Author : Mansur Usman Sufi Category : Arewa Pen
Ubangiji suka
amshi kalmar shahada,
Batare bata lokaci ba jarumi shamsuddin ya auki TAKOBIN AUKAKA ya tofa mata Ayatul-
kursiyyu take takobin ta canza launi kuma rubutun sunayen fiyayyan halitta annabi Muhammad
Sallallahu alaihi Wasallama dake jikin takobin suka fito raau,
Shamsuddin ya dubi su lasmirat yace" waannan sunaye su ne suka bawa su Boka
Dayyubul-Barmas nasara akai na har nasha bakar wahala,
Haia duk wanda yayi rigo da kamun kafa da mai sunan wato annabin rahama s,a,w zai samu
nasara. A komi nasa koda kuwa kafuri ne Allah zai jinkirin ta masa na wani lokaci kafin na
kamashi
Koda jin wannan jawabi daga bakin shamsuddin sai kowa ya sake jin kaunar shugaban halitta
ta arsu a zuciyar sa ,
Batare da wani bata lokaci ba su aljani Huzmal suka sake aukar su shamsuddin aka nufi hanyar
dazata kai su birnin Misra
Bisa mamaki a wannan lokaci sai su Huzmal suka ga cewa karfin gudun nasu ya karu ainun
Abin da basu sani ba shine sirrin hasken MUSULUNCI ne a tare dasu ya basu karfin gudun
Tsawon kwanaki huu aka auka a wannan lokaci bisa taimakon Ubangijin halitta aka iso birnin
Misra
Nan fa waziri ukashat da jama'ar birnin suka fito tarar su sarauniya lasmirat da tawagar ta
Bayan an sauke su an haa liyafar Abinci da abin shaye shaye nau'i daban daban,
Take kowa ya shiga kimtsa cikin sa ana fira cikin nishai
Su ma su Aljani Huzmal sai akawo musu tasu liyafar abisa wadannsu manyan tukwane dake
auke da farfesun naman rakuma da shanu
Nan fa suka fara tanar baki suna rafka koma,
Al'amarin da ya sanya har dariya ta subuce wa yaslir da Sunaila kenan bisa ganin aljanu nayin
kalace,
Bayan kowa ya samu nutsuwa ne waziri ukashat yakashe labarin abinda yafaru bayan tafiyar
lasmirat ya zayyanewa lasmirat daga farko har karshe,
Da abinda yafaru tsakanin su da wannan dodo daya bayyana a fada
Batare da bata lokaci ita lasmirat ta shiga bawa jama'a labarin tafiyar su da abinda yafaru
tsakanin su da shamsuddin da abubuwan al,ajabi da ya nuna
Sa,adda jama'a sukaji wannan labari sai suka cika da inkin al'ajabi kuma suka ce tabbas munyi
imani da Ubangijin jarumi shamsuddin take sarauniya ta biya kalmar shahada
Dubban miliyoyin jama'ar ta suka amsa,
Sai da aka nako guda shamsuddin na koyar da jama'a yadda ake gudanar da ibada kuma yana
jinyar raunukan dake jikin sa
Sannan aka shiga shagalin bikin aurin auren sarauniya lasmirat da shamsuddin, yaslir da
Sunaila,
Bai daga sassan duniya sun halarci taron bikin
Akayi shagalin da ba,a taba yin kamar sa ba
Tun daga wannan rana HASKEN MUSULUNCI ya mamaye ko ina arzikin birnin Misra ya kara
bunkasa
Bisa dole sarakunan dake nahiyar suka dunga zuwa da kansu suka karbar addinin Musulunci,
Jarumi shamsuddin yazo sabon Sarki birnin Misra,jarumi yaslir yazamo shugaban majalisar
sarki,
Musulunci ya cigaba da bunasa.
Karshe
Alhamdulillah