Author : Pretty Sk Category : Hausa Read
Fiƙihu, Hadith, nahwu, insha'i, sarfu da sauransu, sannan na ɗauki Alqur'ani.
Na haddace izu 30 gan, daga lokacin kuma na sanya wasa sosai, har zuwa yanzu ban iya haɗa 60 ba, da yake ma be dame ni ba. (Astagafirullah 😓)
Ina da kaifin hadda sosai, nan fa na fara maraja'an al'qur'ani cikin zazzaƙan muryana mai cike da taushi, ko Ni kaina nasan ina da zaƙin murya, sannan duk wanda ya sanni haka yake cewa.
Duk wanda ya ji karantun nan zai rantse wata Hafiza ce wacce ta ke da cikakkiyar hankali take rerowa.
Ina tsaka da karatu sai ga A'isha ta shigo tana sakarmin murmushi, da yake na kai aya sai na tsaya ina mai da mata murmushin.
Zama ta yi gefan takadduna tana cewa.
“Ina alfari da sabuwar ƙanwar da nake gani a yau, haka nake so ki zama, ba irin wancan ba mai son abin da Allah ya hana.” nasan me take nufi dan haka na ce.
“Insha Allah na sauya daga yarda nake, kuma za ku yi alfahari da nan gaba.” na faɗa amma a zuciya kuwa cewa na yi. *‘Film ɗaya kawai zan yi, ai ba yawa.’*
“Mu yi musaffa.” ta faɗa tana gyara zamanta murmushi na yi duk da nasan A'isha ƙwarowace a karatun Alkur'ani, dan shekara biyu kenan da haɗa sittin, sannan tana zuwa musabaƙa sosai, in da ta ciyo ƙyatuttuka, amma haka mu ka fara yi cikin nishaɗi.
Sallah da cikin abinci ne kawai ya yake rabamu, tare muka shiga kitchen, Aisha ta dafa wa kanta taliya, muna yi muna hira wanda muka manta rabon da su yi tsabar rashin jituwa.
Dining area muka koma in da muka fara cin abincin abinci, sai a lokacin Mom and Dad suka fito, suma wajen mu suka nufa, zama suka yi in da Dad ke cewa.
“Congratulation my Daughter u get 200 score in your Waec.” wani irin ihu na sa ina ɗaga hannu, da sauri A'isha ta buge min kai.
“Alhamdullah.” ta faɗa sai na maimaita ina miƙewa, rungume Dad na yi da Mom Ina jin daɗi.
“Sai ki fara shiri dan kuwa tuni an sama miki gurbi a school, ko zuwa next week sai tafiya.” murmushi na yi a raina ina cewa. ‘Saura abu ɗaya.' a fili kuwa cewa na yi.
“Dad amma ba a hostel zan zauna ba ko?." Kamar yarda na yi tsammani kallona suke yi cike da neman ƙarin bayani.
“Shalele, me yasa kika ce haka?.” Faɗin Mom sai na ce
“Eh to a makarantu irin haka, sai kuga mata suna ɓata ƴan uwansu, ko da wasu ba su so dole ake musu, gaskiya ni ina jin tsoron Hostel, in dai anan zan zauna gaskiya na fasa.........na haƙura.” na faɗa ina ɓoye damuwan dake fuskanta, a raina kuma ina fatan su yarda, dan wallahi ƙarya nake ba zan iya fasawa ba.
“Gaskiya zan fi so ki zauna a Hostel, akwai masu tsaro sosai ba wani abu ai.”
“Mom. Wallahi banso........” da sauri A'isha ta katse Ni.
“Why not a kai ta gidan friend ɗin ta, sai su dinga zuwa tare da komawa gida, sai mu roƙa ta zauna da su.” Gaba na ne ya faɗi dan babu wanda na sani a can ɗin.
“Shawarar nan ta yi, na yarda.” faɗin Dad sai Mom ta ce.
“Nima haka.” sai na yi murmushi dan jin sun yarda.
Falo muka dawo dukkan mu, A'isha na latsa waya sai murmushi take yi, Mom da Dad kallo suke yi, in da ni kuma na faɗa duniyar tunani.
‘Yanzu idan muka je Lagos, wani waje zan kai Dad? Kuma ta ya zan tsallake wannan ƙaryar? Oh Allah ka taimake Ni, ya zan yi?. So nake na zauna a gidan haya ba Hostel ba saboda babu mai takura min, na fita shooting yarda nake so.....................”
“Inayah! Inayah!! Inayah!!!." Da sauri na dawo duniyar mutane, a ɗan zabure na kallon Dad dake kirana.
”Me kike tunani?."
“Dad.........ba........ba komai." na faɗa ina turo baki tare sosa kaina.
“Ok, je room ɗina, za ki ga wani bag da na dawo dashi ɗazu, na aje a wajen bookshelf ɗaga sama.” na ɗaga mai kai ina miƙewa.
Ɗakin na shiga, ban nufa in da ya aikeni kai tsaye ba, sai gaban mirrow na tsaya nufa, na fara taɓe-taɓe, harda ƙwaɗa Jallabiyar Dad, Dan Ina son jallabiyar maza, shi yasa Mom ta hanani zuwa ɗakin, in dai na shiga saina sanya kayansa duk da sun yi min mugun yawa.
“Ba ki gani ba?.” na jiyo ya faɗa da ƙarfi.
“Gani nan zuwa............" Da haka na cire rigar da sauri, a wajen dana ɗauka na ajiye, sannan na nufa wajen da ya aike Ni, na ɗauka, sai na yi waje har da gudu-gudu.
“Dad, wani book na gani shine na fara dubawa, gaskiya ya yi daɗi." Na faɗa ina bashi Jakkan.
“Wani book kenan?.” murmushi na ɗan yi dan bansan me zance ba.
“Ban duba sunan ba, kawai karantawa na yi.” ya ɗaga min kai yana buɗe jakkan.
Zama na yi sai kawai na ga A'isha ta nufo ni tana murmushi da na ɗauka na mugunta ne, take na haɗe giran sama da ƙasa, aikuwa tana zuwa ta kullemin ido tana cewa.
“Tashi, muje.”
“Malama sake ni.”
“Shalele ku zo ta nan." Dad ya faɗa, sai na yi shuru muna takawa, a gabansa muka tsaya sannan na ji ya sanya min abu a cikin hannuna. Sai A'isha ta buɗe min idanuna tana cewa.
“Suprise.”
Zaro dara-daran idanuwana na yi ina kallon wata haɗɗiyar waya a hannuna.
Tsabar an shammace ni da min bazata, sai da na durgushe ina kallon wayar.
Hawaye ne na ji sun cika min ido, da sauri na je wayar ina rungumesa tare da mai godiya wanda bansan menake furtawa ba amma nasan godiya dai nake yi.
Daga shi na rungume Mom wacce ke ta murmushi.
“Yanzu nawa ya huta." Sai na ɗaga mata kai, A'isha na nuna mawa tare da cewa.
“Ashenty......oh Aunty Aisha, kin gani."
“Tubuli-wayuklifullahu ta'ala.” ta faɗa tana kallon wayarta ƙirar Samsung.
“Thanks." Na faɗa ina nufa stairs da gudu.
Ɗakina na shiga tare da aje wayar kan mudubu na fara rawar murna, sai dai na yi kaman na minti 3 sannan na tsaya, sai kuma na tsaya sai na fara gode wa Ubangiji.
Sai da na natsu tukun na kalla wayar da ƙyau, irin na A'isha ne wanda aka siyamata bayan da na fasa mata na ta.
Murmushi na kuma yi sannan na sumbaci wayar, sai na rungumeta a saitin zuciyata, ina jin soyayyar wayar yana shiga cikin jikina.
A kunne take dan haka na latsa, wayyo daɗi, ji nake kaman a mafarki na mallaka waya, dan kuwa wancan muna gama exam na bar ma ƙawata.
“Allah na gode ma." Na faɗa ina shiga nan in fita nan, har da layin MTN a ciki.
Jin wayar na ringing har sai da na tsorata, har ina sakin wayar kan gado.
(DAD❤️) sunan da ya fito kenan, sai da na sauke ajiyan zuciya sannan na ɗauka ina washe baki.
“Shalele sauko ƙasa."
“To, Dad." Da haka na katse kiran sannan na mai da hulana na fito.
Kamar yadda na barsu haka na sake su, sai na nufa su, a tsakiyar su Mom na zauna.
“Shalele."
“Yes Dad." Na faɗa ina kwantawa akan cinyar mom.
“Na baki waya yanzu, dan kin kai riƙewa, ina so ki yi koyi da Yayarki, kamar yarda take yi da waya, babu kallon banza, banda chart da ƙawayen banza, no Facebook by now, sannan in ba group na education ba banyarda ba, banda waya da maza da sunan classmate. Ki kama kanki, ki kula, kin ga wannan wayar, takan jefa mutum masifar duniya da lahira, Na aminta da tarbiyyar da na baku kuma karki ban kunya.” ya kai maganar cikin rauni da lallashi.
Tashi na yi na rungumesa ta gefe ina jin babu daɗi
“Tabbas A'isha ba ta saɓa mana, mun yadda da ita, kema muna so ki zama haka. Duk da ke za ki yi nisa da mu amma a kodayaushe ki dinga tunawa da Allah na kallon ki, ki sa wannan a ranki, amanar kanki za mu baki, kisani idan kika ci Allah zai tambayeki, kuma ke kiwon da Allah ya bamu ne, za mu so mu rabu a duniya lafiya, mu haɗu a aljanna cikin amincinsa.”
“Insha Allah Mom bazan baku kunya ba.” na faɗa ina share hawaye.
“Amma Dad ai zan iya kallo a YouTube?." Na tambaya duk da wallahi babu mai hanani kallon finafinan *NOLLYWOOD.*
“Eh, amma kisan me kike kalla, banda na lalata yara, kuma banda abin da be kamata ba."
“Dama ni Film kawai, irin series haka."
“Za ki iya but banda Nigeria Film.” A'isha ta faɗa da sigan zolaya, hararar wasa na yi mata.
“Ai Nigeria Film kala-kala ne, kaman *The king -........." Da sauri na katse Dad.
“Like, *Two father - How to bake - Treasure in the sky - Poor Mom and Rich Mom - To kill a monkey - Our problems - Maids - Love is blind etc. Ai is normal kallon su.” na faɗa ba tare da nasan aika-aikan da na yi ba.
“A ina kika san wa'inna fina-finan?." Rintse ido na yi ina haɗiye miyau, dan kuwa wa'inna kaɗan ne daga wanda ma kalla a school.
“Da ke fa nake?." Ya kuma tamabaya, dan a gida ban kallo a tv, ko na na fara za'a mai da sunna tv ko labarai.
“Da........dama ranar a wayar A'isha ne na ga an yi posting a facebook, na dukka postern kuma aka rubuta, yara za su kalla." Na faɗa ina fatan ƙaryar ya fitar da Ni.
“Ai banda Facebook a waya na." Aisha ta faɗa tana danne dariyar dake cinta.
“To a ina kika kalla?.” Mom ta tamabaye ni.
“To na manta amma a cikin wayoyin kune."
“Nima banda Facebook a ciki." Sai na ji kaman Mom ta ƙwalamin abu ne a kai.
Fuska na haɗe ina shirin fashewa da kuka, dan in Dad ya gane ƙwarya nake, zai amshe wayar ne, dan ya tsana ƙarya.
Jin sun washe da dariya, ya sa na san wasa suke mun, ai da biyu na miƙe, ni a dole na yi fushi, na dau wayata ina hucewa da gudu.
“Ku dena zolayar min Shalele." Dad ya faɗa yana mai da hankalinsa a kan Tv.
Ina shiga ɗakina na kulle sannan na haye gado dan yau babu barci, sai dai babu komai akan wayar, amma akwai data, da haka na kunna na shiga Tiktok, sai dai Ni ban son kallon raye-raye da shirme na mutane, dan haka na koma Youtube, ai wani ɗan ihu na yi ganin ga fina-finai kaman hauka sun fito.
“School mate." Na faɗa ina kallon poster na wasu ƴam mata da samari cikin uniform na school, sun yi ƙyau sosai, duk da fuskokinsu babu alamun wasa a ciki, da haka na shiga dan kallon Film ɗin ina ji raina fes banda wata matsala................✍️
END
> Ƴar NOLLYWOOD 🔥😁, hmmmm akwai abu.
> Har yanzu ba mu fara wasan ba GUY'S 🥴🥴🥴.
> INAYAH an yi waya, gaskiya zan zo kallo nima.
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.*
Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥
*Keep shining, JAW family!* 🌺
*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*
𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅
Story and writing✍️
```PRETTY SK```
~SAKINA ABDULLAHI~
> *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️
✽»≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»✽
E.P1️⃣7⃣⏩1⃣8⃣.
______________A Kwana a tashi, haka muka dinga shirye-shiryen tafiya, munje kasuwa an yi min siyayya sosai, tare da Mom da Dad za mu je, gaban ɗaya sai na ji kaman na fasa, dan ina son rayuwa jikin iyayena amma in Ina tare da su ba zan zama *ƳAR NOLLYWOOD* ba.
Ranar ba ta kyar, yau Monday, da misalin 9:30 muka nufa Airport, A'isha kuma tun safe mukayi sallama ta tafi school, har kuka muka yi kamar kar mu rabu da juna, amma haka dai ta bar gidan tana hawaye.
A filin jirgin, gaba ɗaya jikina ya yi sanyi, muna nan zaune muna jira a kira ƴan jirgin mu dan Flight za mu bi.
*GIƊAƊO MANSION*
_______Babu wani sauyi dangane da rayuwar gidan, sai dai tsanar da Ammee ke ma Ummee kullum ƙaruwa yake, haka dai suke rayuwa.
Sarah ce tsaye a bakin motar Ahmad wanda zai tafi Lagos dan a can suke shooting film.
“Dear gab da bikin mu zan dawo, series ɗin da muke yi saura kaɗan mu gama." Ya faɗa yana mata wani irin kallo.
Sarah dake kallon ƙasa ta ɗaga mai kai, dan kuwa ba ƙaramin tsanar wannan aikin na sa take ba, babu wanda be san irin iskancin da yake ba, amma babu mai magana saboda Ameensa ta rufe ma kowa baki.
Da tana da dama *NOLLYWOOD* Film za ta fara hanasa dan kuwa irin baɗalar da yake yi sai dai a yi shiru, gashi ko kunya ba ya ji, abun na ba ta mamaki sosai.
“Ba ki ce komai ba?.”
“A sauka lafiya." Ta faɗa a hankali.
“Ki kulamin da kanki da kayan daɗi, wallahi duk na ƙosa, Ni dama Lagos ɗin zamu je tare bayan ɗaurin auren" Tafiya ta fara yi kamar ba da ita yake ba.
Murmushi ya yi sannan ya yi ma Driver magana, take aka buɗe daya daga cikin gets ɗin suka nufa waje..........
*AYAN*
_______Shuru ya yi a cikin mota yana tunanin abin yi, ya yi ma su Abba maganar da ya kamata su nema ba'asi amma sunƙi, sai dai kaman shirye-shiryen bikin suke yi, tsaki ya ja mara sauti, yana shirin fita daga motan.
Sai ya hangi A'isha ta fito daga na ta motan ta, niƙaf ta sa yau, sai ya ɗau waya ya kirata.
“Zo mu gaisa, ina mota na." Ya faɗa yana katse kiran, dan yasan za ta iya kawo mai uzuri.
Motar ta nufo a natse kamar yarda take, tana zuwa ya buɗe mata, sai ta shiga.
“Ina kwana?.” ta faɗa cikin ɗan rawar murya.
“Sun wuce ne?." Sai ta ɗaga mai kai.
“An jima za su wuce.”
“Allah ya tsare su, addu'a za ki musu, ba kuka ba." Sai ta daga mai kai.
“Har Ƙanwata za ta wuce karatu ba mu haɗu ba." Sai Aisha ta yi murmushi dan kuwa sau uku da Ayan ke zuwa, tana ce ma Inayah ta fito su gaisa, sai ta ce _Ba za ni ba eyehh_ da haka take ƙyaleta.
“Aisha." Sai ta kallesa ta cikin niƙaf.
“Daga yau wasan kwaikwayo zai fara, yau zan ƙara ma su Abba magana, to at anytime za ki iya samun kira daga wajensu. Idan har ba ki yi harda za su ɗauka da gaske ba, ba za su bari a yi auren ba, ki yi acting sosai.”
“Karka damu." Ta faɗa tana jin in wannan ne ai an gama dan har kuka za ta yi, kuma za ta zuzuta komai, wannan ake kira da *Heart Flighting when you fail, it's mean......... your heart is die forever* ............
Adam ana sauke sa a airport, nan fa mutane suka an kara da shi, take aka fara mai hotuna, mutane suka zagaye sa dan kuwa A.G ya shahara sosai, babu wanda be san shi ba, ya shiga duniya gaba ɗaya.
“A.G hoto ɗaya............Sa hannun ƙauna......... Please kalla nan.............. Please 1minute Sir." Haka mutane suka cikasa da tambaya, kuma suka zagayesa.
Tsayawa ya yi yana yi ma wasu, signing, wasu kuma hotuna ya yi da su kwanin burgewa.
Daga in da nake na hangi A.G, tauraron mai ci tashe a *NOLLYWOOD*, na kalla fina-finan sa guda 5, kuma duk sun yi daɗi, fiye da misali.
Ai da sauri na miƙe tsaye.
“Ina za ki?." Mom ta faɗa ganin irin yarda na zabura na miƙe.
“Uhmmm.........I want to buy..... Eh gashi can a waje." Na faɗa ina ɗan yaƙe.
“Take." Dad ya ban ₦1000, daban ya hangi abin da nake ambata ba, amsa na yi ina yin waje, ta glass na hangasa wanda ya raba cikin wajen da waje.
Fita na yi ina buɗe ƙaramin jakkarta, pen da memo na ciro ina nufan wajen.
Tun daga nesa idanunsa suka sauka akanta, Budurwar yarinya, fara mai manyan idanu, ga siririn hanci. Black abaya ne jikinta, sai ta yafa vail, ga kuma ƙaramin jakka da black ta rataya, ta yi wani masifaffen ƙyau, ga wani murmushi take sauka a fuskarta har kumatunta suna lotsawa.
“Wow." Ya faɗa yana nufanta, dan mutanen sun ragu mai, ita ma wajensa take nufa.
“Hey." Na faɗa ina tsayawa a gabansa.
“Hello." Ya faɗa a hankali yana min wani irin kallo mai narka zuciya.
“A.G, ai Ni fans ɗin ka ce. Pls your signature." Na faɗa badan iya abin da nake so bake nan.
Da mamaki na ga harda phone number ya sanya min, kuma sai murmushi yake sakin min.
“Gaskiya na gode sosai." Na faɗa ina son juyawa.
“Ya sunan ki?." Ya tambaya.
“Inayah." Da haka na wuce, na barshi tsaye yana bina da kallo, daga sama har ƙasa, har yadda nake tafiyar kai ka ce wata sarauniya ce, be ankaraba har na shige.
Nannauyan ajiyan zuciya ya sauke mai shafan kansa.
Ina kowa ma ciki aka kiramu, shiga jirgi muka yi, take jirgin ya tashi zuwa sararin samaniya.
Ina jin na fito da ƙafar dama, na fito da babban sa'a, gashi daga fitowa na samu number A.G.
A V.I.P muke zaune, murmushi nake yi sosai ina daga bayan su Mom, a hankali bakina ya furta.
“Nollywood gani nan zuwa............” na faɗa ina rufe idanuna tare da wani irin murmushi na musamman...............✍️
END.
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.*
Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥
*Keep shining, JAW family!* 🌺
*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*
𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅
Story and writing✍️
```𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊
```
~SAKINA ABDULLAHI~
> *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️
✽»≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»✽
E.P1⃣9⃣⏩2️⃣0⃣.
___________Ba mu muka sauka ba sai misalin 3:00pm, da yake tun daga can Dad ya gama komai, a airport muka sake haɗuwa da A.G wanda ke ta zabga min murmushi, ina mai da mai kamar irin mun saba ɗin nan. manyan motoci uku ne suka ɗauke sa, in da mu kuma wata guda ɗaya ta ɗauke mu da kayan mu.
A gefan Driver na zauna ina ƙare ma Jahar Lagos kallo, da mutanen da ke ciki, murmushi na kuma yi ina tuna abin da Dad ya ce min shekaran jiya.
‘Mu je school ɗin ku, sai a duba file ɗin ƙawarki, nasan za mu samu