YAR NOLLYWOOD BOOK ONE by PRETTY SK.txt

Author :  Pretty Sk Category :  Hausa Read

Chapter   6 / 9

15K to 18K   out of 25.8K words

number familyn su, in ya so su sai su bamu number ainiyin iyeyenta.’ a lokacin har wani zufa na ji ya yanko min, amma na daure na ce.

“Dad ba sai mun yi haka ba, kawai mu bari in munje can sai mu nemeta."

‘Lallai ba ki da hankali, Jahar Lagos an ce miki wajen wasa ne balle unguwar Ikeja.' Mom ta faɗa, take na fara zazzaɓin ƙyarya haka aka dai fasa zuwa.





“Wow" na faɗa ina kallon wani unguwa da muka shiga bayan munyi tafiya mai tsawo.

Yadda kasan estate ɗin mutum ɗaya wajen, gaba ɗaya gidajen iri ɗaya kuma pentin ma iri ɗaya.


Ɓangaren dake kallon wannan ɓangare kuma, wani babban gatangane wanda ya cinye tsawon wajen. Ciki muka shiga ashe nan ne school ɗin, da mamaki nake ƙare ma school ɗin kallo, dan kuwa makaranta ta fi unguwar mu girma.


Ga manya-manyan gidaje, ajujuwa suma ɓangare-ɓangare, gwanin ƙyau. Ga tsirarun mata da suke sanye da fararan kaya, wasu kuma, farin riga da blue trousers, wandon ne dai kala-kala gwanin ƙyau.


Hmmm kuɗi duniya ne, dan kuwa muna shiga office aka basu certificate, nan da nan Dad ya ƙarasa komai sannan muka fito haraban school ɗin.

“Sir gobe da ƙarfe 7:30am, nan za ta zo, za su ba ta uniform da takaddu, sannan a faɗa masu lokacin zuwa, dan har an fara karatu." Wani wanda ga alamun, malami ne a wajen, ya faɗa.

“Okay Sir thank you." Da haka suka kuma gaisawa, sai ya wuce.

“Can ne Hostel." Dad ya faɗa yana nuna min ɓangaren dama.

Hostel ɗin ne kam, dan kuwa har da igiyar shanya na hango, take na haɗe rai dan banson zaman ciki.


Ko iya zuwan mu nan, na fahimci mugun tsaron da suke dashi, dan ga jami'ai nan ta ko ina, babu daman fita. Baki na ta ɓe ina haɗe fuska.

Sai dai da mamakina muka nufa mota, hawa muka yi sannan muka bar school ɗin, a cikin jerin wa'inna gidajen, na ga mun tsaya a number U.7.

Madaidaicin gida ne wanda muka shiga da mota har ciki, ba laifi yana ƙyau sosai, key Dad yasa tare da buɗewa, Ni dai binsu kawai nake yi.

Ƙaramin falo ne wanda akwai komai na more rayuwa, kujeru, fridge, A.c, TV da sauransu.

“Wow Dad wannan gidan ai ya yi ƙyau sosai.” sai ya ɗaga min kai yana cewa.

“Allah ya so munyi magana da wuri da ba lallai mu samu ba, gaba ɗaya gidajen nan na haya ne, wanda iyaye ke haya wa yaransu. Suna da dokoki sosai wanda duk sai da na bi. Akwai security guard guda uku da na aje miki, sannan ku biyu za ku zauna ke da wata yarinya, ga ɓangaren ki can." Ya kai nan yana nuna min wani ƙofa.


Ban damu da wasu guard da yace ba na rungumeshi ina mai godiya.

“Sai ki kula, dan kuwa yarinyar ba ta son hayaniya, da kyar Dad ya samo yarinya irin wacce za ku ƙaru da juna.”

“To Mom.”

“Kuma ki kama kanki, kar kiga bama kusa ki samu daman aikata abin da be kamata ba, to ki sani Allah yana kallonki, dan mun yarda dake shi yasa muka kawo ki nan. Ki mai da hankali cikin shekara uku ki kammala, in ya so lokacin sai mu aurar da ke, a gidan mijin ki sai ki ƙarasa.” murmushi na yin gaba.


Zan iya cewa ban taɓa tunanin wai ni zanyi aure ba, kwanta-kwata baya cikin tsarina nan kusa, ji nake babu wanda zai iya rayuwa da Ni, domin Ni ɗin nan sai a hankali.


Ƙofar na tura tare da shiga, da wayata na yi amfani wajen kunna hasken ɗakin.

Ɗakin ya yi kyau sosai, babu wasu tarkace, bed, mirrow, wardrobe da bookshelf.


“Gaskiya gidan nan duniya.” na faɗa ina hawa kan gadon, daga nan na duba toilet.

Komai ya burgeni, dan haka na koma falo, nasan su Dad sai gobe zamu koma Kaduna.


Abinci aka kawo mana muna ci sosai, sannan suka tayani jera kayana, kayan abinci muka kai Kitchen. Komai dai ya yi need.



Zaune muke a falon muna ɗan hira sama-sama dan jikina ya min tsami saboda na jima ban fita ba.

“Yanzu Dad ko mai girki ba za ka ne man min ba, Ni ka rage mutum ɗaya a cikin wa'incan samudawa, a kawo mai aiki." Na faɗa ina tuna ganin da na yi musu ɗazu, wallahi manyan mutane masu kaman Samudawan.

“Hmmmm da kanki za ki dinga girki dan kuwa karatu da girki na kawo ki.” sai Mom ta amsa maganar.

“Akwai classes na koyar da abinci a YouTube, su za ki dinga bibiya, sai ki dinga practice kina ci, a kwana a tashi za ki iya."

“Mom ta ya zan kowa girki a waya......Ni dai a'a, kinsan ban zama a gida sai Sunday shi kuna hutawa nake yi, sauran ranakun daga safe har yamma ina school, ko na dawo ban iya wani abu.”

“Eh, yanzu ai kina da time, ki yi karatu ki yi girki, kuma a cikin school ɗin akwai ɓangaren da suka koyar da karatun islamiya duk weekend shima na miki register, sai ki dage dukka." Dad ya faɗa yana gyara kwanciya akan kujera mai uku.


Mom na kalla na yi ina marairaice fuska, murmushi ta yi tana ce min.

“Idan yanzu ba ki iya girki ba sai yaushe? Sai after 3yrs kike so ko me? Kina gamawa aure za mu yi miki, ya rage kanki ki koya ko dangin miji su zageki.” murmushi na ya ina miƙewa tare da cewa.

*“Akwai uban da ya isa ya zageni ne?. Hmmmm wallahi babu dan kuwa sai na rama.”*

“Ban ji me kika ce ba."

“Mom ba da ke nake ba." Na faɗa ina shigewa bedroom.


Anan muka kwana ni da Mom, Dad kuma a falo, washegari da safe suka rakani school, sai da aka ƙarasa min komai sannan na yi sallama da su.


Kuka na yi kaman ƙaramar yarinya, gashi babu daman binsu, haka suka tafi suka barni ina ta rusa kuka, Allah ya so iya kuka ne banda birgima.


Sai dai ina cikin kukan na tuna dalilin zuwa na nan state ɗin, take na yi shuru ina goge hawayena.


Sai washegari zan fara shiga class, da haka na juya zan shiga gida, ɗaya daga cikin wa'inna manyan maza suka buɗe min na shiga, ina kuma fashewa da wani sabon kukan dan kuwa banson kallon su.


Ina shiga room ɗin na kwanta kan kujera ina ƙara fashewa da kuka, ko ma yayane rabuwa babu daɗi, akwai zafi.



Hatta su sai da suka yi kuka, dan ba su ta ɓa yin nisa da ita ba, kullum ina tare da su, ga irin ƙaunar da suke min.





Mom ce ta rungume Dad tana hawaye.

“Yanzu shike nan, na yi nesa da ƴa ta.......... tun farko shi yasa na ce banso amma......" Sai kuka ya ci ƙarfin ta.

“Kiya ƙuri, mu daure shekara 3 ba yawa, kuma duk end of the year ana basu hutu.” sai ta kalla wayarta wanda sunana (SHALELE ❤️) Ya fito kuma shine kira na 7 da ta fara jero mata.

“Sai mun koma gida zan ɗaga, bayan ta karya min zuciya shine za ta dameni da kira.” Dad murmushi ya yi yana goge hawayen da ya taru mai, ai suna hawa mota yasa wayarsa a flighmode dan yasan halin Inayah za ta damesu da kira ne kuma da zai ce ta biyo su ba za ta yarda ba.....
.................✍️
END.

> Update ba yawa ko... I'm sorry, ku yi comments sosai, an jima na kuma saki muku wani.


> Toh fa Inayah an shiga Lagos, fatan sa'a.




💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.*

Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥
*Keep shining, JAW family!* 🌺

*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*



𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅

Story and writing✍️
```𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊
```
~SAKINA ABDULLAHI~
> *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️


✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽



E.P2️⃣1⃣⏩2️⃣3⃣.


*Aisha*

___________Jikinta a mace ta wuni a school, ko bayan da ta koma gida hakan ta kasance, duk da mai aikinsu ana take kwana, ta ji duk babu daɗi.


Da misalin 5:21pm wayarta ya hau ringing, tana dubawa ta ga masoyinta, ɗauka ta yi tana kai kunninta.

“Aishata, iyayena sun ce na kawo ki wajensu yanzu, ya za'a yi? kinsan banson su Dad su san plan ɗin nan." Shuru ta yi sai ta ce.

“Ka zo muje, zan kira Mom na ce zan ni wani waje.”

“Ba matsala?.” ya faɗa a hankali.

“Eh babu." Da haka ta katse kiran.


Number Mom ta Kira, bayan Mom ta ɗauka, ta ɗauki permission na fita dan siyan abu, Take Mom ta yarda.


Da haka ta miƙe, bedroom ta nufa, shiryawa ta yi sannan ta zura hijab ɗin ta, sai dai me, gabanta ne ya fara bugawa ninkin bugawan da yake yi.


Addu'a akwai take ta jerowa duk wanda ya zo bakinta, ta dai sanar wa mai aikinsu za ta fita.

Motarsa ce ke dake daga gefan gidan su, nunfashi ta ja sosai sannan ta nufa tana jin gabanta na tsananta bugu, amma haka ta daure ta isa.

Buɗe wa ta yi ta shiga sa sallama.

“Wassalamu alaikum Beauty.” ya faɗa yana kunna motar.

Da haka ta yi shiru, ta ci gaba da addu'oi.

Motar ta ɗau hanya, dan ma tsakaninsu ba wani nisa.


A bakin katafaren gidansu ya yi parking, kallonta ya yi kuma ga alamu tana cikin damuwa, ya kashe kiran.


“Aisha, mu koma gida kawai, ba son na cutar dake, sai dai ba mu da wani hanya sai wannan. Kina sona nima ina ƙaunarki." Take zuciyarsa ta ce. (ƙarya ne, so kake ka ƙyauce ma auren Ruma)

Sai ya rintse idanunsa.

“Yaya Ayan karka damu, mu shiga." Ta faɗa cikin dauriya.


Horn ya yi aka buɗe mai get ɗin sannan ya shiga.

Maimakon ya shiga ta babban falo sai suka kewaya suka shiga falonsu Abba.


Babu komai a babban parlourn da ya haɗu kaman fadar sarki. A'isha ta san duk kuɗin Dad ba zai kai na wa'inna ba duk da su haɗaka ne.


“Zauna." Sai ta zauna kan carpet. Shi kuma ya bi wata ƙofa ya fita.

Tana zaune tana jan Tally counter da kullum ke yatsarta, ba'a ɗau lokaci ba, ta ji an fara shigowa ciki, sai dai ta kasa ɗaga kai ta kalla mutanen da suka shigo.


A hankali ta ɗaga idanunta ta kalla manyan maza guda huɗu wa'inda suka yi mata kwarjini da cika ido.

Gaishesu ta yi cikin rawar murya, biyu suka amsa biyu kuwa wani irin kallo suna watso mata.

Ayan kuwa kusa da ita ya koma shima ya zauna, sai a lokacin ya ji wani ɓari na zuciyarsa na, hanasa wannan ɗanyen aikin amma ina, (Yana cikin zanen ƙaddararsu wannan ƙaryar, kuma za su yi nadama a lokacin da ya ƙura musu, koda wasa ba su san hakan zai shafi rayuwar aurensu ba......😓)


“Yarinya ya sunan ki?.” muryan Abba cike da kamala ta fito.

“A...A'isha.”

“Mai babban suna kenan, ya ce ke yarinyar Alhaji Musa ne ko?."

“Eh."

“Menene alaƙarki da Ayan?.” faɗin Baba Yusuf cikin ɓacin rai.

Miyau ta haɗiye dan kuwa Ayan ya ce mata.

_(Ni ce musu na yi, akwai babba alaƙar dake tsakanin da ke wanda in ban aure ki ba, akwai matsala, hakan zai iya ɓa ta musu suna da Martabansu.)_

Idanunta ta rufe sannan ta buɗe.

“Saurayina ne." Ta faɗa cikin wani irin rauni.

“Hmmm ba ki san da cewa *GIƊAƊO FAMILY*, ba su auren bare.”

“Abeey........"

“Shut up Ayan. Ba da kai nake ba.” Baba Yusuf ya faɗa cikin ɓacin rai.

Take cikin A'isha ya kaɗa wanda har ɗan ƙara sai da ya yi (Ƙur-ƙur)

“Eh na sani." Ta faɗa a natse.

“Kuma shine kika ci gaba da tarayya da shi. Ko dai dukiyarsa kike kwaɗayi?."

Ya watso mata maganar wanda ta ji kaman ruwan zafi aka watsa mata.


Tasan suna da kuɗi, kuma da za su raba su huɗun nan, babu wanda zai wuce Dad, sai dai su zo kai da kai.


Take wata irin ƙwarin gwiwa ta saukar mata dan kuwa yanzu faɗa za ta yi da soyayyar Ayan, in ma ta ɗaure ta ci, ko ta faɗi, wanda shine zai rabata da shi har abada, dole ta fuskanci wannan al'amarin da kanta.

Take ta ɗaga kanta ta kalla wanda ke maganar sannan ta ce.

“Ko ɗaya, badan kuɗi ba ne nake son Yaya Ayan, domin cikin kuɗi na tashi, kuma wanda suka fi shi kuɗi sun nemeni kawai........”

“Kawai mene?." Baba Yunus ya faɗa shima rai a ɓace.

“Ku kwantar da hankalinku, ku yi mata magana cikin taushi.” faɗin Abba.

Dama Ayan ya nuna mata hoton maza biyu, Ya ce duk mai suka ce karta yi musu, amma sauran komai ta ce.

“Yarinya muna jinki. Me yasa Ayan ya ce aurenki ya zama dole, kuma in be aure ki ba akwai matsala?.”


A hankali ta kalla Ayan, sai ya ɗaga mata kai.

“Daga gani nasan kai ne mahaifin Yayana, dan Allah duk abin da zance kar ka hukunta shi da babban abu, kuskure ne mun riga munyi cikin rashin sani. Ni ɗalibarsa ce, mai sonsa da ƙyaunarsa. Tun baya kulani har ya fara kulani, a kwana a tashi, ya fara sona, soyayya muke yi mai tsafta da shi, sai wata rana yake faɗa min dokar familyn nan, a ranar na shiga damuwa ainun, haka washe gari na je school cikin wani hali, to sai na faɗa ma ƙawata wata Gloria..................Ni bansa shirinta ba sai ta bani wani abu ta ce na sha, ban yi musu ba nasha, sannan ta rakani bakin office din Ayan................shiga na yi shima na bashi wani abu a kofi, be yi musu ba ya sha.......................Sai a lokacin na fara jin jikina......ya na......ya .............” sai ta fashe da kuka mai shiga rai.

Ayan da jikinsa ya yi sanyi dan kuwa yarda yake maganar ka ce da gaske ne.

“Yi shiru, ɗaure ki ƙarasa.” Baba Musa ya faɗa.

Sai da ta share hawayenta sannan ta ci gaba da cewa.

“Ashe maganin gushewar hankali ne da tayar da............ sha'awaaaaa.............take hankalina ya gushe, shima Ya Ayan. shine...... shine...........shine.....muka aikata al...............a....a.....al.....alfasha......” sai wani kukan ya kuma cin ƙarfinta, da sauri Baba Yusuf ya miƙe tsaye da jin furucinta.



“Ƙarya ne, karku mai da mu jahilai. Wannan ai ƙarya ne, hmmmmm ba yau aka haife mu ba, munga shekaran jiya, munga jiya, kuma gamu cikin yau. Ku faɗa mana abinda zai yi dai-dai da hankalin mu."

“Yusuf zauna su gama magana, yi haƙuri. Ayan ci gaba tunda kuka ya hanata ci gabawa.”


Ayan nunfashin ya ja, sannan ya ɗaure ya ci gaba shima cike da tsoron da ya yafa ma kansa.

“Wallahi Abba cikin rashin sani komai ya faru, ban iya tuna komai dake faruwa da ni ba sai bayan mun gama komai, anan na shiga tashin hankalin sosai, bayan faruwar haka da kyar A'isha ta bar kuka dan a tunaninta da gangan na aikata mata haka.......sai yamma sosai na kaita gida wanda har lokacin kuka take yi. Daga nan ba mu sake waya da ita ba har na tsawon sati ɗaya, dan kuwa Ni kaina banda lafiya lokacin. Sai wata rana ina zaune a office damuwa ya isheni, Ina son zuwa ganin halin da take amma ina jin tsoro abinda zai biyo baya.............sai kawai ga ta a office ɗina. Cike da mamakina na ke kallonta, dan ban ta ɓa tsammanin za ta kuma raɓata ba ta ɓa, dan a ganin laifi name................bayan ta zauna shine take bani haƙuri da faɗa min aikin Gloria ce, wai ai tasan addinin mu in an yi haka dole ake aure........” take ya yi shuru yana dafe kansa kaman da gaske.

Ganin haka A'isha da tasa cikin shashsheƙan kuka.

“Yaya wallahi bansan da mugun nufi ta yi ba.......Baba wallahi ban sani ba, kawai daga baya naga saƙonta akan haka, bayan na faɗa mai ya dinga kuka akan ta cucesa dan ya ɓa ta min rayuwa, Ni kuma da haka na ce mai ai dole ya aureni ko kuma na faɗa wa Dad ɗina, ba kuma zance tsautsayi bane, zance da gangan ne.........yanzu haka ina da juna biyu, shi yasa na ta da maganar dan in iyayaena suka sani..............." Sai ta kuma fashewa da kuka.


Ɗakin ne ya yi tsit sai kukan ta dake tashi cikin wani irin yanayi, hatta su Baba Musa sai da jikinsu ya yi sanyi.

“Innalillahi wa'inna ilaiyi raji'un.” shi kawai suke faɗi cike da tashin hankali.

“Mahaifinki ya sani?.” Baba Musa ya tambaya. Girgiza kai ta yi.

“Ayan tashi ka mai da ita gida, sannan ka nema izinin mahaifinta akan next week zamu zo maganar aurenku, ƙwanda a yi auren, in ta haihu sai a sake ɗaura muku aure.” Abba ya faɗa cikin ɗacin rai sosai.

“Yanzu daga sun faɗa sai mu yarda, muje asibiti a duba ta a gani, in babu ciki, kawai su haƙura da juna, in akwai a zubar dashi ko nawane sai mu biya yarinyar. Amma maganar Auren bare be ta so ba, dan wasiyyar Baban mune.” Yunus ya faɗa cikin ɗaga murya.

“Kuma kunsan akwai maganar aure tsakanin su da ƴata.”

“Yusuf, za mu tattauna wannan amma mu fara ji da wannan masifar. Yaro kuje." Kafin Ayan ya miƙe Yusuf ya miƙe yana cewa.

“Wasiyyar babanmu dole mu cika, dan munsan darajar sa." Da haka ya fice sai Yunus shima ya ja tsaki ya fita.

“Ya Allah ka bamu ikon cinye wannan jarabawan.”

“Ameen Musa. Kaina ya ɗaure sosai, dole dai ka aura Ruma ko ba yanzu ba, dan shine maslaha, yanzu ka mai da ita, in ka dawo za mu yi magana, Yarinya ki kwantar da hankalin ki, ba za'a zubar da cikin ba." Da sauri A'isha ta ce.

“Baba dan Allah karku yi mai komai, wallahi be da masaniyar haka...........karku hukuntasa ta hanya mara ƙyau, komai da ya faru ni ce sila.” ta faɗa wani kukan na ƙwace mata.


Hawaye Ayan ya share dan kuwa shima ji yake kaman komai dake faruwa gaske ne.


Cikin rauni Abba ya bar room ɗin sai Baba Musa ya ƙara tausar su sannan ya sallamesu, ta ƙofar da suka shigo nan suka bi har waje.


Sai da motar Ayan ta bar layin tukun ta fara jin iska mai daɗi na ratsata, a bakin wani provision ya tsaya sannan ya fita, be jima ba ya dawo riƙe da leda.

Pepsi ne mai sanyi da suprite, ba ta ɗaya ya yi shima ya buɗe ɗaya.


Shanye nashi ya yi ita kuma ta sha kusan rabi. Numfashi suke

6 / 9