YAR NOLLYWOOD BOOK ONE by PRETTY SK.txt

Author :  Pretty Sk Category :  Hausa Read

Chapter   7 / 9

18K to 21K   out of 25.8K words

mai da wa a hankali.

“Wallahi komai sai ya min kaman a gaske, balle yarda kika dinga zubar min da hawaye, yau na ƙara tabbatar da soyayyar da kike min, da ina da dama rungumeki zan yi in yi miki godiya sosai.....wallahi A'isha ina jin ki a cikin ruhi na. Ina sonki." Ya faɗa yana riƙe mata hannu tare da matsawa.

“Nima ina sonka sosai, ji nayi kukan ya zo min.”

“Hmmm mun iya acting sosai, yanzu damuwana ɗaya, cikin da muka ce, ya zamu yi?.”

“Allah ma sani, kawai idan ka ga alamun za su ta da maganar zai muje asibiti mu yi na ƙarya."

“Shike nan kawai, muje magrib na yi, yau za ki yi kwanan shuru babu su Dad.” ta yi murmushi kewansu na motso mata.............✍️
END.

> Innalillah wa'inna ilaiyi raji'un 🙆🙆🙆🙆🙆 wannan irin ƙarya haka, hmmm anya kuwa Ayan da A'isha ba ku kira babbar matsala ba.

> Kaina ya kulle akansu, hmmm muje dai amma fa da matsala ga alamu.

> Acting kuma ai ke jinin Ƴar NOLLYWOOD ce 🤭, dole ki iya iri-iri 🏃🏃🏃.

*📢 Assalamu Alaikum Everyone!*
Muna farin cikin sanar da ku cewa za mu *buɗe Paid Group* na littafin *ƳAR NOLLYWOOD!* 🎬📖

Idan kina son:
✅ Sabbin *updates*
✅ Karantawa cikin jin daɗi da sauƙi
✅ Tare da wasu *garaɓasa na musamman*

To *ki shirya yanzu* cikin farashi mai sauƙi:
💰 *₦300 only* kafin mu gama.
🕒 Bayan an gama: *₦500*
🌟 *V.I.P Access*: *₦1000*

_Zamu kuma ba kowa *Document* da zarar mun kammala, da kuma password_

Kar ku bari a barku a baya, tafiyar na daban ne wannan karan, domin har yanzu wasa muke yi.


```Idan kun shirya, ku tuntuɓi wannan number:
07038436703.```

~SING BY PRETTY SK~




💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.*

Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥
*Keep shining, JAW family!* 🌺

*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*



𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅

Story and writing✍️
```𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊
```
~SAKINA ABDULLAHI~
> *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️


✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽


E.P2️⃣4⃣⏩2️⃣5⃣.


*INAYAH*

__________Haka na wuni a gidan bani da walwala, amma da Mom ta kira akan sun isa gida, shine na ji dama-dama, ina kwance akan kujera na toshe kunnuwa da Earphone, sai ji na yi ana ƙoƙarin shigowa ɗakin.

Da sauri na zabura sai kuma na tuna yau wacce za mu zauna tare za ta iso.



A hankali ta turo ƙofar, trolley ɗin ta ne suka fara shigowa, sannan ta shigo gaba ɗaya.

Ƙyaƙƙyawa yarinyar wanda za mu yi sa'a ɗaya, sai dai na fita ƙiba amma za ta fini tsayi, ba fara ba ce tana duhun fata sosai, sai dai Beauty ce. Atamfa ne jikinta ɗinkin doguwar riga, ya sha stones sosai.


Murmushi na ga ta yi min, sai na yi mata yaƙe dan ni sai na gama karantar mutum nake sake mai.


Ita da wasu ne suka dinga shigowa da kayayyakinta, na abinci da kayan sawa.


“Ƴar Uwa Barka da gida." Ta faɗa sai na ɗaga mata kai dan ban ji me ta ce ba, ko ɗazu nasan sallama ta yi amma Earphone din kunni ba be bari na ji ba.

“Hey, Sis.” ta kuma faɗa tana ɗaga min hannu, ga dukkan alamu dai yarinya ce mai son mutane.

Earphone ɗin na cire ina kallonta, sai na ja dogon numfashi na furzar sannan na ce.

“You are welcome.”

“Thank you, wannan ne room ɗi na?." Sai na nuna mata da hannu.

Gyalenta ta cire ta fara shiga da kayan Ni kuma ina rakata da ido.

“Haba Inayah ki taimaka mata mana.” zuciyata ta faɗa min.

‘okay, nasan ko zan yi wanki za ta tayani.' na faɗa a kasan leɓe na.


“Can i help you?.” sai ta juyo tana riƙe da leda.

“Na gode."

“No bara na tayaki na ga kayan da yawa." Murmushi ta yi.


Aikuwa tare muka ƙarasa, sannan na ta ya ta shirya kayan, kayan abinci kuma muka kai Kitchen gefe guda ta zuba nata.


Da alamun itama ba rashi dan kuwa ta zo da kaya masu yawan gaske.


A falo muka zauna bayan mun gama, zuwa lokacin har na saki da ita.

“My name is Mubina, what of you?.”

“Inayah."

“Wow nice name."

“Thanks. Wani cost ki ke?." Sai ta kunna mana Tv.

“Gynecologist." Murmushi na yi dan nima shine.

“Wow, same room, same cost and same mate." Sai ta zauna gefena tana murmushi itama.

“Nice to meet you." Ta faɗa, Ni kuma na mai da hankali na ga Tv in da ta sanya Star plus, in da suke yin Film ɗin *KULFHI THE SINGING STAR.*

“Sis Ina son Series ɗin nan." Sai na mai da mata murmushi ina hawa Youtube dan kuwa ban juran kallon India film.


Tare muka yi sallan magrib da isha'i, bayan mun gama muka shiga kitchen.

“Ni dai ban iya girki ba wallahi, kuma an ƙi ɗaukan min mai aiki.” murmushi ta yi sai ta ce.

“Ki ce na fiki ta wannan wajen, dan kuwa na iya wasu abubuwan. Yanzu dai me zamu ci?." Sai na buɗe wajen kayana, ina bin ko ina da kallo.


Indomi na ciro guda huɗu na ce.

“Nima na iya, ki dafa Indomie Ni kuma zan soya ƙwai." Dariya muka yi dukkan mu.


Hanata buɗe na ta pack of Indomie na yi, nawa muka dafa sannan na soya eggs ɗin.

Wallahi da gaske nake na iya siya eggs sosai.


Hmmmm Allah kenan, cikin some hours jinin mu ya haɗu da abota.


Sai 10:54pm muka rabu, ta shiga room dinta Nima haka.



***************

Ina cikin barci na ji yo tana dukkanmin ƙofa, tsaki na ja ina tashi dan jiya sai 1:20am na kwanta.

“Inayah, ki tashi 8:00am ake fara karatu, ance in mutum ya yi late wanke hostle restroom ya ke yi." Ai da sauri na wuntsulo daga gadon ina watstsakewa..

“Thank You, ki shiya ganinan zuwa." Da haka na shiga restroom Ina miƙa.


7:35am na fito cikin uniform tsaf, Farin ƙaramin hijab, sai farar riga mai tsayi, sannan dogon wando, na yi kyau sosai.

Mubina ma tsaf ta shirya, sai dai ba ta sa hijab ba tana cin bread ne.

Nima zama na yi ina ɗaukan bread ɗin.

“Na ƙoshi ki yi sauri." Ta faɗa tana miƙewa. Tea na sha sharp-sharp, sannan muka fita kowacce da jakkanta.


Ina tafiya ina ƙara sa cin bread ɗin.

Masu gadin mu suka gaishe mu, muka amsa, ɗaya kuma sai da ya raka mu har class, sannan ya zauna daga can waje.


Babbane class ɗin wanda zallar ƴammata ne, sai shigowa ake yi, da yake na saba zaman baya sai na ja Mubina muka zauna a can layin ƙarshe.

Wayata na ciro sannan na kira number Dad.

“Shalele ba ki tafi ba?." Ya faɗa daga cikin wayar.

“Ina school, Good morning."

“Morning Dear, what's wrong?." Sai na kalla window in da nake hangen Guard ɗina.

“Dad Guard ɗaya bina yake fa, me yasa?." Na faɗa ina rage murya.

“Yes, biyu masu tsaron gida, ɗaya kuma duk in da za ki zai kasance yana binki.”

“Amma me yasa?.”

“Saboda ina son ki.” ji na yi kaman na fashe da kuka sai na daure na ce.

“I will call you later." Sai na kashe kiran.

“Menene?.” Mubina ta tambayeni.

“Wai wancan mutum Ni zai dinga bi.....tab da sake." Murmushi ta yi sai ta dafa kafaɗata.


Kafin ta yi magana wasu malamai maza biyu suka shigo, ganin kowacce yarinya ta fara sanya I.D card ya sa muma muka sanya namu muna kallonsu.

Gaishesu muka fara yi, suka amsa sannan ɗaya ya yi mana bayaninsa.

Muna da sabbin zuwa, da haka aka dinga kiran sunaye suna fita kowacce tana bayanin kanta a gaban student.

A ƙalla mun kai 50, dan babba ne hole ɗin.

“Mubina Abubakar." Ya faɗa, sai Mubina ta miƙe tsaye.

Sai da ta ƙara gaishe da ƴan aji, da kuma malaman cikin ladabi, sannan ta faɗa bayani duk cikin harshen English.


Tana dawowa ta zauna, take mutumin ya ce.

“Halimatu Musa! Halimatu Musa!! Halimatu Musa." Shuru babu wacce ta amsa.

Haka ya kuma kiran sunan.

“Halimatu Musa! Halimatu Musa!!.”

Malamin dake gefe shine ya nu na sit ɗin mu yana cewa.

“You come.” Mubina ta miƙe sai ya ce.

“Not you, the other person." Sai na miƙe.


Sai a lokacin Mubina ta kalla sunan dake jikin I.D ɗina.

“Inayah dama ke ce Halimatu Musa?.” danne zuciyata na yi bance komai ba na wuce.


Da yake mutumin ya gane ni, dan yasan Dad.

"Aren’t you Halimatu Musa?.” ya tambayeni sai na ce.

“Uhmmm, am HALEEMART MUSA." na faɗa fuskana a haɗe.

Na tsana a dinga kiran sunana da Halimatu, haushi nake ji, shi yasa ban wani amfani da sunan.

Murmushi su biyun suka yi.

“Sorry Haleemart." Me kiran sunan ya faɗa, da alamun ba su da matsala, dan haka ya kuma cewa.

“Introduce yourself." Juyawa na yi na kalla matan da suke kallona.


Take na nuna haka zan dinga tsayawa gaban cameras a Lokacin shooting, sai na yi murmushi ina cewa.

“At first, my name is Haleemart Musa, but I am called Inayah. I do not take offense easily, nor do I like conflict. Whoever keeps to herself, I give her respect; otherwise, I will be disrespectful. I am also your sister's. Than A woman aspiring to become a doctor, and I pray that Allah helps us all." Daga malaman har ɗaluban kowa baki ya buɗe yana kallona.

Ni kuwa ko a jikina na kowa wajena na zauna.

“Inayah bayani kawai akace ba ki faɗa yadda kike so ba."

“Mubina, haka nake ni.” na faɗa ina lumshe idanunwa...............✍️
END.

> Kai Inayah boom 🔥, Allah ya shiryeki.

> Kun fa ji GUY'S.

> Mubina ai kin yi sa'a da ta fara kulaki ma 🤭🤭🤭.

*📢 Assalamu Alaikum Everyone!*
Muna farin cikin sanar da ku cewa za mu *buɗe Paid Group* na littafin *ƳAR NOLLYWOOD!* 🎬📖

Idan kina son:
✅ Sabbin *updates*
✅ Karantawa cikin jin daɗi da sauƙi
✅ Tare da wasu *garaɓasa na musamman*

To *ki shirya yanzu* cikin farashi mai sauƙi:
💰 *₦300 only* kafin mu gama.
🕒 Bayan an gama: *₦500*
🌟 *V.I.P Access*: *₦1000*

_Zamu kuma ba kowa *Document* da zarar mun kammala, da kuma password_

Kar ku bari a barku a baya, tafiyar na daban ne wannan karan, domin har yanzu wasa muke yi.


```Idan kun shirya, ku tuntuɓi wannan number:
07038436703.```

~SING BY PRETTY SK~



💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.*

Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥
*Keep shining, JAW family!* 🌺

*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*



𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅

Story and writing✍️
```𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊
```
~SAKINA ABDULLAHI~
> *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️


✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽


E.P2️⃣6⃣⏩2️⃣7⃣.



*Adam*

________________Tun bayan shigowarsa Lagos sau biyu ya je shooting dan be da wani scene masu yawa, yana da wani target akan new year, so yake shi da kansa ya ɗau nauyin wani zazzafan Film da za su yi, labarin ya riga ga siya, so yake su kammala *LOVE AT THE FIRST SIGHT* .


Zaune yake kan kujera yana shan drink, a yanzu babu abin da yake yawan tunani sai fuskar yarinyar da ta ce mai sunanta *Inayah* , gaba ɗaya ta hanashi sukuni, babu dare ba rana fuskarta yake gani tana mai murmushi.

A kowani lokaci jiran kiranta kawai yake yi, sai dai har yau ba ta kira ba, kuma a ƙalla da haɗuwarsu sun kai 6days, duk sai ya ji ya damu.


Har Sarah ya rage kulawa, dan kuwa Inayah ta sace zuciyarsa.

Ya na so zuwa gobe ya koma Kaduna dan jiya mahaifiyarsa Ammee, ta kirasa akan akwai matsala, wai Ayan ya fasa auren Ruma, kuma yanzu wani auren zai yi.


Hakan ya ɗaga hankalinsa sosai, so yake ya koma ya ji abinda ke faruwa.


Wayarsa ne ya ɗau ƙara, ganin ƴan uwan aikinsa ya sa ya ɗauka.

“Okay, ganin zuwa.” da haka ya miƙe ya nufa room.

Wow bedroom ya haɗu sosai, be tsaya a ko ina ba sai close-set ɗin sa, buɗe wa ya yi sannan ya zaɓa ƙananun kaya ya sanya.


Cikin ɗan Lokaci ya fito sanye da ƙananan kaya kamar ko yaushe. Fita ya yi ya hau motarsa sannan ya nufa in da suke shooting ɗin.

Motar sa ƙirar Bugatti Veyron black ya shiga, a hankali ya dinga tafiya har ya isa, saura 2 Episode a kammala Film ɗin, so suke su sake shi lokaci ɗaya.


Asibiti ya nufa dan a can ne za'a yi shooting ɗin.

Da isansa bakin asibitin, wasu maza biyu suka nufosa da sauri suna takamai baya. Tun anan ya ga masu aikin Film ɗin.


*Jim Iyke* shine mahaifinsa a shirin, wani ɗan babban kafiri.

Zama suka yi, mai yin makeup wata Angel, ta zauna ta yi ma Jim Iyke, sannan aka ba shi wasu kayan na masu kuɗi sosai dan ya sa.

A.G ma makeup aka mai amma na ciwuka dan kuwa a wancan Episode ya yi accident akan soyayyar wata yarinyar wanda mahaifinsa Jim Iyke ya hanasa aurenta, to hakan ya haifar mai da damuwa, har ya yi accident.


Ana gamawa aka shiga ciki, wani room aka basu, A.G ya kwanta ya lumshe idanunsa.

Sanye yake wanda jeans black da white shirt, ya cire sarƙokin jikinsa da ɗankunne, dan a yaro mai hankali ya fito. Fuskansa kaman ciwon gaske, an dai rufe waje biyu da bandage, amma har launin jini aka sanya musu, sannan an yi kaman ana ƙara mai jini.


“Action." Ya ji an faɗa, yasan an fara kenan, yana kwance Mahaifinsa ya shigo a ruɗe yana kallon yaronsa cikin wani hali.

Har yana tuntuɓe ya isa gaban gadon, take ya fashe da kuka kaman na gaske yana jijjiga gadon da yin magana cikin English.

“My Son.... please wakeup...... my son...... Alexx, wallahi yanzu na amince da ka aura Mercy , na yarda , ka tashi na yarda, ko ma wacece kake so by now na yarda. Ko wacce ba ta da ƙafafu na yarda.........oh Jesus help me........" (Astagafirullah 😓😓) Ya kai nan kukan na fin ƙarfinsa.


Take doctor ya shigo sai ga wata budurwar yarinya wacce suka yi mata shiga na talakawa, riga ce T-shirt sai mini-skirt irin na kanti, a ruɗe ta shigo, amma suna haɗa ido da Mahaifin Alexx sai ta juya, a tsorace za ta fita.

“Me................Mercy, please come back.......na amince da Ya aureki yanzu.” ya faɗa yana miƙa mata hannunsa.


Take director ya ce su sake wajen, haka dai aka sake sannan ya yi, bayan ta isa gaban dagon tana kuka, fuskar A.G take ta shafawa kamar t samu fuskar yaro, tana ce mai da ya tashi ta dawo.


Bayan sun ɗau lokacin da director ya basu umarni.

A hankali ya buɗe idanunsa kaman dama wanda yake a sume ɗin. Ya ɗan ɗau lokaci kafin ya gane suwake akanta.


Nanfa mahaifin ya shaida ya amince, da auren na su. take Mercy ta rungumesa suna kuka kamar da gaske.


Sai da suka tsara wajen sosai yanda zai sanya mutane zubda hawaye dan kuwa duk wanda ya kalla Film ɗin daga farko, dole ya yi hawaye, dan ya na son Mercy duk da talaka ce, sai mahaifinsa Jim Iyke, ya hana saboda yana so ya yi mai auren jari, haka dai aka gama labarin.

Gobe ne shooting na ƙarshe, da haka aka tattara kayan aiki.


A.G ne rike da hannu Mercy suna ɗan hira, shifa dan ta ɓa jikin mace a wajensa ba wani abu bane.


Sai da suka ɗau lokaci suna hira kafin ya yi kissing na ta a kumatu suka rabu.


Gidansa ya koma hankali kwance, yana shiga ya yarda carkey kan kujera ya nufa Kitchen, be jima ba ya fito riƙe da plate wanda ya zuba snacaks a ciki, zama ya yi yana kunna Tv, sai ya fiddo wayarsa, saƙonnine ta kowani App Suka fara antayowa, shi har gajiya yake da amsawa, Saƙonta ko kiranta kawai yake jira, yana so ko sau ɗaya ne ta kirasa sai dai shiru har yanzu.............



*A'isha*

_______Kallon screen ɗin yawarta take yi, ganin wayar ta kuma katsesa ba a ɗauka ba sai ta koma wajen sakon Yaya Ayan wanda ya shigo yanzu, sai ta shiga.

‘yanzu ko hoton ki ba za ki tura min ba.' shine a rubutu ce sai ta mai reply.

‘Ba ka ta ɓa cewa kana so ba.' tana tura mai ta fita, take kiran Shalele ya shigo.


Murmushi ta yi sannan ta ɗauka ta na ajewa akan mirrow dan Video call ne.

A'isha da ke sanye da hijab fari iya ciki sai shuɗin doguwar riga na yadi, murmushi ta kuma yi tana kallon ƙanwarta dake zaune kan kujera, Pjmask ne jikinta pink colour, da band wanda dogon gashinta ya zuba ta baya.

“Ina kika sa wayan ne, 4 missed call na miki fa?.”

“Sorry, earphone yana jikin wayar ne, shi ya sa ban ji ringing ɗin ba.” sai Aisha ta ɗaga min kanta.

“Ya makaranta fatan ana gane karatun ko?."

“Eh Alhamdulillah. Kun fara exam ku ai."

“Eh, mun gama."

“Allah ya taimaka.” take fuskar A'isha ta ɗan bayyana damuwa sannan ta ce.

“An sanya ranar aure na.” murmushi na yi.

“Masha Allah, wata nawa?, Allah ya sa sai ƙarshen shekara, yarda idan na zo na ci uwar ƴar fili, dan rawar da zan yi hmmmmm." Na faɗa ina ɗan mistsike idanuna.

“Hmmm yau yaushe?.”

“Saturday."

“On Friday na satin nan, shine auren.” da sauri na zaro manyan idanuwa ina cewa.

“Dad ya ba da sadakan ki ne?.” harara ta watso min.

“Eh mana, wani irin aure ne za'a sanya sati ɗaya......faɗa min me yasa?.” murmushi ta yi, ita har yanzu a yarinya take kallona shi yasa ta ce.

“Ayan zai yi tafiya ne, so ana ɗaurawa za mu wuce tare." Sai na ɗaga kai.

“Kenan bana gida za'a yi bikinki? Gaskiya ban so ba wallahi." Na faɗa har da turo baki.

“Ina zuwa Sis.” ta faɗa tana katse kiran.


A'isha ji take tun yanzu ta fara na daman ƙaryan da ta yi, gaba ɗaya kwana biyun nan cikin wani irin yanayi take ciki.

‘Ki turomin na ki, da na Shalele, tinda Allah ne haɗa mu ba.’ ta karanta saƙon Ayan, take ta shiga gallery ta tura mai guda uku sannna ta yi offline.

Kan gado ta koma ta kwanta tana tuna abubuwan da suka faru a ɗan kwanakin baya, wanda a dukka a cikin wata ɗaya ne ya faru......................✍️
END.


> Sannu A.G, kana duniya wlh, gaskiya Sarah an cuceki 😓😓.

> Aisha 🥺 bara dai mu ji me

7 / 9