Author : Mansur Usman Sufi Category : Arewa Pen
Abinda Ya Kawo izuwa wannan birni nawa
Alfarmar da nake nema a wajen ka ina so ka biyo ni izuwa gidan sarauta domin ina so mu
tattaunawa wata muhimmiyar magana
Yakai wannan jarumi kayi sani cewa kai ne jarumi na farko a rayuwa ta dana taɓa fafata yaƙi da
shi har ya samu nasarar kai ni kasa
Sa'adda sarauniya lasmirat ta zo nan a tambayar ta sai saurayin ya dube ta yace
" Ni dai da farko suna na yaslir ibn Hulzal na fito ne daga wata nahiya da ake yiwa laƙabi da
Nashmir
Game da Alfarma da kika nema a waje na kuwa bazan amince da ita ba
Sai kin yarda kuma kinyi mini alkawarin cewa zaki dunga daraja kowane ɗan adam,
Ma'ana za ki dai na azabtar da mutane da zaluntarsu,
Sa'adda saurayi yaslir ibn Hulzal yazo nan a zancen sa sai sarauniya lasmirat ta zurfafa izuwa
kogin tunani
Sa'adda talakawa da sauran jama'ar kasuwar suka ga yadda sarauniya lasmirat ta ƙasƙanta
kanta a gaban saurayin sai suka cika da matukar mamaki da al,ajabi domin fiye da shekaru
masu yawa hakan bai taɓa faruwa tunda lasmirat ta hau bisa karagar mulki
Daga can sai ta ɗago da kanta da dubi saurayi yaslir tace"na amince da wannan sharaɗi naka
yakai wannan jarumi,
Koda gama faɗin hakan sai sarauniyar lasmirat ta yiwa wani badakare inkiya da hannu kamar
badakaren yasan abinda take nufi sai kawai ya janyo waɗansu fafaren dawakai ya iso gaban ta
ya risina ya rike ta linzamin dokin ɗaya,ta kama ta hau.
Ta na mai yiwa yaslir nuni da yau bisa ɗayan dokin take ya kama dokin ya hau
A lokaci guda suka sakarwa dawakan linzami sauran tsirarun dakarun suka mara musu baya a
ka cigaba da tafiya,
Jama'a suka bisu da kallo cike da tsananin mamaki
****
A can kololuwar sararin samaniya inda Allah (s,w,t) yayiwa halittu iyaka a nanne sarki Hamras
ibn zulaibu ya sanya aka gina masa ƙasaitacciyar fadar sa.
Wacce masana suka tabbatar da cewa babu wata fada data Kaita ƙawatuwa da kayan alatun jin
daɗin rayuwar duniya.
Domin an ce sai da bakaken aljanu guda dubu shida suka shafe shekaru goma suna aikin ginin
fadar dare da rana babu sassauci.
Binciken bokaye da matsafa ya tabbatar da cewa Sarki Hamras yakasance jinin wata Kabila da
ake kira da Banu lahzar.
Waɗanda aka tabbatar dacewa sun mamaye rabin sarakunan duniya,
A rayuwar sarki himras fiye da abu uku, yana matukar adawar ace akwai wani sarki a duniya da
ya fisa KARFIN MULKI
Abu na biyu kuma shine ya tsani ma'abota addinin musulunci.
Bakomai yasanaya hakan sai domin mahaifinsa sarki zulaibu ya mutu ne sakamakon kwabza
yaki da wani jarumi ma, abocin addinin Musulunci,
Akwai waɗansu muhimman sirrikan tsafi da mahaifin sa zai sanar da shi waɗanda da zarar ya
sanar dashi ɗin zai mulki duniya baki ɗaya,
Amma sai ya zamana waccan jarumin ya hallaka sa batare da ya sanar dashi sirrikan tsafin ba,
Abu na karshe da sarki Himras ya tsana shi ne wani gawurtaccen jarumin ma,abocin addinin
Musulunci,wanda binciken da yayi ya tabbatar masa da cewa shine zai kawo karshen mulkin sa
a doran kasa.
Lokacin da sarki Himras ya ga cewa a halin yanzu basa da abokan gaba da suka huce
ma'abota addinin Musulunci sai ya zurfafa izuwa cikin halarar tsafin sa domin ya gano wata
hanya zai bi ya kawar da musulmi kuma ya mulki duniya baki ɗaya,
Abin da bincike ya tabbatar masa shine bazai taɓa cika wannan buri na sa ba face ya mallaki
wata tsafaffiyar takobi mai suna TAKOBIN ƊAUKAKA
Amma koda ya mallaki takobin bazai samu nasarar sarrafa takobin ba face ya haɗiye gashin
kan waɗansu mutum biyu,
Waɗannan mutum ba wasu ba ne face" sarauniya lasmirat da boka Dayyubul-Barmas,
Sa'adda sarki Hamras yaga gagarumin aikin dake gabansa na mallakar TAKOBIN ƊAUKAKA,
da silin gashin boka Dayyubul-Barmas da sarauniya lasmirat sai ya umarci waɗansu gwarazan
dakarun aljanun sa domin su yanko masa gashin boka Dayyubul-Barmas da sarauniya lasmirat
Bisa jagorancin aljani Huruful-labarus.
Aljani Huruful-labarus yakasance GWARZON MAYAKI da masu Bincike suka tabbatar dacewa a
jinsin baƙaƙen aljanu babu mai karfin damtsen sa.
Bayan Sarki Hamras ya tura Aljani Huruful-labarus sai ya shiga shiri sai da ya kwana arba'in ya
na tsuma kansa da tsumin tsafi, sai ya fito ya shiga izuwa duniya domin mallakar TAKOBIN
ƊAUKAKA.
Al'amarin saurayi yaslir da sarauniya lasmirat kuwa, tafiyar daƙika arba'in kacal suka yi suka
iso izuwa gidan sarauta
Gidan sarautar yakasance kasaitacce mai girma da faɗi tamkar gari guda, gaba ɗaya katangun
ginin gidan anyi su ne da wani irin farin gilashi
Babu wani BASARAKE ko attajiri dazai yi arba da wannan gidan sarauta face ya Zamo
cikekken ɗan ƙauye,
Tsayawa masalta tsaruwar gidan sarautar zai iya zamo wa ƙauyanci sai dai abinda idanu suka
gani kawai
Duk inda mutum ya duba bayi ne hade da kuyangi
da barori na kai komo suna hadima
Duk inda sarauniyar lasmirat da saurayi yaslir suka gufta a cikin gidan sarautar sai dai kaga
jama'a na zubewa kasa suna kwasar gaisuwa cikin girmamawa,
Lokacin da aka iso wani bangare mai ɗauke da manyan falo guda uku haɗe da kewayen wanka,
kayan more rayuwa sai
Waɗansu tsala-tsalan kuyangi na kai komo a cikin turakar,
Da sauri wata dattijuwar mata mai kimanin shekaru hamsin ta rugo izuwa inda sarauniyar
lasmirat take ta zube ƙasa bisa gwiwoyin ta ta kwashi gaisuwa
Bakin ta na kyarma kuma kanta a sunkuye tace "me kike da buƙata ya shugaba ta?
Lasmirat ta dube ta tace" yake zarima kiyi sani cewa bakomai nake da bukata ba face ina so
wannan baƙo dake tare da ni a basa kulawa da dukkanin wani abu da ya buƙata kiyi sani cewa
yana da matukar muhimmanci agareni
Koda jin wannan batu sai zarima ta sake risina wa tace angama ya shugabata bin umarnin ki ai
shi ne ibada ta,
Tana gama faɗin hakan ta mike tsaye tana Mai yiwa saurayi yaslir nuni da ya biyo bayan ta
Batare da bata lokaci ba yaslir ya kama linzamin dokin sa ya sauko sannan ya rufa mata baya
Amma koda ya waiga ya haɗa idanu da sarauniya lasmirat sai yaga tana yi masa wani
mayataccen kallo mai ɗauke da alamar tambaya.
Cikin hanzari sarauniya lasmirat ta juya taɗa linzamin dokin ta ta nufi bangaren da turakar ta
take,
Lokacin da isa sai ta shiga izuwa kewaye ta tsala wanka sannan ta shiga tsaɓa ado tana mai
fuskantar wani madubi
Tana cikin wannan hali ne sai ta jiyo motsin tafiya a bayan ta
Koda ta waiga sai tayi arba da shi ba wani bane face wazirin ta mai suna ukashat
Waziri ukashat yakasance dattijo mai yawan shekaru amma duk da hakan babu gajiya a tare da
jikin sa,
Yana da kaurin jiki, dogo ne tsaka-tsaki,yana da tarin gemu da ƙasumba fararen sol,
Fuskar sa tana da kwarjini
Ukashat yakasance ɗan uwa a wajen mahaifin lasmirat wato sarki kazmal kuma babban aminin
sa, bisa wannan dalili ne yasanya duk abinda lasmirat zata zartar sai ta nemi shawarar waziri
ukashat,
Bisa al'ada duk sa'adda waziri ukashat zai gana da sarauniya lasmirat yana sanya ayi masa
iso,kuma zai shigo ne fuskar sa cike da annuri
Amma a wannan karon sai ga fuskar sa a murtke babu annuri tamkar an aiko masa da saƙon
mutuwa,
Kawai sai ya zaune a bisa wata kujera dake fuskantar lasmirat ya dube ta cikin tsananin fushi
yace" yake lasmirat shin menene yasanaya za ki karrama wanda ya wulakanta ki a gaban
talakawa?.
Tabbas hakan zubar da darajar wannan masarauta ta mu ne da muka gada tun iyaye da
kakanni,
Shin yanzu da wane irin idanu zamu kalli sauran sarakuna abokan gabar mu?
Wai shin ma bakya tunanin cewa wannan saurayi ɗaya daga cikin abokan gaba ne yayi ɓadda
kama domin ya yaudare ki?
Koda jin wannan tambaya daga bakin waziri ukashat sai sarauniya lasmirat ta dube sa a nutse
tace"yakai waziri kayi sani cewa ko kaɗan bana taɓa da nasanin karrama wannan saurayi kuma
jiki na ya bani cewa tabbas bazai cutar da Ni ba, hakika zai zamo mai amfani a gare ni.
Ukashat ya katse ta ta hanyar ɗaga mata hannu yace " Haƙiƙa ke yarinya ce, tabbatas Abin da
Babba ya hango yaro ko ya taka tsani bazai iya gani ba.
Ban yi mamakin maganar ki domin na fahimci cewa tsananin kauna da soyayyar wannan
saurayi ce ta makantar da idanuwan ki, ta sanya har kika manta da burin zuri'armu na kare
martabar wannan masarauta,
Koda wannan batu daga bakin ukashat sai sarauniya lasmirat ta fusata ainun ta dakawa
matsawa ta dube sa tace" yakai ukashat kayi sani cewa ni nake da ikon bayar da umarni a
wannan masarauta don haka abin da naga ya dace shi zan aiwatar,
Tana gama faɗin hakan sai ta miƙe tsaye ta fice daga cikin turkar ta bar waziri ukashat a zaune
Cikin alamun tsantsar damuwa waziri ya mike tsaye ya fice daga turakar zuciyar sa cike da
takaici.
Da shigar saurayi yaslir izuwa cikin turakar, sai ya tarar turakar takasan ce ƙasaitacciya da aka
ƙawata ta da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin jin daɗin rayuwar duniya.
Gaba ɗaya turakar shimfiɗe take da wani koren kilishi mai taushin gaske,
Bayan yaslir ya fito daga kewayen wanka wani wanzami yayi masa gyaran fuska da saje, sai
wata kuyanga ta kawo masa waɗansu fararen tufafi masu taushi ya sanya a jikin sa,
Nan take tsakanin kyawun sa ya fito fili ƙarara, kawai sai ya nufi teburin da aka tanadar masa
abinci da abin sha ya shiga kimtsa cikin sa,
Bayan ya kammala ne da yake a wannan lokaci duhun dare ya fara Kawo kai,
Sai ya kunna fitulun dake turakar ta kaure da haske,
Sannnan ya zauna a bisa kan gadon sa kuma ya zurfafa izuwa kogin tunani,
Yana cikin haka ne sai yaji an turo kofar shigowa turakar
Ai kuwa kofar na buɗewa sai ya yi arba da ita ba wata ba ce face sarauniya lasmirat ta caɓa
ado wani irin daddaɗan ƙamshi na tashi daga jikin ta.
Cikin Wata irin tafiya mai ɗaukar hankalin duk wani ɗa namiji,ta nufi wata ƙasaitacciyar kujera
dake fuskantar yaslir ta zauna a kan ta,
Cikin annurin fuska ta dubi yaslir tace"yakai yaslir kafin mu kai ga tattaunawa abinda ya taramu
anan Yana da kyau ka sanar dani labarin rayuwar ka.
Koda jin wannan tambaya sai idanun yaslir su ka ciki da kwalla ya dubi lasmirat yace" ya
sarauniyar kyawu shin ina dalilin son kiji labarin rayuwa ta?
Lasmirat ta numfasa tace"Domin sanin labarin ka ya na da matukar muhimmanci a gareni,
Yaslir ya yi gyaran murya a karo na biyu sannan yafara dacewa
***
Kimanin shekaru arba'in baya anyi wani ƙauye da ake kira da suna Darul-Na'am.
Gari ne mai ɗauke da arzikin noma, kiwo, Sarkin dake mulkin kauyen yakasance adali mai
tausayin talakawa
Ana kiransa da suna Abu-salimat, Abu-salimat yakasance GWARZON MAYAKI mai tarwatsa
maza a filin daga,
Yana da ƴa guda ɗaya kyakkyawa tagaban kwatance ana kiran ta suna salimat ta gaji mahaifin
ta a kyawawan halayen mahaifin ta.
Ƙauyen Darul-Na'am na karkashin mulkin wata babbar masarauta da wani kasaitaccen sarki ke
mulki mai suna Husnalu ibn kailub,
Sarki Husnalu yakasance GWARZON MATSAFI, kuma mashahurin mayaki, daɗin daɗawa
kuma yakasance AZZALUMI nagaban kwatance,
Ƙwace,kashe rayukan al'umma,tare da farauce dukiyoyin su ba a bakin komai yake a wajen sa
ba,
A rayuwar sarki Husnalu babu abin da yake tsananin kauna fiye da ɗansa guda ɗaya mai suna
Hatmal,
Yarima Hatmal yakasance ɗan lele a wajen sarki Husnalu baya son ɓacin ransa ko kaɗan,
Bisa al'adar Sarki Husnalu duk bayan shekara ɗaya sarakunan dake ƙarƙashin ikon sa kan biya
sa haraji na dukiya da adadin ta yakai dinare dubu ɗari tara, gami da kayan amfanin gona da
dabbobin ni'ima
Tsakani na da gimbiya salimat akwai soyayya mai karfi, kasancewar mahaifina shi ne wazirin
mahaifin ta,tun muna yara ƙanana muke kaunar juna.
****
Wata rana daga cikin ranakun da sarakunan ke kaiwa sarki Husnalu haraji, kamar yadda aka
saba duk shekara,
Sai yazamana cewa a wannan shekara anyi tafiyar tare da ni da masoyayi ta gimbiya salimat,
Bayan dukkanin sarakunan sun kammala hallara a fada,
Bayan shiru da ya mamaye fadar na ɗan wani lokaci sai aka hango sarki Husnalu da yarima
Hatmal sun shigo fadar, suna sanye cikin suturu iri ɗaya hatta takalmin dake kafar su iri ɗaya
ne,
Koda jama'a suka hango sarki sai suka miƙe tsaye domin girmama a gare su,
Kai tsaye sarki Husnalu da yarima Hatmal suka huce izuwa inda karagar mulki take suka zauna
a tare,
Sannan sauran jama'a suka zauna, batare da bata lokaci ba sarakunan suka dunga tashi daga
wajen zaman su suna zuwa gaban na Husnalu suka kwasar gaisuwa sannan su gabatar da
harajin su da jama'ar da suka yi musu rakiya
Sarki na farko da ya gabatar da harajin da ana kiransa da suna zulaibu, yana mulkin wani ɗan
ƙaramin gari mai suna madinatul-shaswal,
A gaba ɗaya sarakunan da suka hallara a fadar babu wanda yakai zulaibu yawan shekaru da
kuma dadewa akan karagar mulki,
Sai da sarakuna biyar suka gabatar da harajin sannan aka iso kan sarki Abu-salimat,
Abu-salimat ya mike tsaye ni da gimbiya salimat muka mara masa baya, dakaru na biye da mu
ɗauke da akwatin dinare gami da kayan amfanin gona, har mu ka isa inda karagar mulki take,
muka zube ƙasa muka kwashi gaisuwa muna masu sunkuyar da kawunan mu.
Kawai sai waɗansu dakaru daban a fadar suka karɓi wadannan akwatin dinare suka lissafa
kuma suka bincike kayan gonar suka tabbatar da ingancin su sannan suka ɗauke suka fice
daga fadar,
Ana cikin wannan hali ne na ɗan saci kallon yarima Hatmal ai kuwa sai na ga ya ƙurawa
gimbiya salimat idanu yana mai yi mata wani irin kallo daya sanya hantar ciki na ya kaɗa, Ku
ma tsoro ya kamani.
Domin kallon da naga Yarima Hatmal na yi mita kallo ne ma nuna kamuwa da soyayya.
Jikina a ssnyaye na mayar da kai na kasa, sannan sarki Husnalu ya Umarce mu da mu fice
daga fadar,
Cikin hanzar sarki sarki Abu-salimat ya miƙe tsaye muka rufa masa baya muka fice daga fadar
Fitowar mu keda wuya sai muka fara shirye-shiryen komawa izuwa ƙauyen Darul-Na'am
Bayan an kammala ne muka hau bisa dawakan mu muka fice daga kasar Baitul-sharhal muka
nufi hanyar da zata sadamu da ƙauyen Darul-Na'am,
A wannan lokaci sarki Abu-salimat ne akan gaba tare da wani hadimin sa mai suna Haimar
suna hirarrakin su cikin nishadi,
Ni da salimat muna hira irin ta masoya, ana cikin wannan hali ne gimbiya salimat ta dube ni
tace"ya masoyi na kuma hasken rayuwa ta shin nayi maka wata tambaya mana
Cikin annurin fuska nace faɗi tambayar ki ya abar kauna ta
Salimat tayi ajiyar zuciya ta ce " shin a halin yanzu yaya matsayin soyayya ta yake a zuciyar
ka?
Koda jin wannan tambaya sai na tuntsire da dariya na dubi lasmirat nace " shin kina kina
tantama ne akan matsayin ki a rai na ko kuea.
A,a kawai ina so naji matsayi na ne
Salimat ta faɗa fuskar ta cike da annuri,.
Murmushi nayi a karo na biyu nace" Ai matsayin ki a waje na tamkar hanta da jini ne domin
babu abin da zai raba tsakanin mu face mutuwa,
Salimat tayi murmushin jin daɗi tace " Ni kuwa ka zame mini tamkar numfashi a rayuwa ta,
Nan take mu duka biyun muka fashe da dariyar farin ciki
Ana cikin wannan hali ne muka jiyo alamun takun sawaye a bayan mu,
Cikin firgici muka ja linzamin dawakan mu muka tsaya koda muka wai ga sai muka yi arba da
waɗansu ZARATAN DAKARU masu matukar yawa
Shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matukar kwarjini daban tsoro,
Har mun yunkura zamu zare takubban mu sai sarki Abu-salimat yayi mana nuni da mu dakata
Bisa lura da yayi cewa basu bane dakarun face na sarki Husnalu
Sannu a hankali dakarun suka iso har izuwa inda muke suka yiwa dawakan su Turkiya,
Sarki Abu-salimat ya dubi wani garjejen kato mai kirar samudawan farko wanda da alama shine
shugaban dakarun yace dasshi" yakai muraizu shin wane saƙo kuke tafe dashi izuwa gare mu
ina fatan dai bamu saɓawa mai girma Husnalu ba,
Sadauki muraizu ya bushe da dariyar mugunta mai kama da kukan jaki daga bisani ya murtuke
fuska tamkar an masa da saƙon mutuwa,
Cikin Wata irin kakkausar murya yace" ya kai Abu-salimat kayi sani cewa bakomai ne ke tafe da
mu ba sai domin ka bamu yar ka salimat mu Kaita izuwa ga sarki saboda ɗan sa Yarima Hatmal
ya kamu da soyayyar ta kuma yana so ne ya aure ta
Cikin matukar kaduwa Abu-salimat ya dubi muraizu a lokacin da idanun sa suka zazzaro yace"
shin wace irin maganar banza kake yi yakai muraizu anya