TAKOBIN DAUKAKA BOOK COMPELET BY MANSUR USMAN SUFI.pdf

Author :  Mansur Usman Sufi Category :  Arewa Pen

Chapter   6 / 9

15K to 18K   out of 24.6K words

na barewa, kai bazaka taɓa cewa wuyan nasa zai iya ɗaukar nauyin rafkeken kan
nasa ba, yana ɗauke da tafkeken kirji mai ɗauke da curi curin tsoka,

Cikin sa rubdumeme ne tamkar an kifa kwarya, ƙafafuwan sa yan sirara ne tamkar sillan kara,
yana ɗauke da wata murtukekiyar jela, Du dudu tsawon sa bai huce kamu ɗaya ba,

Tabbas duk inda muni yake wannan aljani ya cika mummuna, idan kuwa za,a yi gasar muni ta
duniya zai iya zama na ɗaya,

Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin su aljani Huruful-labarus da aljanin,

Daga can sai Huruful-labarus ya dubi aljanin ya dakamasa tsawa ya dube sa a wulakance yace"
yakai wannan ɗan ƙaramin kwaro a cikin aljanun duniya, shin wane ne kai, kuma wane irin
rashin sani ne ya kawo ka nan wanen,

Yi maza ka amsa mini waɗannan tambayoyi kafin naga irin hukuncin daya dace dakai,

Koda jin wannan batu daga bakin aljani Huruful-labarus sai aljanin ya kyalkyale da dariya har da
kwalla,

Al'amrin da yayi matukar bawa Huruful-labarus da tawagar sa mamaki kenan kuma ya basu
mamaki,

Abin da ya basu mamaki shi ne taya ya wannan aljani da bai huce ɗaya daga cikin su ya
maƙure shi ba zai dunga ɓabbaka musu dariya

A lokaci guda ɗan wadan aljanin ya tsuke bakin sa kuma ya murtuke fuska tamkar an aiko masa
da

SAƘON MUTUWA cikin kakkausar murya yace" yaku waɗannan kananan jarumai kuyi sani
cewa suna na Sahibul-Muluk,

Kuma Ni ne shugaban yan fashin aljanun wannan nahiya baki ɗaya, Hakika kunyi babban
kuskure da har kuka tsaya a gaba na kuke faɗa mini magana amma yanzu zan ganar daku
kuren ku,

Koda jin wannan batu sai aljani Huruful-labarus ya fusata ainun ya dakawa yaran sa tsawa su
kayi ɗauki kan Aljani Sahibul-Muluk suka ihu da kururuwa mai firgitar wa,

Nan take aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar muni ban tsoro daban al'ajabi,







Sa'adda da aka yamutse da azababban artabu tsakanin shugaban Yan fashin wadannin aljanun
duniya,

Wato aljani Sahibul-Muluk, da tawagar aljani Huruful-labarus,

Sai yaƙin yazamo abin tsoro gami da ban mamak,

Domin kuwa duk irin girma da kwarjinin Huruful-labarus da yaransa sai ya zamo abanza,

Domin kuwa Sahibul-Muluk yazame musu alƙaƙai sun rasa yadda zasu yi dashi,

A inda zaka ga ya taƙarƙare ya ƙirɓawa ɗaya daga cikin su naushi yayi katantanwa sau uku ya
faɗo ƙasa tim!

A wasu lokutan idan hannun sa ya naushe su sai dai kaji kashi yayi ƙara ruƙus,

Nan fa ihu da hargowar aljanun ta ci ka dajin baki ɗaya,

Inda ace mutum yana tsaye a wannan waje sai yayi tsammanin cewa YAKIN DUNIYA ya taso,

Sa'adda da aljani Huruful-labarus dake tsaye a gefe guda ya na kallon artabun da akeyi yaga
yadda aljani Sahibul-Muluk yazame wa yaran sa ANNOBA ƊARI,

sai ya cika da matukar mamaki kuma ya fusata ainun,

Abin da ya basa mamakin shine yadda Sahibul-Muluk ke ragargazar dakarun tamkar na'ura ce
ke sarrafa shi,

Tabbas wannan shine fa abin da masu iya magana

ke cewa" GABA DA GABANTA

Aljani ya taka wuta"

Koda Huruful-labarus ya lura cewa idan har aka cigaba da wannan yaƙi a haka dakarun nasa
zasu iya karewa sai kawai ya taƙarƙare ya kwarara wawan ihu ya zare wata sharbebiyar takobi
a damtsen sa yayi ɗauki kan Aljani Sahibul-Muluk,

Aka ruguntsume da sabon azababban yaƙi, Sahibul-Muluk ya tare sa ya wanzu yana kare hare
haren tare da mayar da martani ta hanyar kai bugu da naushi,

Ana cikin wannan yaƙi ne Huruful-labarus ya samu nasarar laftawa Sahibul-Muluk wani sara, jini
yayi tsartuwa ya zuba a ƙasa,

Sahibul-Muluk ya kwarara ihu sakamakon tsananin zafida zugin da yaji, cikin zafin nama ya
mayar da martani ta hanyar kai wa Huruful-labarus naushi a fuska,

Huruful-labarus ya zille tare da zamewa harin sannan ya sanya takobin sa a karo na biyu ya
tsarge Sahibul-Muluk gida biyu, take gangar jikin ta fado ƙasa rikica jini ya kwarara tamakar an
buɗe fanfo,

Koda samun wannan nasara sai Huruful-labarus ya ɗaga kansa izuwa sama ai kuwa sai yayi
arba da wata yar ƙaramar halitta,

Bata ba ce face Aljani Huzmal ɗauke da su sarauniya lasmirat,

Nan take Huruful-labarus ya busa musu wata irin gagarumar Iska daga bakin sa,

Tsananin karfin iskar ya tashi hankalin duk wata halitta dake rayuwa a dajin, kuma ta sanya
fuka-fukin aljani Huzmal na ɓangaren dama ya karye take suka rikito daga sararin samaniya,

Sai suka faɗo a kan tafin hannun Huruful-labarus Huzmal yana mai tsandara ihu sakamakon
tsananin raɗaɗin da yaji a fuka fukin sa daya karye,

Sarauniya lasmirat,boka Dayyubul-Barmas, yaslir da Sunaila kuwa sun galabaita ainun domin
koda wata gaɓa a jikin su basa iya motsawa,

Cikin matukar farin ciki aljani Huruful-labarus yace" yaku abokan tafiya kuyi sani cewa wani abin
farin ciki ya same mu ku sani cewa waɗannan bil'adama da kuka gani akan tafin hannu na sune
abinda muka fito nema wato sarauniya lasmirat da boka Dayyubul-Barmas,

Koda gama faɗin hakan sai ya nuna su sarauniya lasmirat da ɗan yatsan sa na hagu take wata
igiyar tsafi ta bayyana a ɗaɗɗaure su tamau!

Kawai sai ya jefasu a cikin aljihun rigar sa tamkar ya jefa kwallon goriba,

Kawai sai ya yunƙura ya tashi zuwa sararin samaniya yana tsala gudu yaran sa na biye da shi.

Huruful-labarus da tawagar su ka cigaba da tsala gudu a sararin samaniya ɗauke da su
sarauniya lasmirat a cikin aljihun sa,

Sai da suka shafe tsawon dakika ɗari huɗu sannan aljani Huruful-labarus yayi umarni a yada
zango

Inda aka yada zangon yakasance daji mai matukar kwarjini daban tsoro,

Yana ɗauke da waɗansu dogayen bishiyu masu siffofin ban tsoro,

Ko iya shirun da wanzu a dajin ya isa ya jefa tsoro a zukatan JARUMAI,

Yayin da aka sauka a cikin dajin sai a kayi turus!

Bakomai akaga ni face wani kyakkyawan saurayi sanye da fararen tufafi zaune bisa wani buzu
na fatar damisa ya fuskanci alkibila yana gabatar da wata irin ibada mai ban mamaki,

Nan fa aljani Huruful-labarus da yaran sa suka ƙurawa saurayin idanu cikin tsananin Mamaki,

Abu na farko da ya basu mamaki shi ne taya ya bil'adama guda ɗaya ya shigo wannan daji mai
matukar haɗari, alhalin shi bai kasance wani mashahurin matsafi ba,

Wani abu da yafi ɗaure musu kai shi ne menene yasanya da saurayin yayi arba dasu bai firgita
ba,

Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan,

Kawai sai suka zuba idanu suna kallon yadda saurayin yake gudanar da ibadar,

Bisa mamaki sai suka ga ashe har ya kammala ibadar tasa ya ɗauki wata jakar fata ya rataya a
kafaɗar da ya kunna kai izuwa wani bangare a dajin,

Al'amarin da ya fusata Huruful-labarus kenan yasha gaban saurayin yana mai dakama sa tsawa
ya dube sa cikin matukar fushi yace

"Yakai wannan saurayi ma,abocin GAJERAN KWANA,

shin wane ne kai a cikin bokayen duniya da har zaka nuna rashin ladabi a gareni?

Koda jin waɗannan tambayoyi sai saurayin yayi murmushi da ya ƙarawa fuskar sa kwarjini da
haiba kawai ya sake kunna kai izuwa dajin batare da ya bawa Huruful-labarus amsar tambayar
sa ba

Cikin fushi Huruful-labarus ya kai masa duka da fuka-fukin sa

Kafin dukan yakai saurayin ya ɗaga hannayen sa sama ya karanta waɗansu addu,o,i na
musamman ya shafa a fuskar sa,

Kawai sai aka ga wata irin murtukekiyar igiya ta ta ɗaɗɗaure aljani Huruful-labarus da yaransa
kuma igiyar tsafin da ta ɗaure su sarauniya lasmirat ta bace ɓat, suka faɗo daga cikin aljihun
rigar aljani Huruful-labarus,

Har a wannan lokaci a matukar Galabaice suke boka Dayyubul-Barmas da sarauniya lasmirat
kaɗai basu ji jiki sosai ba,

Yayin da saurayin yayi arba da su lasmirat sai ya cika da matukar mamaki.

Lasmirat ta miƙe tsaye da 'ƙyar boka Dayyubul-Barmas yayi koyi da ita, yaslir d Sunaila da
aljani Huzmal na zaune dirshen a ƙasa cikin halin galabaita.


Sa,adda lasmirat ta haɗa idanu da saurayin sai taji wani abu ya ɗarsu a zuciyar ta wanda ta
kasa Bamban ce ko mene ne a iya tsawon rayuwar ta bata taɓa ganin namiji mai kyawun
saurayin ba,

Kallo ne ya wakana a tsakanin su na ɗan wani lokaci lasmirat nayi masa kallo mai ɗauke da
alamar tambaya,

Daga can sai lasmirat ta buɗi baki cikin wata irin tattausar murya mai rikita duk wani ɗa namiji
cikin annurin fuska ta ce

"Yakai wannan saurayia ma'abocin kwarjini da haiba shin wane ne kai?

Kuma ya akayi ka samu nasarar ceto rayuwar mu a hannun waɗannan aljanu?

Koda jin waɗannan tambayoyi sai saurayin ya zurfafa izuwa kogin tunani da ga bisani ya dubi
lasmirat da fararen idanun sa masu haske tamkar madara cikin zazzakar murya yace

"Yake wannan sarauniya ma'abociyar kyawu game da tambayar ki ta farko

Suna na shamsuddin ibn Abbas na baro birnin mu ne domin ɗaukaka kalmar Ubangiji.

Na samu nasara akan waɗannan aljanu ne ta hanyar neman taimakon Ubangiji na ,

Cikin matukar mamaki lasmirat ta sake budar baki a karo na biyu tace" shi wane ne wannan
Ubangijin naka?.

Shamsuddin yayi murmushi yace" Ubangijina shi ne wanda ya halicci duniya da abinda ke cikin
ta babu abin da ya gagare sa komai yana iko a kansa, shine mai ciyar da tsuntsayen dake cikin
duhuwar daji dama kifaye da ke karkashin Teku,

Tsananin duhun dare ko na Teku baya ɓuya gare sa.



Jarumi shamsuddin ya cigaba da jawabin sa bisa tambayar da sarauniya lasmirat ta yi masa,

A inda ya cigaba da cewa Ubangiji shi ne ya wanzu tun babu babu ita kanta,

Bashi da farko ba shi da ƙarshe,

Sa'adda sarauniya lasmirat taji wannan jawabi sai nan take mamaki ya kamu ita da abokan
tafiyar ta,

Shiru ne ya wanzu a tsakanin su na ɗan wani lokaci daga bisani lasmirat ta matsa daf da inda
shamsuddin yake ta yadda suna iya jin numfashin juna ta dube sa tace"yakai shamsuddin ina
so ka ɗan bani lokaci zan yi shawara da abokan tafiyata,

Da jin wannan batu sai shamsuddin ya gyaɗa kai

Lasmirat ta matsa kusa da abokan tafiyar ta ta dube su tace" Yaku abokan tafiya ta shin me
kuke gani game da wannan baƙon jarumi shamsuddin Ni ina ganin idan muka haɗa tafiyar dashi
zai bamu wata gudun mowa ta musamman, domin ku duba fa kuga yadda Ubangijin sa ya bore
masa sarrafa aljanu
Koda jin wannan batu daga bakin sarauniya lasmirat sai boka Dayyubul-Barmas ya dube ta
cikin kakkausar murya fuskar sa a murtke tamkar an aiko masa da WASIKAR MUTUWA,

Yace"ya shugabata kiyi sani cewa ni ashawara ta bazamu haɗa tafiyar mu da wannan baƙon
jarumi ba domin idan baki manta ba acan baya lokacin da kika ziyar ce nagaya miki cewa
saurayin da zaki aura har ki samu Haihuwa shine namijin da yafi Kowa talauci a duniya, kuma
shine zai hanamu cika burin mu na mallakar TAKOBIN ƊAUKAKA,
Shin yanzu bakya tsammanin cewa wannan baƙon jarumi shi ne saurayin da zai hana cika
muradin mu,

Tabbas jikina ya bani cewa babu wani alkairi a tare da wannan jarumi.

Lokacin da sarauniya lasmirat ta ji wannan batu daga bakin Boka Dayyubul-Barmas sai
hankalin ta ya ɗugunzuma ainun ta sunkuyar da kanta ƙasa tana mai zurfafa cikin kogin tunani,

Abu na farko da ya faɗo mata arai shin yanzu idan wannan baƙon jarumi shi ne wanda yafi
kowa talauci a duniya shin taya ya zata iya cire soyayyar da ta kama zuciyar ta a Lokaci guda,

To wai shin ma boka Dayyubul-Barmas da yake wannan magana yana da tabbacin cewa
Wannan baƙon jarumi shine saurayin da zai hana su cimma muradun su na samun TAKOBIN
ƊAUKAKA,

Domin haka ai bashi da hujjar dazai zargi baƙon jarumin, haka dai lasmirat ta cigaba da wannan
tunani ta saƙa wancan ta kunce wancan,

Daga bisani ne dai sai ta dubi boka Dayyubul-Barmas tace" yakai Dayyubul-Barmas kayi sani
cewa babu wata hujja da zata sanya mu janye tafiyar mu da wannan baƙon jarumi ba,

Abu ɗaya ne kawai zai kawo mu janye kuɗirin na mu shine ka gudanar da bincike bisa halarar
tsafin ka ka tabbatar mana da zargin da kake yi,

Sa,adda boka Dayyubul-Barmas ya ji wannan batu daga bakin lasmirat sai ya dubeta yace "ya
shugabata kiyi sani cewa da ace wani zai iya taimaka mana da bamu samu nasarar ɗauko
zobunan sihiri ba,

Amma masu iya magana na cewa"Ba,a kwacewa yaro garma"

Zanyi duk abinda kika faɗa sai dai duk abin da ya biyo baya kada ki zargi ko a sai kanki,

Koda jin wannan batu sai Hankalin sarauniya lasmirat ya ɗugunzuma ainun hantar cikin ta
takaɗa amma sai kawai ta basar ta nufi inda shamsuddin yake tana mai sakar masa tattausar
murmushi tace"yakai wannan jarumi ma,abocin kyawu da kwarjini kayi sani cewa na tattauna da
abokan tafiya ta kuma dukkan mu mun roki alfarma a wajen ka da kayi mana rakiya izuwa
mallako waɗansu abubuwa,

Shamsuddin yayi murmushi yace" Nasan dukkan abinda kuka fito nema wato kubar
miftahul-daryal da TAKOBIN ƊAUKAKA tunda kun samu nasarar ɗauko zobunan sihiri a cikin
kogon fatalwa,

Dajin wannan batu mamaki ya turnuƙe lasmirat ta dube sa cikin mamaki"ya akayi kasan
abubuwan da muka fito nema ya jarumin jarumai

Shamsuddin yayi murmushi yace"ya shugabata idan bazaki manta ba ko a baya na gaya miki
cewa ikon Ubangiji na ya huce haka

Hakika Ubangiji na ya bayyana mini dukkan Abin da ya gudana daku a cikin mafarki na.

Sai dai kafin na amince da buƙatar ku tilas ne ku amince da sharudda na guda biyu

Na farko shine duk sa,adda wani abu ya taso na neman taimako sakamakon wata musiba zan
zuba muku idanu sai kunyi dukkan abinda zaku yi kun gaza sannan na gwada tawa dubarar,

Sannan idan Ubangiji na ya bani ikon mallakar TAKOBIN ƊAUKAKA kuyi mini alkawarin cewa
za ku ƙarni addinina na Musulunci

Sa,adda sarauniya lasmirat ta ji waɗannan sharuɗɗa daga bakin shamsuddin sai tace"Duka
mun amince da wannan sharuɗɗa naka ai biyan buƙata yafi dogon buri,

Koda gama faɗin hakan sai shamsuddin ya koma kan buzun sa ya cigaba da gudanar da ibadar
sa, lasmirat ta koma wajen abokan tafiyar ta,

Sai da aka kwana biyu a wannan waje aljani Huzmal yayi jinyar Fuka fukan sa su yaslir suka
samu karfin jikin su sannan aka cigaba da tafiya

A halin yanzu tafiya ta canza daga tawaga ɗaya zuwa biyu wato sarauniya lasmirat da su aljani
Huruful-labarus da jarumi shamsuddin

Maimakon a wannan karon a hau bisa aljani Huzmal sai shamsuddin ya ce kowa ya hau ɗaya
daga yaran aljani Huruful-labarus bisa izinin Ubangiji ɗayan su bazai saɓa daga Umarnin da
aka yi masa ba,

Da yake a wannan lokaci da aka fara tafiya da hasken rana ne,

Lokacin da duhun dare yafara kawo kai sai shamsuddin yayi umarni aka yada zango

Take aljanu shida dake ɗauke da, yaslir,Sunaila, Dayyubul-Barmas, lasmirat da shamsuddin
suka saki manyan fuka fukan su suka sauka a turba,

Ana sauka aka kafa tantuna bayan an kafa ne sarauniya lasmirat ta shiga tanti ɗaya tare da
sunaila,

Boka Dayyubul-Barmas da yaslir, shamsuddin sai ya shiga nasa shi kaɗai

Aljani Huzmal yana tsaye bisa bakin kofar tantin su boka Dayyubul-Barmas, su aljani
Huruful-labarus kuwa suka karkasu izuwa kowace kusurwa a dajin domin tabbatar da cikekken
tsaro,

A cikin tantin sarauniya lasmirat kuwa bayan sun kammala kalaci ita da sunaila,

Sai lasmirat ta kwanta Bisa kan gadon ta domin ta samu rintsawa amma duk sa,adda ta rufe
idanun ta sai taga babu abinda take gani face fuskar jarumi shamsuddin yana yi mata
murmushi,

A wannan lokaci tuni Sunaila ta fara sharar barci har da minshari,

Haka dai lasmirat takasance a cikin wannan hali har barci yayi awon gaba da ita,

Tabbas lasmirat ta kamu da matsananciyar soyayyar wacce bata taɓa tsammanin zata shiga ba,

Tabbas da ace jarumi shamsuddin zai zaɓeni a matsayin a matsayin abokiyar rayuwar sa

Tabbas zan iya hakura da mulkina dukiya dama komai da mallaka domin na samu soyayyar sa ,

Kamar yadda ya wakana a masauki su lasmirat haka al'amarin yakasance a masaukin su yaslir

Ina da bayan sun kammala kalaci sai boka Dayyubul-Barmas ya zira hannun sa a aljihun rigar
sa ya ɗauko madubin tsafin sa ya shiga gudanar da bincike bisa halarar tsafin sa.

Shi kuwa shamsuddin tun Kafin ya shiga tantin ya ɗaura alwala yana shiga ya dauko dabino da
ruwan sa a cikin salka ya ɗan kimtsa cikin sa,

Sannan ya shimfida buzun sa ya shiga gudanar da Sallah, batare da kalli abincin da su lasmirat
suka kawo masa ba,

Amma a ɓangaren su aljani Huruful-labarus kuwa suna cikin yin rangadi a tsakanin tantunan ne
sai wani ɗaya daga cikin yaransa .mai suna Barbusa ya dubi abokin sa yace "yakai saltir wai
yanzu haka zamu zauna muna ji muna gani wannan yaro shamsuddin yana juya mu tamkar
yana sarrafa waina (masa) a cikin yanda
Me zai hana bazamu shammace su ba mu hallaka su mu kama gaban mu,

Baka tsoron mai girma Hamras zai aiko da wata musiba ta hallaka mu,

Koda jin wannan batu sai idanuwan saltir suka zazzaro ya dubi saltir cikin alamun tsananin
tsoro yace" A kul ɗin ka yakai aboki na kayi sani cewa tun ina yaro karami mahaifina ya
gargaɗeni akan irin waɗannan mutane ma'abota addinin musulunci yace a halin yanzu a duniya
babu hatsabibai kamar su

6 / 9