YAR NOLLYWOOD BOOK ONE by PRETTY SK.txt

Author :  Pretty Sk Category :  Hausa Read

Chapter   1 / 9

1 to 3K   out of 25.8K words

𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅

_TAP THIS LINK TO JOIN MY GROUP👇_
https://chat.whatsapp.com/Be241ldCcFS5kAxa5V8lpy

_TAP THIS LINK TO JOIN MY CHANNEL👇_
https://whatsapp.com/channel/0029Vb64I4aGzzKQsSeaKA2K

_TAP THIS LINK TO JOIN IN AREWAPEN 👇_
https://arewapen.com/u/prettys01


*✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽*

_In the name of Allāh the Entirely Merciful, the Especially Merciful._


_Godiya da yabo su ƙafa tabbata ga ubangiji talikai mamallakin sammai da kasai Allah❤️._

_Tsira da amincin Allah su Kara tabbata ga fiyayen halita annabi Muhammad (s. a. w)❤️_

*GODIYA MARA IYAKA*
_Ga dumbin mabiya litattafaina a duk inda kuke cikin kasar Allah. Ina matukar alfahari daku, kuma ina kaunarku kamar yadda kuke kaunata 😍💃 nima PRETTY SK Ina ƙaunarku har cikin raina 💋❤️._

> “I will succeed. Not immediately. But definitely.” in shaa Allah.

*GARGAƊI*
_Wannan littafin mallaka nawa ne *Pretty SK ✍️* , Ina Gargaɗin kar wani ya sauyamin komai dake cikin littafin nan, sannan kar a sanya min shi a YouTube ko wani website ba tare da izini ba, ga duk mai son karantawa ko wasu daga takadduna to direct ya min mgana._
> 07038436703 \ 08126151523.

_WANNAN ZAZZAFAN SHIRIN MAI TAKEN 𝒀𝑨𝑹 𝑵𝑶𝑳𝑳𝒀𝑾𝑶𝑶𝑫 ZAI ZO MUKU DA SABON SALO MAI BAN MAMAKI, HARGITSI MAI CHAKWAKIYA, ƘADDARA MAI RADAƊI, FARINCI MAI YANKE WA DA HAƘURI MAI CUTARWA......HMMM DUKKA DAI A CIKIN LITTAFIN NAN *ƳAR NOLLYWOOD*._

*_ITA SAM BA KANNYWOOD TAKE SO BA, HOLLYWOOD TAKE SO AMMA GANIN YA MATA NISA KUMA AKWAI MATSALA YASA TA KOMA SON NOLLYWOOD GADAN-GADAN, BA TA JIN DUK DUNIYAR NAN AKWAI MAI HANATA FILM ƊIN NOLLYWOOD......... HMMMM KU DAGA NAN KUSAN AKWAI MATSALA NA MUSANMAN._*


______________________________________

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.*

Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥
*Keep shining, JAW family!* 🌺

*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*
_Jarumta shine taken mu, Rubutu shine madubin mu, basira shine aikin mu, motsa zuciyar masu karatu shine baiwar mu, mun rungume alƙalami dan haskaka al'umma_

______________________________________

*𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅*

*Dream – Love – Rebellion – Evil – Drama & Hatred*

Story and writing✍️
```𝐏𝗿𝗲𝘁𝘁𝘆 𝐒𝐊
```
~SAKINA ABDULLAHI~
> *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️*


_BOOK ONEIS FREE🥰_



_E.P________1️⃣⏩2️⃣_



“ACTION” Faɗin wani ƙaton baƙin mutum dake zaune kan kujerar roba.

Yana sanye ne da riga t-shirt da wando three-quarter, wiyarsa na ɗauke da sarƙan cross, sai p- cap da ke kansa, a kallo ɗaya za ka fahimci babban arne ne, duba da shigarsa da kuma fuskarsa da babu hasken musulunci ko kaɗan.


Take masu cameras suka fara ɗaukan video na wani saurayi dake tsaye shi da wata budurwa. Saurayin shi dai dogon wando ne jikinsa da riga mai dogon hannu, sai macen dake tsaye gabansa, riga ce iya gwiwa ke jikinta, ta matseta sosai, ya bi jikin ta ko ina, sannan ga kanta wanda ta sanya attachedment kai ka ce kashin tane dan yarda ya zauna.


A karo na ba adadi na yi murmushi, ina tsaye daga gefan Director, duk na ƙosa a ban dama da na shiga filin nima.

A lokacin da ya kalleni alamun zai yi min sign na shiga filin, take wani duka ya shiga fatata, wanda ya sa na tsala ihu ina dawowa duniyar gaskiya, baki na yana faɗin.

“Director see meeeee." A ɗan gigice na tashi daga barcin da ya ɗauke ni a mota.

Tsaki na ja mai tsayi wanda babu wanda zai ce daga ƙaramin bakina ya fito, take na kalla gefan da na ji wannan dukan. Sai idanuna suka haɗu da na ƴaƴanta da ke dallamin harara.

“Shashasha!, fitar min a mota, saboda ke na yi latti, yanzu 8:12am, ni da zamu shiga Lecture 8:00am. Fitar min a mota, in banda hauka daga gida zuwa nan shine za ki yi barci, harda shegen mafarkin nan ne hauka.” ta faɗa cike da ɗaga murya, murmushi na ɗan yi dan wallahi ina so naga ina ɓa ta mata rai.

“Stop insulting my dream ehe, because it means more to me than anything else in life.” Murmushi kallon mahaukaciya ta yi min.

“Hmmmm yaro man kaza, fita kafin na makeki, kuma wallahi idan ba ki bar wannan maganar ba sa na faɗa ma Dad."

“Uhmmmm a huce haka Ashenty." Na faɗa ina buɗe motar.

Makarantar mu na kalla wanda manyan motoci ne ke ta sauke yara, har na fara tafiya na tsaya cak da jin abin da take cewa.

“So you left your lunch bag with me, right?."


Dan nasan sai 6pm zan koma gida shi yasa na koma baya tare da ɗaukan lunch bag ɗina.

Ga ƙaton jakka ga lunch bag, ɗauka na yi sannan na marairaice fuska, kallon yayata nake wacce muke maka da ita, sanye take da dogon hijabi ɗinkin Jalbab, maroon colour, ta yi ƙyau sosai, fara ce mai dogon hanci, ga ƙaramin baki, sannan ga fararen idanuwa masu ɗaukan hankali, ba ƙyarya muna da ƙyau mai sunan ƙyau, dan Dad ɗin mu shuwa ne Mom kuma buzuwa ce.

“Uban me kika tsaya yi, rifomin ƙofata.” ta faɗa tana son ta da motar.

Fiƙi-fiki na yi idanuwa sannan cikin ladabin da nake yafa ma kai na idan ina bukatar abu a wajen ta nace.

“Auntyna.....Aunty Aishataahhh." Murmushi ta yi dan tasan sauran.

“Please give me some money for break.” Na faɗa cikin salon magiya.

“A gabana Mom ta baki ₦500, to kuɗin me zan kuma baki?." Tsaki na ja a cikin raina, amma da yake ina so sai na ce.

“Wallahi bayarwa zanyi, wata yarinya zan ba kyauta.”

“Hmmmm.” ta faɗa tana ciro ₦500 daga jakkarta, bani ta yi, na amsa ina washe baki har dimple ɗina na lotsawa.

“Ko duk duniya za su taru bazan yadda ke ce za ki yi ƙyautar kuɗi ba, hmmm na sanki fa." Da haka ta figa mota da gudu dan dama ita gwanace da iya wasan mota.


Murmushi na yi ina ɗaga kafaɗa, dan ko a jikina, da haka na nufa bakin get, har an fara taran latti, amma da yake ansan ban yin latti sai suka bar ni na wuce.


Babban makaranta ne wanda a ido kasan na masu kuɗi ne. Duk wasu masu ji da kuɗi to yaransu a school ɗin nan suke. School ne wanda akwai Musulmai da kiristoci, uniform ɗin mu, blue and white ne, Rigar blue mai gajeran hannu zuwa gwiwa, sai farin riga ta ci mai dogon hannu da ƙwala.

Musulmai mukan sanya legis a ciki, sannan gaba ɗaya bama sanya hijab, sai hula. To Ni wani lokacin ma nawa na jakka, haka nake yawo na da gashin kaina. A lokacin islamiyya ne kawai muke sanya hijab blue har ƙasa .

Tafiya na fara yi cikin babban makarantar, har na hau stairs, bene na ƙarshe a can S.S section yake, ina hawa na nufa S.S.3, hamdala nayi ganin babu teacher, shiga na yi kai na tsaye, bayan na yi signing da rubuta time ɗin da na shigo, akan wani book dake kan desk na teacher, dan haka tsarin yake shiyasa ko wani class akwai agogo babba daga saman whiteboard, Dan kana shigowa ka duba tare da rubuta lokaci.

Da mazan dake set ɗin gaba muka fara gaisawa ta hanyar tafawa, haka muka dinga kashe tafi muna cewa.

“Hey/Hello.”.

Haka sai da na bi kowa na ajin, mu 24, maza goma mata sha-huɗu.

Sit ɗin ƙarshe na nufa wanda a nan nake zama, kowani desk mutum biyu ne, akwai wajen aje bag da lunch bag, ajewa na yi ina gaisawa da wacce take gefena, wato mutumiyata.

“Jennifer, how are you?.”

“Am fine Dear Rose.” murmushi na yi dan sunan na a school kenan *Rose*, saboda ina son sunan.

Yau dai ban cire hula ba na barshi, daga lokacin teachers suka fara shigo ma na, har zuwa lokacin break, dama lokacin nake jira, ƴan class ɗin wasu suka fita wasu kuma suka zauna.

Ni dai nishaɗi nake sosai ba dan komai ba sai dan abin da Jennifer ta fito min da shi, *Waya* ce, ƙirar tecno spark 4, Wanda yake mallakina, babu wanda ya san ina da shi sai Jennifer, na sha wahala sosai kafin na haɗa kuɗin wayar, sannan kullum in na zo ina ba ta 500 na data.

“Thank you so much jennifer.” na faɗa dan ganin wayar a 100%. Murmushi ta yi tana cewa.

“Yesterday, *To Kill a Monkey* Episode 5 was released." Take na buga desk ɗin gabana, tare da ɗan ihun murna sannan da yi mata waƙan Auta waziri.

“Ahhhh, ki sani komai, nisan-nisa ba zana barki baaa......ba za na ɗauki watanki in ijiyeki anan baaaaa....” na faɗa ina nuna zuciyata, dariya muka yi harda tafawa, ƴan aji kuma suka yi murmushi dan yarda na yi waƙan ba magana, har wani action na yi fa.

“Me too I love you Rose.”


Da haka ta yi waje ni kuma na toshe kunnuwa na hau kallon *Nigeria Film* kamar yarda na saba, downloading nake yi wani lokacin kuma Jennifer ke turo min.

Ni dai Allah ya yi da son fina-finan 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅Saboda shi, yasa na siya waya, na sha wiya sosai kafin na haɗa 35k, kullum aka ban kuɗi nake tarawa, sannan na yi ta ƙarerayin, daga in ce.

“Zan sai abu - Wata ba lafiya zamu siya mata abu, - an sake abu a class ɗin mu, to ance duk sai mun haɗa kuɗi, amma Dad na ce ni zan biya dukka.”


Hmmmmm da haka na siya wayar, so nake da mun gama secondry school, na ta fi University a wani state, a can zan zama *ƳAR NOLLYWOOD*, wanna shine burina kuma muradina, ban jin akwai mai shiga tsakanin wannan burin nawa.



Film biyu na kalla sannan aka dawo class, haka muka kuma shan karatu, nifa duk wasana nice first class, Banda wasa akan karatu, ban ta ɓa cin second position ba, ko dan idan na je shiga Film na shiga da class.





Sai 2:00pm aka tashi, sai da muka yi Sallah sannan muka ci abinci sai muka koma part ɗin Islamiyya, ƙawata Kirista ce ta wuce gida, sam ban jin daɗin Islamiyya saboda banda ƙawa, kuma ina sa wasa sosai, zan iya cewa ko Exam ban wani yi na islamiya, gaba ɗaya sai a hankali dai.


Kamar kullum sai 6:00pm aka tashi, Driver na be da lafiya shi yasa Ashenty ke kawo ni da ɗauka ta, ina tsaye daga bakin get ta cikin school, sai gata nan ta faka, sai da ta fito muka yi signing tare sannan muka bar bakin school ɗin, dama dokace idan student ya shiga shi zai yi signing, in kuma aka tashi sai wani nashi ya zo su yi signing da rubuta number.


Na gaji sosai shi yasa ban ne ma faɗar ta ba, ita ma Driving kawai take yi a natse.

Bayan mun ɗan yi tafiya muka shiga layin mu, bayan mun kai bakin get ɗin mu, ta yi horn.

Sai da me gadi ha buɗe get sannan muka shiga gidan, sai da ta daidaita parking sannan na fito, da gangan na bar lunch bag ɗina.


Tafiya nake yi cikin sauri-sauri harda ɗan gudu duk dan karta kirani.



Babbane gidan mu sosai, wanda ya gaji da haɗuwa dan kuwa mahaifina mai suna Alhaji Musa babban mutum ne wanda yake cikin siyasar ƙasar nan, sanan yana da kamfanoni Barkatai, a taƙaice dai yana da kuɗi sosai.

Gidan mu mai hawa biyu ne, akwai ɗakuna masu yawa a ciki amma kaɗan daga ciki ne muke amfani da shi.

Mu huɗu ke rayuwa a ciki bayan masu aiki, Dad, Mom, Ashenty da kuma Ni.

Dukda ba mu kaɗai suka haifa ba, an fara haifan Muhammad wanda shekara ɗaya ya yi ya rasu, sannan aka haifa wani Usman shi kuma tun yana jariri ya rasu, sai Ashenty, kafin ni ma an haifa Sadiq sai dai shima ba mai tsawon rai bane, ko shekara be yi ba ya bar duniya sai kuma Ni, hmmm mazan suke sheƙawa suka barmu, Allah dai ya jiƙasu.


Ina shiga babban falon namu na yi kan Mom wacce ke kallon labarai a N.T.A, rungumeta na yi ina murmushi.

“I'm back Dear." Na faɗa ina sakin ta.

“My Daughter you're welcome.” sai na zauna gefanta ina cire hijab ɗin islamiyya, idanunwa ta zuba min dan kuwa kaf gidan mu na zarce kowa a ƙyau.

Mom fara ce sosai wanda yayi sirki da ja-ja, tana ƙyau sosai, ga jiki masha Allah, nakan rasa tsakanin ita da Dad waya fi ƙyau haka kuma da A'isha, amma dukkansu suna cewa na fisu ƙyau sosai.

“My beautiful girl, Kullum ƙara ƙyau kike yi, balle yanzu da aka fara zama ƴam mata.” ina jin ta faɗa haka na miƙe ina ina gudu-gudu, tare da dariya, a nan na bar hijab ɗin da jakkata. Murmushi ta yi tana ɗan girgiza kai.

“Inayah akwai kunya.” da haka ta mai da kanta ga tv.

Ni kuwa stairs na hau, ɗakin farko shine nawa amma na wuce na shiga na gaba wato na Ashenty, ina san zuwa room ɗin ta saboda tana da tv, ai kuwa Ina shiga na kunna tare da hayewa kan bed Ina zaɓan channel. (African zone) shina shiga wani Nigeria Film suke yi mai suna *Two father* .

Ina cikin kallo Hajiya mai ɗaki ta shigo tana dallamin harara dan kuwa ta tsana na shigar mata room saboda ɓata mata nake yi kuma ban gyarawa.

“Shine kika bar min lunch bag ɗin ko? Hmmmm Inayah bansan yaushe ki ka raina ni ba.” ta faɗa tana cire Jalbab ɗin jikinta.

Maimakon na bata amsa sai na ce.

“Aunty Aisha yanzu za'a gama, Please ki bari ya ƙare, ban fara daga farko ba amma so nake nasan waye real father ɗin.”

“Hmmm lallai kam.” ta faɗa tana kashe Tv. Tashi na yi daga gadon ina tafiya tare da cewa.

“Very soon za ki fara gani na a ciki, ko meye abin damuwa akan haka, Insha Allah very soon zan......” ban gama faɗin abin da ke bakina ba ta janyo ni zuwa baya, sannan da sauri ta tasha gabana tana kulle ƙofar harda murza key amma ta bar key ɗin jinkin ƙofar.

Kallona take cikin ido kamar yarda nima nake kallonta cikin ido, har ɗan wani hawa na yi kamar wacce za ta fashe, ba ko tsoro na tsaya gabanta muna kallon juna, har da ɗan ɗaga mata gira na yi dan neman ƙarin bayanin akan abin da ta yi min, A'isha kuwa kallona take kamar da rufeni da duka, sai dai yarda ba za ta iya ba saboda tana mugun sona......................✍️
END.

> The beginning 🤭🤭🤭🤭

> 𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅

> A yi haƙuri da Update na riga na raba su a haka.

*PRETTY SK* Marubuciyar Littattafan👇:

📘 *DAGA INA TAKE* free book
📗 *RASH ƁOYAYYEN MASHEƘI* free book
📙 *BARRISTER* Paid book₦300
📕 *THE SLAVE* free book
📒 *ZAMU HAƊU* Free book
📓 *KWANA HUƊU* Paid book₦300
📔 *GOLD DIGGER'S* Paid book₦300
📚 *HASASHE KO BURI Book ONE* Paid book ₦500
📝 *ISLAND OF WITCHES 👹* Free book
📘 *DARE ƊAYA ALLAH KANYI BATURE* _Paid Book ₦500_
📔 *YAUDARA ZALLA ❤️*
HIKAYOYI kuma sune :
*SARAUNIYA HIDAYA 😬🔥*
*SARKIN MU🤣*
*MOHINA DA MATSAFIYA💀*
*RAMUWA💀🔥*


#LIKES👍
#SHARE👌
#COMMENTS☹️🔥

*𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅*

_TAP THIS LINK TO JOIN MY GROUP👇_
https://chat.whatsapp.com/Be241ldCcFS5kAxa5V8lpy

_TAP THIS LINK TO JOIN MY CHANNEL👇_
https://whatsapp.com/channel/0029Vb64I4aGzzKQsSeaKA2K

_TAP THIS LINK TO JOIN IN AREWAPEN 👇_
https://arewapen.com/u/prettys01





💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

🕊️ *May Allah keep us united, uplift us, and make our pens a means of positive change.*

Much love and respect to each and every one of you. ❤️🔥
*Keep shining, JAW family!* 🌺


*JARUMAI WRITER'S TEAM📚✍️*

*BOOK ONE IS FEEE, WHILE BOOK 2 IS ₦500*


*𝒀𝒂𝒓 𝑵𝒐𝒍𝒍𝒚𝒘𝒐𝒐𝒅*

Story and writing✍️
```PRETTY SK```
~SAKINA ABDULLAHI~
> *PRETTYN JAJIRTATTU 💪✍️




✽‌»‌≿━༺🌹﷽🌹༻━≾»‌✽


_E.P______________3⃣⏩4️⃣._






_Previous_
> Kallona take cikin ido kamar yarda nima nake kallonta cikin ido, har ɗan wani hawa na yi kamar wacce za ta fashe, ba ko tsoro na tsaya gabanta muna kallon juna, har da ɗan ɗaga mata gira na yi dan neman ƙarin bayanin akan abin da ta yi min, A'isha kuwa kallona take kamar da rufeni da duka, sai dai yarda ba za ta iya ba saboda tana mugun sona......................✍️


_Continuotions_


__________________“Inayah, magana zan yi dake.” ta faɗa tana zama kan sopa, ganin ta sake rai nima na sake nawa ina zama a kan dressing mirrow, sai da ta furzar da iska daga bakinta sannan ta ce.

“Sherunki nawa?." Jin tambayar da ta min yasan na ɗan murmushin basawa sannan na ce.


“Shekarun ki a cire 3 kacal, ke 21 ni kuma 17 kinga kusan mate muke.” wani kallo ta watsi min shi yasa na ɗan natsu.

“Hmmm, be serious. I don’t want madness.” sai na gyara zama ina ƙara ware mata dara-daran idanuwana masu haske da ƙyau.

“Me yasa kike son zama ƴar Film?.” sai da na yi fari da manyan idanuna, sannan na ce.

“Coz I love it.”

“Ke yanzu rayuwar Ƴam matan Hausa Film ne ke burgeki.......” da sauri na katseta.

“Nifa ba kannywood nake so, *NOLLYWOOD* nake so.” Hannu ta ɗaga min alamun na yi shuru.

“Ke fa Musulmace. Dad da Mom ba su da burin da ya wuce ki zama Doctor, amma......”

“Nifa bance ba zan zama doctor ba, dukka zan haɗa.” da sauri ta miƙe tsaye, sannan ta nufa tvn dake jikin bango ta kunna.

Channel ɗin ɗazu ne in da ake wani film, ɗaga gani zai yi daɗi har na fara murmushi sai na ji ta ce.

“Yanzu wannan kike so? Yanzu irin wannan iskancin kike so ki din ga yi.” ta faɗa a daidai in da aka nuna club, mata da maza suna rawa, mata da wasu tsinannun kaya, yawanci saman ƙirjinsu duk a waje, Mazan dai sun fi shiga mai ƙyau, yawan ci suna jikin juna, suna rawa abun dai ba tsari.

Wani aka hasko wanda ga alamun star ɗin Film ɗin ne, shi da wata budurwa ne suka riƙe da juna, magana ya fara mata tana yin murmushi, sai kuma ta raba jikinsu za ta wuce da saurin saurayin ya juyo da ita tare da haɗe bakinsu waje ɗaya.

Da sauri na kauda kai na daga Tvn.

“Ki kalla mana. Ba irin wannan kike so ba.” cikin ɗaga murya

1 / 9