Author : Mai Dambu Category : Read Hausa Novels
[3/19, 8:30 PM] Mai Dambu: **Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna
son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne
150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha
Allah*
Oum Muwaddah......
MJ
BOOK-2
14-Feb-2020
مسب الله نمحرلا !ٖ!!ميحرلا
Fasa ihu Anim yayi cikin karaje, ya shiga fasa duk wani abu me amfani a gurin, juyawa yayi
yana kallon bokan. Take idanunshi suka zama yellow, wani irin hayaki ya fita da mugun gudu
suka shige idanun bokan, take bokan ya sheka ihu yana shure-shure. Tuni ya sheka lahira, shi
kuma Anim ya koma ya zauna, yana numfashi. *"SAFINAH! ta yaudara ta auri wani bani ba! Sai na bata kyauta ba musamman"
*Flashback*
A ranar da motar Anim tayi hatsari, ba a cire shi a raye ba ya rasu. Kasancewar akan Idon Hjy
Nuratu! Aka yi abin sai suka yi amfani da damar su suka ɗauki gawar zuwa gidan wani tsohon
maharbi amma bokane. Kallonsu yayi cikin mamaki yace.
"Abinda kuke bukata akwai hatsari sosai."
Cikin ko ina kula mamie tace.
"Duk hatsarinsa ina son a lalata rayuwar yarinyar ce, ta yadda bazata farin ciki ba, kuma kaga
ya mutu da burin mallakarta, idan muka daga shi da wannan burin Toh zai addabi rayuwarta."
Shiru bokan yayi yana kallon gasar Anim wanda jini ke fita a cikin sa, tashi yayi ya shiga dakin
shi can sai gashi ya fito, yace.
"Mu kama gawar zuwa ciki"
Haƙa suka kama shi zuwa cikin dakin, suka shimfida sannan, ya share gefen guda ya fara
kunna candry, ja,baki,fari,.... Aka shimfida wani har kyale, suka daura shi akai sannan suka
koma gefen, bokan ya cigaba da aikinsa.
Sun kusan awa guda suna abu guda Kafin bukatar su ta biya, dan dakin guguwa ce ta
cika dakin Can ta lafa sannan suka ganshi zauna kanshi sunkuya.
"Anim Matawalle!"
Sake kiranshi sukayi amma bai d'ago kansa ba, sai da suka yi a karo na uku ya d'ago
kanshi da Idanunsa da suka koma yellow.
"Mun tashe ka ne dan ka dauki fansan abinda aka maka, idan bai maka ba zaka iya
komawarsu kayi kwanciyar ka."
Wani baƙin ruwa ne ya shiga sauka a Idanunsa, ya fashe da kuka, basu dakatarshi ba.
"Sai na hana kowa nutsuwa sai na cusa musu damuwa da bakin ciki. Sannan na kashe
SAFINAH haka ne zai kashe wutar fansan dake ci a ruhina."
Sun jima suna kara mishi hudubar tsiya, sannan suka barshi a dakin.
(Motar sau dama mutane na tambaye akan ghost, shin akwai su? Scale Basu domin duk
wanda ya mutu ya mutu ne dan aya guda ce mutuwa, mushrikai batattu sune suke haifar da
ghost, ta hanyar amfani Ni da demons, bakaken ifiritai dan haka sai ku duba halin da Anim yaƙe
ciki, kuma abinda na manta shine su Demons suna, aiki da Burin dake rn mutum ne, da burin
da ya mutu akai.)
........ Tun daga ranar Anim ya fara wannan abubuwan da suka faru a baya, kallon gawan
bokan yayi sannan ya tsallaka shi.
***
Rufa min akayi suka shiga min fifita, Khalilah suka shigo da Ummi. Ruwa Batul ta watsa min,
ajiyar zuciya na sauke tare da atishawa. Kuka nake son nayi amma yaki zuwa min lumshe
idanuna nayi. Tare da juya musu baya.
Fita Duk sukai aka bar ummi ita ɗaya a dakin.
"Sam banga abin damuwa ba! Tunda....
*"""
...... "An rigada an daura toh me nasuma kiyi hakuri ki rungume kaddararki, karki zama mara
godiyar Allah mana, idan kina haka ya kike son Ni naji, don Allah ki kwantar da hankalinki, kuma
kiyi biyayya ga mijin da aka baki. Koda kuwa jinjirine, toh kiyi mishi biyayya, idan kika min haka
kin gama min kome,"
Kuka ne ya kwace min, shi kenan sun rabani da Dr. Rufe idanuna nayi. Naki magana
haka ta gama min nasiha ta fita, taja min kofar haƙa na cigaba da kuka, su kuwa basu fasa
shagalinsu ba, ina jin Yadda gidan ya kaure da hayaniya, ji nake kaman kaina zai kunne, ga
zazzaɓin da ya rufe ni. Babu wanda ya kuma bin kaina, sai wajen karfe uku Ummi tashigo min da lafayya, peach
colour. Ta shiga ban daki ta haɗa min ruwan wanka, haka tasani a gaba har ban daki, ta
taimaka min na cire kayana sannan tafita, a sannu na shiga cikin ruwan wankan, Banda
kamshin turaren wanka babu abinda ke tashi. Banɗakin gaza fitowa nayi sai da ta min magana,
sannan na fito. A hankali take shirya ni.
"SAFINAH!!! Yanzun kin fita daga ikonmu kin shiga ƙarƙashin ikon abokin rayuwarki! Kin buɗe
wani sabon shafin rayuwarki, wanda yake d'auke da kalubale da yawa tare da matakai hawa
hawa, a yanzun kina matakin farko na Amarya.
A yanzun yan uwansa da danginsa zasu zo domin samun alaƙa a tsakaninku, idan kina da
dabara sai ki janye su. Zuwa jikinsu, dukda wasu dangin ba a iya musu amma dole ki rufe
idanunki ki kuma mikar da hannunki a koyaushe hannunki ya zama shine a sama da nasu,
Mahaifiyarshi, dole koyi yadda zaki kyautata mata, badan kome ba sai dan ya haifa miki miji, ta
kuma bar miki shi, wannan matar ta cancanci a yaba mata, sai dai ki sani wasu suna da
kawazuci akan yaransu, koda zata fito miki da wani hali kiyi mata uzuri, dan ita ɗaya tasha
wahalar shi, dan yau ta nuna jin zafin ta akanshi karki ga laifinsu, dan ko kece kika wayi gari
ana juya miki akalar yaronki sai inda karfinki ya ƙare. Sai matakin zamantakewa, babbar
matsalar da muke fuskanta a cikin wannan karni shine mata sun koma kamar Jakuna akan
jima'i, no shi din kamar jijjiyar bishiyar Aurece, ko nace hanyan bishiyar aure. Sannan idan babu
ita a cikin rayuwar aure toh ana fuskantar kalubale, wanda yakan kai har kotu a raba auren,
idan kuma aka samu yayi yawa shima akan iya raba auren,, sabida zai zama cutuwa. Abinda
yasa mai miki magana saboda Yadda wasu matan suke mu'amala da magungunar mata, wanda
sanadin haka ya haifar musu da matsala, kafin ki fara shan maganin ki fara duba wani Irin miji
gareki, dan akwai maza dayawa. Wani ko ya'ya yaga mace, toh yanzun zai shiga cikin lalura
bukata, wani kuma idan mace zata kwance gayarta ta kwanta a gabanshi fesa zai tsallakata ya
wucce, wani kuma da zaran sun shiga fagen fama da mace, ko minti biyar baya kaiwa zai
sauka, wani kuma har sai ki ce mishi kin gaji bazaki iya ba, yake iya jin tausayinki, ya kyaleki,
idan kina fahimci miji ko yana da buƙata amma baya komawa, maganin mata banɗaki bane, sai
dai fruit. Da tsarki da ruwan zafi, idan kuma kika fahimci yana da matukar damuwa toh dole ko
zama me haɗa maganin mata da kanka domin bana son ko sayi magani a gurin kowa.
Sai matakin mijin shi kanshi sai kin iya zama dashi, in ba haka toh ko shekara baza a rufa ba
zai sakoki, shi na miji ko ya'ya yake yana ma'aurata son girma, wani lokacin kai za'a batawa
amma dan a zauna lafiya zaki bashi hakuri, kuma yayita shan kamshin sai jiki kamar ki rufe shi
da duka ya miki laifi kina bashi hakuri yana ce miki. "Eh ai dan kin renani ne, dan kin ga ke ɗaya ce wallahi kika sake na karo aure zaki sha wahala,
dan matukar nasami Macen da zata daina bata min toh"
Yadda kasan kike da tsiwar nan zaki amsa mishi, wanda kuma yin haka ke tinzirasu yayita
fada Yana kunyataki a gaban mutane, haka ba dai dai, bane idan zaki iya hakuri yazo da zafin
kan nan,
Nadan zaki ji zafi amma sai ki shanye kice toh ai wallahi aka hutar dani, yawan aikin gida,
kuma ka samomin abokiyar hira, Allah wane nice zan haɗa maka kaya, ke ya gaya miki dan ki
fusata ke sai ki maida mishi dan yaji cewa baki da damu akan haka, karshe idan yaga baki
damu ba ce miki zai yi mahaukaciya, ke har murna kike dan zan kara aure, k'inga kinyi laifi yazo
yana faɗa kin manna mishi hauka, matsalar da muka samu ke nan a cikin alummar hausa, wata
mace tana ƙoƙarinta amma mijin baya gani, wata kuma zaki sha mamaki idan.kia ga yadda
mijinta yake kokarin Ganin ya kare mata mutumci amma bazata gani ba karawa ma sai ta haɗa
mishi da fitsari, wanda haka na cirewa namiji soyayyarki a zuciyarshi, dole mu zamo masu
hikima dabara, dan wallahi wani na mijin baki taba cin amininsa sai da dabara, wani kuma kome
zaki yi idanunsa na kanki, kiyi ƙoƙarin sanin waye mijinki, dabi'arshi ma'amalarshi da jama'a,
babu ruwanki da wayarshi. Sannan mataki na gaba kishi toh kishi ke kawo kishiya, musamman
jahili kishin da ake yin nan na kashe mazaje kishi, halal ne. Amma banda mahaukacin kishi,
nayi imani da Allah kin haddace Alkur'ani, tartilil da tafsir, kinsan wasu hukunce-hukuncen akan
addini. Kuma kina da sani akan addu'o'i, zanyi bakin ciki naji kina daga mishi hankali akan kinji
yana waya da wata, sabida kuna ƙoƙarin dakatar da abinda ALLAH yace ne, idan kika nuna bai
isa ya kawo miki ita ba, kin isa ki hanashi bin matar layi ce, kuma yaje yayi yadawo gidan yayi
wanka, me tsoron Allah shine zai yi a waje amma wanda ya riƙa, a cikin ban dakinki zai yi kuma
ya zo ya kwanta a gadon, saboda yace zai aure kince da yayi gwara a yadda Abuja da Bama
bamai, kin hanashi, ba dole yaje wajen gun matar banza ba, matukar kika iya da mijinki. Kuma
kika masa Adalci a zaman kuma kika nuna mishi dan Allah kike zauna dashi, Wallahi bazai taba
cutarki ba, idan kika rike Allah babu yadda ya Isa cutar dake."
Ummi bata barni a haƙa ba sai da yayita fada min wasu dabarun da yadda zan zauna da
mijina yan uwanshi mahaifiyar shi, abokansa da makotansa, uwa uba Yadda zan kilace mishi
dukiyar shi, yadda zan kula da al'amuran shi. Sosai ummi tayi min bayani akan rayuwar aure,
tun ina jin kunyarta har na sake, tana gama min tace." "Hmm! Ki daina jin kunyata, dan Ni banga abin jin kunya ba, kiyi ƙoƙarin bin mijinki zaki zama
taurariya, sannan iya gyaran jiki aka miki, idan an kwana biyu ki min magana akwai haɗin da
za'a kawo min daga Maiduguri. kin nutsu don Allah ki bar wautar nan kingan rayuwar aure, kin
ajiye kuka da shirme ki, bana son rigimar, ki zauna lafiya da kowa koda wasa bana son rashin
kunyar nan, sai miskilancin nan ki ajiye a gefe, ki rungume Rayuwar Aurenki. Ban sani ba
amma toh Allah ya baku zaman lafiya da kwanciyar hankali."
Daga haka tayi ficce abinta, can sai ga Nanah Asma'u da abinci, kasa ci nai sabida bana jin
dadin kome...
....... Da yamma ina kwance suka kawo me makeup, aikuwa nace bani so, indai dan Ashraf
za a min kwalliya wallahi bazanyi, ba kai kira na tsani Ashraf, ehhe.
Ganin naki yardar Amin kwalliyar suka kira Ummi aikuwa na bare baki nayita kuka, karshe
tace su ake kawai, tunda bana so, haka nayi ta juyin Abuna ashe dinner suka shirya zasu yi,
naki kula batun, sai da aka fara mangariba na tuna Dr da yace shi zai zo ya ɗauke dan ya gama
mana visa, kuka na cigaba dayi kamar ƙaramar yarinyar, Bayan sallar Isha, aka zo fita dani,
dakin ummi aka kaiyi tayi dan abinda zata Iya, sannan aka zo zasu kaini dakin Abba, anan ne
nace bansan zancen ba, na rike ummi ina kuka. Itama kuka take sabida na riƙe sosai dakyar
aka cireni a jikinta ina kuka, sannan suka kaini Palourn Abba nan shima yayi min nashi, sannan
ya sakawa Umma da Aunty Inna, da Ya kaka Yayarsu Ummi. Aunty Kuma Yayarsu Abba, suka
fita dani, tare da rakiyar mutane. Tunda aka sani a motar na kifa kaina, nake kuka har muka bar
gidan, bansan unguwar da suka kaini ba. Na dauki Umma nacewa.
"Yawwa shiga da bismillah, Ubangiji yasa an kawo ki kenan sai dai ki rakashi ko yarakaki,"
sai da naji zuciyata ta buga yo taya zanso haka ai duk k'iyayyarsa da nake ji bazan so naga
gawan Uban yarana ba.
Take zuciyata tace.
*Umma Zance ki Inconcluvise ♀️, don da yarone angon ba zanyi fatar takaba ba, sai dai Ni
narigashi Dan nayi imani da Allah babu Macen da ta isa rabashi da yaransa, idan kuma ta nace
zata sheka*
(Ki min munahuka kice baki sonshi ki kuma koma hmm)
A baƙin gado akace na zauna, da bismillah nan suka shiga bin gidan wanda yaji kyau bana
wasa ba, kitchen dina kuwa kome na ciki orange da brown ne, dakine akayi amfani da minti
green da cream. Sai falon inda aka hada black & Whiter, kowa sai magana yake akan gidan,
tsarin gidan Ni kuwa ina can na cusa kaina tsakanin cibiyoyina, ina jin suka gama suka tafi, sai
Batul da Khalilah aka bar min, bayan tafiyarsu. Sai ga abinci aka kawo mana, lokacin na shiga
ban daki, bayan tafiyar masu kawo abincin na fito, suna min magana na haye can karshen
India best ɗina na kwanta, ban kuma bin takansu barci yayi gaba dani, saboda ciwon kan da
nake fama dashi...
***
Da asuba ina tashi nayi wanka da alola, nazo na gabatar da sallah,ina azkar su Khalilah
suka tashi ban daki suka shiga, ina jin fitowar su lokacin Ni har na kwanta, barci me karfi yayi
gaba dani, dan nasa damuwa a raina. Kuma ya haifar min da zazzaɓin me zafi, har zuwa ranar
ina kwance ana hidima. Zuwan Dudu dan Sophia ta gaya mishi gani nan ba lafiya allurar da
magani ya bani, sannan ya tafi. Ina jin akwai wani abinda za ayi amma ganin bani da lafiya dole
suka hakura, Ni kuwa da ake gun gwara nayi pretend bani da lafiya, dan bazan je wata uwar
mata dani ina tafe dan jinjirin kanina na nunani a matsayin matar shi tirrr, wallahi bani zuwa ko
ena, a gidan ma sabida kar ayi dani yasani yarda aka min kwalliya, amma da bazanyi kome ba.
Na tsani wannan auren da shi mijin ma, sai na shuka mishi rashin mutunci sani yake zancen,
sai yayi Yaren Jordan bayan larabci, sai ya gwammace bai Aureni ba, mayye kawai dama
larabawa me suka sani da zaran sunga mace, penis dinsu take tashi toh sai naci Uwar
zandariyar ma, dani yake mara kirki ko yaushe yasan dadin mace da har iskancinsa bazai tsaya
kan kananun ba sai Ni guzumemiya dani wai zai aura lallai nayi sake Reni me girma ya ratsa
tsakaninmu da Ashraf dani yake zancen zan kamashi sai ya gane bai da wayo....
Anya Didi
(Am Sorry idan baku manta ba na gaya muku cewa Ni yar Bauchi ce amma haifaffiyar kudu dan
haka kuyi har da Hausata)
[3/19, 8:31 PM] Mai Dambu: **Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna
son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne
150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha
Allah*
Oum Muwaddah......
MJ
BOOK-2
15-Feb-2020
Pagen.✌️
Ni kaina ina jinjina kallar rashin mutuncin da zan shukawa Ashraf, yadda bazai taba tunain haka
yan naija dama suke, dan sai masai gudu jordan da a kafata ji, dani yake zance ba dai ya nace
sai da ya aureni, toh Insha Allah, sai na haɗa mishi zafin kan da sai ya rasa yaadd zai dani, ko
sunana yaji fecce zai yi da kafarshi,na rasa gane me yasa ya addabi rayuwata, ga yan mata
kaca² amma dan fitsara wai nice zai aura, mara kirki bayan ya dauke min dan Abinda darajata
shi yasa ya nanikewa rayuwa, inba haka ba taya Wancan Dudu zai makale min, da rashin
kunya wato dan yaga na haifar min Yara shine yake jin kanshi daya dani, bani manta kwanaki
har dace min.
"Safinah! Duk abinda kike bazai dame Ni ba sabida ni namijine kuma na rantse da Allah na miki
illar da bazaki gane haƙa ban sai nan gaba, zaki gane haka duk duniya idan ba dani kika haɗa
shimfida ba toh wallahi duk wani namiji kallon mara lafiya zaki mishi, dan haka ki bar zazzafa
k'iyayyar da kikt min dan zai iya rikiɗewa ki faɗa son ba tare da kin sani ba, kinga dan tsohuwar
baiwata tafada SOYAYYA da boss ɗinta ba wani laifi bane, amma akwai cutarwa dan Ni Yarone
karami wanda nake lokacin kuruciyata ga kuɗi ga mulki ga kyau ga Nasaba, gashi yan mata sai
haukacewa suke a kaina suna cewa Indai. Ba Balarabe ba sai sun rataye kansu Ni kuwa haka
bai dame Ni ba, idan kema zaki faɗa sona ko Kuma kin faɗa tun asali zaki iya kirana kice,
Yayana Ashu zo.na gaya maka sirrin zuciyata, aini na faɗa rijiya kaunarka, tare da rataye kaina
a bishiyar