TAKOBIN DAUKAKA BOOK COMPELET BY MANSUR USMAN SUFI.pdf

Author :  Mansur Usman Sufi Category :  Arewa Pen

Chapter   3 / 9

6K to 9K   out of 24.6K words

kuwa a cikin hankalin ka kake kuwa?

Muraizu ya bushe da dariyar mugunta har ya kusa faɗowa daga kan dokin sa daga bisani ya
haɗe rai yace"Tabbas garau nake nasan Abin da nake faɗa ina cikin hayyacina,

A halin yanzu ba neman shawarar ka muke yi ba face zartar da umarnin mai girma Husnalu,

Koda jin wannan batu daga bakin muraizu sai na fusata ainun ya dakamasa tsawa cikin
matukar fushi na dube nace " karyar ka tasha karya yakai wannan la'ananne kuma BAKIN
AZZALUMI kayi sani cewa karyarka tasha karya baza mu taɓa lamunta da wannan magana
taka ba,
Kafin na gama rufe bakina sadauki muraizu ya fusata ainun ya zaro kibbau guda biyar a gadon
bayan sa ya ya saka a cikin bakan sa yaja ya ɗame cikin wani irin zafin nama ya harba kibban

Kafin ɗaya daga cikin mu yayi wani yunkuri kibiyoyin guda biyar sun sauka a kan waɗansu
jama'ar mu mutum biyar sun faɗi kasa matattu



Mutum biyar ɗin sun kasance dattijawa kuma manyan yan majalisar sarki da muke matukar
alfahari dasu a cikin ƙauyen Darul-Na'am

Koda sarki Abu-salimat yayi arba da gawarwakin yan majalisar tasa sai hawayen takaici da
bakin ciki suka zubo masa,

**

Lokacin da saurayi yaslir yazo daidai nan a labarin sa sai hawaye suka zubo daga idanun sa,

Al'amarin da ya sanya sarauniya lasmirat ta kamu da matukar tausayin sa kenan.

Har ta buɗi baki da nufin tace wani abu sai kawai suka ga sararin samaniya yayi dubu dunɗim!

Cikin matukar firgici lasmirat da saurayi yaslir suka ruga mike tsaye zumbur suka ruga izuwa
wajen turakar, suna fita suka ci karo da Sarkin yaƙi,

Sarkin yaki ya dubesu cikin tashin hankali yace " ya shugabata muna cikin gudanar da ayyukan
mu na tsaron kofa kawai sai mu kayi arba da wata gibgegiyar halitta mai matukar muni daban
tsoro tana ta hallaka mutane,

Ya shugabata na rantse da karfin mulkin ki babu wata halitta da zata tsira da ga sharrin halittar,

Kafin Sarkin yaki yagama rufe bakin sa sarauniya lasmirat ta tari numfashin sa tace" A yi maza
aje a busa ƙahon yaƙi,

Batare da lasmirat ta jira Sarkin yaƙi ya furta wani abu ba ta shige gaba yaslir ya mara mata
baya yana mai dogare da sandar sa,

A can cikin gari kuwa halittar ta wanzu tana ta hallaka mutane jama'a suna ta guje-guje da
ifice-ifice domin tsira da rayukansu,

Duk inda halittar ta sanya a gaba sai dai kaga gawarwakin jama'a birjik kwance a ƙasa cikin jini,

A wasu lokutan ma sai kaga halittar ta sanya hannun ta ta yaye rufin ɗaki ta ɗauko mutum ya na
ihu ta sanya a bakin ta ta laƙume tayi loma ɗaya dashi,

Ana cikin wannan hali ne sai aka hango sarauniya lasmirat da saurayi sun rugo wajen a bisa
dawakai cikin gagarumar shigar yaƙi suka tsaya cak,

Kawai sai lasmirat ta dakawa halittar tsawa,

Koda halittar taji an dakama tsawa sai ta tsaya cak a waje guda ƙurawa su lasmirat idanu tana
mai nazarin su,



Ita dai wannan halitta takasance,shirgegiyar aljani mai matukar tsawo,muni,gami da ban tsoro,



Babu wata halitta da zata yi arba da wannan aljanar face firgici, Saboda matukar munin ta



Duk irin dakewar zuciya irin ta lasmirat da saurayi yaslir sai da tsoro ya ɗarsu a zukatan su,



Dakarun dake bayan su kuwa sai jikin su yakama kyarma yana tsuma tamakar ace kyat su cika
wandon su da iska saboda tsananin tsoro,

Sai da aka shafe tsawon dakika talatin a cikin wannan hali ana kallon kallo



Daga can sai aljanar ta bushe da dariyar wanda ta haddasa girgizar kasa,



Nan fa bishiyoyi suka dunga karairayewa suna zube ƙasa, gida je su ka dunga rushewa suna
hallaka, ƙasa tana tsagewa dawakai da mahayan su suna rufta wa cikin ta,



Ihun mazaje,mata, tsofaffi gami da yara ya cika dodon kunne,



Sa,adda sarauniya lasmirat taga yadda jama'ar ta ke hallaka sai ta cika da tsananin baƙin ciki
maral musaltuwa,



Cikin fushi ta sake dakwa aljanar tsawa a karo na biyu tana mai cewa "yake wannan shu'umar
aljana yau duhun ta cika idan har kin isa ki fito muyi fito-na fito na rantse da karagar mulki na sai
na ga bayan ki,



Koda jin wannan batu sai aljanar ta tsuke bakin ta komai ya samu dai dai tuwa bishiyoyi suka
daina karyewa duwatsu suka daina fashewa kasa ta dai na tsagewa,



Aljanar ta buɗe bakin ta wanda yafi kama da kofar gari cikin murya mai ban tsoro tamkar saukar
aradu tace"yake wannan sarauniya kayi sani cewa bakomai ne ya kawo wannan birni naki ba
sai domin ya kashe mutanen birnin ki kuma na mallake ki saboda wata muhimmiyar buƙata ta,



Kafin aljanar ta gama rufe bakin ta saurayi yaslir ya tari numfashin ta yana mai daka mata tsawa
cikin fushi yace"yake rafkananniyar aljana kuma yar tsakuwa a cikin jerin JARUMAN DUNIYA,

kiyi sani cewa karyar ki tasha karya ina mai tabbatar miki dacewa bazaki tsira daga sharrin mu
ba,



Sai ki shirya ka maza nan bisa kanki,



Yana gama faɗin hakan ya sakarwa dokin sa linzami yana mai gyara rikon sandar sa cikin
hanzari lasmirat ta mara masa baya tana mai ɗaga takobin ta sama,



Sauran dakaru mutum dubu arba'in sukayi koyi dasu



Ana haɗuwa aka kacame da azababban yaƙi mai matukar tayar da hankali



Domin kafin a haɗu sai da aljanar ta sanya hannu ta ta ɗebi dakaru mutum hamsin har da
dawakan su ta watsa a bakin ta ta taunesu tayi kalaci dasu,



Sannan ta afkawa su lasmirat.



Lokacin da aka kacame da azababban yaƙi tsakanin shu'umar aljana da su sarauniya lasmirat,



Sai lasmirat da yaslir suka wanzu suna kaiwa aljanar sara da suka cikin tsananin zafin nama
JURIYA DA BAJINTA



Duk sa'adda makaman su suka sauka a jikin aljanar sai kaji sun bada kara ƙal ƙal !! Tamakar
karfe suka sara

In banda lasmirat da yaslir suna cikin kariyar tsafi da tuni sun hallaka,



Idan aljanar ta kaiwa yaslir da lasmirat hari da hannayen ta, idan suka goce duk abin da hannun
ta ya sauka akai sai dai kaga ya tarwatse,idan kuwa a ƙasa ne sai ya haddasa wani rami zurfin
gaske,



Take dakaru da dawakan su zasu afka cikin sa suna ihu da kururuwar neman taimako,



Nan fa waje ya cika da ihun mazaje mata da yara da matasa,



Karafniyar ƙarafa ta cika dodon kunne, JINI DA KASA suka cakuɗu, ƙura ta turnuƙe sararin
samaniya,



Lokacin da aka shafe dakika ɗari biyu da sittin ana wannan bakin gumurzu,



Sai ya zama na cewa aljanar ta samu nasarar hallaka dakaru Fiye da dubu shida,



Amma bata samu nasarar koda lakutar jikin su lasmirat ba sai ta cika da matukar mamaki kuma
ta fusata ainun,



Abin da ya bata mamaki shi ne ya akayi sarauniya lasmirat da saurayi yaslir suka kasance
masu tsananin zafin nama, tabbas yau ta haɗu da takadiran jarumai, hakika rashin wannan
nasara ƙasanta darajar ta ne da kimar ta,

Koda tazo nan a tunanin ta sai kawai ta canza salon faɗan ta yazamana cewa tana haɗa kai
bugu da naushin hannu da ƙafa,



Ai kuwa nan take labari yasha Bambam, domin a halin yanzu daƙyar su yaslir ke iya mayar da
martani



Idan ta daki gini ya tarwatse sai kaga duwatsun sun yiwa su lasmirat lugudan duka,



Sai da aka shafe tsawon dakika dari da ɗoriya ana wannan fafatawa,



Ana cikin wannan yaƙi ne aljanar ta kaiwa sarauniya lasmirat da yaslir wawan naushi da nufin yi
musu farat ɗaya,



Amma kafin hannun ta yakai gare su sai suka daka tsalle a sama tamkar an harbosu daga cikin
baka suka bar kan dawakan su



Sai gashi hannun ya sauka akan dawakan sun tarwatse tamakar an talitse tumatir,



A daidai wannan lokaci ne yaslir da lasmirat suka sauka akan aljanar bisa tsakiyar kanta su
shiga kafta mata sara babu sassauci,



Nan fa yazamana sun riki ta aljanar yazamana cewa ta daina kaiwa dakaru hari



Sai dai ƙoƙarin taga ta jefo su yaslir daga kan ta, ana cikin wannan hali ne aljanar ta samu
nasarar damƙo su yaslir ta hannun ta ta matse su nan take suka sume sakamakon maƙurewar,

Ashe ta samu nasarar karya ɗan yatsan yaslir, lasmirat kuma ta samu gocewar ƙashi, a hannun
ta,



Koda samun wannan gagarumar nasara sai aljanar ta bushe da shu'umar dariya



Sai da tayi dariyar ta ishe ta sannan ta tsuke bakin ta kawai sai ta juya ta nufi kofar fita daga
birnin tana mai koɗa kanta gami da yiwa kanta kirari, tana mai cewa



" Saini GAWURTACCIYA uwar hatsabibai,



GUGUWAR YAƘI nake mai share MAYAKA,



ANNOBA ƊARI nake duk wanda ya Kusan ceni zai baƙun ci barzahu,



Ni ne gararriya uwar gagararru,







Haka ta cigaba da yiwa kanta kirarin tana lafiya a cikin birnin,



Duk sa'adda ta ajiye kafarta ɗaya sai dai kaga ƙasa tana girgiza tamkar zata tsage abin da ke
saman ta ya faɗa cikin ta

Koda sauran dakarun suka ga abin da yafaru sai suka dunga ɗame kwari da bakan su suna
Harbin aljanar



Duk tsananin yawan kibban sai yazamana a banza domin ko gezau batayi ba



Sai dai ma kaga ta sanya hannun ta ɗaya tana karkaɗe kibiyoyin kamar tana kaɗe ganyayyakin
bishiya,



Kwatsam bazato babu tsammani sai aka ji aljanar ta kurma wawan ihu kuma ta faɗi ƙasa tim,



Ta saki su sarauniya lasmirat suka faɗo ƙasa babu alamun rai a tare dasu ,



Kuma akaga aljanar ta ɗaga hannayen ta sama tana mai roƙon gafara



Al'amarin da yayi matukar bawa dakarun mamaki kenan, suka rugo izuwa wajen domin su ga
abin da ke wakana,



Su na isowa sai suka ja linzamin dawakan su suka yi turjiya,



Ai kuwa sai su kayi arba da wata kyakkyawar budurwa,



Budurwur takasance dogowa mai matsakaicin kaurin jiki, cikin ta ashafe yake tamkar bata cin
komai ba,

Kuma a tsuke yake daga ƙasa, ƙugunta mai faɗi ne yayi tudu sosai, gashin kanta mai tsawo ne
ya zuba har izuwa kan kafaɗun ta baƙi ne siɗik tamakar gilashi, a jikin ta tana sanye da tufafi irin
na mutanen birnin sun, kanta daure da bakin rawani idanun ta kaɗai ake gani,



A sannanne dakarun suka fahimci cewa wannan bakuwar budurwa ce ta ceci rayuwar su
sarauniya lasmirat,



Bakuwar budurwar ta nuna aljanar da ɗan yatsan ta na hagu take aljanar ta ƙame, tamakar
gunki, komai na jikin ta ya daina motsi,



Faruwar hakan keda wuya sai budurwur ta taka da ƙafafuwan ta izuwa inda su yaslir ke
kwance,



Kawai sai ta buɗe bakin ta ta karanto waɗansu kalamai da ita kaɗai tasan me take faɗa,



Tana gama rufe bakin ta sai aka ga sarauniya lasmirat da saurayi yaslir sun mike tsaye zumbur
tamakar babu wani abu da ya same su.



Kafin wani daga cikin su yace uffan, budurwar ta sake nuna aljanar a karo na biyu da ɗan
yatsan ta,take ruhin aljanar ya dawo jikin ta, komai nata yana yin motsi,



Budurwur ta buɗi baki cikin wata irin zazzakar murya tamkar ana busa sarewa tace" yake
wannan AZZALUMA kiyi sani cewa na yarda zan barki Lafiya kici gaba da rayuwa amma bisa
sharaɗin cewa za ki dai na zaluntar al'umma,



Cikin ladabi da ƙan-ƙan da kai aljanar tace Muryar ta na rawa saboda tsoro" Na amince ya
shugabata na ɗaukar miki alkawarin cewa bazan kara cutar da wata halitta har abada,

Koda jin wannan batu sai budurwur tayi wa aljanar nuni da ta tafi,



Cikin hanzari aljanar ta miƙe tsaye ta buɗe manyan fuka-fukan ta tashi zuwa sararin samaniya
tana mai keta gajimare cikin tsananin gudu keta Sa'a ta ɓace,



Nan fa gaba ɗaya jama'ar dake wajen suka cika da matukar mamaki maral musaltuwa,



Abu na farko da ya basu mamaki shi ne yadda ta ceto rayuwar su sarauniya lasmirat kuma suka
warke sumul,



Abin da yafi basu mamaki kuma ya ɗaure musu kai shi ne yadda bakuwar budurwar take
sarrafa aljanar tamakar tana juya waina (masa) a tanda,



A ɓangaren sarauniya lasmirat kuwa, mamaki ne ya cika zuciyar ta ta kasa cewa uffan,



Yaslir kuwa yafi kowa mamaki domin ko a mafarki bai taba ganin ya mace mai baiwar sarrafa
irin wadannan aljanu ba,

Kawai sai ya ƙurawa budurwur idanu yana nazarin ta, duk da kasancewar fuskar budurwur na
rufe da rawani amma idanun ta kaɗai yaslir ya kalla ya fahimci cewa ta nunka sarauniya
lasmirat a kyawun sura,



Lasmirat da yaslir suka taka da ƙafafuwan su izuwa inda budurwur take tsaye, suka risina da
kawunan su kasa domin girmama wa agare ta,

Sannan lasmirat ta ta dube ta cikin murmushi mai taushi tace"yake wannan basadaukiya mace
mai kamar maza shin mene ne labarin ki?



Menene kuma dalilin da ya sanya kika ceci rayuwar mu ni da jama'ar birni na?.



Koda jin waɗannan tambayoyi sai budurwur tayi shiru tana mai nazari,



Daga can sai ta ɗago da kanta ta dubi yaslir, lasmirat tace cikin tattausar murya



" Da farko dai suna na Sunaila na fito daga cikin wata nahiya da ake yiwa da Haurul-zamras,



Abin da ya baro dani daga birnin mu shi ne domin na sadu da waɗansu irin mutane da ake yiwa
laƙabi da musulmi,



Babban burina shi ne na sadu da su kuma na karɓi Addinin su domin na samu nasarar ɗaukar
fansa akan azzalumin sarki da ya rusa mini farin cikin rayuwa ta,



Wannan nasara da kuka ga na samu na sarrafa wannan aljana ba tsafi ba ne kawai ina neman
taimakon Ubangijin ma'abota addanin Musulunci ne,



Sa'adda jaruma Sunaila tazo nan a bayanin ta sai mamaki ta turnuƙe su yaslir,



Sunaila ta ɗora da cewa" Na shigo wannan birni naki ne na ɗan wani lokaci ne domin na bincika
ko zan dace na samu irin waɗannan mutane ma'abota addinin Musulunci,

Koda jin wannan batu Daga bakin Sunaila sai lasmirat ta ce"Kada ki samu damuwa yake
Sunaila zan baki masauki har zuwa lokacin da za ki sadu da mutane ma'abota addanin
Musulunci, domin ba za mu iya biyan ki taimakon da kika yi mini ba,



Koda jin hakan sai sunaila ta cika da matukar farin ciki tace" Godiya nake ya shugabata,



Da jin haka sai lasmirat ta matsa daf da ita ta yadda suna iya jin numfashin juna ta dafa kafaɗun
ta tace da ita" yake Sunaila daga yau bana so ki kirani da shugabar ki face abokiyar ki ko
Aminiya,



Sa'adda Sunaila ta ji hakan sai ta gyaɗa kai cike da farin ciki,



Cikin hanzari sarauniya lasmirat da yaslir suka juya suka nufi gidan sarauta,jaruma Sunaila na
biye da su,



Ana cikin tafiyar ne lasmirat ta lura cewa yaslir yana satar kallon jaruma Sunaila ta wutsiyar
idanu,



Nan take taji kishi ya turnuƙe ta, domin ta fahimci cewa yaslir yana yiwa jaruma Sunaila kallon
SO ne,



Kawai sai ta jefe sa da wata irin haramta, a lokacin da yake satar kallon,



Take yaslir yaji hantar cikin sa ta kaɗa, kuma kunya ta kama sa ya sunkuyar da kansa ƙasa aka
cigaba da tafiya,har aka isa gidan sarauta ɗayan su bai ce uffan ba,

Har zuwa masauki lasmirat da yaslir suka raka jaruma Sunaila,



Sannan kowa ya tafi izuwa bangaren sa,



Lokacin da yaslir ya kwanta a bisa kan gadon sa domin ya huce gajiyar dake tattare dashi, sai
barci ya gagare sa,



Duk sa,adda ya runtse idanun sa sai ya yaga fuskar jaruma Sunaila rufe da rawani,



Tana yi masa murmushi, nan take yaji tsananin SO da begen Sunaila ya mamaye zuciyarsa,



Wani abu da ya faɗo masa arai shi ne shin hararar da lasmirat ke yi masa a ɗazu mene ne
ma'anar sa shin tana tsananin kishi ne da kallon Sunaila da yayi,



Shin ke nan hakan na nufin ita sarauniya lasmirat ta kamu da matukar kaunar sa kenan?.



Amma yanayin tsayuwa da tafiyar da Sunaila tayi a ɗazu a filin yaƙi iri ɗaya ne sak da na
masoyiyar sa gimbiya salimat,



Shin jaruma Sunaila ita ce masoyiyar salimat?



Sa'adda yaslir yazo nan a tunanin sa sai ya shiga cikin tsananin damuwa,

Kuma yaji gaba ɗaya

3 / 9