YAR NOLLYWOOD BOOK ONE by PRETTY SK.txt

Author :  Pretty Sk Category :  Hausa Read

Chapter   2 / 9

3K to 6K   out of 25.8K words

kamar yadda ta yi maganar nima na ce.

“Ni sam ba haka ba, ba zan yi irin wannan ba, kuma Ni a maid nake so na fito, a ban kaya ne mutumci zuwa ƙasan gwiwa kamar dai wannan uniform ɗin nawa.” shiru ta yi tana girgiza kai tare da min wani irin kallo.

“Fita...... Fita.” ganin yadda ta haɗe fuska yasa na fita da sauri, dan Ni ko a jikina, ko tsoron ta faɗa masu Dad ban yi saboda nasan tana sona ba za ta so ta ga ina kuka, kuma Ni Ko sun sani babu mai hanani film ɗin NOLLYWOOD 🔥.



********** ********** ******

*★GIƊAƊO MANSION★*

_______Babban gida ne wanda yake da get guda huɗu, cikin gidan kuwa kai ka ce gari ne guda, dan kuwa Mansion ɗin ba ƙarami bane, gida ne mai hawa huɗu. Masu gadi kuwa a ƙalla sun kai 40 kowanne suna riƙe da bindigu, sannan duk wanda zai shiga sai an yi bincike kuma sai wani daga gidan ya tabbatar da wajensa zai je.


Parking lot kuwa motoci ne ajere kala-kala masu tsaɗa.

Masu gadi ne suka buɗe get ɗaya sannan wata mota ta kunno kai zuwa cikin gidan, a hankali motar ta faka a jerin motocin dake wajen, sannan aka buɗe, wata budurwar falullata ce ta fito tana kulle motar, farace masha Allah, a ƙalla ba za ta wuce 21yrs ba, cikin gidan ta nufa tana taunar chewing gum a natse.

Ƙofar mai aiki da nunfashi ne, ya jin an matso yake buɗe wa, shiga ta yi wani tanƙameman falo mai ɗauke da kujeru ba iyaka, ga dukkan alamu gidan Family House.

“Sarah." Da sauri ta juya dan jin muryan mahaifiyarta. Ilai itace murmushi ta yi tana nufan ɓangaren da take.

“Ya makarantar." Mahaifiyar ta faɗa cike da kulawa.

Ko ba'a faɗa ba ana ganinsu anga jini ɗaya, dan suna kama da macen dake zaune, Babbar mace mai jiki masha Allah, ga haske ga ƙyau, kana ganinta kasan jinin Fulani ne tsantsa.

“Alhamdullah.” budurwar ta faɗa cikin sanyin hali.

“To masha Allah, je ki huta.” sai ta miƙe har ta fara tafiya sai ta ji muryan wani saurayi daga stairs na uku.

“Darling.....Darling.” tsayawa ta yi cak sannan ta ja ƙaramin tsaki ta na ɗaga kanta, da fuskarsa ta fara cin karo yana mata ɗan iskan murmushi.

“Ki jira ni ina zuwa." Ya faɗa yana fara saukowa, daga in da yake zuwa wajenta akwai nisa sosai, amma tsayawa ta yi cak har sai da ya sauko.

Saurayi ne wanda a kallo ɗaya za ka gane ɗan Allah ya shirya ne, dan kuwa shigarsa ma ya bayya haka, riga da wando ne jikinsa ƙananan kaya, sai wasu sarƙoƙi a wiyarsa kusan guda uku, haka hannunsa ma akwai su banda sosai, harda ɗankunne yake da shi a kunnuwan biyu. yana da ƙyau sosai, gashi dogo mai cika ƙirji, Babban star ne na fina-finan NOLLYWOOD, kuma tantairin mara jin magana dan kuwa kaf gidan shine babban ɗan Allah ya shirya, har zanen tattoo yana da shi a gefen wiyarsa ɓarin dama har ƙasa, ina da ka mai wani lafiyayyen zanen wata dabba.

“Darling ya kike?.” ya faɗa da zazzaƙar muryarsa kuma cikin ɗan taushi.

Saurayine ƙyaƙƙyawa dogo mai hasken fata sosai, sai dai shigarsa yana rage masa ƙyau sosai.

“Lafiya." Ta faɗa da ɗan rawar murya.

“Nasan kin gaji, je ki huta zuwa an jima zamu haɗu .” ɗaga mai kai ta yi sannan ta fara tafiya har da gudu-gudu ta hau stairs.


A hawa na biyu ta yi kwana room 25 nan ta buɗe ta shiga. Tana shiga ta kulle da murza key.


Hijab ɗin jikinta ta cire tana zama a ƙasa, ɗabas, ita har ga Allah ta tsana rayuwar *GIƊAƊO MANSION,* domin kuwa irin matsalolin dake cikin gidan, ji take dama Allah ya sa an haifota a talaka masu rayuwar kunci da ya fi mata akan rayuwar gidan *GIƊAƊO MANSION*


Gida mai yawar al'umma, mai mabanbanta mutane da halaye, family ɗaya ne dukka amma yadda kasan gidan haya ko gidan yari, haka ake rayuwa a wahale babu damar rabuwa saboda wata *WASIYYA* guda ɗaya da ya zama silar zamansu a gidan, wato *WASSIYAR GIƊAƊO* wasiyyar da ya zama suka zama tsintsiya wanda bai da madauri kwata-kwata.



Sai da ta jima sannan ta miƙe ta shiga bayi, wanka ta yi sannan ta sauya kaya, ba ta fita har sai da ƙarfe 8:00pm ta buga wanda lokacin cin abincin dare ya yi, ko ba ka jin yunwa dole ka hallaci cin abinci safe da dare, wannan dole ne, da safe ƙarfe 7:30am dole kowa ya fito ko da ba za ci komai ba, sai ka fito.


Doguwar riga ne jikinta sai ta yafa vail sannan ta fita. A hankali take tafiya kamar wanda ƙwai ya fashe nawa, dama ita haka take da sanyi.

Ji ta yi an bangajeta da sauri ta riƙe ƙarfen stairs ɗin da sauri, tana bin wacce ta buge ta da kallo. Girgiza kai ta yi tana ƙarasa sauka, sun saba da irin rayuwar nan a cikin gidan, balle ƴan ɗakinsu.


Daga ko wani ɓangare sauka ake yi zuwa wajen cin abinci, ita ma nan ta nufa. Babban Dining area ne wanda yake da kujeru 50, kowa zama yake a nasa, gaba ɗayansu su 47 suka halarta wajen, babu mutum ɗaya, dan gaba ɗaya ƴan gidan su 46 ne yara da manya.


Manya da yara duk suna zaune, amma babu wanda ya fara cin komai.


Sarah tana saukowa ta zauna gefan mahaifiyarta tana ɗan yaƙe kamar yadda ta saba.

“Ina Ayan? Shi kullum sai ya ɓa ta lokaci, salon ayi ta zaginsa” Bafullatanar dake gefen Sarah ta faɗa tana haɗe fuska.

“Ummee ku mai uzuri, zai fito yanzu." Sarah ta faɗa tana mai kallon wanda ke zama a gefan ta, Ahmad ne wanda aka kira da A.G. murmushi yake sakin mata har da kashe mata ido.

“Ummee Barka da dare." Ya faɗa yana kallon mahaifiyar Sarah.

“Yauwa." Ta faɗa tana kauda kanta da kuma jin tsanar Ahmad a cikin ranta, kaf gidan shine ɗan Allah ya shirya, kuma aka rasa duk cikin samarin gidan wa za'a Sarah da shi sai shi.


Manya maza guda huɗu uwaye 6 kowanne matansa biyu, amma biyu sun rasu, sannan kowa suna da yara mata da maza.

*GIƊAƊO* shine kakan wannan dangin wanda yaransa biyu ne kacal Yusuf da Yunus sai yaran ƙannin sa wanda ya mai da su na shi, Adam da Musa, gaba ɗayansu ya raina cike da so da ƙauna.

*GIƊAƊO* mutum ne mai tsatstsaurar ra'ayi, sai Allah ya bashi yara masu matukar biyayya. Shi ya gida wannan tangamemen gidan kuma anan ya yi rayuwa har mutuwarsa.

Sai dai ya mutum ya bar *WASIYYA, kan cewa, so yake duk su aura mata biyu, su haihaifa, kuma su dinga haɗa aure a tsakanin su, ko da wasa kar wani nasu ya auro bare, ya zamana jininsa shine a cikin zuri'arsa.*

Da haka yaransa suka ɗau wannan wasiyyar da muhimmanci, kuma ba su yi wasa da shi ba, ƴan dangi suka auro dukka, suka haifafa kuma suke haɗa aure, ko mutum ya so ko bai so ba haka nan yake yarda, a wasa-wasa, an yi aure 8 na yaran gidan. Yaron Musa ya aura yarinyar Yusuf, sannan yaron Yusuf ya aura yarinyar Adam, sai yaron Yunus ya kuma auren yarinyar Adam.


Haka suke haɗa wa, kuma a gidan kowa ke rayuwa, yanzu mata huɗu suka rage da maza biyar, sai kuma yara masu tasowa.

“Ina Ayan?." Faɗin Baba Adam wanda shine mahaifin Ayan da Sarah da wasu biyu.

“Kunsan halinsa ai, sai ya gama ɓa ta mana rai zai fito." Matar Yusuf ta faɗa wacce ita ce mahaifiyar Adam (Ammee), kuma ƴan ɗakinta sun fi kowa rashin mutumci da iskanci, duk dan Ammee tana ganin ai dukiyar GIƊAƊO ta su ce, ba ta su Adam ba, dan su yaran ƙaninsa ne.


Abubuwa dai a gidan babu daɗi sam, ga uban dokoki mara sa tsari. Sai dai babu wanda yake da ikon furta komai idan Iyaye maza huɗun nan suka yanke.

Gaba ɗayansu ƙyawawane sai dai wasu sun fi wasu haske, amma gaba ɗaya jini ɗaya ne a jikinsu na cikakkun Fulani.

Cike da izza da kamala yake takowa, tafiya yake kaman wani basarake ko yarima, ƙyakykywan saurayi ajin farko, dogo mai cikar haiba da kalama, wanda a kallo ɗaya za ka fahimci tarin ni'ima da Allah ya yi mai, yana cikin faɗin ƙirji, ƙyawawan idanuwa masu rikata mata, Ayan kenan, gagara kowa a gidan sai mahaifansa.


Shine mutum ɗaya, wanda yake faɗa da tsarin gidan, be da wasa ko kaɗan, abu idan ba ya zama dole ba, ba ya magana, sam be da surutu haka yake, gashi shine duk yafi mai da hankali akan GIƊAƊO'S INDUSTRIES duk da ba kullum yake zuwa ba dan Lectural ne na Islamic studies anan Kad-poly. Sai dai duk da haka yake da mahassada a gidan.


Amma shi sam be damuba ko ta kansu baya bi dan rayuwarsa kawai yake yi, yana da tsare-tsaren sa ba irin da gidan ba duk da wasu lokutan iyayensa na taka mai burki, da yake mutum ne ma mai biyayya sai yake musu biyayya kamar yarda suke so, badan yana so ba...................✍️
END.

> Kunfa ji Jama'a. AYAN, AHMAD (A.G) DA SARAH, da alamun kuna cikin taurarin labarin🥺.

> GIƊAƊO MENTION 😬😬


> WASIYYA 🙆

> Mu haɗu dan yi wa Inayah karatun natsuwa🤣, ga duk kan alamu a bauɗe take.


*PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:

📘 *DAGA INA TAKE* free book
📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book
📙 *BARRISTER* Paid book₦300
📕 *THE SLAVE* free book
📒 *ZAMU HAƊU* Free book
📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300
📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300
📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500
📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book
📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_
📔 *YAUDARA ZALLA ❤️*
HIKAYOYI kuma sune :
*SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥*
*SARKIN MU🤣*
*MOHINA DA MATSAFIYA💀*
*RAMUWA💀🔥*




*𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅*

_TAP THIS LINK TO JOIN MY GROUP👇_
https://chat.whatsapp.com/Be241ldCcFS5kAxa5V8lpy

_TAP THIS LINK TO JOIN MY CHANNEL👇_
https://whatsapp.com/channel/0029Vb64I4aGzzKQsSeaKA2K

_TAP THIS LINK TO JOIN IN AREWAPEN 👇_
https://arewapen.com/u/prettys01



💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.*

Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥
*Keep shining, JAW family!* 🌺

*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*



𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅

Story and writing✍️
```PRETTY SK```
~SAKINA ABDULLAHI~
> *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️


✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽



E.P5️⃣⏩6️⃣


_______Sai da ya gaishe da kowa sannan ya zauna gefan Ummee wacce ke sakar mai murmushi.

“Kai kullum sai an jiranka?." Sai ya shafa tarin gashin kansa mai tsayi da laushi sannan ya ce.

“I'm Sorry Abba." Ɗan tsaki Abba ya yi sannan ya ce.

“Ina Daughter?.” take fuskar Ayan ya haɗe dan shi a duniyar nan ya tsana ganin Daughter (Ruma.)

“Abbana ganin nan."


Kusan gaba dayansu suka kalla in da suka ji muryan na ta.

Sarah a cikin ranta ta ja tsaki, domin kuwa Ruma ba ta hankali sam, wani wando da riga ne ta sanya wanda sun matseta kamar ba ƴar Fulani ba, mutane masu ado da kunya, ita kam sam ba ta da kunya, sanya ƙananun kaya a wajen ba komai bane, kuma babu mai yi mata magana.

A haka ake so a haɗa ta Ayan, shi kuma baya santa, sai dai aurenta shi zai kawo kusanci tsakanin Umminsu da Ammeen Ahmad dan kuwa Ruma ƙawar Ahmad ce.

“Daughter zauna.” Abba ya nuna mata waje kusa da Ayan wanda nan ne muhallinta.

“Ruma ba kunya, za ma ta yi fa a can tana jiran shi." Ahmad ya faɗa yana kallon Ayan, shi ai Ayan be ma san yana yi ba sam.

“To ina ruwanka kai kuma.” faɗin Baba Musa.


Daga haka suka yi addu'an cin abinci sannan aka fara ciki, abinci ne kala-kala sai ka za ɓa, kowa da wanda yake so kuma shi yake ci.

Sarah ta kalla agogo 8:38pm, at least an ɓa ta sama da 39mnt ana taruwa kafin a fara ci.


Daga masu cin abincin sai masu tsakura sai masu aika wa juna kallon soyayya, da masu aika wa juna na ƙiyayya, haka dai kowa ya gama sannan aka yi addu'a aka tashi.



Babu abin da ya ci a wajen dan kuwa a ƙoshe yake, ya dai zaune ne kamar yadda ya zama wajibi ga kowa.

A hankali ya ke tafiya yana hawa stairs, da sauri ya ji ansha gabansa, ko be kalla ba yasan Ruma ce.

Ƙasa yake kallo dan haka da fararen ƙafafunta ya fara cin karo, murmushi gefan baki ya yi, muryansa mai cike da amo da sauti ga sanyi ya ce.

“Matsa min daga hanya.” cike da salo ta ɗan ƙara matsawa dab da shi.

“Baby me yasa kake min haka? Karka manta nice matarka ta gobe, idan ba mu saba tun yanzu ba sai yaushe?.” tsaki ya ja sannan ya kewayeta yana ci gaba da tafiya. Ƙwafa ta yi sannan ta sauka babban falon.



Sarah kamar ta fashe da kuka, dan kuwa ta cika ta yi fam, barci take ji gashi tana da assignment amma Ahmad ya hana tashi. Tun ɗa zu yake mata hira wanda ko fahimtarsa ba ta yi.

Ita sam ba ta yi da ce ba, ta so ace Mubarshir aka zaɓan mata sai dai Ahmad ya nuna maitarsa akan ta, shi ne aka bashi ita. A lokacin hauka ne kawai ba ta yi ba.

“My Heart, bara na barki ki je ki kwanta." Da sauri ta miƙa tsaye, sai ya sa hannunsa ya mai do ita kan kujera, yana gab da ita, har suka jin numfashin juna suke, shi dama besan kunya ba, dan kuwa a finafinan da yake yi, har kiss ɗin ah-lul kitab yana yi, ga shi duk Film idan ya yi sai ya tura mata ko kunyar irin baɗalar da yake ba ya yi, ba ya ji, in ta yi magana sai yace wai “Akwai lession a ciki, karki damu faɗa karawa muke yi.”

A lokutan sai ta ji kaman ta rufesa da duka amma babu dama.

“Tell me something special." Ya faɗa har da kashe mata ido ɗaya.

Tasan Idan ba ta faɗa mai kalaman soyayya ko ɗaya ba ce to za su kwana anan.

“I love You." Ta faɗa a hankali. Murmushi ya yi.

“So nake ya fito daga zuciyar ki.” ya faɗa yana juyo da fuskarsa sai tin na sa.

“I love you." Ta kuma faɗa har da hawaye.

“Me too. Mai da hawayen nan ko wallahi na lashesu da harshe n....” da sauri ta haɗiye kukan, hannun ta ya saki ai kuwa da gudu ta haura sama, dama sun saba in da suka zauna taɗi da kuka take wucewa.......

(Pretty ta ce ku ji wani bala'i.)



*********** ***********

Ina cikin ƙaton bargo duk da ba sanyi ake ba, jin ana buga ƙofar room ɗina, yasa na dafe ƙirji na ina fatan ba Mom ba ce.

“Inaya ki buɗe, nasan kina jina." Na ji muryan Mom, haɗiye miyau na yi sannan na yaye bargo.

“Ina babban tauraruwa ace ba zan iya kafcen Film ba." Na faɗa ina sauya mood ɗina, dama na ƙware wajen basaja.

Ƙofar na buɗe tare da yin miƙa da hamma. Ko da Mom na harararta ban sauya ba duk da gaba na yana faɗi.

“Ban wayata?.” Mom ta faɗa sai na zaro ido ina dafe kai.

“Mom dama ban dawo miki da shi ba!?." Da haka na juya wajen extension ɗin ɗakin, wayar Mom na jikin chargi, dan kuwa tun jiya na sato shi, kallo nasha sosai.

“Na manta ne, dan da wuri na gama assignment." Na faɗa ina miƙa mata wayar, fizga ta yi.

“Bance ki dena ɗau min waya ba, sai kin tambaye Ni." Da sauri na rungumeta ina murmushi, lokaci guda kuma ina muryan kuka.

“Ki ya ƙuri, assignment ɗin da wuya ne, amma ba zan sake ba, kuma na ce kima Dad magana ina son waya amma kin ƙi." Na kai nan ina ƙaƙalo kuka, take kukan ya zo harda uban hawaye ka ce dukana aka yi.

Mom jikinta ne ya yi sanyi, sai ta sake ni tana sharemin hawaye.

“Ki dena kuka, kuma kinsan waya sai kin gama secondry, ki daure saura kadan kinji shalele." Na ɗaga kai Kamar wata mai ladabi.

“Kin yi salla?." Na ɗaga kai duk da ƙarya nake yi.

“Yauwa shi yasa nake sonki, shirya kafin A'isha ta cinye min ke da faɗa." Da haka Mom ta fita.

A'isha dake bakin kofana ta shigo tana min wani kallo.

“Hmm Mom na ruwa, ba ta san ƴar basaja ta haifa ba.” hararar ƙasan ido na yi mata, ina share hawayen.

Ganin jikina a mace ya sa ta ƙaraso tana ta ɓa Ni.

“Dama kukan gaske kike? Me aka miki?." Ta faɗa tana zama gefena, take na sake fashewa da wani kuka mai motsa zuciya.

Jikinta ne ya yi mugun sanyi dan kuwa A'isha na mugun so na. Take ita ma hawaye suka fara cika idanunta dan ko da wasa ba ta son wani ya sani damuwa.

“A..A... Auntyna.." na faɗa ina rungumeta.

“Me aka miki?.” ta faɗa tana raba jikinmu. Kallonta na yi sosai ganin hawaye tab idanunta, sai na tsaya da kukan.

Take na fashe da wani mugun dariya ina dafe cikina, harda kwanciya kan gado.

Kallon mahaukaciya ta yi Galala, sannan ta tureni.

“Dama na ƙarya ne?.” ta faɗa tana miƙewa tsaye kuma a fusace. Sai da na yi dariya mai isata sannan na miƙe ina dafa ciki.

“Wayyo daɗi, haka zan dinga tsuma masu kallona a tv, kinga baiwa ko?." Na faɗa ina share hawaye, ga kuma dariyar ya ƙi barina.

“Amma ya kika ga scene ɗin ya bada citta.......” da wani irin zafin nama ta yo kaina, dama a ready nake.

Da gudu na shige restroom Ina murza key. Ina ji tana dukan ƙofar Ni kuma na ci gaba da dariya kamar sabon kamu.


Wanka na yi tare da alwala, na ƙosa Driver na ya dawo dan bansan tuƙin A'isha, ya yi tafiya ne na sati ɗaya, shi yasa take kai ni school.


Bayan na fito wanka na kullu room ɗina sannan na yi sallah, bayan na idar na shafa mai. Uniform na sanya, riga da ƴar ciki, sai legis sannan na tsaya gaban mirrow.

Gashin kai na mai tarin yawa na ta je sannan na ƙulle, hular na sanya

2 / 9