Author : Surayyams Category : Read Hausa Novels
kullum yaumin idan mahaifiyarta na mata tambaya akan rashin yuwar aurenta da ahmed
bayan tasan baya tsallake maganan mahaifyrsa abun yakan dameta aranta bana wasa ba.
Ganin jikin kafayat yy sanyi nan Hajiya fatihat ta cigaba da xugata tana cewa "that woman is
busy planning sumting againts u. Hala ma bata son ki aure mata danta ne sabida dantaga ke ba
haushiya bace irinta
Magangunu kala kala babu wanda bata mata akan lamarin ba
Wani Tunani kafayat tayi aranta sai taji kmr tafara amincewa sa xancen mahaifyrta, karde
maganan mahaiyrtan gaskiyane,karde hajiya khadijatu kabilanci xata nuna mata, ta hada
Ahmed aure da wata bahaushiya ba ita ba?
Lumshe idonta tayi sosai tanajin fargaba mai karfi dan da alama Da damshi damshin gaskiya
acikin wnn xancen dan tasan kowacce uwa burinta kenan rayuwar danta ya xamo yana under
control dinta..
Ta bude baki xatayi magana kenan wayarta yafara ringing nan take sabuwar wakar davido na
timeless album dinsa wato "unavailable" ya karade ilahirin cikin dakin.
Kusan atare suka dubi kan screen din suka kalli lambar mai kirar atare.
Agaban screen an rubuta "Anty tems" yana yawo akai. Adan mamakance Kafayat tace why is
Anty ramouto calling me kode har Ahmed yace musu xai aure ni ne?
Wani Doguwar tsakin takaicin mahaifyrtan taja muryanta kasa kasa tanamai cewa oya keep
dreaming .
Ko kulata batay ba da rawar jiki ta dau wayar tabi ta rusuna kasa cikin girmamawa kamr wanda
ake kallonta.
Acikin harshen yarensu ta fara gaishe da Anty ramatou. Wadda take ce mata Anty tems sabida
bakaramin sabawa da su tayi sosai ba. Ita kanta Bata san Suna janta ajikin su ne bane sabida
suna son Ahmed lallai yay aure daga kabilar su na yoruba dan sam basa son uwarsa tace xata
hadashi da wata yar bahaushiya.
Har kasa kafayat ta tsuguna da wayar a kunne tanamai cewa
"o dara irọlẹ
Gud evening ma
Anty tems whatsup kiloshele? Any latest
Daga ta dayan bangaren Anty temi tace "Der is alot oo, but first thing first,i wll like to see u
today.. we have a big meeting with u _iyawo wa_
Tsaye kafayat ta mike kalman _iyawo wa_ yana ringing acikin brain dinta cos its means "our
future bride" jikinta harna rawa kmr wacce xata tashi sama tace really?
Hararar da uwarta take binta dashi yasa ta dan nitsu Ahankli tace Ahhhh but i hope dai Akan
batun aure na da Ahmed ne anty tems.
Daga ta dayan bangaren anty tems din tadan gutsira mata labari sama sama na abunda ake
ciki na batun cewa sun saka ma baban Ahmed daci sun takura mashi har yaje ya bawa Ahmed
sati biyu akan daya kawo musu dalili ko su Aura mata shi. Kafayat taji kamr xata fashe dan
murna dan tasan Ahmed will neva escape marying her in two weeks time din nan dan tasan dai
baida wata budurwan daya shaku da ita sosai sai ita,
nan anty tems tace mata Kedai kawai kiyi kiyi marmaxa kixo family house kisamemu musan
abinda muke ciki
Godiya ta mata snn ta katse wayar jikinta harna bari babu wani jira tafara shiri ta kwaso nan ta
kamo nan kamar wata mahaukaciya, nan ta dauki karamin jaka tasaka hadaddun kaya guda
biyar aciki da kayan kwalliyarta da su turare kala kala da jaka mai kyau da damin kudi dubu dari
biyar kusan rabin dan ribar kasuwancin ta na satin da sauran tarkacen jewrlies dinta
Mamaki da takaici yabi ya ishe mahaifiyarta amma bata ce mata uffan ba harsaida ta kammala
shiryawan snn tace mata wai ina xakije ne kafayat? Ke Daga kawai sun kiraki sun gaya miki
magana saiki dibi jiki yuuuu xakije gidansu aikin shashanci da bauta.
Kafayat Tace Ahhh mumy nifa ba gidan su Ahmed xanje ba, Anty temi ne tace naje suna nema
acan family house dinsu gidan Anty mojushola. Mum Wai bakiji me take cewa bane? She said
in two weeks time xasu aura min Ahmed yeeeyyyy.. omo mi iyawo
Tsawa matar ta dakata mata tace "Shut up jare
Ure a disgrace to woman race _itiju lori rẹ_ awon desperate gang,omo busy body.. kafayat wai
yaushe ne xaki san darajar kanki ne? Innice namiji yake having scnd tot akaina baxan jirashi ba,
kafin ma yagama min yanga saidai yaga har na nemi wani wanda yake sona nayi aure na
nabarshi. In Ahmed yana sonki why wud he take two weeks to decide. Ur just a desperate bitch
girl.
A mugun masife kafayar ta kalleta tana huci da alaman maganan ya ci mata rai,a cikin yanayin
tsawagoron rashin kunya tace mumy pleassse Abegggiiii. What is dis now, why are u alwys
negative?
Mamar tata xatay magana tabi ta tsareta da tsefaffen ido tanamai cewa "i ave heard enough of
u mum, me kika taɓamin arayuwata? U left me here to die wadann mutanen ne suka rikeni
yanxu kuma a memakon Kiyi supporting dina akan abunda nake so sai dai kokarin juyamin
mind dina kikeyi akansa ur evil plan againts me will not work witch.
Ta juya a xafafe xata tafi uwartata ta fixgota tare da daura mata mari akan fuskarta.
Kafayat is me ure calling a witch akan namiji? After all the insult i went trou in oda to secure ur
future dan ubanki olodo shegiya,saketa tay tana mai cewa "Okay fine.. ga hanya nan jeki.
Amma kisani, Idan har aurenki da damilare baiyu wann karon ba.
Cikin katseta kafayat tace are u going to trow me out of this house bcos this is my father house
not urs...
A mamakance Fuska a matukar daure matar tace ohhh really? Ni ai baxan taba korarki nan
gidan ba, akan me xan koreki acikin gidan danine na sha wahala wajen kwato miki shi?
Kafayat da kinki da kinso nine na tsuguna na haifeki snn nice agaba da kowa wajen son naga
rayuwarki tayi dede.
Xatayi maganan ta tsareta da hannu tanamai cewa:
"listen and listen carefully kafayat, inhar maganan aurenki da Damilare baiyu ba wann karon
kisaka aranki cewa nice xan xaba miki miji dakaina nan gaba.
Rai abace kafayat tace okay fine mum..nikuma nayi mikii alkwari baxan dawo gidan nan ba face
saina auri Ahmed .
Tun bata karasa furta hakan ba mahaifyar taja doguwar tsaki ta fita tabarta awajen a tsaye.
Abun na mugun damun kafayat aranta amma hakanan ta basar da komi taja akwatinta ta wuce
babban mansion din late Alhaji jimada dake anguwan gwarimpa inda family house dinsu Ahmed
yake....
SURAYYAHMS. 08060712446 chat only..
" What did u guys think about this chapter? ....
[5/28, 9:20 AM] SURAYYAHMS: *KISHIYAR ƘABILAH 6..*
BY SURAYYAHMS.
Tunda kafayat ta dau motarta tahau kan titi tana tuki babu abunda yake dawo mata akanta sai
maganan da sukayi da mahaifiyarta, tafiya take amma bakaramin bugawa kirjinta yakeyi ba, ta
rasa da wanne xataji tasan dai inhar bata samu Ahmed ba babu Abunda xai hana mamanta yi
mata auren dole, atake taji kasala na dirar mata akowani sassa na jikinta,da kyar da wuya ta
kaucar da wnn fargaban tafara tunanin yadda xata yi tasamu cikar burinta akn Ahmed,
musmmn aynxu data san da cewa xancen ya kwabe mata yaxamo mata tamkar kashin kifi a
wuya, tasan dolene komin rintsi komin wuya tasan yadda xatayi su tsaida maganan auren nan
nasu da Ahmed damilare kafinan tace xata shiryawa komawa gidansu taje ta gamu da bala'i da
masifa irinna mamanta dayake jiranta.
wajajen karfe 1 dai dai na rana kafayat ta iso gaban babban gate na Jimada's family house
dake cikin wani hadadden estate dake anguwar gwarimpa.
Duplex ne babban gaske sai parking space gari guda mai dauke da motoci kala kala da basufi
guda takwas aciki ba. Kana ganin gidan xa kasan gidane daya kafa dumbin tarihi.
Mai gadinsu bahaushe dan garin yobe yana bude mata gate kai tsaye ta shiga bata tsaya
kulawa da gaisuwarsa ba. Tana fita ta wuce babban sashin su anty mojushola, Kayanta ma
anan ta bar ma masu aiki su suka ciro a booth suka kai mata cikingidan.
Dan babban falone dake shimfide da turkish carpet brown mai gida gida, ga saitin kujeru manya
na daidai rufin asiri masha Allah palon sai kamshin turare yake ko ina tsaf tsaf babu ko digon
datti, Anty moju ne a tsakar falo tanakan dadduma tana sallan axhr, kana ganinta kasan tadan
kwana biyu a duniya tanada jiki sosai da manyan maxaunai.
After some mints ta sallame sallan cikeda natsuwa sann ta daga kai ta kalli kafayat data kusan
kwantawa kasa agabanta sabida tsabar nuna girmamawa.
A mugun ladabce ta shiga Gaishe ta _o dara irọlẹ_ ma..
Anty mojushola dake murmushi sosai tace _irọlẹ mi darling, iyawo wa iwaju_ (Evening my
darling our future bride) tana murmushi sosai tace "kafayat hows ur mother? Fatan tana lpya ?..
Wani irin murmushi kafayat tayi kanta na can kasa tace Alhamdulillahi she is fine maaa _o
ṣeun_
Anty moju tace its okay.
_ọlọrun bukun fun ọmọ mi_ (God bless u my child) ure welconme
Tace Ameen oo _o ṣeun_
A dede nan Anty temi ta tarar dasu, nan kafayat ta miƙe tana murmushi sosai ta koma gefenta
itama ta rusuna har kasa suka gaisa suka danyi hira awajen lunch kadan kafin nan kafayat tayi
xcusing dinsu taje quest room in da kayanta yake tayi sallahn axhr tayi wanka ta sake cancanda
kwalliya snn ta sauya wani kayan mai kyau ta dawo kasa.
As usual bata xauna acikinsu ba direct kawai ta wuce kitchen ta shiga kkrin shirya musu wani
irin hadadden dinner, she planned to cook igbin chops with yam wanda kafin ma ta fara hada
girkin saida ta tsaya ta hada musu wani irin tasty mushy butter crumbs na taɓawa snn ta hado
musu da cold and refreshing smoothie takawo musu har cikin falo inda suke xaune suna kallo,
anan ma babu wanda bai saka mata Albarka ba, hirar lamarinta da Ahmed suketayi suna
tabawa ita kuma tanacan kitchen tana shirya musu abincin dare. anty mojushola tayi tayi akan
Ahmed yaxo gidan da daddare ayi dinnern tare dashi amma sunkira wayarsa sau babu adadi
basu same sa ba,duka line dinsa a kashe suke tun da rana, kai Har gidansu sun kira amma duk
ba a sameshi ba.
Kafayat kuwa tana kitchen tanakan aikinta happly da Farko ta tafasa doyarta ta xuba a wamer,
sauran kuma tayi tuwon sakwara da shi shima tasaka shi a wamer na daban,for igbin dinta bata
wani bata lokaci ba ta nemo shelled jumbo snails (dodon ƙodi) da scotch bonnet pper, tattasai
da albasa da lemon tsami, bay leaf, manja, shrimp powder da seafood bouillon powder Nan danan Ta hada igbin chops into 2 difrent ways, daya tayi sauce daya tayi stew. Wanda xa'a
iya serving dinsu duka da tuwon sakwarn da tafasashen doya.
Bayan ta kammala hada abincin ta hado musu da drinks masu dadi kala kala ta jera komi akan
dinning table snn tahaura sama domin yin wanka.
Kafin kace wani abu gida ya cika da yan uwa da jikoki cos Anty ramatou bata tsaya nan ma
saida ta gayyaci surkunayen su wanda suke nan a nigeria suka xo da yayansu yin dinner. Anty
Nurat itace matar babban yayansu Ahmed, wato brother kaziim AREMU yana da yaransa uku
duk maxa, "shehu", "sulu"da "femi". Saidai shi mijin nata yana kasar waje bai dawo ba tukuna.
Sai Anty Adizatu itace matar Brother Hamzat dimeji, yaranta biyu duka mata, medina bolanle da
karimat omolara. Brother hamzat Shine mafi kusanci da Ahmed dan haka komi na shirin da
akeyi na bikin Ahmed shine yake saka bakinsa aciki kai tsaye.
Sai sistersu xainab moturayo wanda daga ita sai Ahmed din, itama bata nan taje oshogbo inda
gidan mijinta yake ita kuma danta dayane dan karami shine shafi'u dake tadan samu matsalar
rashin haihuwa.
Anty nurat taxo da Autarta femi, sai Anty Adizat kuma taxo da duka yan matan nata wato
Medina da karimat 10 and 13yrs old.
Around 7:30pm lokcin kowa yaci kwaras an hallaro kan dinning table
Kafayat was really feeling like a bride musammn ma dataga matan yayun Ahmed sunxo da
yayansu anacin abincinta anata xuba santi already su medina da su femi da karimat sunata
kiranta da sunan iyawon Uncle Dami.
Duk dama rashin halattar Ahmed ixuwa wajen dinnern yaso yadan dameta aranta amma
soyayyar da familynsa sukata nuna mata awajen ne yyita sassaita mata xuciya.
Itakanta ta nemei shi awaya sau babu adadi amma duka layukansa a kashe. Around 10pm aka
kammala hira kowa ya watse.
Nan Kafayat ta koma makwancinta da tunanin hirar tsokananta da sukayi a tsakanin Anty temi
da su anty nurat na cewa yakamata su hada ma kafayat da Ahmed grand surprise engagemnt
party a gidan. Acikin wasa da dariya sukayi hirar amma da mamakinta sai taji washe gari da
safe Anty temi tana sake dago mata da maganan.
A bangaren Ahmed kuwa aikinsa kawai yake kkrin kammalawa da wuri domin ya samu
isasshen daman yin tafiyarsa cikin kwnciyar hankli batare da tashin hankli ba. Jiya monday din
da sukata kiran layinsa akashe bai dawo gida ba ne, a office dinsa ya kwana yana aiki shiyasa
bai kunna wayarsa ba.
Yau Tuesday morning da Asubah ya dawo gidan batare da sanin kowa ba yy wanka ya shirya
kansa ya kara ficewa asibitin Dr hassan don ya kammala da can shima...
Gobe Wednesday by 9.am jirginsa xai tashi ixuwa calabar, and he want to beat it on time ixuwa
lokacin daxa aci taron ogoja market festival dan anan ne kawai yasan xai iyacin karo da Adiaha.
Jimada family house
Tuesday morning
wajajen karfe tara saura na safiya kafayat ta fito ta kammala musu komi tana kan Goge goge a
kitchen sai ga Anty tem ta shigo,hira suka kamayi suna dan raha a tsakanin su, Anty ramatou
tafara gaya mata Yadda suke son komi yayu sabida dama sunkirata ne dan su shirya tarban
Ahmed a matsayin angonta na next week.
Anty ramotou ta bata 100% tabbaci na cewa komi xai tafi musu daidai sabida aganinsu sati
biyun nan kamar gobe ne so babu amfanin jira shiyasa suka kirata kawai domin taxo afara dan
shirye shirye...
Idan ana maganan auren nasu Kafayat will be blushing all the way like jinjirin biri. Sai kaga har
tana kasa iya haɗe ido da su anty temi a tunaninta sun riga sun dawo surukunai.
Sukuwa abunda suke so kenan suga sun same total submission and biyayya daga wajenta, ta
inda koda anyi Auren sune xasuyi controlling Rayuwar Ahmed tunda Hajy khadijatu uwarsa
itace take juya musu kan dan uwansu Bello, But with kafayat by their side sunsan xasu same
nasu daman suma ata wajen Ahmed.
Haka suka nitsar da kafayat suka nuna mata cewa babu wani abun kunya wajen ya mace idan
tayi proposing ma namijin datake so dan ba haramun bane.
Tunda Ahmed yaki ya furta mata yana son ta kuma yana son suyi aure sukace toh ita saita
shirya furta masa dakanta inhar Ahmed ya amsata toh basai ma anjira 2 weeeks din nn ba xa'a
fara shirin aure .
Hakanan su anty nurat da anty najat suka taru suka cikama kafayat kasa aciki, aka fara shirya
grand suprise proposal party wa Ahmed. Kasuwa suka baxama na musammn aka sissiyo kayan
ado wanda xai saka Ahmed ya kasa iya rufe bakinsa inyagani. Wani hadadden backless red
flowing gown kafayat ta siya mai tsada na dubu arba'in da biyar da takalmi mai tsini da head
crown da flowers da rings dinta masu kyau.
Har dare sunakan yawon siyayya agari suna shiri ma suprise engagement party kafayat kuwa
tasha hadadden gyaran gashi da attachement cos batada dogon suma sai tayi manicure da
pedicure tasaka nails dinta masu shegen kyau da tsada she is ready shining like a bride kowa
sai yabonta yakeyi ranar
Shiyana can yanata aiki baima san me sukeyi anan ba, Tun safiyan ranan tuesday din anty
ramatou taxo gidansu ta same hajy khadijatu ta gaya mata abunda suke shiryawa, itama batayi
kasa agwiwa ba tasaka albarka akan lamarin dan aganinta kafayat will make a good wife to her
son ahmed inhar yana son auren ita bata da matsala sam.
Sunyita nemansa awaya still yauma tuesday din amma basu same shi ba,sai can da yamma lis
kafin nan yabaro asibiti ya taho gidan agajiye da niyyar shiryawa tafiyarsa na gobe da sassafe.
Samu yy hanklin maman sa duk ya tashi dan ta nemesa awaya har ta gaji,tun bai Xauna ba
tafara bashi labarin tafyar, haka tayi tayi dashi akan cewa ya shirya kawai gobe da safe karfe
takwas suje gidan su anty mojushola tare amma haka nan yaki mata sam yace baxaije ba dan
yasan baida wann lokcin domin kuwa karfe tara jirginsa xai tashi ixuwa garin calabar, toh gashi
abun nasu suprise ne ba ason agaya masa harse yaje ya gani hjya khadija ta rasa ta yadda
xata soma shawo kansa.
8:30 am na safiyar wednesday aka shirya masa suprise party din.
Kafayat is already feeling sooo excited dan gani take ko ba dan Allah ba idan Ahmed yaxo yaga
idanun manya awajen kamar irinsu anty moju da mahaifyarsa da su Anty temi hala xai hkra ya
amsa batun aurensun kawai even if its out of compulsion. Sosai ta saka ranta akan wann lamari
shiyasa ko wani baccin arxiki bata samu tayi ba.
Batasan da cewa shawo kansa dan yace xaixo wajen ma saida akata drama da shi agidansu
sosai ba...
Karshenta ma Anty mojushola ne ta kirashi dakanta awaya ta dinga kuka tana kora masa
ashariya ahakan ma saida ta hadashi da babansa kafin nan yace musu xaixo tare da