Author : Mansur Usman Sufi Category : Arewa Pen
sai ya shafe
tsawon kwanaki ashirin batare da yaji ɗuriyar su ba
Sai kawai ya nutsa bisa halarar tsafin sa domin yaga abinda ke wakana,
Ai kuwa nan take ya ga dukkanin abinda ya faru tsakanin Huruful-labarus da jarumi
shamsuddin, tun daga inda Huruful-labarus ya rusawa su sarauniya lasmirat wannan iska sihiri
suka kamu da barci mai nauyin gaske,
Har kawo inda shamsuddin ya samu galaba akan Huruful-labarus a lokacin da suka fafata
artabun,
Duk daga farko har karshe ya bayyana a cikin madubin tsafin sa,
Sa,adda Sarki Hamras yaga wannan al'amari a cikin madubin tsafin sa sai ya cika da matukar
bakin ciki maral musaltuwa,
Kuma yasha alwashin cewa komai daren dadewa sai ya ɗauki fansa akan jarumi shamsuddin
Kwanaki nabin kwanaki mako nabin mako sai gashi sarki Hamras ya shafe tsawon kwanaki
arba'in cif yana da tafiya
A ranar kwana na casa'in ne sarki Hamras yana tafiya a sararin samaniya cikin sauri yana mai
keta gajimare cikin matsanancin gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya
Yana cikin wannan hali ne yaji gajiya yafara kamashi
Kawai sai ya yanke shawarar ya sauka ya huta idan yaso sai ya cigaba da tafiya,
Koda gama kammala tunanin hakan sai kawai ya shafi wani gurin shafi a damtsen sa na hagu
take yayo ƙasa sulu lu lu luh!
Ya dira a bisa turaba tamakar yakasance mai fuka-fuakai
Inda ya sauka yakasance daji mai ɗauke da manyan tsaunuka da bishiyoyi, duwatsu da
ƙwazazzabai,
Hakika dajin yatara dukkan wata sifa ta kwarjini
Daga can nesa sai sarki Hamras ya hangi wani kerarran gida kwarya ɗaya jal a dajin
Al'amarin da yayi matukar basa mamaki kenan kuma ya ɗaure masa kai ya ce a cikin ransa
Shin ko wane ne. Mai mallaki wannan gida kawai sai ya yanke shawarar ya shiga izuwa gidan
domin yaga ko mene ne a cikin sa
Koda gama yanke shawarar hakan sai kawai ya durfafi gidan gadan gadan
Idan ka ɗauke karar takun sawaye sarki Hamras dake haddasa motsawar busassun
ganyayyakin bishiyun da suke zube a ƙasa babu abinda kunne keji
Wannan shi ne a binda ya faru ga sarki Hamras na mai mulkin Daular aljanu,
*****. *****. *****
Lokacin da aka kacame da azababban yaƙi tsakanin su boka Dayyubul-Barmas da yaran Uban
muridan duniya KIRMALU IBN SHAMSHAN
Sai yaƙin yazamo mai matukar firgici daban tsoro
Karar karafniyar ƙarafa ta cika tsaunin Darul SHAFRAS baki ɗaya
Suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama JURIYA DA BAJINTA irin
ta JARUMAN DUNIYA
Nan fa su boka Dayyubul-Barmas suka fara gane kuren su domin tsananin zafin naman
muridan ya huce tunanin bil,dama
Kai iya hargowar muridan ta isa ta firgita duk wata halitta mai numfashi,
Abangaren jarumi shamsuddin kuwa wani abin mamaki ya faru domin dai gashi a zahiri muridan
na kallonsa amma sai ya zamo basa iya ganin ballantana su tunkari inda yake,
Su kansu su boka Dayyubul-Barmas sai da suka cika da matukar mamaki da ganin hakan,
Abin da basu sani ba shine addu'o i da shamsuddin ke karantawa shine ya makantar da
idanuwan muridan. Basa iya ganin sa
Sai da aka shafe tsawon dakika ɗari biyar ana fafata artabun babu sassauci
Yazamana cewa su boka Dayyubul-Barmas basa iya mayar da martani sai dai ƙoƙarin kare
kansu kawai.
Al'amarin daya fusata muridan kenan kuma ya basu mamaki,
Domin a iya tsawon wanzuwar su a saman tsaunin Darul SHAFRAS basu taɓa yin gamo da
halitta mai karfin damtse tamkar su sarauniya lasmirat,
Koda su kazo nan a tunaninsu sai suka sake zage damtse suna kaiwa mu hare haren bazato
Tabbas masu iya magana na cewa idan kiɗa ya canza dola ne rawa ta canza
Faruwar hakan keda wuya sai ya zama na cewa a wannan lokacin muridan sun fara samun
nasarar kaftausu sara a sassan jikin su,
Duk wanda ɗaya daga cikin muridan ya kafta sara sai kaji ya tsandara ihu jini yayi tsartuwa,
Kuma ya kife a kasa yana nishin wahala,
Cikin abinda bai gaza dakika ɗari biyu ba muridan suka zubar da su boka Dayyubul-Barmas
kasa babu wanda yake wani kwakkwaran motsi a cikinsu,
Sai nishi kawai suke yi numfashin su na fita sama sama
Koda samun wannan gagarumar nasara sai muridan suka bushe da dariyar mugunta suka
shiga buga ƙafafuwan su a kasa,
Nan take sautin ɗariyar yayi sanadin sumewar su boka Dayyubul-Barmas,
A lokaci guda tamkar haɗin baki muridan suka tsuke bakunan su tamkar an aiko musu da
WASIKAR MUTUWA kai kace basu taɓa dariya ba tunda Allah ya halicce su,
Sarkin muridan duniya KIRMALU IBN SHAMSHAN ya sake ratso wannan hanya ta tsakiyar
yaran sa ya taka da kafafafun sa har izuwa inda su sarauniya lasmirat ke kwance,
Yaran sa nayi masa kirari suna cewa
Gaisheka KIRMALU mai duniya
Hadari sa gaban ka inda kake so!
Daji kake ba,a yi maka ƙyaure koda mahaukacin kafinta,
Kai gajimare mai zubar da ruwan musiba da bala'o'i
Kai ne. SARKIN SADAUKAI na duniya,
Sa,adda uban muridai KIRMALU yaji kirarin da yaransa ke yi masa sai ya wangale bakinsa
yana mai ɓaɓɓaka dariyar farin ciki,
Duk wannan abu dake wakana jarumi shamsuddin yana tsaye a gefe guda yana kallo
A lokaci guda KIRMALU ya murtke fuska tamkar an aiko masa da SAƘON MUTUWA
Kawai sai ya zare wani mashi a gadon bayan sa mai baki biyu ya daga sama da nufin ya farka
cikin sarauniya lasmirat da Sunaila,
Koda ganin abinda ke shirin faruwa sai shamsuddin ya falafala da azababban gudu izuwa kan
uban muridai yana mai karanto waansu addu'o'i na musamman a cikin ransa tare da maimakon
Ubangijin musulunci,
Yayin da rage saura taku goma tsakanin su, sai a sannanne muridan suke iya ganin
shamsuddin da idanuwan su,
Kafin aya daga cikin su yayi wani yunkuri shamsuddin ya shammace shugaban muridan ya
gabza masa wani wawan naushi a fuska,
Bisa mamaki sai aka ji uban muridai KIRMALU ya kurma wawan ihu sannan ya jefar da mashin
dake rie a hannun sa,
Al'amarin da ya harzua zukatan sauran muridan kenan kuma fusata ainun suka afkwa
shamsuddin da azababban yai suka wanzu suna kai masa miyagun hare haren
Shamsuddin ya wanzu yana karewa tare da zillewa harin muridan tare da maida martani cikin
bakin zafin nama ta hanyar amfani da hannun sa da kafa wajen kai bugu da naushi,
Tabbas ikon Ubangiji ya huce tunanin an Adam domin abinda mutum yake ganin bazai yiwu ba
sai kaga Ubangiji ya samar dashi,
Domin kuwa duk wanda shamsuddin ya nausa a cikin muridan sai kaji inda ya nausa in ya ya
karye yayi kara as ruus, ya kurma wawan ihu,
Nan fa ihu da kururuwur muridan ta cika dodon kunne da tsaunin baki aya,
Duk inda shamsuddin ya sanya gaba sai dai kaga muridan na zubewa kasa matattu tamkar
yana sassabe a gonar auduga jini yana kwaranya,
Wohoho Hakika duk wanda ya iya ya huta inda ace mutum yana tsaye a wannan waje yaga
yadda shamsuddin ke hallaka muridan dola ne ya jinjina masa ya tabbatar dacewa ya cika
SARKIN SADAUKAI,
Kafin shuewar dakika ari shamsuddin ya hallaka gaba aya muridan ya zubar da gawarwakin su,
Sa'adda uban muridai KIRMALU IBN SHAMSHAN ya yi arba da gawarwakin jama'ar da sai
kawai ya mie tsaye zumbur yana mai kurma wawan ihu
Take wata irin gagarumar Iska ta dunga fitowa daga hancinsa da bakinsa wacce ta sanya
gashin kan shamsuddin ya mimmike ,
Kuma tayi sanadiyyar farfaowar su sarauniya lasmirat daga dogon suman da suka yi.
Sa'adda sarauniya lasmirat,boka Dayyubul-Barmas, yaslir, Sunaila,saltir, Huzmal,Barbusa,
Huruful-labarus, suka yi arba da gawarwakin muridan kwance cikin jini kuma jikin shamsuddin
duk ya aci da jini muridan sai suka cika da matukar mamaki,
Suka ce a cikin ransa shin taya ya akayi shamsuddin ya samu gagarumin karfin da samu
nasarar hallaka muridan
Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan kawai suka zuba idanu domin suga abinda
zai faru tsakanin shamsuddin da uban muridai KIRMALU,
Uban muridai KIRMALU na kammala kururuwur sai kawai ya zare wata zabgegiyar adda a ugun
sa mai kaifin tsiya ya falfala da azababban gudu izuwa inda shamsuddin yake duk sa'adda ya
ajiye afarsa aya sai kaga kafar wajen ta tsage ta rufta izuwa ciki,
Koda ganin hakan sai shamsuddin ya zare takobin sa ya kwala kabbara da karfi ya ruga kan
uban muridai don tarar juna,
Lokacin da ya zamo saura taku goma a tsakanin su sai shamsuddin ya zamo an wada agaban
uban muridai tamkar an ajiye yanwa a gaban kare,
Lokacin da aka hau sai aka ruguntsume da azababban yai mai matukar firgici daban tsoro,
Shamsuddin ya wanzu yana kare hare haren uban muridai tare da mayar da martani cikin bain
zafin nama JURIYA DA BAJINTA,
Duk sa'adda uban muridai ya kai masa hari da addar sa idan ya goce duk abinda takobin ta
sauka a kansa sai kaga yayi bindiga ya tarwatse yazama gari koda kuwa gini komai warinsa,
nan fa shamsuddin da uban muridai suka tashin hankalin duk wata halitta dake fadar,
Gaskiyar masu iya magana da suka ce fadan da yafi karfin ka sai ka zamo an kallo,
Kuma tabbas idan gwani da gwani suka hau, juriya da naci suka ci karo da juna dole ne yai ya
zamo tashin hankali daban tsoro,
Hakan ne yafaru dasu boka Dayyubul-Barmas domin koda suka lura cewa duwatsun da su
shamsuddin ke rusawa a fadar suna neman danne su sai suka rarrafa da afafuwan su izuwa
bayan waansu duraku a fadar suka lae suna hangen abinda ke wakana
Sai da aka shafe tsawon sa,a aya cur ana wannan bain artabu
Shamsuddin bai samu nasarar koda lakutar jikin sa ba duk kuwa da cewar yana karanta addu'a
na musamman a cikin zuciyar sa
Ana cikin wannan artabu ne uban muridai ya samu nasarar make takobin dake hannun
shamsuddin a lokacin da ya daka tsalle da nufin ya hau kan kafadar sa
Kawai sai uban muridai KIRMALU ya canza salon faan sa a inda ya shiga kaiwa shamsuddin
hari da karfin damtse bada makami ba ,
Shamsuddin ya wanzu yana zillewa harin tare da amfani da dubaru da hikimomi, yana mai
kwala kabbara gami da neman taimakon daga sunayen fiyayyan halitta annabi Muhammad
s,a,w,
Nan take wani irin gagarumin karfi ya shige sa kawai sai ya daka tsalle sama ai ku wa sai gashi
a saman uban muridai tamkar an janye sa da ungiya,
Kawai sai ya dunkule hannayen sa biyu ya irawa uban muridai KIRMALU naushi a wuya,
Saboda arfin naushin sai da asusuwan wuyan sukayi ara ruus as!
Uban muridai ya kurma wawan ihu, Kafin ya sake wani yunkuri shamsuddin ya sake gira masa
wani naushin.
Kawai sai akaga jikin uban muridai ya sandare ya yi asa zai fao,
Koda shamsuddin ya lura cewa zai rikito daga saman uban muridai sai kawai ya dako wani
wawan tsalle naban al'ajabi da mamaki ya sauka abisa turba,
A lokacin da gangar jikin uban muridai KIRMALU ta fai asa rikica, tamkar an jefar da toron Giwa
ko shurawa bai yi ba
Nan fa mamaki ya turnue su sarauniya lasmirat Bisa ganin gagarumar bajintar da shamsuddin
yayi na hallaka uban muridai KIRMALU da yaran sa.
Al'amrin su shamsuddin kuwa sai da suka shafe tsawon kwanaki huu a saman tsaunin Darul
SHAFRAS,kowa ya warke sumul daga raunukan dake jikin sa,
Bayan shamsuddin ya samu nasarar ebo ruwan ma,ul- hayat a wani bangare a tsaunin,
Sannan su aljani Huzmal suka sake aukar su aka cigaba da tafiya,
Ana cikin wannan tafiya ne a lokacin da rana ta take sai sarauniya lasmirat ta dubi Sunaila tayi
gyaran murya sannan ta kawo gwaron numfashi ta ajiye tace " ya Sunaila inyi miki wata
tambaya mana idan bazaki damu ba,
Sunaila tace " ina sauraren ki fai tambayar ki,
Lasmirat ta ce" A can baya lokacin da kika samu nasarar akan wannan aljana acan birni na
lokacin da na tambaye ki labarin rayuwar ki kin faa mini cewa baban Burin ki shine ki sadu da
mutane ma,abota addanin Musulunci, domin aukar fansa akan wani azzalumun sarki shin
Jarumi shamsuddin baya aya daga cikin mutanen da kike nema ne?
Koda jin wannan tambaya sai sunaila tayi murmushi
Duk da kasancewar fuskar ta na rufe da rawani sai da lasmirat taga alamun loawar kumatun ta
a lokacin da tayi dariyar,
Sannan ta dubi lasmirat yace" ya yar uwa ta kiyi sani cewa bawai ina tantama Game
shamsuddin ba ne tabbas yana daga cikin ma, abota addanin Musulunci da nake nema sai dai
ina so na kammala haa waansu hujjoji ne sannan na kari Addinin sa,
Koda jin wannan jawabi daga bakin Sunaila sai lasmirat ta gyaa kai Sannan ta bui baki akaro na
uku da fara wannan tattaunawa ta ce"Amma kina ganin Ubangijin shamsuddin bashine abinda
dogaro ba kuwa ki dub kiga yadda ya samu nasara akan su aljani Huruful-labarus da uban
muridai wanda boka Dayyubul-Barmas yagaza kare mu,
Koda jin wannan batu daga bakin lasmirat sai sunaila tace"Tabbas duk abinda kika faa akan
shamsuddin haka ne harma ya huce haka inda ace kin taa karanta jarumi Hilal da irin nasarar
da ya samu a rayuwarsa da ke kunshe a cikin littafin KARSHEN ZALUNCI,
da zaki tabbatar dacewa girma da sha,anin ma,abota addanin Musulunci ya huce yadda ake
tsammani,
Koda jin wannan batu sai sarauniya lasmirat tayi ajiyar zuciya sannan ta kawo gwaron numfashi
ta ajiye tace" Ta ijan idan kuwa har haka ne abinda shamsuddin yayi abaya bakomai bane. Face
sharar fage domin ke gaban mu yafi na baya yawa,
Tafiyar kwanaki arba'in akayi aka iso kogon Garul- barzahu inda kubar miftahul-daryal take
Sai da shamsuddin yasha gwagwarmaya dakyar da taimakon Ubangijin halitta ya samu nasarar
kashe miyagun halittun dake ciki,kuma ya samu nasarar auko kubar miftahul-daryal,
Hakika su sarauniya lasmirat sun ga iko da kudirar Ubangiji a wannan rana
Bayan kwanaki biyu sai aka sake cigaba da tafiya domin isa gidan boka Daryalu domin ebo
ruwan koramar sa
Yayin da aka iso cikin koramar sai aka tarar tana auke da waansu irin halittu masu auke da
fuka-fukai irin na jemagu suna da kawuna irin na bil,adama, suna wani irin gurnani mai sanya
firgici daban tsoro.
Nanfa aka ruguntsume da azababban yai mai matukar firgici daban tsoro yazamana cewa kowa
ya gane kuren sa,
Sai da aka wuni cir ana artabu babu sassauci, sannan aka samu nasarar hallaka halittun amma
kowa ya samu manyan raunuka a jikin sa
Nan fa yazamana cewa tsananin azabar dasu lasmirat suka sha tasa jikin su yayi sanyi kuma
gwiwoyin su sukayi sanyi dukkanin su suka yi nadamar yin wannan tafiya domin wata buata ta
jin dain duniya musamman sarauniya lasmirat,
Bisa wannan dalili ne yasanya dukkanin su suka yanke shawarar karbar addinin Musulunci
Bayan sun karbi kalar shahada ne a wajen shamsuddin
Sai shamsuddin ya bayyana wa sarauniya lasmirat cewa dukkanin bayanin da boka
Dayyubul-Barmas yayi mata aiki ne. Na bokaye ma,ana sihiri shi kuma sihiri karya ne
Saboda haka imani da tayi da Ubangijin musulunci zai biya mata dukkan bukatun ta kuma
muradin ta ya cika na samun aukaka a duniya da ma tsawon rayuwa
A sannanne Sunaila ta cire rawanin dake kanta fuskar ta ta bayyana a fili arara
Sa, adda kowa ya yi arba da fuskar sulaina sai mamaki ya kamashi ,
Yaslir kuwa bai san sa,adda ya ruga izuwa inda take ba ya kura mata idanu hawaye na zuba
daga fuskar sa
Nan take ita ma Sunaila kwalla ta zubo mata
Bakomai ne ya sanya hakan ba sai domin a yanzu ne yaslir ya tabbatar da zargin sa cewa
Sunaila ita masoyiyar sa gimbiya salimat
Kawai sai suka rungume juna cikin matukar farin ciki maral musaltuwa gami da tsantsar
soyayya hade da shauin juna,
Ana cikin wannan hali ne sai kawai akayi arba da boka Dayyubul-Barmas ya bayyana tsulum
hannun sa rike da wata zabgegiyar takobi ta haske mai matukar kyawu ba wata ba ce takobin
ba face TAKOBIN AUKAKA
Abinda basu sani ba shine. A lokacin da yaji dukkan su sun karbi addanin Musulunci sai ya faki
idanun su ya bace yaje ya haa kai da sarki Hamras mai gidan su aljani Huruful-labarus, da
tsohuwa zahira wacce sarki Hamras ya shiga gidan ta a cikin wannan daji a lokacin da ya fito
farautar shamsuddin ,
Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin su shamsuddin da su boka Dayyubul-Barmas,
A lokaci guda boka Dayyubul-Barmas,sarki Hamras ,tsohuwa zahira suka yi kukan kura suka
afkawa shamsuddin da azababban yai mai matukar firgici da tashin hankali,
Dakyar shamsuddin ya hallaka su duka bisa taimakon Ubangiji dukkan su sukayi mutuwar
hulakanci
Tabbas da ace mutum yana wannan waje zai ga yadda gawar boka Dayyubul-Barmas ta
hulakanta dole ne takaici ya kamasa bisa ganin yadda duk wahalar da boka Dayyubul-Barmas
yasha abaya gashi ta tashi a banza yayi mutuwar asara
Tabbas rayuwar kafirci wahala ce kuma arasa ce
Amma shamsuddin yasha wahala tamkar ransa zai fita,
Koda su aljani Huruful-labarus suka ga abinda ya faru da mai gidan su sarki Hamras da kuma
irin abubuwan al,ajabi da shamsuddin yayi sai nan take suka bayar da gaskiya da