TAKOBIN DAUKAKA BOOK COMPELET BY MANSUR USMAN SUFI.pdf

Author :  Mansur Usman Sufi Category :  Arewa Pen

Chapter   7 / 9

18K to 21K   out of 24.6K words


Kafin saltir ya gama rufe bakin sa sai kawai su kaji wani sanyi gami daddaɗar iska ta mamaye
wajen kafin kace me

Gaba ɗayan su sun bungire kasa sun fara sharar barci har da minshari,

Sarauniya lasmirat, Sunaila da yaslir suma nauyin barcin su ya karu ainun,

Kuma wani irin gurnani mai ban tsoro ya mamaye wajen baki ɗaya.

Sa'adda wannan iska mai ɗan karan daɗi ta bugar dasu aljani Huruful-labarus, tare dasu
sarauniya lasmirat suka kama barci mai nauyin gaske kuma wani gurnani na mamaye wajen
sai,

Kwatsam bazato babu tsammani sai aljani Hafsul-Habarus ya bayyana a wajen,

Yayin da yayi arba dasu Huruful-labarus sai ya cika da matukar farin ciki kawai sai ya taƙarƙare
ya bushe da dariyar mugunta,

Sai da yayi dariyar ta ishe sa sannan ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa,

Kawai sai ya miƙa gabza gabzan hannayen sa domin ya ɗauko su aljani Huruful-labarus,

Yayin da rage saura kamu goma hannayen sa su isa sai wani mutum ya bayyana gaban sa
tsulum,

Ba wani bane face jarumi shamsuddin,

Hafsul-Habarus ya ja hannayen sa baya ya dubi shamsuddin cikin tsananin fushi yana mai daka
masa tsawa mai kama da saukar aradu

Nan take bishiyoyin dake dajin suka dunga karairayewa suna zube ƙasa, duwatsu suka dunga
bindiga suna farfashewa, kuma su lasmirat suka farfaɗo daga dogon barcin da suke yi suka fito
daga cikin tantunan su a firgice suna masu zare makaman su,

Sa'adda sarauniya lasmirat, Dayyubul-Barmas, yaslir, Sunaila, Huzmal, aljani Huruful-labarus
da yaran sa sukayi arba da aljani Hafsul-Habarus sai suka firgice suka zube kasa,

Sunaila, yaslir,da Huzmal suna masu sakin fitsari a wando saboda tsananin firgici,

Shi kansa boka Dayyubul-Barmas a matukar firgice yake,

Nan take a lokaci guda aljani Huruful-labarus ya tsuke bakin sa ya murtuke fuska,

Take komai na dajin ya samu dai dai tuwa

Cikin Wata irin kakkausar murya mai kama da kwaran kwatsa Yace"yakai wannan bil'adama
ma'abocin tsaurin idanu shin wane ne kai dazaka hanani zartar da umarnin shugaba mai duniya
sarki Hamras,

Yi maza ka amsa mini waɗannan tambayoyi kafin na ganar dakai kuskuren ka,

Sa'adda shamsuddin yaji wannan batu daga bakin aljani Hafsul-Habarus sai ya yi gyaran murya
yace" yakai wannan mushriki makiyin Allah kayi sani cewa babu wani mai daraja face
yakasance bawan Ubangijin musulunci mahalicci

Abin da nake so dakai shi ne ka kadaina bautawa wanin Allah ka dawo izuwa TAFARKIN
TSIRA,

Wato addanin Musulunci,idan kuwa kaƙi yanzun nan zan roƙi Ubangiji na ya bani nasara na
hallaka ka,

Koda jin wannan batu daga bakin shamsuddin sai Hafsul-Habarus ya fusata ainun, idanuwan sa
suka kaɗa sukayi jajur!

Saboda fushi har wani irin tiririn bakin hayaƙi na fita daga kofofin hancinsa,

Kawai sai Hafsul-Habarus ya zare wani makami a jikin sa,

Shi dai makamin yakasance dogo tamkar mashi, daga saman sa kawunan takobi ne guda biyu
ɗaya na zarto mai cako-cako ƙasan kuma ya na da siffa irin ta lauje wanda ido bai taɓa gani ba,

Tabbas wannan makami abin tsoro ga dukkan wanda yayi arba da shi,

Sannan ya taƙarƙare ya kwarara wawan ihu ya ruga izuwa kan shamsuddin,

Koda ganin hakan sai shamsuddin ya dunkule hannayen sa ya ruga kan Hafsul-Habarus aka
tari juna aka kacame da azababban yaƙi mai matukar tayar da hankali da ban tsoro,

Wohoho Hakika gaskiyar masu iya magana da suka ce,

Ranar bikin gwanaye sai wane da wane ne ke fitowa a taka rawa,

Kuma idan ana babbakar Giwa ba,a jin ƙaurin bera

Tabbas fadan da yafi karfin ka sai ka zamo da kallo,

Hakan ne yafaru da su sarauniya lasmirat,

Ba shiri su lasmirat suka rike tsaye suka runtuma da gudu izuwa cikin dajin , suka laɓe a bayan
waɗansu bishiyoyi suka hangen artabun da akeyi tsakanin shamsuddin da Aljani
Hafsul-Habarus,

Nan take su jarumi shamsuddin suka tashi hankalin duk wata halitta dake dajin ya kama girgiza
kasa ta dunga tsagewa tana zaftarewa bishiyoyi na faɗa wa cikin ta, duwatsu suka dinga
murginawa kan juna suna karo.

Wani abin mamaki da yafaru shine, duk yawan hare haren da Hafsul-Habarus ke kaiwa
shamsuddin yana samun nasarar zillewa koda sau ɗaya makami bai taɓa jikin sa ba,

Idan kuwa shamsuddin ya naushi wata gaɓa a jikin Hafsul-Habarus sai aji ya kwalla kara,.

Bakomai ne yasanya hakan ba sai domin duk sa'adda shamsuddin ya naushe san sai yaji wajen
tamakar an ƙonashi da ruwan zafi yana yi masa raɗaɗi da zugin tsiya,

Al'amarinn da yayi matukar bashi mamaki kenan bisa ganin yadda yakasa samun nasara akan
shamsuddin,

Shin wannan wane irin jarumi ne da za,ace na kasa samun nasara akansa alhali koda makami
bai riƙe ba , amsar tambayar da Hafsul-Habarus ya kasa bawa kansa kenan,

Kawai ya sake zage damtse yana cigaba da kai Hafsul-Habarus miyagun hare haren babu
ƙaƙƙautawa,

Daga can nesa su sarauniya lasmirat na hangen artabun da ake yi tsakanin ZARATAN
MAYAKAN biyu,

Sa,adda sukaga yadda Hafsul-Habarus ke yakasa samun nasara akan shamsuddin sai suka
cika da matukar mamaki da al,ajabi kuma suka tabbatar da cewa shamsuddin ya cika jarumin
kawarai mai karfin Allah na isa.

Nan take sarauniya lasmirat taji soyayyar jarumi shamsuddin takara shiga zuciyar ta,

Ita kanta Sunaila sai taji a cikin ranta cewa i na ma dai ace masoyin ta yana da jarumataka irin
ta shamsuddin

Abin da su duka biyun basu sani ba shine tsananin taimakon Ubangiji ne,

Ke ɗawainiya dashi bayin kansa bane,

Sai da shamsuddin da Hafsul-Habarus suka shafe Tsawon sa,a ɗaya da daƙika ɗari biyar suna
ɗauki ba daɗi batare Hafsul-Habarus ya samu nasarar lakutar jikin shamsuddin ba,

Nan fa Hafsul-Habarus ya sake fusata ainun ya haɗa da kai bugu da naushi hannu da kafa

Sa,adda shamsuddin ya fahimci cewa wankin hula zai kaishi dare sai ya cigaba da riƙon Allah a
zuciyar sa yana mai cewa,

Ya Ubangiji ka taimaki bawan ka mai rauni akan mushirikin bawan ka. Don matsayin annabin
ka,

Ai kuwa yana kammala hakan sai shamsuddin ya taƙarƙare ya ƙirɓawa Hafsul-Habarus naushi
a ciki,

Saboda karfin naushin sai da cikin Hafsul-Habarus ya yi ƙara fam fam! Tamkar an daki Tanki,

Ya faɗin ƙasa yana murginawa gami da turmutsutsu Cikin sa yana murɗawa,

Kafin yayi wani yunkurin jarumi shamsuddin ya sake ƙirɓa masa wani wawan naushin a cikin sa,
take. Cikin nasa yayi bindiga ya fashe tamkar an buga katuwar ganga, kayan cikin sa suka fito
waje jini ya dunga tsartuwa yana feshi yana malala a ƙasa tamkar an balle ƙorama,

Sa,adda su sarauniya lasmirat suka ga irin nasarar da shamsuddin ya samu sai suka fito daga
inda suke laɓe suna masu yi masa jinjina suna cewa

G ausheka GOGA SHA YAƘI,

SADAUKIN SADAUKAI

Ciwon idanun kananun kwari

JARMAI SHA YAƘI uban maza DODON MAZAJE

Amma boka Dayyubul-Barmas sai ya murtuke fuska tamkar an aiko masa Da sakon mutuwa,

Kafin su kai inda yake gangar jikin sa ta zagwanye ta narke ruwan ya tsotse a cikin ƙasa,

Suna karasowa sai shamsuddin ya dubesu yace fuskar sa cike da annuri yace " Yakamata
kowannen ku yaje ya kwanta a samu ishashshan barcin saboda tafiyar dake gaban su,

Koda gama faɗin hakan sai shamsuddin ya juya ya shiga izuwa tantin sa,

Take kowa ya shiga nasa tantin a ka cigaba da barci,









Acan birnin misra kuwa tun daga ranar da sarauniya lasmirat ta tafi izuwa ɗauko TAKOBIN
ƊAUKAKA domin ta samu damar ɗebo ruwan ma'ul-diya'u,

Waziri ukashat ya cigaba da tafiyar da sha,anain mulki bisa tsari da adalci,

Wata rana waziri ukashat na zaune a fada,

Wata kyakkyawar budurwa na zaune a gefen sa na dama cikin ado na keta raini ba wata ba ce
face gimbiya Hulaifat yar waziri ukashat,

A gefe guda kuma fadawa ne a zazzzaune bisa shimfiɗu na alfarma

fadar ta cika maƙil ana tafiyar da sha,anin mulki,

Kwatsam bazato babu tsammani sai kawai akaga wani waje ya zabtare a fadar ya rufta izuwa
kasa

Kwatsam sai ga wani narkekeken dodo ya fito,

Shi dai wannan dodo yakasance jibgegen basamude ,fuskar sa mummuna ce babu kyan gani

Hannayen sa tafka tafka ne tamkar bishiyar kuka,tafukan kuwa su na da faɗi tamakar faranti,
ƙafafuwan sa manya ne tamkar da dutse aka yi su, kirjin sa ya kumburo ya tara kwanji, kofofin
hancinsa manya ne idanuwan sa jajawur tamkar garwashi girman kowanne daga cikin su yakai
girman lemon zaƙi,
Tabbas wannan dodo ya cika abin tsoro domin babu wani jarumi da zai yi arba dashi face ya
firgice

Nan fa yazamana cewa fadar ta kaure da guje-guje gami da ifice-ificen jama'a

Cikin matukar tashin hankali waziri ukashat ya miƙe tsaye zumbur daga kan karagar sa ta mulki
yana mai zare zare takobin sa take fadawa da sauran dakarun dake fadar suka yi koyi dashi

Aka fara kallon kallo tsakanin su da dodon,

*****. *****. ****

Kashe gari tunda duku dukun safiya bayan su sarauniya lasmirat sun yi kalaci an kammala shiri
tsaf!

Sai kawai kowa ya bisa kan ɗaya daga cikin yaran aljani Huruful-labarus aka cigaba da tafiya
domin isa izuwa tsaunin SHAFRAS,

Tafiya kwanaki talatin kaɗai akayi aka iso tsaunin DARUL-SHAFRAS

a iya tsawon wannan tafiya babu abin da ke sanya wa atsayar da tafiya face idan jarumi
shamsuddin zai gudanar da ibadar sa,

Inda aka tsaya ɗin yakasance daji ne ma,abocin kwarjini daban tsoro,

Tsakanin su sarauniya lasmirat da inda tsaunin DARUL-SHAFRAS yake ake tazara mai yawa
don haka sai suka cika da tsananin mamaki bisa Ganin yadda tsaunin yakasance

Tsaunin DARUL-SHAFRAS yakasance mai matukar tsawo inda ace mutum zai kalle sa daga
nesa sai yaga cewa har ya shige cikin gajimare,

Babu wani ɗan itaciya da yayi tsiro a wajen face waɗansu irin duwatsu masu ɗauke da siffofin
bil,adama da dodanni masu ban tsoro

Sai da aka shafe tsawon lokaci a cikin wannan hali sai daga bisani boka Dayyubul-Barmas yayi
umarni aka tashi aka nufi tsaunin gadan gadan

Nan fa jarumi shamsuddin ya dunga kallon abubuwan kudirar Ubangiji na halittun sa da tajallin
sa iri daban daban,

Yayin da aka sauka a tsaunin sai kowa yasha jinin jikinsa kuma hankalin sa ya ɗugunzuma
ainun,

Bakomai ne yasanya su hakan sai bisa ganin yadda tsaunin DARUL-SHAFRAS yakasance

Daga sama tsaunin yakasance mai ɗauke da manyan gine gine da aka yi su da zallar duwatsun
wuta kirar mutanen farko mai ɗauke da manyan ɗakuna tamkar akwai wata halitta da ta taɓa
rayuwa a wajen

Babu wani waje da mutum zai ajiye ƙafar sa face akwai ƙasusuwan bil,adama ko wasu sassa
na jikin sa yana duk ta lulluɓe su,alamun dake nuna cewa wata halitta ta daɗe bata ziyarci
wajen ba,

A wasu lokutan sai kaga mutum an rataye da igiya har ya zagwanye yazamana kwarangwal,

Babu abin da zai firgita Mutum shine yadda tsaunin DARUL-SHAFRAS yakasance shiru tsit
tamkar babu wata halitta a cikin sa domin koda yan kananan tsuntsaye babu,

Nan fa hankalin kowa ya ɗugunzuma ainun, amma bisa mamaki sai kaga shamsuddin bai
razana ba

Nan fa su duka raya a ransu cewa shin menene yasanya shamsuddin bai razana da ganin
kwarjini tsaunin ba,

Amsar tambayoyin da suka kasa bawa kansu kenan

Boka Dayyubul-Barmas ne ya katse shirun da ya wanzu budar baki sannan yayi ajiyar zuciya ya
kawo gwaron numfashi yace

"Yaku abokanan tafiyata kuyi sani cewa mun iso tsaunin DARUL-SHAFRAS inda zamu ɗauki
ruwan ma'ul Daryalu,

Sai dai kafin hakan ina san na samar daku waɗansu dokoki

Da farko dole ne kowannen ku ya kiyaye amfani da dukkanin wani abu da danganci sihirin tsafi,

Abu na biyu kuwa shine dole ne kada wani ya shiga wani waje face yasanar dani na basa
umarni,





























Yana gama faɗin hakan sai ya juya ya dubi shamsuddin fuskar sa babu annuri tamkar an aiko
masa da SAƘON MUTUWA cikin kakkausar murya ya ce " yakai shamsuddin kada ka manta
alkawarin dake tsakanin mu dakai na fito rayuwar mu a lokacin da wata musiba ta taso mana
muka kasa tseratar da kan mu idan har ka gaza ceto rayuwar mu

Tabbas zamu yanke tafiyar mu daki domin hakan ya tabbatar mana cewa Ubangijin ka ya gaza
wajen taimakon ka,

Koda jin wannan batu sai jarumi shamsuddin ya yi murmushi yace"Da yardar Annabi mai daraja
Annabi Sallallahu alaihi Wasallama Ubangiji na bazai bani kunya ba,

Dajin hakan sai boka Dayyubul-Barmas ya zare wani makami a jikin sa ya kunna kai izuwa cikin
wani falo,

Sarauniya lasmirat, yaslir, Huzmal, Huruful-labarus da yaransa, da Sunaila tana mai gyara
rawanin ta suka mara masa baya , jarumi shamsuddin a ƙarshe har yazamana sun basa tazara
mai yawa,

Da shigar su izuwa cikin falon sai suka tarar yakasance makeken mai tsawo da faɗi ba'a iya
hango ƙarshen sa, sai suka ci-gaba da tafiya suna kallon abubuwan ban al'ajabi iri daban daban

Yar gajeriyar tafiya suka yi suka iso wata ƙasaitacciyar fada,

Fadar an ƙawata ta da mau,ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya,

Ko ina a fadar a tsaftace yake, tunda karagar mulki har na yan majalisa babu kowa akai

Nan fa kowa ya cika da matukar mamaki bisa ganin ƙawatuwar fadar,

Musamman sarauniya lasmirat da take ganin cewa idan aka kwatanta fadar ta da wannan fadar
ta tan bakomai ba ce face kango,

Koda koda a tarihi bata taɓa ganin fada mai ƙawatuwa da tsaruwa tamkar wannan fada ba,

Babu abin da yafi bawa su boka Dayyubul-Barmas mamaki kamar yadda aka shirya kayan
ciye-ciye da tanɗe-tanɗe a bisa wani kayataccen teburin na azurfa, kamshin abincin ya mamaye
fadar baki ɗaya, taimakar an haɗawa wani BASARAKE walima

Nan fa aljani Huzmal da Huruful-labarus suka fara tanɗar baki,har su na dalalar da yawu daga
bakin su basu sani ba saboda tsananin kwaɗayi,

Kafin su farga ɗaya daga cikin yaran aljani Huruful-labarus mai suna Barbusa ya ya faki idanun
su ya sunkuci wani katon faranti ɗaya mai ɗauke da wani farfesun naman tsuntsu yayi loma
ɗaya dashi ya tanɗe bakin sa

Tabbas rashin sani yafi dare duhu inda ace Barbusa yasan abinda zai faru da yayi hakuri da cin
wannan naman tsuntsu ya cigaba da dalarar da yawun sa saboda kwaɗayin abincin,

Domin haɗiye abincin nasa keda wuya sai kwatsam aka ga waɗansu jibga jibgan samudawan
muridai suna ratsowa daga bangon fadar suna fito wa, hannayen su ɗauke da miyagun
makamai, dangin gatari,al'amudi',majaujawa,takobi da mashi,

A dadin su yakai dubu hamsin da ɗoraya, Gaba ɗaya gurnanin muridan ya cika fadar baki ɗaya,

Muridan sun Kasan masu damatsa,suna rafka rafkan kawuna, suna da matukar kwarjini da
muni,duk sa'adda dayan su ya ajiye lafceciyar ƙafar sa a fadar sai kaji ƙasa ta amsa saboda
karfin takun,

Haƙika waɗannan muridai sun kasance ababan tsoro domin duk da irin dakewar zuciya irin ta
Boka Dayyubul-Barmas, lasmirat,Sunaila , yaslir sai suka ɗimauce, tamkar ace ƙyat suka zura
da gudu,aljani Huruful-labarus,saltir da Barbusa har sakin gudawa sukayi a wando saboda da
firgici,
Shi kansa jarumi shamsuddin a matukar razane yake kawai saboda addu'ar da yake ne
yasanya tsoro ya kau daga daga zuriyar sa ,

Nan fa nan fa aka fara kallon kallo tsakanin su Dayyubul-Barmas da muridan lokacin da
muridan suka kammala yi musu kawanya sai suka buɗe wata hanya a tsakiyar su ta yadda
mutum goma zasu iya tsaya a jere

Take wani gurnani ya dunga bayyana a hanyar gami da karfin takun sawaye,

Sannu a hankali sautin yana ƙaruwa jim kaɗan sai ga wani narkekeken muridi ya bayyana,

Shin dai muridin yafi sauran girma da kwarjini sannan ya na ɗauke da rigar sarauta a jikin sa
alamun dake nuna cewa shine shugaban muridan,

Shugaban muridan ya karewa su Boka Dayyubul-Barmas kallo, kawai sai ya bushe da dariyar
mugunta mai kama da haniniyar doki,

Sannan daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da SAKON MUTUWA

Sannan ya buɗe wawaken bakin sa daya fi kama da bakin rijiya saboda girman sa cikin
kakkausar murya

" Lalle marhaban da zuwa fadar uban muridai KIRMALU IBN SHAMSHAN,

Yaku wadannan bil'adama kuyi sani cewa yau fiye da shekaru dubu shida babu wata halitta da
ta taɓa zuwa tsauni na DARUL-SHAFRAS sai ayi

Na tabbata cewa abinda ya kawo ku baya rasa nasaba da Ruwan ma'ul Hayat

Ina so kuyi sani cewa kun kawo kanku gidan musiba da bala'o'i na rantse da gemun mai girma
Baddadul-sihir ɗayan ku bazai sauka kasan wannan tsauni a raye ba,

Domin hakan ya zamo darasi ga bil'adama masu taurin kanki da wauta irin yaƙi,

Koda shugaban muridan duniya KIRMALU IBN SHAMSHAN yazo nan azancen sa Sai ya sake
bushe da dariyar mugunta a karo na biyu

Koda can sai ya murtuke fuska kawai sai ya dakawa yaransa tsawa dake nuna su afkawa su
boka Dayyubul-Barmas

Take yaran suka ɗauki kansu suna ihu da kururuwa mai firgitar wa

Nan fa ana haduwa aka ruguntsume da azababban yaƙi mai matukar muni ban tsoro gami da
tashin hankali,













Al'amarin sarki Hamras kuwa tun sa,adda da ya tura hadimin aljanin sa wato Huruful-labarus
domin ya ɗauko masa gashin kan sarauniya lasmirat da boka Dayyubul-Barmas

7 / 9