Author : Pretty Sk Category : Hausa Read
ga ƴan gidan, ranar Ummee tasha kuka, amma saboda tasan ba da gangan ya yi ba sai ta sauka daga fushin. Amma wunin yau kuwa, babu annuri a tare da ita, sai ya ji duk babu daɗi, so yake zuwa an jima ya leƙata sai ya ƙara ba ta haƙuri.)
“M.D.” jin an kira sunansa babu sakayawa ya sa ya kalla A.G dake nufosa cikin fusata da ɓacin rai.
Kaf gidan babu mai kiran sunan sa saboda sunana Baba Giɗoɗa ne, shi yasa yake da farin jini, wasu sukan danganta hakan sunan da ci ne.
Miƙewa Ayan ya yi, dai-dai nan A.G ya iso gabansa yana wani muzurai kamar damusa.
Dama sam ba sa shiri, ko gaisawa ba ta wani haɗasu duk da zasu aura ƙannan juna ne.
“Akan me yasa ka fasa auren Ruma? Eh akan me yasa? Wannan ai rashin mutumci ne, yarinya tun yaushe take sonka duk abin da kake mata haka take ci gaba da sonka amma a yau wai an sauke auren ku!!.” ya kai nan kaman wanda zai buga Ayan.
Tsayinsu ɗaya amma Ayan ya fi A.G cika, da haiba, amma bayan wannan komai suna da shi ne zaratan maza, jarumai masu siffar ƙarfi da jarumta.
Ayan kuwa murmushi ya yi mai sanyi sannan ya ce.
“Abbeey (Bana Yusuf) da kansa ya ce anfasa, dama ni ba so nake ba, kuma da kake cewa tuntuni take sona, shin ni na aiketa? Na fita hakƙinta tun da tasan bana sonta......”
“Hmmmmm nima na fasa auren ƙanwarka!.” ya faɗa duk da yana mugun son Sarah.
“Wallahi da na fi kowa murna, kai kanka kasan ba sanka take ba. Hmmm wannan labarin ne mai daɗi, Bara na je na sanar ma Sarah.” da haka ya kewayeshi ya nufa Main door.
Ayan be son ya jima yana magana da A.G dan zasu samu babban matsala, A.G akwai shi da naci, shi kuma be son maimaita abu ɗaya, kuma yasan A.G komai zai faru sai ya auri Sarah Dan ba ƙaramin sonta yake ba. Murmushi kawai ya yi ya shiga ciki.
A.G ƙafa yasa ya buge kujerar dake gabansa, ɗan huci ya fara yi kaman wanda ya ci gudu, sai kuma ya zauna yana tunanin ta ina zai fara.
“Tunda ba ka so, to wallahi sai na aureta............eh sai na aureta......Ina son Sarah amma saboda kai Ayan zan ƙuntata mata, zan sa ta sha wahala sosai, sai daga baya na ba ta haƙuri, amma yarda Ƙanwata ta yi kuka, haka zan sanya ta ka ƙanwa.” ya faɗa cikin ɗaukan alwashi sannan ta furzar da iska daga bakinsa..
******************
Ummee ce zaune kan prayer mat tana kallon Yaranta su huɗu da Allah ya ba ta, ita da Ammee sune kawai masu yara huɗu-huɗu, amma sauran suna da yawa. Dan Baba Musa yaransa 9 maza huɗu mata biyar, duk sun yi aure a cikin gidan.
Sannan shima Baba Yunus yaransa 8, 5 sun yi aure , sai Namiji ɗaya Fahad da kuma mata biyu amma su ba su girma sosai ba.
Baba Yunus matansa biyu, haka Baba Musa shima, amma Abba matarsa ta biyun ta rasu tun shekarun baya, yarinyarta ɗaya, ƙanwar Sarah ce amma ita booding school.
Rufaida ita ce babba a ɗakin ta aura Yaron Baban Musa na farko, sai Abdulrahman shi kuma ƴar ɗakin Baba Yunus ya aura, sai Ayan da kuma Sarah.
Duk suna zaune jikinsu a mace da abin da ke faruwa.
“Ummee...." Da Sauri Ummee ta ɗaga mai hannu alamun ya yi shuru.
Shurun ya yi yana kallon ƙasa.
“Ni ba wai auren wata ne ban so ba, kai yanzu har kana fatan ka auro wata ta shigo gidan nan?...........kai yanzu idan ka kawo ƴar mutane nan gidan ba ka cuce ta ba?............idan kana kusa babu wanda zai yi mata komai, amma idan ka fita ba?........mu kanmu ya muke a cikin gidan nan..........sannan abubuwan nan da suka faru kowa ransa ya ɓaci da kai sosai, hatta Abba shiru kawai ya yi, ni dai da ka ji nawa ka aura Ruma ɗin, ko dan ita maiyuwa mu samu wata iska mai daɗi a gidan.” ta kai tana jin babu daɗi, sannan ta ci gaba.
“Kamar yarda Abbanku ya ce............*Rabo*, shine zai kawo A'isha gidan nan. Ina fatan Allah ya baku zuri'a ɗayyiba.” da haka ta miƙe ta shige room ɗin ta.
Jikinsu duk ya yi sanyi, tabbas a gaba ɗaya gidan suna samun takura da matsi, dan ma suna da baki shine suke san iska.
Sai gashi Ayan ya rikito musu babban aiki.
“Ni yanzu Sarah na ke ji...........A ganin su Ammee za su bar maganar nan ne? Za su iya ɗaukan fansa akan Sarah." Rufaida ta faɗa cikin damuwa.
“Anya Ahmad zai iya bari a cutar da ita? Yana sonta sosai.” faɗin Abdulrahman sai Ayan ya ce.
“Hakane, amma kuma ba wani zama yake ba. Sai dai mu ai muna nan.” ya faɗa yana riƙo hannun Sarah.
“Yaya Ayan, karku damu Ni na yarda da mutum ba zai tsallake ƙaddarar sa ba. Yanzu dai gobe ne auren na ka ko?.” sai ya yi murmushi yana mai ɗaga mata kai.
“Angon da babu shiri, gidan ma kaman ba biki ba.........”
“Maman Hibba (Rufaida) shi kansa angon ba wani natsuwa ga rai ba. Fatana a kawo amarya lafiya ba tare da anyi rikici ba.”
“Ameen Sarah.” da haka suka sauya hiran akan na bikin duk da babu abin da za'a yi sai dai walima, haka dai suka tsara kuma suna fatan komai ya tafi lafiya dan sunsan ƴan gidan nan balle wannan shine karo na farko da za'a kawo mace cikin gidan.........✍️
END.
> Ya Allah 😓, hmmmm ba zance komai ba gaskiya.
> Nifa har yanzu ba mu shiga labarin ba, wasa kawai muke yi 😬😬😬.
> Typing mood 😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩😩🥴.
A nan zan katse muku dan kar na baku cittan da yawa. Sai dai ku sani bamu yi komai a labarin ba.
1. Shin ya rayuwar A'isha da Ayan za ta kasance a *GIƊAƊO MANSION* 🔥.
2. Ya *Ƴar NOLLYWOOD* 🔥 ne? Kusan dramer da zai biyo baya kuwa..........Za ta yi? Ta yaya? Idan ta yi mai zai biyo baya?........kai jama'a ku dai jiraye Ni a book 2.
Ina faɗa musu kwanan Zafin na sa daban ne, dan 1 bisa 5 muka yi, wannan duk sharan fage ne, ainihin cittar yana book 2.
BOOK TWO IS FIVE HUNDRED ONLY ₦500.
Ga Mai so ya min maganan direct.......
08126151523/07038436703
Pretty Sk ce 😁🥰🥰🥰🥰🥰.
I love You All my FAN'S 😘.
Akwai wani book da zan sadaukarwa wa ku insha Allah mai suna SAKEENAT 😓, ba zan ce komai ba ku dai nema kawai 👌👌👌👌❤️
*SAKEENAT ABDULLAHI ✍️😁*
```TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!
Na Book 2.```
_________ _GIƊAƊO MANSION_
Wannan daren akwai jama'ar da suka kasa barci, wasu sun yi amma ba na daɗin rai ba, duk da akan abin da ya faru, mutane da yawa sun shirya tarwatsa farin cikin da ya rage ma Ummee da Ayan, sun shirya hargitsa rayuwar ƙaruwar da ya kawo, sun shirya haka tuggu iri-iri a cikin gidan, da dama kowa ya kwanta rai a ɓace, ya yin da suke tunanin Ayan yana can shi da ƴar iskan ƙaruwarsa suna jin daɗin juna..........✍️
________“Uhmmm dama ina da sha'awar film ne.......duk da a yanzu karatu nake amma ina so.........shine na ce ba ra na tambaya ke. ” ina tura mai ya gani dan haka na gyara zama na sosai ina jiran amsarsa.
“Ok, sai dai ni ban san wani manya a fina-finan kannywood ba, kinsa Ni NOLLYWOOD nake yi, amma zan bincika miki.”
Murmushi na yi ina tura mai.
“Sir A.G, NOLLYWOOD ɗin nake so.”........✍️
______“Ƙanwata, ai na yi fushi ace ba ki ta ɓa nema na a waya ba sai yau, ko gaisuwa ai.......” da sauri ya ji ta katseshi cike da masifa tana cewa.
“Ni ba gaisuwa na kira mu yi ba. A yanzu kai miji ne ga Yayata, to Kira na yi dan na yi maka fashin ɓaƙi, nasan ba lallai ka gane hausan ba idan A'isha ta faɗa maka........Amana na baka ita, ka kula da ita fiye da komai, ka sanyata farin ciki a kodayaushe, hakan zai faranta min, amma idan wani ya sanyata kuka hmmmmmm to ta na da mai kare mata wato Ni.” tana kai wa nan ta katse kiran..........✍️
________
(_Assalamu Alaikum, Barka da wannan lokacin A.G.....sunana Inayah maybe ka manta amma kai ka ban number ka. PLS akwai maganar da nake so mu yi is very important.... thanks.-) ............✍️
_________
*Inayah*
Na rasa meke min daɗi, nasan yau Yayata za ta sha kuka sosai, shi yasa ni fa banson na yi aure, haka kurin a rabani da iyaye ne, na koma wani gidan, cikin wani family ɗin, na zama kamar mai aiki, miji ya min duk abinda yake so, ya kwana da ni kuma na tashi na yi mai girki.......hmmm shiyasa ban kawo aure a jerin rayuwata sam.........✍️
_________“I'm fine the Star of NOLLYWOOD.” ganin yana online ya sa na koma na kwanta ina jiran reply ɗin sa. Ganin yana on typing yasa na ji wani sanyi yana ratsani sosai, murmushi ya ƙi barin fuskanta, sai na ji duk na ƙosa na ga saƙon da zai turo min....................✍️
_______“To ki faɗa akan menene zan yi alƙawarin.”
“So nake ki yi min alƙawari, idan har wani abu ya sameki mara daɗi da mai daɗi za ki faɗa min, bance da sirrin aurenki ba, amma duk abin da ya kamata na sani, to ki faɗa min. A family house aka ce za ki zauna. Maybe akwai wanda za su yi kishi da ƙyawun da Allah ya miki. To Ni dai duk uban da ya shiga harkan ki, ki faɗa min, zan ji da kowa, nan da 8 month zan dawo, to a gidan ki zan cinye hutun, komai da za'a miki kawai ki tara in na zo zan ji da komai, dan duk wanda ya taɓa ki dole ne yi mai wankin babban bargo.” A'isha murmushi ta yi mai sauti.
“Sai aka ce miki kowa ne irin ki, kowa ne mai neman faɗa. Kai wallahi na za ci wani abun ne za ki ce.”...........
Jama'a mudai haɗu kawai____________₦500 ONLY.
8126151523-Opay number.
Sakina Abdullahi 😁👌🥰🥰🥰🥰🥰🥰
*📢 Assalamu Alaikum Everyone!*
Muna farin cikin sanar da ku cewa za mu *buɗe Paid Group* na littafin *ƳAR NOLLYWOOD!* 🎬📖
Idan kina son:
✅ Sabbin *updates*
✅ Karantawa cikin jin daɗi da sauƙi
✅ Tare da wasu *garaɓasa na musamman*
To *ki shirya yanzu* cikin farashi mai sauƙi:
💰 *₦300 only* kafin mu gama.
🕒 Bayan an gama: *₦500*
🌟 *V.I.P Access*: *₦1000*
_Zamu kuma ba kowa *Document* da zarar mun kammala, da kuma password_
Kar ku bari a barku a baya, tafiyar na daban ne wannan karan, domin har yanzu wasa muke yi.
```Idan kun shirya, ku tuntuɓi wannan number:
07038436703.```
~SING BY PRETTY SK~
*ALHAMDULILLAH ❣️*