TAKOBIN DAUKAKA BOOK COMPELET BY MANSUR USMAN SUFI.pdf

Author :  Mansur Usman Sufi Category :  Arewa Pen

Chapter   4 / 9

9K to 12K   out of 24.6K words

duniyar tayi masa ƙunci, nan take ya ƙudiri aniyar cewa sai yaga fuskar
Sunaila kafin tabar wannan birni.



***























3

Kamar yadda ya wakana ga saurayi yaslir haka al'amarin yakasance ga sarauniya lasmirat,



A inda ita ma barci ya gagare ta,

Abu na farko da ya faɗo mata arai shi ne, shin Mene ne yasanya yaslir zai kamu da soyayyar
Sunaila, Alhalin ta nuna alamun so,

Sannan taya zai kamu da son wacce koda fuskar ta bai gani ba,

Sa'adda sarauniya lasmirat ta zo nan a tunanin ta sai taji zuciyar ta tayi ƙunci, kuma tasha
alwashin cewa sai ta bayyana soyayyar ta ga yaslir a lokacin da suka gudanar da tafiya ɗauko
TAKOBIN ƊAUKAKA,

Da ɗebo ruwan ƙoramar boka Daryalu.

Tun da tana so ne tafiyar ta kasance har da jaruma Sunaila za a yi ta,

Daga wannan shawara ne sai ta ɗauko madubin tsafin ta domin gudanar da bincike don irin
wainar da ake toyawa a duniya,



***

Acan inda aka fafata yaƙi kuwa dakaru sun shiga aikin su na kwashe gawarwakin jama'a da
waɗanda suka samu raunuka aka shiga duba lafiyar su,

Kasancewar a wannan lokaci duhun dare ya fara Kawo kai sai aka kunna fitar ice aka cigaba da
aiki

Inda ace mutum zai ga yadda ake kwashe gawarwakin jama'a jini na kwaranya sai ya rantse
yace a mahauta yake,

Waɗanda suka rasa iyayen su, ya'ya da yan uwa gami da gidaje sai suka shiga rusa kukan
baƙin ciki

Domin a iya tsawon wanzuwar birnin Misra ba'a taɓa ganin tashin hankali irin na yau ba,

Kashe gari tunda duku dukun safiya sarauniya lasmirat ta umarci kuyangi suka shirya nau'ikan
kayan abinci da abin shaye shaye da tanɗe tanɗe a bisa wani dogon teburin azurfa, a cikin wata
ƙasaitacciyar turaka ta musamman,

Kuyangi na cikin kammala aikace aikace a cikin turakar sai ga sarauniya lasmirat ta shigo,

Cikin ƙayatattun tufafi irin na manyan sarakai,

Koda shigowar ta sai gaba ɗaya kuyangin suka zube ƙasa suka kwashi gaisuwa

Lasmirat ta amshi gaisuwar sannan ta umarci wata kuyanga ta tafi zuwa masaukin su yaslir ta yi
musu iso, kuma ta ce tana gayyatar su walima,

Jim kadan da ficewar kuyangar sai ga yaslir ya shigo

Turakar,yana sanye cikin shiga riga da wando na alhariri masu taushi da ƙyalli,

Yana shigowa ya risina ga sarauniya lasmirat sannan yaje ya zauna abisa wata kujera dake
fuskantar ta,

Ana cikin wannan hali ne Sunaila ta shigo, ta shigo turakar duk da cewar ta canza tufafin dake
jikin ta amma har a wannan lokaci fuskar ta rufe da rawani idanun ta kaɗai ake gani,

Bayan ta miƙa gaisuwa ga lasmirat sai ta zauna a kujerar dake fuskantar lasmirat da yaslir,

Lasmirat ta dubi yaslir da Sunaila tace" yaku waɗannan baki masu daraja a gare ni, kuyi sani
cewa na kiraku nan ne domin shirya muku walima bisa taimakon da ku kayi mini,

Wanda bani da abin da zan saka muku dashi

Koda gama faɗin hakan sai sarauniyar lasmirat ta tsiyaya ruwan inibi a cikin yan kananan
kofunan zinare guda uku ta miƙawa yaslir da Sunaila kofuna biyu suka karɓa,

Sannan ta ɗauki na uku a hannun ta, kamar hadin baki a lokaci guda suka kai kofunan bakunan
su suka shanye ruwan inibi,

Sannan aka shiga hidimar ciye-ciye da tanɗe-tande ana fira cikin nishaɗi,

A cikin firar ne lasmirat ta dubi yaslir tace"In tambaye ka mana ɗazu da ka shigo naga fuskar ka
akwai alamun damuwa shin ko me ya kawo hakan,

Yaslir ya shafi sajen sa da gemun sa yace" na ɗan makara ne shi ne ya sanya Ni cikin
damuwar,

Koda jin amsar wannan tambaya sai lasmirat tayi murmushi ga yaslir mai ɗauke da alamar
tuhuma,

Sannan ta gyaɗa kai cikin gamsuwa,

Al'amarin da sanya yaslir yaji hantar cikin sa ta kaɗa,

Amma sai ya banzatar da abin aka cigaba da ciye-ciye da tanɗe tanɗe kamar babu wani abu.

Bayan kowa ya kimtsa cikin sa an samu nutsuwa kuma shiru ya wanzu,

Sai lasmirat ta dubi yaslir da Sunaila tace"yaku ababan soyuwa a rai na, kuyi sani cewa babbar
muhimmiyar maganar da nake so mu tattaunawa Ita ce, ina so ku taimake ni muyi wata
gagarumar tafiya tare daku,

Nan take lasmirat ta kashe labarin abinda ya wakana tsakanin ta da boka Dayyubul-Barmas
akan batun ɗauko TAKOBIN ƊAUKAKA ta zayyanewa su yaslir da ga farko har karshe,



Sannan ta ɗora dacewa yaku waɗannan baki masu daraja a gare ni kuyi sani cewa idan har
kuka taimake ni wajen cika burina



Ina mai tabbatar muku dacewa zan raba kasa uku,dukiya, da komai nawa kowannen ku ya
ɗauki ɗaya



Sa'adda sarauniya lasmirat ta zo nan azancen ta sai yaslir da Sunaila suka cika da matukar
mamaki, kuma suka zurfafa izuwa kogin tunani,



Sannan daga bisani yaslir da Sunaila suka dubi lasmirat Cikin haɗin baki suka ce mun amince
da wannan bukata taki ya mai karamci,



Koda jin wannan batu sai sarauniya lasmirat ta cika da matukar farin ciki mara musaltuwa,



Kuma ta labarta musu ranar da zasu gudanar da tafiyarsu,



Ranar da tafiya dajin Husumul-kadar tazo, sarauniya lasmirat, yaslir da Sunaila suka yi
gagarumin shiri,



Suka hau bisa dawakai suka nufi hanyar da zata sadasu da gidan boka Dayyubul-Barmas,



Bayan lasmirat ta bayar da rikon sarautar ta a hannun waziri ukashat,

Kuma waziri ukashat ɗin da sauran al'ummar gari sun yi musu rakiya har zuwa kofar gari,



Lokacin da sarauniya lasmirat suka iso gidan boka Dayyubul-Barmas sai suka ja linzamin
dawakan su suka yi turjiya,



Su kayi cirko- cirko suna masu ƙarewa gidan kallo, shi dai gidan boka Dayyubul-Barmas
yakasance ɗan madaidaici da aka ginasa da zallar duwatsun wuta masu ƙyalli, yana da kofa
guda ɗaya da akayi ta da zallar karfen jauhari,



Bakomai yasanaya su sarauniya lasmirat suka yi wannan cirko-cirko ba sai bisa ganin Kofar
gidan a garƙame, kuma ya na lulluɓe da wata yanar gizo gizo



Ana cikin wannan hali ne kwatsam sai akaga boka Dayyubul-Barmas ya bayyana tsulum! a
gaban su fuskar sa cike da annuri,



Yana sanye cikin kyawawan tufafi na alfarma,sun yi matukar yi masa kyawu, a hannun sa yana
rike da wata isgar tsafi,wacce take canza launi Lokaci zuwa lokaci, wani lokacin ta koma
baƙa,shuɗiya ko Koriya,



Lasmirat ta yi murmushi ga boka Dayyubul-Barmas daya ƙarawa fuskar ta annuri tace"ya abin
dogaro na shin ina dalilin rashin bayyanar ka akan lokaci domin gudanar da wannan tafiya
tamu?



Dayyubul-Barmas yayi murmushi yace" ya sarauniyar kiyi sani cewa bakomai bane ya sanya
ban bayyana akan lokaci ba sai domin na kara gudanar da bincike ne game da tafiyar tamu,

Koda jin wannan batu sai lasmirat tace " ka gafarceni ya uban bokaye,



Dayyubul-Barmas ya tari numfashin ta yace "ba sai kin wahalar da kanki wajen sanar da ni
sunayen a bokan tafiyar ki ba,



Yaslir da Sunaila, dukkan su ilimin tsafi ya bayyana mini abin da ya gudana tsakaninsu da su,



Tabbas kin yi tunani mai kyau, domin Sunaila da yaslir zasu yi matukar taimaka wajen wannan
tafiya tamu,



Yanzu ina ganin abinda ya kamata mu fara yi shine tafiya domin ɗebo ruwan koramar boka
Daryalu, domin hakan shi ne zai bamu damar fuskantar dajin Husumul-kadar,



Koda gama faɗin hakan sai boka Dayyubul-Barmas ya kwallawa aljanin sa kira sau uku,



Aljanin ya bayyana gaban sa ya kwashi gaisuwa, duk da kasancewar su lasmirat suna da
dakakkiyar zuciya sai da suka razana da ganin aljanin,



Aljanin yakasance garjejen kato karfaffan gaske,yana da rafkeken kai tamkar dutse,mai ɗauke
da waɗansu manyan idanu jajaye,tamakar kwallon goriba,yana da katon hanci da rafkeken baki,
sannan ya da manyan fuka-fukai guda shuda,



Boka Dayyubul-Barmas ya dubi aljanin cikin nutsuwa yace"yakai Huzmal ibn kuddar kayi sani
cewa ban kirawo ka nan ba sai domin ina so ka ɗauke mu izuwa Husumul-kadar domin ɗauko
zobunan sihiri a cikin kogon fatalwa,

Daga nan kuma mu huce izuwa inda ma'ul-diya'u yake mu ɗauko kubar miftahul-daryal,



Yakai Huzmal ibn kuddar kayi sani cewa wannan shine aikin ka na ƙarshe da zaka samu ya ci



Yayin da aljani Huzmal yaji wannan batu sai ya risina ya ce" An gama ya shugabana



Yana gama faɗin hakan sai ya shimfiɗe gadon bayan sa boka Dayyubul-Barmas, lasmirat, yaslir
da Sunaila suka hau suka zauna



Sannan ya yunkura ya ya tashi sama ya na mai buɗe fuka-fukan sa yana mai keta gajimare,
cikin sa wani irin azababban gudu na keta sa'a



Tun da aka fara wannan tafiya babu wanda yace kala har yazamana an shafe tsawon sa,a uku



Ana cikin wannan hali gyangyaɗi ya fara ɗaukar boka Dayyubul-Barmas koda ganin hakan sai
dariya ta suɓucewa sarauniya lasmirat wanda ta sanya Dayyubul-Barmas dawo cikin hayyacin
lasmirat ta dube sa tace" Haba dodon bokaye ai bai kamata ace irin ku suna suna barci ba,



Koda jin wannan batu sai dariya ta suɓucewa boka Dayyubul-Barmas ya dubi lasmirat yace"Taɓ
ɗi jan wannan fa shi ake cewa wai ana wata ga wata Dara ta ci gida ke yanzu wannan
gyangyaɗi da nayi shi ne ya baki mamaki, tabbas da ace kin taɓa jin labarin boka shu'umanu da
baki yi mini wannan dariya ba,


Wane ne kuma boka shu'umanu?



Lasmirat ta tambaya a ƙagauce,

Dayyubul-Barmas ya ce" boka shu'umanu wani hatsabibin matsafi ne da ya shiga alwar tsafi ta
tsawon shekaru uku domin ya karance wani muhimmin littafi da ake yiwa laƙabi da KUNDIN
JARUMTA,



Babu wani mahaluki walau mutum ko aljan da zai mallaki kundin ya karantasa baki ɗaya face ya
mulki duniya,



A daren ranar da boka shu'umanu zai kammala wannan karatun littafi ne wani irin barci mai
nauyi ya ɗauke sa



Sa'adda boka Dayyubul-Barmas ya zo nan azancen sa sai mamaki ya kama lasmirat, yaslir da
Sunaila,



Lasmirat ta ce" shi kuwa Boka shu'umanu da ya farka daga barcin me ya faru dashi,



Koda jin wannan tambaya sai Dayyubul-Barmas ya ce"Ai wannan tambaya taki labari ne mai
tsawo sai dai ki nemi littafi KUNDIN JARUMTA ki karanta,



Lasmirat ta gyaɗa kai aka cigaba da tafiya,







Kwanaki nabin kwanaki,mako nabin mako sai gashi su sarauniya lasmirat sun shafe kwanaki
ashirin da uku suna tafiya,

A iya tsawon wannan kawanki babu abinda ke sanyawa a tsayar da tafiya face idan wani daga
cikin su zai yi bawali ko kuma lokacin barci yayi,



Ana cikin tafiyar ne saurayi yaslir ya dubi Sunaila yace da ita" ya JARUMAR JARUMAI,



shin mene ne dalilin daya sanya kika ƙi bayyana fuskar ki a garemu?



Koda jin wannan tambaya sai sunailata sunkuyar da kanta ƙasa kamar mai tunanin wani abu,



Daga can sai ta ɗago da kanta ta dubi yaslir tace"Ai wannan rufe fuska tawa yana da matukar
muhimmanci agareni anan gaba zaka tabbatar da abinda na faɗa



Idan kuwa har ka na so ne kaga fuskar ta wa to yazama wajibi ka amince da sharudda guda
uku

Da farko zaka yanko mini kan riƙeƙƙen zaki da ya shekara arba'in,

Na biyu kuma zaka ceto rayuwar abokan tafiyar mu har sau uku

Abu na karshe shi ne zaka farauto mini damisa guda biyu ka kawosu gare ni,

Sa'adda saurayi yaslir yaji waɗannan sharuddan daga bakin Sunaila sai sai ya shiga nazari.

Abu na farko da ya faɗo masa arai shi ne menene fa'idar waɗannan sharuɗɗa da Sunaila ta
gindaya masa,

To amma tun da a halin yanzu bashi da burin da ya huce yaga fuskar Sunaila dola ne ya amince
da wannan sharuɗɗa,

Kawai sai yayi gyaran murya ya dubi Sunaila yace" Na amince da wannan sharuɗɗa naki ya
JARUMAR JARUMAI

Duk wannan tattaunawa da ake tsakanin yaslir da Sunaila sarauniya lasmirat ta na sauraron su

Koda taji yaslir ya amince da sharuɗɗan jaruma Sunaila domin ya yi arba da fuskar ta kawai

Sai zuciyar ta takama tafarfasa tamkar zata kone kuma tsananin kishi ya turnuƙe ta,

Lallai lokaci yayi da zaki bayyana soyayyar ki ga yaslir domin matsawar yayi arba da fuskar
Sunaila

Abin da kike gudu zai fara

Koda jin wannan shawara daga zuriyar ta sai lasmirat sai ta bar abin a ranta

Amma sai wani tunanin ya faɗo mata,shin wai ma me yasa zaki kamu da soyayyar wanda bazai
ji kiranki ba,kuma Bayan cewa bashi ne namijin da zaki aura ki samu Haihuwa ba,

Sa'adda tazo nana atunanin ta sai taji zuciyar ta tayi mata ƙunci,

Har lasmirat ta buɗi baki zata ce wani abu sai boka Dayyubul-Barmas ya dubi aljani Huzmal
yace dashi"

Yakai Huzmal ai sai ka sauka a turba domin mun iso dajin Husumul-kadar

Koda jin wannan umarni dai Huzmal ya saki fuka fukan sa ya sauka a turba,

Boka Dayyubul-Barmas ne yafara saukowa sannan lasmirat, yaslir, Sunaila ce a ƙarshe,

Nan fa aka yi arba da dajin Husumul-kadar yakasance mai ɗauke da manyan bishiyoyi masu
tsawo tsiya babu duwatsu ko ɗaya a cikin sa face waɗansu manyan koguna guda uku masu
ban tsoro,

Wani irin farin hayaƙi ya mamaye dajin baki ɗaya babu alamar haske rana a cikin sa,

Tabbas wannan daji yakasance mai ban tsoro,

Tsawon daƙika arba'in su lasmirat na karewa dajin kallo sai daga bisani boka Dayyubul-Barmas
ya dube su yace" yaku abokan tafiya kuyi sani cewa a cikin wannan daji ne zamu ɗauko
zobunan sihiri,

Sai dai ina so kuyi sani cewa wannan daji ne na ɗauke da musibu da bala'o'i da sai mun yi da
gaske zamu tsira da rayukan mu,da wannan nake yi mana fatan samun nasara,

Koda gama faɗin hakan sai boka Dayyubul-Barmas ya shafi sandar tsafin sa take ta rikiɗa
izuwa wani ƙaton sungumi

Sai kawai ya kunna kai izuwa cikin dajin yana mai cewa aljani Huzmal sai ka jira mu anan

Lasmirat, yaslir da Sunaila suka mara masa baya,

Tun da aka shiga dajin Husumul-kadar sai da aka shafe tsawon dakika ɗari biyu koda motsin
tsuntsaye ba,a ji ba,

Al'amarin da ya ƙara jefa tsoro a zukatan su sarauniya lasmirat kenan.

Lokacin da aka iso inda wannan koguna suke sai aka shiga nazari

Boka Dayyubul-Barmas ya dube su yace" A cikin waɗannan kogunan dutse uku ne zamu ɗauko
zobunan sihiri sai dai ba za mu iya gane wanne ne wanda zobunan ke ciki ba,

Karfin shirin tsafi bazai taba tasiri a cikin su face dole mu shiga izuwa kogo na farko ko zamu
dace ,

Lasmirat ta dubi Dayyubul-Barmas cikin damuwa tace to mai hana bazamu koma baya ba
domin mu gudanar da bincike mu gano kogon da zobunan sihirin ke ajiye a cikin sa,

Dayyubul-Barmas ya ce "Ai bisa sharaɗin wannan daji idan mutum ya shigo baya fita kodai ya
samu nasarar ɗauko zobunan sihiri ko kuwa ajali Ya riske shi a ciki,

Koda gama faɗin hakan sai boka Dayyubul-Barmas ya matsa kusa da kofar kogo na farko ya
ɗaga kansa sama ya karanta waɗansu haruffa da aka rubuta da tawadar za'afaran jikin wani
allon karfe a saman kogon,

Yana kammala karantawa sai kofar kogon ta buɗe wani irin tiririn bakin hayaƙi ya surnano daga
cikin sa,

Boka Dayyubul-Barmas ya tusa kai izuwa ciki, lasmirat, yaslir da Sunaila suka yi koyi dashi,
lokacin da Sunaila wacce ita ce ta karshe ta sanya kafarta ta biyu sai kofar kogon ta mayar da
kanta ta rufe ruf

Tamkar bata taɓa budewa ba,

Lokacin da su sarauniya lasmirat suka shiga izuwa cikin wannan kogon dutse na farko a cikin
dajin Husumul-kadar,

Sai suka ci-gaba da tafiya a cikin sa suna ganin abubuwan abubuwan al'ajabi kala daban
daban,

A wasu lokutan sai suji alamun takun sawaye a bayan su amma dazarar sun waiga sai su ga
basu ga komai ba,

Haka dai suka ci-gaba da tafiyar babu sassauci, har yazamana sun shafe tsawon dakika ɗari
huɗu batare da an haɗu da wani abu mai cutar wa ba,

Yana cikin wannan tafiya ne kwatsam bazato babu tsammani sai su lasmirat su kaji wani
mahaukacin gurnani ya mamaye kogon dutsen gaba ɗaya ya kama girgiza tamakar zai
rugurguje, sannu a hankali wani takun sawaye yafara bayyana,

Kwatsam sai wani mutum ya bayyana tsulum Tamkar an jefoshi daga sama,

Mutumin yakasance narkekeken kato, rabin jikin sa na gwaggwan biri ne, rabin kuma na
bil,adama ne,

Yana matukar tsawo tamakar tsauni, yana da tarin kwanji tamkar jikin sa yakasance na
dutse,fuskar sa mummuna ce mai matukar kwarjini daban tsoro, mau ɗauke da gashin gemu da
ƙasumba buzu buzu babu kyan gani, wani irin tiririn bakin hayaƙi na fita daga hancinsa duk
sa'adda ya busar da numfashi,
Tabbas wannan mutum ya kasance abin tsoro domin babu wani jarumi da zai yi arba dashi face
ya ɗimauce,

Sa'adda su sarauniya lasmirat suka yi arba da mutumin sai suka firgita ainun

Lasmiratda yaslir jikin su yakama kyarma

4 / 9