TAKOBIN DAUKAKA BOOK COMPELET BY MANSUR USMAN SUFI.pdf

Author :  Mansur Usman Sufi Category :  Arewa Pen

Chapter   5 / 9

12K to 15K   out of 24.6K words

yana tsuma tamkar nazari

Dayyubul-Barmas da Sunaila ne kaɗai basu yi ba amma su ma a matukar razane suke,kawai
dai karfin hali ne irin na GWARAZAN MAYAKA

Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin su lasmirat da



Sai da aka ɗauki wani lokaci ana wannan kallon kallo,



Sai daga bisani ne mutumin ya takarkare ya bushe da dariyar mugunta wanda ta haddasa
girgizar kogon kuma wani ƙara mai kama da aradu ya bayyana,

Bashiri su lasmirat suka sanya hannayen su biyu suka toshe kunnuwan su domin ji sukayi
kamar zasu kurman ce,



Sai da narkekeken kato ya tsuke bakin sa sannan komai ya samu dai dai tuwa, kogon ya dai na
raurawa,kuma su lasmirat suka dawo hayyacin su kuma har ma suka lura cewa ashe mutumin
yana ɗauke da wata gabgegiyar jela wadda akalla tsawon ta yakai kamu arba'in,



Narkekeken katon ya dakama musu tsawa data sanya hantar cikin su ta kaɗa ya dube su cikin
wata irin kakkausar murya mai kama da kukan jaki yace



"Yaku waɗannan bil'adama ma'abota GAJERAN KWANA shin wane rashin hankali ne ya shigo
da ku wannan kogo bayan cewa fiye da shekaru dubu uku babu wata halitta walau mutum ko
aljan da taɓa yin wannan ganganci



Sai dai nasan cewa bawai rashin sani ya kawo ku nan ba sai domin kwaɗayin daukar zobunan
sihiri



Dake ajiye a ɗaya daga cikin waɗannan kogunan dutse biyar na cikin dajin Husumul-kadar,



Ina mai tabbatar muku dacewa kun tafka babban kuskure da zuciyar ku ta bayyana muku
dacewa zaku fita daga wannan daji a raye ɗauke da zobunan sihiri

Kafin mutumin mai siffa biyu yagama rufe bakin sa boka Dayyubul-Barmas ya tari numfashin sa
Yana mai dakamasa tsawa yace

"Yakai wannan mummunan halitta kayi sani cewa kwarjini da girman ka bazai bamu tsoro ba

Shin ko ka manta ne cewa karfi a zuciya yake bawai a jiki ba,

uma idan akwai rai to da rabo, kaga kenan akwai yiwuwar samun nasara akan ka kuma har mu
ɗauke zobunan sihiri,

Caraf mutumin ya tari numfashin boka Dayyubul-Barmas ya dube sa yana mai bushewa da
dariyar mugunta a karo na biyu, sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da
saƙon mutuwa,

"Tabbas gaskiya ne maganar ka amma fa kar ka manta cewa masu iya magana na cewa"
Alamar karfi tana ga mai ƙiba,

Wani abu ma da baku sani ba shi ne shi kansa matsafi zarratu ibn lauhat da ya sana'anta
zubonan sihirin a halin yanzu ba shi da iko dasu ballantana wani bil'adama karan kaɗa miya,

Sannan ma yanzu idan kun samu nasarar hallaka ni taya ya kuke tsammanin zaku tsira daga
sauran musibun dake cikin wannan daji,

Bayan cewa ma kuma a cikin ku babu wanda yasan inda zobunan sihiri suke a cikin koguna
biyar ɗin,

Koda gama faɗin hakan sai narkekeken katon ya zira hannun sa a cikin wata akwatu ta baƙin
ƙarfe da ke kusa dashi a ɗauko wani zabgegen gatari na zallar mulmulallan farin karfe yana
sheƙi,walwali da ɗaukar idanu ya yunƙura izuwa inda su sarauniya lasmirat suke tsaye,

Koda ganin hakan sai boka Dayyubul-Barmas ya ɗaga sungumin sa sama yana mai kurma
wawan ihu ya ruga izuwa kan halittar,

Yaslir ne ya mara masa baya hannun sa rike da takobi tsirara,

Sunaila da sarauniya lasmirat ta suka ru fa masa baya,



Mu haɗu a littafi na biyu domin jin cigaban wannan ƙayataccen labari.



Mansur Usman Sufi

Littafanyaki.com.ng


Takobin Daukaka

Book 2 compelet

Littafin Yaki

Mansur Usman Sufi



Ana haɗuwa aka kacame da azababban yaƙi mai matukar muni daban tsoro,

Ana fara wannan gumurzu ne su sarauniya lasmirat suka fara gane kuren su,

Domin ƙarfin saran su su duka hudun bai kai ɗaya na mutumin mai siffa biyu ba,

Domin duk sa'adda daya kaiwa ɗaya daga cikin su sara idan ya zillewa harin duk sa'adda
gatarin ya sauka a ƙasa sai kaga ya haddasa rami mai tsawon kamu ashirin, idan kuwa akan
dutse gatarin ya sauka sai kaga yayi bindiga ya tarwatse

Sai da aka shafe tsawon sa,a ɗaya ana wannan baƙin artabu babu sassauci,

Ana cikin wannan hali ne wani tunani ya faɗowa mutumin mai siffa biyu,

Abin da ya faɗo masa kuwa shine shin mene ne dalilin da daya sanya ya kasa samun nasara
akan waɗannan bil'adama alhalin baya ta ɓa fafata yaƙi da wata halitta a cikin abinda bai gaza
dakika goma ba face ya zare mata ruhin ta daga gangar jiki,

Tabbas akwai wani abu Ruwa baya tsami banza

Koda narkekeken katon ya zo nan a tunanin sa sai ya fusata ainun zuciyar ta kama tafarfasa
tamkar zata fasa kirjin sa ta fito waje,

Kawai sai ya canza salon faɗan sa yazamana cewa ya sake zage damtse wajen kai wa su boka
Dayyubul-Barmas miyagun hare haren fiye da ɗazu

Gami da haɗawa da kai mu su naushi da bugu hannu da ƙafa,

Kaico gaskiyar masu iya magana da suka ce idan kiɗa ya canza dole ne rawa ma ta canza

Faruwar canza salon faɗan keda wuya sai mutumin yafara samun nasarar naushin su boka
Dayyubul-Barmas,

Yazamana cewa idan ya naushe sun sai kaga sunyi sama tamakar an janye su da ƙugiya
sannan daga bisani su faɗo ƙasa tim

Idan fuska ya nausa sai kaga hanci da baki na yoyon jini, idan kuma ajiki yayi naushin sai wajen
yayi tsami, jini ya tari,

Amma saboda JURIYA DA BAJINTA irin ta JARUMAN DUNIYA sai kaga sun mike tsaye zumbur
an cigaba da artabu

Inda ace mutum yana tsaye a wannan waje a lokacin da ake wannan artabu yaga yadda su
boka Dayyubul-Barmas ke yakin cikin juriya da nacin tsiya

Dola ne ya jinjina musu ya tabbatar dacewa sun cika GWARAZAN MAYAKA masu dakakkiyar
zuciya,

Ana cikin wannan ɗauki ba daɗi ne Sunaila ta kaiwa narkekeken katon hari da takobin ta a
hannun sa a lokacin da yake ƙoƙarin tarwatsa mata kai

Bisa sa'a sai gashi takobin ta tayi tasiri a jikin ɗan yatsan sa har jini yayi tsartuwa.

A dai dai lokacin ne sarauniya lasmirat ta samu nasarar laftawa narkekeken katon sara a kafar
sa take inda ta sara ɗin ya haddasa wani katon rauni jini yayi tsartuwa gami feshi,

Al'amarin da yayi Matukar bawa sarauniya lasmirat da Sunaila mamaki kenan domin tunda aka
fara wannan yaƙi hakan bai faru ba, domin idan takubban su suka sari mutumin sai dai suji
tamkar dutse suka sara tartsatsin wuta ne kawai yake tashi gami da kara marar daɗin sauraro,

Sa,adda mutumin mai siffa biyu naga raunuka biyu a jikin sa kuma dukkanninsu suna zubar da
jini sai kawai yayi wurgi da gatarin sa gefe guda ya takarkare ya kwarara wawan ihu wanda ya
mamaye kogon dutsen kuma ya haddasa wata yar ƙaramar girgizar ƙasa,

Kafin ɗaya daga cikin su yayi wani yunkuri mutumin mai siffa biyu ya shammace su ya gabza
musu wawan naushi a fuska cikin zafin nama a lokaci guda su duka huɗun suka zube kasa
magashiyan numfashin su na fita sama

Kawai sai ya wurgila jelar sa izuwa inda suke kwance,take ya samu nasarar kanannaɗo boka
Dayyubul-Barmas, Sunaila da lasmirat da jelar sa,

Nan take suka fara gani dishi- dishi sakamakon naushin da mutum yayi musu kuma suka ji
tamkar ƙasusuwan jikin su zasu karye, saboda yadda jelar tayi kanannade su tayi musu ɗaurin
Hunhun goro,

Sa,adda Sunaila ta duba taga babu yaslir sai tace a ranta shin ina yaslir ya shiga ko kuwa ya
rasa rayuwar sa ne?

Amma idan har yana raye wannan itace damar sa ta farko dazai ceci rayuwar mu ɗaya daga
cikin sharuddan da zai bi har ya samu nasarar ganin fuskata,

Abin da Sunaila bata sani ba shi ne lokacin da mutumin ya kanannaɗo su da jelar sa yaslir ya
gangara izuwa wani rani dake tsakiyar kogon dutsen,

Lokacin da boka Dayyubul-Barmas ya ga irin mummunan halin da suke ciki sai ya shiga ƙoƙarin
ceto rayuwar ta karfin sihiri,amma shiru kakeji malam ya ci shirwa,

Koda mutumin mai siffa biyu yaga cewa Boka Dayyubul-Barmas na ƙoƙarin cewa rayuwar
abokan tafiyar ta karfin sihiri sai ya sake bushewa da dariyar mugunta har da kyakyatawa,

Ya shiga koɗa kansa yana yiwa kansa kirari yana mai cewa

"" Nine gagarau uban gagararru

Guguwa nake maganin karmami

Wutar bala'i mai tada hankalin duniya,

Mutum dubu kalacen dafe,aljanu dubu goma kalacen yamma""



Kammala yiwa kansa kirarin keda wuya sai kawai ya yi nuni da ɗanyatsan sa na hagu izuwa ga
wannan akwatin bakin karfe daya ɗauko gatarin sa a ciki,

Take wata irin gagarumar wuta ta bayyana a cikin akwatin tamkar dama can akwai ta,

Kawai sai ya juyar da jelar sa izuwa inda akwatin take, nan take tiririn zafin ya sumar da su
boka Dayyubul-Barmas.









Mutumin mai siffa biyu ya bushe da dariyar mugunta bisa ganin wannan gagarumar nasara da
ya samu akan su boka Dayyubul-Barmas,

Dariyar tasa ta haddasa girgizawar kogon, a lokaci guda kuma ya tsuke bakin sa tamkar an aiko
masa da SAƘON MUTUWA kawai sai ya nufi wata kofa a cikin kogon dutsen,

Kwatsam bazato babu tsammani sai mutumin yaji an dankara masa wawan sara a gadon bayan
sa,

Saboda karfin saran sai da sai da takobin ta nutse a gadon bayan sa,

Kawai sai ya kwarara ihu tare da waigawa bayan sa domin ya ga wanda ya sareshin.

Ai kuwa yana waigwa sai yayi arba da jarumi yaslir hannun sa riƙe da zaratan takubba masu
kaifi da tsinin tsiya,

A dai dai lokacin ne jini yafara kwaranyo wa daga inda yaslir ya sare shi ,

Mutumin ya dakawa yaslir tsawa wanda ta sanya kogon ya amsa da karfi,

Bisa mamaki sai mutumin yaga ko gezau yaslir bai yi ba, al'amarin da yayi matukar bashi
mamaki kenan,

Domin bai taba dakawa wata halitta tsawa ba face ta ɗimauce,ko ma ta rasa rayuwar ta,

Wani tunani da ya faɗo masa shi ne, taya ya wani makami yayi tasiri akan sa Bayan cewa
hakan bai taɓa faruwa ba,

Lallai bakaramin kuskure kayi ba da ka manta da wannan bil,adama,

Sa'adda halittar yazo nan a tunanin sa sai zuciyar sa ta kama tafarfasa tamkar zata kone jikin
sa yakama kyarma yana tsuma tamkar mazari,

Kawai sai ya miƙa hannun sa ya ɗauko wannan Gatari nasa Sannan ya kwarara wawan ihu ya
ruga izuwa kan yaslir yana mai ɗauke da su boka Dayyubul-Barmas a ɗaure a jelar sa,

Sa,adda yaslir yaga halittar ya rugo izuwa gare sa cikin mugun tanadi,

Sai kawai ya gyara tsayuwar sa, lokacin da ya rage sauran taku

Sai yaslir ya dako wawan tsalle tamkar an harbo sa daga cikin baka yana saman ya kaiwa
halittar sara da takubban sa biyu a kafaɗa,

Bisa sa,a sai gashi ya same Shi har jini na zuba a kafadar tasa

Cikin gwanin ta yaslir ya yi katantanwa a sama sau uku ya dira ƙasa a bisa duga-dugan sa cikin
gwanintar yaki,

Sannan suka kacame da azababban artabu mai matukar muni,ban tsoro daban al'ajabi,

Sai da aka shafe tsawon sa,a biyu ana wannan gumurzu babu sassauci,

Tsawon wannan lokaci babu wanda ya samu nasarar lakutar jikin abokin gwamin sa,

Duk sa'adda mutumin mai siffa biyu yakaiwa yaslir sara inda ya goce duk abinda gatarin ta
sauka a kansa sai kaga wajen yayi rami mai zurfi,

Idan akan Dutse ne sai Dutsen yayi bindiga ya tarwatse,

Kafin cikar dakin talatin yaslir yafara galabaita saboda yadda yake zillewa harin mutumin,

A dai dai lokacin ne kafafatun yaslir suka faɗa cikin wani rami a kogon kuma wani dutse ya
danne sa,

Wohoho! Wuya mai sa dole, shi kuwa tsoro na iya sawa mutum ya aikata abin da ko a mafarki
bai taba tunanin zai iya ba idan yaga bala'o'i,

Koda yaslir yaga halin da yake ciki kuma ya tabbatar da cewa idan har bai yi wani abu ba zai
iya rasa rayuwar sa

Sai kwai akaga yaslir ya sanya hannayen sa biyu ya ture Dutsen daya danne sa ta ƙarfin
tsiya,kuma ya naushe sa da hannayen sa biyun cikin baƙin zafin nama take dutsen yayi sama
tamkar an janye da ƙungiya ya daki fuskar mutumin mai siffa biyu,

Take halittar ya ɗimauce ya gigice yayi jifa da gatarin sa ya sanya hannayen sa biyu akan fuskar
sa yana rusa ihu,

Koda yaslir ya duba hannun daya naushi dutsen sai yaga ko ɗan yatsan sa bai karye ba
ballantana hannun yayi ciwo,

Sai ya cika da matukar mamaki, kawai ya kama gefen ramin da ya faɗa ya fito waje,

Yana fitowa sai ya zare wata takobin daban a jikin sa ya falfala da azababban gudu zuwa kan
halittar ya daka tsalle sama ya soka masa takobin a ƙahon zuciyar sa,

Nan take mutumin ya kurma wawan ihu sannan ya fadi kasa,yana shure-shuren mutuwa jini ya
dunga kwarara da tsartuwa daga kirjin sa.

Kafin wani lokaci komai na jikin sa ya daina motsi alamar rai yayi halin sa,

Take wannan wuta dake ci a cikin wannan akwatu na mutu murus kuma jelar halittar dake daure
da su lasmirat ta sake su,

Sakamakon jinin dake zuba daga jikin halittar shi ne yayi sanadiyar farfaɗowar su boka
Dayyubul-Barmas,

Sunaila ce ta fara farfaɗowa koda ta buɗe idanuwan ta dake rufe cikin baƙin yanki koda tayi
arba da yaslir a tsaye rike da takobi tsirara jikin sa duk ta ɓaci da jinin mutumin mai siffa biyu
daya hallaka, sai ta cika da matukar mamaki,

Sannan baka Dayyubul-Barmas, lasmirat suka cika da Mamaki bisa ganin bajintar yaslir.

Bayan kowa ya samu nutsuwa kuma ya sanya wa kansa magani a raunin dake jikin sa,

Sai aka sake ɗungumawa aka fice daga cikin kogon dutsen

Lokacin da Sunaila wacce Ita ce a ƙarshe ta fita sai ƙofar kogon ta mayar da kanta ta rufe
tamkar bata taɓa budewa ba,

Haka dai su boka Dayyubul-Barmas suka dunga shiga kogunan dutsen yazamana cewa sun
sha ɓakar wahala wajen yaƙar halittun dake ciki

Sai a kogo na biyar ne bayan sun samu nasarar fafata yaƙi da wata SIHIRTACCIYAR mucijiya
suka samu nasarar ɗauko zobunan sihiri,

Amma kowannen su ya samu raunuka a jikin sa masu yawan gaske,

Domin sai da su kayi kwana shida suna jinyar jikin su sannan suka fice daga dajin da fitar su
suka tarar da aljani Huzmal ya bararraje yana ta sharar barci,

Tabbas Bambancin aljani da bil'adama a bayyane yake yanzu duk tsawon kwanakin da muka
shafe a cikin wannan daji Huzmal barci yake yi bai farka ba,

Jaruma Sunaila da yaslir ne sukayi wannan furuci a zukatan su batare da sun bayyana kowa ya
ji ba.

Boka Dayyubul-Barmas ya katse shirun daya wanzu ta hanyar zungurar aljani Huzmal da
kwagirin tsafin sa dake rike a hannun sa,

Firgit! Huzmal ya ɗago kansa yana mutsittsike idanu cikin magagin barci, yace" Kai wane ne ya
katse mini wannan daddaɗan barci da nake yi wanda ban fi daƙiƙa goma da farawa ba,

Koda jin wannan batu sai boka Dayyubul-Barmas ya dakamasa tsawa yace" kai bana son
maganar banza yi maza ka ɗauke mu izuwa tsaunin SHAFRAS domin ɗauko kubar
miftahul-daryal

Ka sani cewa daga nan izuwa tsaunin SHAFRAS tafiya ce ta tsawon kawanki arba'in bisa
ingarmar doki,

Ina so ka kai mu a cikin abinda bai gaza kwanaki uku kacal ba,











Sa'adda Huzmal yaji wannan batu daga bakin mai gidansa boka Dayyubul-Barmas sai ya
wartsake ya dawo cikin hayyacin sa ya dubi Dayyubul-Barmas cikin ladabi ya ce" Ka gafarceni
ya shugabana naji dukkan bayanin ka amma ina so nayi maka wata tambaya wai shin kwanaki
nawa kuka shafe a cikin wannan daji?
Koda wannan tambaya sai Dayyubul-Barmas yace " Kwanaki arba'in muka shafe

Huzmal yace "Taɓ ɗi jan amma kuwa in dai haka ne ku bil'adama kuna hakuri da kuƙe yin barci
sau ɗaya a rana,

Amma ni gashi na shafe tsawon kwanaki arba'in i na barci amma ji nayi tamkar barcin daƙiƙa
goma na yi,

Ya shugabana na rantse da girman halarar tsafin ka inda za,a bani gaba ɗaya kwanakin
rayuwar da kowannen ku zai yi a duniya a ace nayi barci iya adadin kwanakin a waje na bai
huce kaso ɗaya bisa uku na barcin da na keyi a rana ɗaya ba,

Sa'adda aljani Huzmal yazo nan azancen sa sai mamaki ya turnuƙe yaslir,Sunaila da sarauniya
lasmirat har dariya ta kuɓucewa musu,

Huzmal na kammala wannan furuci sai ya shimfiɗe gadon bayan sa kowa ya hau ya zauna

Sannan ya bude manyan fuka fukan sa ya luluƙa izuwa sararin samaniya, cikin matsanancin
gudu babu sassauci,

******. *****. ******

A,amarin su tawagar sarki Hamras kuwa, waɗanda ya tura domin su yanko masa gashin kan
boka Dayyubul-Barmas da sarauniya lasmirat domin ya samu nasarar mallakar TAKOBIN
ƊAUKAKA kuwa bisa jagorancin aljani Huruful-labarus kuwa

Sun wanzu suna gudu a bisa sararin samaniya domin zartar da umarnin shugaban su,

Ana cikin wannan tafiya ne kwatsam bazato babu tsammani sai tsulum suka ga wani ɗan
wadan aljani ya bayyana tsulum a gaban su tamkar an jefoshi daga sama,

Aljanin ya na ɗauke da ranƙwalelen kai mai ɗauke da manyan idanu ja jajur.wuyan sa ɗan siririn
ne tamkar

5 / 9