Masarautar jordan Book 2 Complete By Mai Dambu

Author :  Mai Dambu Category :  Read Hausa Novels

Chapter   18 / 37

51K to 54K   out of 109.3K words

tsabar kunya kamar zan fashe da kuka nace.
"Ashuu!?"

Sam na manta ita ce na ce mata Ashu.
"Amma na maida mishi kuɗin Aurenshi, ɗan haka ki bar kawo min zance shi."

"Amma Ummi aka ce min bai amince"
D'aga min hannun tayi cikin fusata tace.
"Karki dawo min hannun agogon baya"
"Ummina!?
"Zaki dawo da halinki!?"
Girgiza mata kai nayi,
"Good girl"
Tace min,

Mikewa nayi na shiga ban daki na fashe da kuka bayan na kunna panpo.

Tana sane da kuka na shiga yi, ko a jikinta. Koda na fito biris tayi dani, washi gari aka sallame
mu.
A hanyar mu na komawa muka sake haduwa a Traffic Jam, yana wata Hond new model, kafin
na dawo daga tunani ya b'ace min, kalle-kalle na fara sai da Ummi ta rike Ni sannan na dawo
hayacina.
★★★
Sannu a hankali kaina ya fara daukar zafi, dan yanzun Zan iya kiran kaina da mahaukaciya
eh mana, tunda ga dai Ashraf yana min gizo, yau ma na shiga sahad store. Niman wani mai Ni
da yaran, sai Ihu suke sunga wasu toys ya d'aga musu hankali, shine nima suka d'ago min
nawa Sense din. Gabana ne ya fad'i, cike da tsoro na d'ago kaina. Bazan iya cewa shi din ne ba, amma tabbas
ina kyautata zargin haka, jan Hannuna yaran Suke suna cewa.
"Didih! Muje ki saya mana!?"
Hankalina na kan shi yana gurin biyan kud'i,
Sanye yake da riga me hula, wanda ya hanani ganin zahiri fuskar shi, takawa nake
zuwa inda yake kafin na isa wasu matasa maza da mata sun mana katanga dashi, har ya fita
hango shi nayi zai shiga mota na fita da sauri, na isa inda motar yake na bud'e da karfi.
"Hoo! Sorry na zata wani ne da nasani ashe ba shi bane."

Murmushi yayi a hankali na juya tare da barin gurin.

*"SAFINAH!!!?*
Ya ambata bayan ya cire mask din fuskar shi. Juyawa nayi ina kallon motar, da sauri yaja
motar wanda nake ji kamar da zuciyata yake gudun.
Jingina nayi da wata mota na kifa kaina na sake wani Irin kuka, tabbas Ashraf ya gama kama
zuciyata, irin kamun da bana iya tantance fari da baki, Ni kuma tawa kaddarar kenan.

"Madam kin bar yara suna kuka."
Da sauri na shiga suna kuka, durkusawa nayi suka rungume Ni, nima kuka nake sosai.
Hakura nayi da sayayyar nasa kai zan fita, wanda yake zaune gurin biyan kudi yace..
"Madam an biya muku kudi kayan wasan da suke so."

Mamaki ne ya kuma kurmushe Ni.

(Auntys & Mommys... Don Allah kanena yan matan nan wanda shekarunsu bai wucce 20yrs
ba a koya musu girki, namiji ya kan iya zama da kazamar mace idan ta iya girki, ya kan iya
zama da mummunar mace idan ta iya girki, ya kan iya zama da mafad'aciya idan ta iya girki, ya
kan iya zama da mara kunya idan ta iya girki, amma batun gaskiya shine kome kyan mace da
nasabarta Wallahi zaman zai sha tangard'a sabida shi yayi imanin da Tumbin sa, ita kuma tayi
imani da lalace, kanena da kuke tunanin zaki auri handsome guy, mr right, mr perfect, Yes burin
kowacce mace kenan amma shin wani Irin tanadin kika mishi, wallahi yana da kyau mufahimtar
da juna mu, shi namiji sak ne shi. Taya zaki dauki Yar 20/19/18/18/16 itace kankanuwar cikin su,
amma baki nuna mata yadda zata kilace mishi tummys dinshi ba. Yana son kawo friend dinsa
cin abinci amma yana tsoron kawo su, Why Mommys,!? Why Auntys!? Wallahi idan kika koya
mata girkin nan, shine bokanta!? Kika nuna mata zaman auren Ibada ce, shine Malaminta!?
Kika nuna mata biyayya!? Na rantse da Allah koda d'igo kwalla d'aya yaga ya fito daga idanunta
sai ya rikice!? Ku da kanku kuke kalublantar Ashraf, akan SAFINAH!? My Dear wannan story
ne, ki d'aura Kanwata a saiti Wallahi tallahi, sai ta juya shi ayita tunanin Ta wanke ta bashi ya
sha. Kuma duk bala'in da zasu yi yana manne da ita, Mommys da gaske nake ki gwada wannan
shine sirrin rayuwar aurena � har yau ana tambayata me kikawa kikawa Usman da baya
iya nutsuwa idan baki nan idan nace banyi kome ba karyatani suke, abinda na yarda
dashi mijina yana kokarin ƙare hakkina da sauke nauyin da yake kanshi, Ni kuma ina ƙoƙarin
kyautata mishi ba hana idan ya ta bani na ishe shi da fitina ba, Yes amfani auren Babba kenan
Wallahi ki gama fitinarki ya kalleki Yace ai Yarinta na damunki Don Allah gobe abinda zan yi ai
sai yafi na jiya tunda an kalleni ance min yarinya, haka ya faru ne sabida daukar zaman da nayi
a ibada kuma mutu kara ba, bana iya hange Kowa sai shi. Duk zaman da ya lalace toh an
bawa zuciya jagoranci ne, idan da zamu bawa Allah jagorancin rayuwar auren mu zamu gyara
abubuwa fa Allah yasa mu dace )


*Har yanzun dai Ni yarinyar ce kamar Yadda yake ce min� Allah abin dariya sai
ka gama tsiyarka a bika da kalmar yarinta shekaru Goma baya da suka same kakarmu tace
musu Ni yarinya ce shine ake bina da kalmar Nagode ma a haka*
[3/19, 8:35 PM] Mai Dambu: *number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda

yake a 500fs  +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
   *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne
150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha
Allah*

Oum Muwaddah....

2️⃣3️⃣
  Kasaike nayi ina kallon yadda ake zuba musu kayan a motarmu har bayan motar. Muna koda
aka gama muka dawo gida, wucce d'akina nayi na zauna tare da cusa hannuwana nayi cikin
gashin kaina na,

  "Da alamu na haukace ko Son Ashu ya haukatani"

Ni d'aya nayita surutu, Ina cikin jarabawar So, dan bana fahimtar kome na Rayuwata, da Abuja
yayi min zafi sai na haɗa kayana zuwa gidan Aunty Yaanah, ko zan same.

Da yaran muka tafi, tunda nazo na same nutsuwa kan, tunda na ajiye tunanin Ashu muna bin
dangi da yan uwa, lokacin da nakai Yaran gurin yayansu Ummi Sheikh Hayatudeen ya dauke su
yayi musu addu'a sosai tare da sanya musu albarka yace.
"Mahaifinsa! Yana da kirki wancan Satin yazo a nan yayi Sallah Jumma'a. Yaron Akwai nutsuwa
a tare da shi ga kamala da zati, kiyi ƙoƙarin kin shiga al'amarin shi da Mahaifiyarshi, ki samu
damar da zaki dinke barakar dake tsakaninsu, sannan Kiyi hakuri dashi, ya tashi a bahagon
rayuwa, bai fahimci farin ciki ba sai da ya haɗu dake. Basarake ne bai san kome ba sai akanki
don Allah ki bashi farin ciki da nutsuwa, dan idan ya rasa nutsuwa dake har abada bazai kuma
fahimtar ki ba, kiyi ƙoƙarin gyara tsakanin su Allah shine gatarki Dan Dama ko baki zo ba zan
saka a kawo min ke, sannan banga dalilin da Mariam ta rike ki ba ta barki ki koma d'akin mijinki
kema zaki nutsu."

Wayyo garin dad'i na nesa wato duk sabida Ashu ake min nasiha, "Allah Nagode maka da
ni'imar da kai min."

Koda muka bi sauran zuri'anmu kowa da abinda yake fad'a akan jarumin maza, kowa yabon
shi yake, da alkhairin da yake musu.

Gidan Hajja Kaka naje na sameta hakimce tana duba littafin Hadri, da medical glass ɗinta,
wani kallon banza tayi min sannan ta maida kan littafin gabanta a raina nace.
*Da alamu aljanun basa kusa yau.*

Shigowar Yaran kawunaina ne yasani dogo kai suma suka shiga murna, tare da cewa.
"Didih Feener! Yau kece a gidan mu, gashi zamu fita zuwa Two days shopping mall"
Inji Meenal,

Murmushi nayi sannan nace.
"Eh nice! Nima ina son zuwa dan naso zuwa Abuja amma ban je ba, ku tashi muje"

Wani kallon da matar nan tabi yan matan dashi yasu mik'ewa, nima kuma na mik'e.
"Ke! SAFINAH ki fita idona na rufe, dan na lura baki san hakkin aure ba, kin dibo jiki daga Abuja
baki nemi iznin mijinki ba, kika zo sannan baki zauna waje guda ba sai yawo kike masa da yara
salon Mayu da masu kambi baka su tab'a masa yara toh babu inda zaki ki zauna idan ya dawo
ki tambaye shi."
Ko kallonta banyi ba na mike tare da saka hijab dina cike da jin haushi nace.
"Idan ya matsu ya bayyana kanshi Ni kuma sai na kare hakkinshi sannan Ni babu auren wani a
kaina! Yan mata muje kunji."

Duk yadda take masifa ban kulata ba sai bar mata yaran nayi tare da tafiyata,. Tunda muka
isa muka siya abinda ya kawo mu, tunda zuwan mu wani mutum yake like min, duk abinda na
dauka sai ya dauki biyu ya saka min.
Tun ina bata rai har na hakura, tsinkewa zuciyata tayi sakamakon hango Ashu
hannunshi hard'e a kirjinshi, yana bina da wata irin azababben kallo, wanda yake dafa ruhina da
zuciyata.
Ashe na kai hannun zan dauki, wani set na pant da bra wanda yake zuwa a kwali, ban dauka
ba, sabida kallon da yake min, yana waje ne fa amma Tsabar masifar shakkar shi na kasa yin
komai.

"Malama! Me kika kallo haƙa!? Tun dazun nake miki magana baki ce kome ba sai kallon waje
kike."
Ajiyar zuciya na sauke sannan na buɗe baki zanyi magana makalewa maganar tayi
sakamakon jin an zuro hannu ta k'uguna, jan janyo Ni baya, kamshi oud na shaka, na zub'e a
jikinshi sharaf. Kallon Mutumin yayi cikin zafin kishi yace.
" Kaci arzikin!? Ina cikin wani yanayi da wallahi sai na baka mamaki, tunda tace maka Ita
mallakin wani ne sai ka fita harkanta."
Ina jin shi yajani zuwa inda ake biyan kome, ya biya mana.

Koda su Meenal suka zo, suna ganinshi suka fara murnar, biyan musu kome yayi sannan yaja
hannuna muka bar gurin, tafiya mukayi sosai sannan muka nufi wani unguwar tsayar da motar
yayi sakamakon cika mishi kunne da nayi da kuka, ya juya zuwa gidan Hajja, koda muka isa ya
kai hannu ya zai ta bani aikuwa nasaka mishi kuka, tare da buge mishi hannu ina faɗin. "Dalla kyaleni, mugu kawai"
D'alle min bakin yayi ba rike ina kuka.
"Na farko ranar da aka zo sace ki! Na biyu a Traffic Jam! Na uku a Sahad!"
Haushi ya bani na d'ago kaina. Buɗe motar nayi zan fita, ya riko hannuna.
"Kiyi hakuri!"
"Eh hakurin kayane mad'e gamo ka dauka Ni ka maida yar iska mara kamun kai, sha-sha-sha,
ballag."

Fincikoni yayi yana hucci, tsoro ya bani, sune kaina nayi cikin shakkar idanunshi.
"Kar na kuma jin kin zagi kanki, in ba haka ba toh zanyi bulala wanda yafi duka zafi dan na
san ajima bamu haɗu ba, dole kofar takoma ta rufe."
Kwallar bakin ciki ne ya zubo min, banza nayi dashi. Shiga ciki muka yi, sai hira.
D'akin mu a da idan munzo gidan na nufa, ina shiga kamshi turaren shi yayin min barka da
zuwa, zama yayi a falon suka cigaba da hiran amma shi da ido yake binsu kasancewa hiran da
shuwa suke, sai turanci da suke jefawa shima sabida ya shiga hiran.

...... Gyara dakin nayi dan kome na d'akin zaune yake da ɗuwais dinshi, ina cikin aikin ya
shigo, ban san ya shigo ba sai da naji an make min ɗuwais dina na tashi a tsorace, ina binshi
da mugun kallo. A raina nace dole na kwaci kaina a hannun d'an renin hankalin.

Ban daki ya shiga, na juya zan fice murda kofar naji gam ya rufe.
Kumbura fuska nayi kama yana gabana na fara kunkuni ina cewa.
"Wallahi ba zan yarda da mulki ba, aurene dai nima nace banayi eyyee!"
Fitowa yayi alamun alola yayi zai tafi share ruwan fuskar shi yayi ya watsa min a fuska.

Fuuu nazo kamar zan bangaje shi na fita, yayi bake nake a baƙin kofar, tare da watsa min
wasu mugun kallo.
Tsayawa nayi k'am kamar na rufe shi da duka.
"Kinga ada na rashin Kunyarki anjima zamu raba reni."

Tsaki naja kasa kasa, ya kalleni cikin murmushin mugunta ya d'aga kafadarshi.
"Kar naga kafarki a waje"

"Kutt! Hmm lallai fa! fita zanyi abuna wallahi."
Kaina a sunkuye nake maganar, leka fuskana yayi yaga naki yarda mu had'a eyes sai yasa
kai ya fita yana fad'in "idan ban isa dake ba ki fita."

Kwalla ce ta cika idanuna lallai Ashu harda.
Can shashin zuciyata tace.
*Toh meye yayi miki!? Da kike jin haushinsa*
Tsaki nayi a fili nace.
"Kome mana!? Yana sane da komai yake guje min"

*Toh kinsan hujjar shi!?*
"Ban sani ba!!?"
Na saka tsawa, Ni ɗaya nayita shirme nan ina jin haushinsa.
Ina zaune a gurin ya shigo rike da software drinks, ya zauna a bakin gadon karfe, wanda ake
ce masa keke napep.

Bud'e murfin yayi sai da yasha sannan ya mika min, harara na dalla mishi sannan na cigaba da
kumbure kumbure na.

Yana gama sha ya kwanta abinshi cikin ko in kula, ya fara waya haushi kamar na mutu,
ina ji ina gani ya gama ya fita abinshi yarana suka shigo. Nan ne na mike dan lokacin sallah ya
wucce ni,ina idarwa ana kiran la'asar, suma da suka gama dungure wai sunyi sallah, suka
kwanta nima kwanciyata nayi dan bamu tashi ba sai karfe shida, yana shigowa ya shiga ban
daki wanka yayi dan garin Maiduguri akwai zafi sosai, sannan ya fito ya saka jallaɓiya da
hularshi nan, kallon shi nayi na tuna wani lokaci muna yara A makotarmu baban Faruq ya tafi
aikin Hajj. Lokacin dudu yana yaro shine muka nacewa mutumin da zuwa, shine yaje kasuwa ya
sayowa Dudu A sallame d'an naci har da hularshi.
Ganin yadda nake mishi dariya Abin ya bashi haushi, fita yayi yana kwafa, yadda zasu raba
reni.
Bai dawo gidan ba sai karfe takwas, ina zaune bayan na idar da shafa' da Wutir. Ya shigo da
leda a hannun, kallona yayi ya ajiye sannan ya fita, bai shigo ba sai wajen tara yana shigowa
yaga abinda ya kawo a gurin, tsayawa yayi rike da k'ugunshi cikin ɓacin rai, yake kallon kayan.
"Nasan Ummi mace ce ta gari! Kuma macen da tasan darajar mijinta da aurenta! Bazan miki
dole ki fahimce ni ba, amma da da zafi yau magidanci ya kawo abu gidan shi ba'a tare shi an
amsa ba! Sannan ya kawo abu tun awa d'aya da ya wucce ba a duba ba, sabida rashin sanin
darajar aure Nagode sosai"
Durkusawa yayi ya dauƙi ledar ya fita, ya kaiwa su Meenal ya dawo yayi wanka ya saka
kananun kaya wanda ya fidda kuruciyar shi, ina kallon shi yasa kai ya fita abinshi. Kuka ne ya
kwace min, " tabbas nayi laifi amma ina zai tafi da dare nan!? yaushe Ashu na ya fara yawon
dare !? Na shiga uku! Yaushe ya fara niman mata! Nasan halin Jarumi bayi da hakuri akan
mace fa." Ni ɗaya sai surutun nake, dole na shiga damuwa domin duk macen da tasan ciwon
kanta dole ta shiga damuwa musamman tasan yanayin mijinta, kai koda bai da cikakken hankali
bane Muhammad dina matashi me jini a jika. Ina zaune a gurin nayi kuka har na godewa Allah,
Ummi nakira na saka mata kuka, murmushi tayi sannan tace.
"Toh me nene kuma!? Ba kin ganshi ba sai ki share hawaye Allah ya jagoranci aurenku"

"Ummi! Ban san me na mishi ba sai wani fad'a yake min."
"A'ah Safinah nasanki da rashin kulawa, kina son Ashraf amna wani lokacin ke kike assa
rigimarku, don Allah ki nutsu ki

18 / 37