YAR NOLLYWOOD BOOK ONE by PRETTY SK.txt

Author :  Pretty Sk Category :  Hausa Read

Chapter   3 / 9

6K to 9K   out of 25.8K words

wanda wasu suka ce idan na sa yafi min ƙyau, amma da gangan nake cirewa.

Sai na fito fes kamar a sace Ni, na yi ƙyau sosai dan Allah ya ban ƙyau na musamman.


Jakkata na ɗauka sannan na fita, Dining area na nufa, abinci na gani yana tiriri, take na hau ci wanda bansan na waye ba, amma ga dukkan alamu na A'isha ne, dan ita ke cin Indomi sosai kuma wannan girkin na ta ne.

Da gayya na hau ci da sauri-sauri, yana ƙonani, sai da na cinye eggs ɗin, sannan na ci iya cina duk na jakwalkwala Indomie.



“Wayyo! Indomie na ya huce ai.....” haɗiye sauran maganar ta yi tana kallona ina kai loma bakina.

“Inayah, waya ce ki taɓa min abinci na?."

“A...Auntyna na za ci Rabi (mai girki) ita ta aje min." Na faɗa ina jin cikina ya cika amma saboda neman rigima na kuma kai wani bakina.

“Lailai ba ki da .....”

“Aisha." Mom ta faɗa tana daga falo.

“Mom Indomie na girka na tsaya nemo yaji shine ta cinye min.”

“Ki ya ƙuri kinsan yarinya ce, duba kaman Doya aka yi, sai ki ci ko yayane."

“Na ƙoshi.” ta faɗa tana dungure roba yajin makan shi ya yi mata laifin.

Ganin ta yi waje nasan wucewa za ta yi ai da sauri na miƙe, Rabi ta miƙo min lunch bag ɗina na amsa ina komawa falo.

“Za ta wuce." Na faɗa ina amsar ₦500 wajen Mom.

“A dawo lafiya." Na ɗaga mata kai ina gudu, ga nauyin jakka, ga ciki ya cika sannan ga abinci.


Ilai ta kunna motar tana zuba horn ajere kai ka ce wani ne ya biyota. shi kuma me gadi yana bude get, ai da sauri na buɗe motar ina shiga baya ban gama kulle motar ba ta figesa.

Da sauri na kulle ina addu'a, dan kuwa Aisha da figa motar ne da wani irin gudu.


Ganin gudun bana wasa bane, sai faman kutsa motoci take, tana cin taya, yasa na fara ihu, ina mata magiya.

“Aunty karki kashe ni....wallahi za ki yi ma Dad and Mom asara.......za ta kashe babbar tauraruwa......dan Allah ki min rai......Aunty wayyo." Nai ta faɗa amma a banza dan kuwa sai kutsawa take yi kamar mun yi sata an biyo mu.


Kafin ka ce me sai gamu a school, jikina duk ya yi tsami dan ko zaman kujera ban yi ba, haka na fito ina sauke ajiyar zuciya, kallonta na yi ina cewa.

“Insha Allah gobe Driver na zai dawo, na dena hawa motar....." Take ta baɗe ni da ƙurar motarta tana ƙara hawa titi kamar wacce ta bugu.

Girgiza kai na yi, sai na nufa cikin school raina a ɗan ɓa ce, da abin da ta yi min, ina kumbure-kunbure dan ma Allah ya kawo mu lafiya.............✍️
END

> Ƴar NOLLYWOOD 🔥

> Fatan yana zuba sweet 😍

> Update ba yawa ko..... I'm sorry everyone, na riga na rarraba ne kunji.

#LIKES👍
#SHARING☹️👌
#COMMENTS🙏👌




*𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅*

_TAP THIS LINK TO JOIN MY GROUP👇_
https://chat.whatsapp.com/Be241ldCcFS5kAxa5V8lpy

_TAP THIS LINK TO JOIN MY CHANNEL👇_
https://whatsapp.com/channel/0029Vb64I4aGzzKQsSeaKA2K

_TAP THIS LINK TO JOIN IN AREWAPEN 👇_
https://arewapen.com/u/prettys01


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.*

Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥
*Keep shining, JAW family!* 🌺


*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*



𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅

Story and writing✍️
```PRETTY SK```
~SAKINA ABDULLAHI~
> *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️


✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽



E.P7️⃣⏩8️⃣.

__________Abu kaɗan ke ɓata ma A'isha rai, dama ga ta uwar fushi, haka ta shiga school ɗin su, parking ta yi ta fito, tana jin yunwa amma taurin kai ba zai barta ta ci komai ba, department ɗin su ta nufa.

Ko da ta shiga zama ta yi, gaisuwa ke haɗata da kowa, haka aka gama lecture biyu tana aji amma ba ta fahimci komai ba.


________Ajin ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Take student suka gaishe sa sai ya amsa yana nufan wanjen zaman malamai, a hankali ya kai ƙyawawan idanunsa kanta, da sauri ya janye yana jin wani ɗa ci a cikin ransa, zai iya cewa tunda ya fara koyarwa yau shine karo na farko da ya shiga class ɗin ba ta kallesa ba, duk da ta ji an kira sunan sa. *Sir M.D* amma ba ta ɗago ta kallesa.


Haka ya gama Lecture hankalinsa na kan Aisha wacce har ya gama ba ta kallesa ba.

Yana fita ta sauke nan nauyan ajiyar zuciya tana lumshe idanunta, kifa kanta ta yi a kan desk, tana kallon bayanin da ya yi a jikin board.

Wata budurwar ce ta shiga ga dukkan alamu ba musulma ba ce saboda shigar dake jikinta.

Tana shigowa ta nufa Aisha sannan ta ce.

“Hey Sis, Sir M.D ya kiran ki, ya ce ki sa me sa a office ɗin sa." Ji ta yi gabanta ya yanke ya faɗi, sai a lokacin ta dawo cikin hankalinta, miƙewa ta yi sannan ta yi waje.

Haka ta taka har zuwa bakin office ɗin sa, sai kuma ta tsaya dan gani take makar ƙarya ne, duk da wacce ta kirata ta santa sosai, mamaki take akan kiran na sa, dan kuwa Sir M.D be kula mata, ba ya magana da su privacy.

Sai dai ita tun da ta fara ganinsa ta kamu da soyayyar da ba ta san ya shigeta ba, tana da samari masu yawa amma hankalinta yana kan M.D, idan ya shiga class ɗin su to da idanunta yake fara cikin karo ta na aika mai tsadaddan murmushi, haka duk in da za ta gansa a school ɗin nan take zuwa.

Ta sha wahala kafin ta samu numbersa amma ranar da ta yi gigin kirarsa, ranar ya sameta ya yi mata faɗa sosai, maimakon ta rage bibiyarsa sai ta ƙara, kullum sai ta tura mai saƙon, safe, rana da dare, na kulawa da tambayar ya ci abinci, ba ta damuwa da rashin reply amma ya zama mata aikin yi na kullum.

Wai shine kuma a yau ya ce a kirata. Knocking ta yi.

“Yes coming." Ta ji zazzaƙan muryarsa ta faɗa.

A hankali ta tura ƙofar ta shiga bakinta ɗauke da sallama, sai dai har lokacin fuskarta na haɗe duk da kuwa bazatan da Sir M.D ya yi mata.

“Ina kwana....sir wai kana nema na?.” ta faɗa daga can nesa.

A karo na farko da ya yi mata murmushi kenan sannan ya ce.

“Eh, zo ki zauna." Ba musu ta ƙara sa ta zauna a ɗan ɗarare.


Ya ɗau kaman minti 3 yana kallon fuskar, tabbas A'isha ƙyakƙyawa ce, wacce ta cika gaba ɗaya abubuwan da ake nema ga budurwar mace, ƙyau, ilimi, hankali, natsuwa, mu'alama mai kyau da mutane, ƙyautta ma kowa da sauran abubuwa wanda ya bincika da kansa.

“Me aka miki?.” ta jin tambayar kamar daga sama.

Ɗago idanunta ta yi suka haɗa ido ta sauri ta kauda kanta.


“Sir ba komai....."

“Ƙarya ba ɗabi'ar ki ba ce... Tell me.” sai ta saki fuskarta, dan kuwa abin da Inayah ta yi mata ne kawai yake ɓata mata rai.

“Sir ba wani abu bane.”

“Ina so na sani, nasan wa ya ta ɓa min ke.” ya faɗa hankalinsa kwance, mamakin abin da ya ce ta yi amma sai ta share.

“Kawai ƙanwata ce ta ɓa ta min rai amma ya wuce.” ta faɗa tana jin tasirin idanunsa akan fuskarta, ji take kaman ta nitse a ƙasa.

“Me ta miki?” murmushi ta ɗan yi sai ta ce.

“Ba wani serious abu bane......”

“Ina so na sani." Ya faɗa a ɗan zafafe.

“Kawai na gama ɓa ta lokaci na yi wa kaina breakfast, shine ta cinye, kuma tasan ban iya cin duk wani abu da wani zai dafa sai nawa, shine na ji haushi, kuma na ɗauke ta zuwa school, ta dinga min hauka a cikin mota.” ta kai maganar cike da shaƙwabar da ba tan ta yi ba, murmushi ya yi sannan ya tashi daga kujerar, a hankali ya za gayo in da take sai ya zauna a gefan ta.

Take daddaɗan turarensa ya cika ƙofofin hancinta lumshe idanunta ta yi sannan ta buɗe.

“Ki faɗa mata na ce, duk ranar da ta sake ɓa ta miki rai zan haɗu da ita. Please ki koma yarda na sanki mai yawan murmushi, kinfi ƙyau." Dariya ta ɗan yi.

“Aisha." Ya faɗa a natse sai ta kallesa tana amsawa.

“Na'am."

“Magana zan yi da ke mai muhimmanci.”

“Ina jinka, fatan ban yi laifi ba?."

“Hmmm, ko ɗaya, Kinsan Ni sosai, zan iya cewa tunda nake ban ta ɓa tsayawa da mace na yi hira da ita kamar yarda nake yi yanzu, kinsan dalili?." Sai ta girgiza kai.

“Saboda soyayyar da kike nuna min...... A'isha, kina nuna kulawarki a kai a kodayaushe, saƙon nin ki ba su ta ɓa makaraba, Ni kuma ban taɓa gajiya da karanta su, ko da na sameki na yi miki faɗa, maimakon ki dena sai ki ka ci gaba, daga lokacin Ni kuma na fara bincike akan ki, na samu abubuwa masu yawa kuma masu daɗi wanda ko wace mace take fatan a sameta da shi........ke kin samu, zama na yi nai tunani akan ki, kuma a yanzu zan iya ce miki na amsa Soyayyarki.” ya faɗa yana mata murmushi, ita kuwa saboda maganganunsa sai ta kasa natsuwa, ji take kaman ta fashe da ihun murna.

“Na yarda da wani abu, duk mai sonka ko yayane ka so shi. Ban ta ɓa soyayya, amma har ga Allah ina Ƙaunarki A'isha saboda halayenki.” take hawaye ya gangaro daga idanunta na murna.

Murmushi ya yi sannan ya miƙe, hawayen ta share tana ce wa.

“Tabbas a yau ka farantamin. Ya Allah ka faranta mai shima. Alhamdulillah alhamdulillah." Ta faɗa tana fita cikin sauri harda gudu.

Dafe kansa ya yi yana mamakin irin soyayya da A'isha ta faɗa.

Shi kansa ya ɗau lokacin kafin ya zauna dan kuwa zuciyarsa ce ta yanke mai wannan shawarar, yana zama ya rintse idanunsa, be mata ƙarya ba, be ta ɓa soyayya, sai dai sau ɗaya wata yarinya ta taɓa burgesa, ya so ko sau ɗaya su sake haɗuwa amma be samu dama ba.

(A lokacin da ya je Abuja, wani school an gayyace sa Quiz competitions na makarantu, ya je kuwa, a cikin yaran da suka wakilci wata makaranta ya ga yarinyar, duka da ƙarama ce sosai amma ta burgeta sosai, kuma a gaba ɗaya Quiz ɗin ita ce ta ci, be manta sunan da ake kiran ta da shi ba *QUEEN ROSE* sannan shi ya ba ta ƙyautarta, aka musu hoto. Bayan da ya dawo Kaduna, ya yi ta bincike a makarantar mai wannan sunan sai aka ce ta fita a school ɗin, da haka ya bar maganar amma kullum yana tunawa da ita.)

Yasan al'adar gidansu amma shi so yake ya aura mace daga waje, so yake ya aura bare, ko dan tsallake auren *Ruma* . Tsaki ya ja dan tuna sunan Ruma da ya yi.

A yanzu A'isha zai aura duk da ba ya sonta amma yana ƙaunarta, zai aureta dan ya faranta mata sosai, shi sai yau ya ga kaman ta mai kama da yarinyar da yake nema.


_____Ko da ta fito motarta ta nufa kai tsaye, ciki ta shiga ta kulle, sai da ta sha kuka ta gode ma Allah, sannan ta jin gina da kujerar tana jin daɗi a ranta.

Take wayarta ta hau ringing tana dubawa ta ga M.D cikin sauri ta ɗauka tana kaiwa kunninta.

“Please ki samu ko biscuits ne ciki kin ji.” ya faɗa cikin wani salo da ƙwantar da murya.

“Insha Allah, Sir M.D thank you Soo much."

“By now a dena cemin Sir pls." Murmushi ta yi.

“To me zance?." Ta ji bakinta sun furta ba tare da izinin ta ba.

“Uhmmmm *AYAN* ."

“To Yaya Ayan." Sai ya yi murmushi.

“Take care." Da haka ya katse kirar, bin wayar ta yi da kallo cike da mamaki.......✍️
END.

> Hmmmmm wallahi zafin 🔥 labarin nan, na daban ne. Wato Sir M.D shine AYAN na Familyn *GIƊAƊO MANTION* hmmmmmm 🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔 muje dai GUY'S.

> GIƊAƊO'S FAMILY Rayuwar ku sai ku kam 😓.

> Wacece ROSE? Kuna tunanin abin da nake tunani kuwa........🙆🙆🙆🙆🙆🙆.

#LIKES👍
#SHARING☹️👌
#COMMENTS🙏👌





*𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅*

_TAP THIS LINK TO JOIN MY GROUP👇_
https://chat.whatsapp.com/Be241ldCcFS5kAxa5V8lpy

_TAP THIS LINK TO JOIN MY CHANNEL👇_
https://whatsapp.com/channel/0029Vb64I4aGzzKQsSeaKA2K

_TAP THIS LINK TO JOIN IN AREWAPEN 👇_
https://arewapen.com/u/prettys01


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.*

Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥
*Keep shining, JAW family!* 🌺

*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*


𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅

Story and writing✍️
```PRETTY SK```
~SAKINA ABDULLAHI~
> *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️


✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽


E.P9️⃣⏩🔟



________Inayah, yau makarantar bai min daɗi ba saboda, Jennifer ba ta zo school ba, haka dai school ɗin ya zama min lami, ko da A'isha ta zo ɗauka ta ban yi mata magana ba har muka koma gida, na dai lura sai faman murmushi take yi, sai nima na shareta saboda abin da ta yi min na ɗazu ya ɓa ta min rai sosai.


Bayan ta yi parking na fito fuskana babu yabo ba fallasa.

Ina shiga falo na nufi Kitchen aje lunch bag ɗina na yi sannan na fito sai na ga mom na saukowa daga stairs, murmushi take yimin sai dai Ni na kuma ɗaure fuska.


Jakkana na ɗauka na yi hanyar room ɗina , har zan wuceta sai ta riƙon.

“Waya ta ɓa shalele?.” ta faɗa tana dawo dani gabata, shuru na yi ban yi magana ba, sai ta ɗaga mun fuskanta na kalleta.

“Me aka miki?.” ta faɗa dan yanayin da na koma.

“Babu komai..........ina zuwa." Na faɗa ina wucewa, bina ta yi da ido dan kuwa yanayin na wa ba magana abin ka da kullum ina nishaɗi.



“Ke kin yi ma Shalele wani abu ne?." Mom ta tambaya A'isha wacce ta zauna a falo bayan shigowar ta.

“Haka na ganta, ko magana ba mu yi ba, sai dai ko tun faɗar safe da muka yi ne." Sai ta ɗaga kai tana zama a kujera, sai dai jikinta ya yi sanyi, dan Inayah sam ba haka take ba.


“Hajiya, yau fa Shalele ba ta ci komai ba, da alamun ko buɗe lunch bag ɗin ba ta buɗe ba. Sannan ga wannan a ciki"

Mai aikin su wato Rabi, ta faɗa tana miƙa ma A'isha ₦500, sai A'isha ta yi mata alamar ta wuce da shi, sai ta yi godiya tana koma wa Kitchen.

Mom ta kalla A'isha da ta ɗan zaro ido, a ce tun safe mutum be ci komai yanzu ana shirin kiran sallar magrib.

“Da matsala me aka mata?.” A'isha ta faɗa cike da damuwa.

“Muje room ɗin." Da haka suka nufa room ɗin Inayah.




Ina shiga ɗakina na kulle ko ina sannan na kashe haske, kwanciya na yi kan gado ko takalmi ban cire ba, gaba ɗaya haushin kowa na ke ji, so nake yau a gidan kowa ranshi ya ɓaci dan kuwa abinda A'isha ta min ya ɓa ta min rai, sannan ga Jennifer da ta ƙi zuwa school, sai abu ya haɗe min, shi yasa ko magana banyi da kowa ba.

Jin ana buga min ƙofa yasa na yi wani murmushi sannan na yi magana a hankali.

“Ai yau sai hankalin kowa ya tashi, hmmm." Na yi ƙwafa ina toshe kunnuwana.



Mom da hankalinta in ya yi dubu ya tashi ta kira Dad a waya akan Inayah ba lafiya. Sun bubbuga ƙofar kamar me amma na kasa tashi.

Nikam wani wahalalliyar barci ne ma ya ɗauke ni.



Dad a ɗan ruɗe ya shigo gidan dan kuwa Allah ya dasa musu soyayyata kamar me.


Lokacin har an yi sallar isha'i, dan daga office ɗin sa zuwa nan akwai nisa, ina jin muryan Dad na tashi daga kwancen, bayi na shiga na yi wanka tare da alwala, lokacin dana fito na dena jin motsin kowa a wajen, sallah na yi magrib da isha'i sannan na zura kayan barci, yunwa nake ji sosai dan haka na buɗe ƙofar na fita ina ƙara haɗe rai.

Ga yunga da ya cinye Ni hakan yasa tafiyata ta koma kamar mara lafiya.

Mom, Dad, da A'isha suna tsaye kaman wa'inda aka yi wa mutuwa, sai suka ganni a falon, da sauri Mom ta nufoni tana riƙeni dan ganin kaman zan faɗi.

“Inayah....Inayah....." Mom ta faɗa sai na kalleta.

“Meke damunki?.” ta tambaya idanunta na cika da hawaye, a cikin raina kuwa nishaɗi ya kamani dan kuwa yau *Film* ake yi a gidan nan, tun yanzu ƙwanda na dinga practice.



“Shalele ba ki jin muna dukan ƙofar ɗakin ki bane?.” A'isha ta faɗa tana riƙoni.

Har lokacin na ƙi magana. Dad sai ya riƙo ni yana kwantar da murya.

“Tell me My bloodline. What's wrong with you?.” sai ga hawaye ya zubo min sai ya sa hannunsa ya sharemin.

“A....A...abinci.” na faɗa da ƙyar, ai da sauri A'isha ta nufa Kitchen, Tea ta haɗo min sannan Dad ya ban a baki, sai da na ƙoshi sannan na ce.

“Ku kwantar da hankalinku, kawai wani abu ne ke damuna....." Na faɗa cikin sanyin murya.

“Shalele faɗa min meke damunki, ko kina wa'inda suka fimune?.” na girgiza wa Mom kai.


A cikin raina kuwa dariya na ke yi, sai daurewa nake yi saboda karta kuɓuce min.

“Kuna so na zama Doctor ko?." Suka ɗaga mun kai.

“Ra'ayin ku shine nawa, akwai wata ƙawata, tare muke, ina sonta sosai, to ra'ayin mu ya zo ɗaya, ita dama a can wajen iyayenta za ta ƙarasa, shine jiya suka ɗauke wai a can za ta yi waec....... So nake mu yi University ɗaya......dan Allah ku taimaka.........” sai na fashe da kuka, kallona kawai suke yi dan ba su fahimci in da na nufa ba.

“Yanzu me kike so?." Dad ya tamabaye ni.

“*University College of Medicine (LASUCOM)*......” da sauri Mom ta ce.

“You mean Lagos State University?." Na ɗaga mata kai.

“Alfarma ce kawai, amma in ba ku so shike nan, dama kawai ina so ne mu yi karatu tare.” da haka na miƙe tsaye ina son na wuce, ga wani ɗan jiri da ke ɗibana.

“Ki yi ƙoƙari a weac Ni kuma zan kai ki.” sai na rungume Dad.

“Dad har Legos....gaskiya a'a?." Faɗin Mom, ita dai A'isha kallon mu kawai take.

“Shike nan, in dai ɗayan ku bai so ba za Ni ba." Na faɗa ina barin falon, da ido suka bini har na ɓa ce musu.


“Inayah problem, yanzu duk makarantu sai na can? Kuma

3 / 9