya juya ya fara balbalin bala'i, Ni kuwa na kara b'are mishi baki l,
dan Wallahi yau rigima nake ji shi yasa ana min abu kaɗan sai kuka. Bakin ciki ya kara kama
shi, juyar da kanshi yayi.
Kuma abinda na Fahimta cikin ne yasani haka, domin kuwa ba haka nake ba, bana kuka sai
an b'ata min rai yau nice nake kukan banza.
Suna shigowa suka mika min laidar,
Koda muka isa gidan babu wanda yace min uwaki SAFINAH, nima ina jin rigima ban bi
takansu ba,
★★★
Rayuwarmu tana tafiya ce abisa tsarin Ubangiji, komai ma haka a sannu a hankali cikin ya fara
tasawa, tunda gashi ya shiga wata shida ina niman na bakwai, zamanmu ya sauya domin kuwa
Ashraf yana ƙoƙarin bamu hakkinmu har ita Natashah wacce take ganin kamar karfinta yasa
Ashraf yake mata komai, idan taba kafafa kallonta nake sabida bazan iya maida mata martani
ko raddi ba, dan haƙa kawai zata shiga yiwa kanta kirari da gwad'oso.
........ Abinda bata sanin ba, mijin da take ihu akan shi, nice nake bashi kowacce shawara
musamman akanta da Mahaifiyarshi, sai dai ganin cikina fara fitowa Nannah ta bud'i baki tace
min.
"Bani da Yadda zanyi dake ne, SAFINAH da ko numfashi sai na hanaki shaka, na tsani
Tarayyarki da Ashraf, bana sonki bana kaunarki ki fita a rayuwarsa mana."
Shiru nayi tare da murmushi sannan nace mata.
" Allah ya hucci zuciyarki"