Author : Surayyams Category : Read Hausa Novels
tay kyau sosai kafin
nan ranar bikinta
Fattening session shine abuna farko da suke farayi wa yan matansu kafin ayi musu bikin su na
aure musammn idan yarinyar tadanja shekaru.
Wajajen karfe 8 na dare aka kammala hidimar mai gabaki daya kowa ya watse sabida idan waje
yay duhu akwai babban dodonsu dayake fitowa daga land of death yay nashi rawar ayayinda
shine zai tattara sauran dodonin su koma land of death sai kuma wani shekara in lokcin festival
dinsun ya zago.
Bayan an kammala komi Adiaha da wasu tsirarrun yan mata da za'a aurar dasu tun acikin daren
aka kaisu makaken gidan direct bayan ankammala sallamarsu daga gidajen iyayensu da duk
wani abunda suke bukata.
A daren ranar sosai Adiaha ta rungume iyayenta tanamai neman gafararsu tana kuma kuka
sosai dan aranta ta riga tasan ba lallaine su kara ganinta acikin dadin rai ba. Tasan in har
Ahmed ya nemi kakarta yay mata bayani awaya yau din kamr yadda tace mishi toh babu
shakka zata iya kasancewa acikin garin iyanzu dan ta dauketa dan sun riga sun yanke hukuncin
cewa zatazo ta dauketa ta gudu da ita inhar iyayen ta basu amince mata akan batun auren
Ahmed acikin sauki ba.
Kowa saida yaji tausayin Adiaha musammn yadda ta nemo yafiyar dukkan yan uwa da
kawunan ta duk andauka ko nitsuwa da nadamar abunda tay ne yasakata take wayann
emotional dramas ne.
Haka kuwa Har aka rakota gidan da ake musu fattening din aka sallamata cikin iyayenta babu
wanda ya fahimce komi datake ciki..
Dagata fannin gidan Alhaj bello jimada kuwa
Komi na tafiyane yadda yake gidan ya zamo boring sabida kowa sauraran ranar dawowar
Ahmed yakeyi akota wani bangare .
Banda cin abinci da tsinannen gulma babu abunda kafayat takeyi agidan, harsai ta gaji da
zaman shige da fice sann zakaga tay shiri ta fice kasuwa wajen business dinta kafin nan sai ta
dawo da can yamma.
Fanninsu Anty mojushola kuwa bakaramin kullatar hajya khdijatu sukayi aransu ba musmamn
ma da suka san da cewa aynzu dan uwansu alhaj bello yana musu kallon wanda basada
gaskiya.
Sosai anty moju take baza mulkinta cikin hargagin borin kunya.
sune da laifin amma kuma sunfi kowa hatsala da yin tsananin fushi da nuna cewa suna gaba da
kowa. Duk damuwarsu sudai sunfiso ace ita da sukayiwa laifin ita ta saukar da kanta ta zo
hargidan ta basu hakuri.
Hajy khadijatu tana da saukin kan da zata iya yin musu hakan dan kokadan batason fitina kuma
Allah baiyi ta da girman kai ba, saidai babban dadarta hajy maimunata ta dau zafi sosai akan
marinta da mijinta yay, snn tay mata iyaka akan su anty moju tace mata sam bata amince mata
dataje har gidansu snn ta basu wani hakuri ba musmmn ma akan gaskiyarta.
Haka suke zama haryau su anty moju shola basa amsa gaisuwarta basa ma son wani abu ya
hadasu bare sumata magana dan gani suke ta gama da dan uwansu bello.
Hjy khadijatu bata wani jin dadin yanayin nasu sosai sabida fushin nasu yana bala'in girgiza
mata duk wani nitsuwa da kwanciyar hanklin zaman aurenta ata fannin mijinta sabida shi
mutum ne da baison amsar laifin yan uwansa acikin sauki ,ta lura da cewa borin kunyar tasu
kadai ma yana raunana masa zuciyarsa sosai dan har gani yake kamar taurin kai kawai takeson
nuna masa da girman kai irin tasu na matan hausawa shiyasa taki sakin fuskanta da su
haryanzu.
.
Ata fannin Ahmed kuwa tun isarsa jos bai iyayin ma yayansa bayanin komi ba har saida ya huta
sosai snn yaci abinci sann suka zauna suka fara tattaunawa.
Brother hamzat yana da few contacs dayayi contacting awajeje kala kala domin a abincika
masa komi da komi game da rayuwar Adiaha dana iyayenta dan su tabbatar da kima da kuma
darajarsu.
Daga can kasar waje ma har brother kazim ya biya kudi yay hiring private investigators yau ne
aka kawo masa dukkan wasu bayanai akan familyn Adiaha, komi an tattaro musu acikin file
including family background, education, Level of IQ, blood group, Heredity sickeness irinsu
genetic diabetes, cancer, malformations, da blood diseases, mental illnesses,harda blood
counts dinta.
Komi da komi saida sukasa aka binciko musu basu kyale koda kwayar zarra na information din
su ba..ahakane suka san cikakken labarin abunda ya faru atsakanin kakarta hajy hajara
ayayinda ta kawo miji daga yola da tace zata musulunta da irin rikicin da akayi
Private investigators will tell u evrything about ur clients life including time date where and when.
Hakan yasaka suka samu cikakken ilimi akan su batare da saninsu ba, Anan ne Ahmed ya jijji
irin rayuwar da Adiaha tay abaya, duk sunayen samarukanta da yanayin yadda tay rayuwa da
su, wanda yasaka ya dadaji aransa kamar kawai taimaka mata kawai zaiyi amma badon takai
da ya aureta ba dan ya lura kmr bata da class sam sam.
Yayunsa kuwa duk idonsu arufe yake akan son dan uwansu dan duk yadda yake nuna musu
adiahar ce kawai ta matsa tana sonshi haka suma suke kallon abun a brain dinsu. Tun daga
nan inda yake fassara musu ita ta rasa kima da darajarta na ya mace gabaki daya. Shirin auren
nasu sai ya zamo kamar temakon ta kawai zasuyi amma bawai dan ta zame musu wani abu
mai matukar muhimmaci ko daraja ba.
Har gara gara ma abokinshi banji idan sunyi waya yakan tuna masa da cewa Adiaha zata
bukaci space a zcyarsa tare da kulawar sa sosai duba da cakwakiyar da ta jefa rayuwarta aciki
sabida shi, amma yayunsa kam dukansu babu ruwansu da wann, sai abunda Ahmed yace
musu yana so sukeyi, inda ma ace yau zaice musu ya fasa auren da babu fashi suma duka
bayanshi kawai zasu bi dan sosai suke da dabiar nuna cewa nasu nasune na wani dan banza.
Bisaga yanayin yadda aka gaya musu ake aure a al'adar garinsu adiaha suka hau tsara
kominsu dan su zamo ready dan Kirar kakar tata kawai suke jira domin suje yola suji me ake
ciki kuma.
Ahmed ya mugun matsuwa akarkare komi dan yau yake cika sati guda awajen amma duk ya
matsu yanason yaga angama ya koma Abuja bakin aikinsa.
Ata fannin Adiaha kuwa jiyan wani sabuwar dare ne agareta mai cike da tsananin firgici da
dumbin damuwar rashin gani da kuma jin Ahmed koda awaya ne.
Tunda aka kaisu gidan kulawar taga kowa na bacinshi peacefully amma ita Sam ta kasa iyayin
baccin dan daga ta runtsa kadan saita fara mafarkin cewa gatan nan da kayan aurenta amma
sosai kayan yakeci da wuta sai kuma taga ta fada awani irin rijiya mai tsananin duhu da ban
tsoro.
Hanklinta sosai ya tashi da irin wann mafarkin dan acikin daren kusan sau uku tay irin wann
mummunan mafarkin kuma duk abu dayane yaketa maimaituwa
Batadai san ma'anarsa ba amma yanayin yadda take ganin kanta acikin ha'ulai acikin mafarkin
yakan sakata jin tsananin fargaba da tsoro tare da nanikakkyar kokonto akan batun Auren nan
nata da Ahmed.
Yadda taga rana jiya hakan yau ma taga dare
Da sassafe ne ta samu tadan runtsa kadan kafin lokcin tashinsu yay dan shiryasu.
Tana cikin baccin taji kamar ana tabata tana dan farkawa taga wata tsohuwar mata tana ce
mata lokcin wankansu yay..da kyar adiaha ta sauka akan gadon tana share kan kumburarrun
idanunta da suka haura sama tsabar bacci bai ishesu ba.
Tsohuwar matar ce tay mata jagora aka kaita har wani dakin wanka inda aka shirya wani
tangamamen traditional sit bath bowl da kuma ruwan wankan dilka da akeyiwa amare. Towel
din jikinta ta cire gabaki daya ta aje akan cliff hanger duk ta kasa iya daga idonta sama ganin
yadda tsohuwar ta kure surar jikinta da kallo da wani irin yanayin kyabe baki da gulma a
fuskarta.
Da kamr bazata ce mata komi ba harsanda ta jawo ta kusa snn ta dube ta sama da kasa da
harshen yarensu acikin salon karin magana tana cewa "jikin mace tamkar rubber yake wanda
indan aka jashi zai dawo dede amma ba tear tear rubber irin wann ba. Da Wani irin kallon rashin
fahimta da jin haushi Adiaha tabi matar musmmn ganin yadda take jan fatar jikinta snn ta turo
baki gaba tace i dont understand. What do u mean by dat?
Matar ta kyabe baki ta dubeta a tsaye tun daga kan nonowarta har izuwa kan cikinta, da
cinyoyinta da kuma kasan mararta snn ta dafata ahankli cikin yanayin fada mata gaskiya tace
.."Nne, My doter, ur body look loose,i bet u most have slept with so many men or have been
married before? Why did u look older than ur age?
Adiaha tay mata wani irin kallon irin 'can pls mind ur own business?
Murmushi tsohuwar tay snn ta dafata ahankli tana cewa "Aure zakiyi yan mata ,jikinki shine zai
dauki kashi 70% na duk wani wahalar zaman aurenki (ya akayi kina karaman yarinya mai
kankantar shekaru amma jikin ki baida karfi sam sam) ta ja fatar adiaha ta sakeshi tana cewa
"ur body lacks its elesticity, tace "my dear This your body will not last long ooo..irinku ne daga
haihuwa daya jiki ya ragwabe tayay kenan zaku iya rike mazan zamanin nan?
Ayanayin damuwa sosai Adiaha ta kalle jikintan sosai, snn tace " i dont know, what shud i do
maaa? Cikin sauke ajiyar zuciya Matar tace inde kinason jikinki ya dawo hayyacinshi dolene sai
kin dauki lokaci anan kina shirya kanki batare da kin nemi namiji ba..
Muna da duk wani abunda zamuyi amfani dashi domin a gyara maki jikinki ciki da waje dats if u
so wish.
Cikin sauke ajiyar zuciya da kokonto adiaha tace " ok, zanyi tunani akai.
Matar batace mata komi ba ta bata waje dan tasan irinsu daga angaya musu gaskiya zasu fara
tunanin kudinsu ake so aci. But in her heart she really pitty adiaha.
Hankli kwance Adiaha ta shige cikin bahon ta zauna ruwan zafin na turarata sosai ayayin da
tunani kala kala suka shiga dawo mata mind dinta, she is soo woried akan Ahmed, ta damu
sosai akan batun yuwar cimma burinsu ayau, tunanin hakan bakaramin faduwar gaba da bugun
zuciya yake saka mata ba, sai can snn ta soma tunani akan abubuwan da matar nan tafada
mata akan jikinta dazu. Ita dai harynzu a brain dinta bata yarda da cewa jikintan nan bazai iya
jure wahalar zaman aure ba, "aure is not about sex and sumbmission? Well, she had sex tun
tana 15 years,tasan dai she is very good in bed izuwa yanzu, ta iya sex styles kala kala, dan
datake karama kafin tagama scndry mazan da sukayi saurayi da budurwa da ita in suna sexing
dintq wasu har suma sunayi ajikinta tsabar ta iya sosai. Saidai komi yana iya canzawa da
shekaru, tasan dai datake karama sosai kafin ma taje tafara karatu a university maza
dayawane suke kwadayin jikinta har takejin ko farinjini ne yay mata yawa. But during her
university days tasha wahala dan sosai ta fahimce cewa ba hakan ba ne, kawai kowa rabonsa
yake dauka ajikinta sabida batasan darajarshi ba, tunda ta fahimci hakan saita soma ganin salo
salo na yaudara da walkanci kala kala daga wajen maza. Har ya kaiga maza sun gama raina
mata hankli kowa yakanzo yayi manipulating dinta ne da kalman baki inya samu iya abunda
yake so ajikinta sai ya rabu da ita koma yaci mata mutunci.
Not long bayan ta tuba da harkan biyewa maza ta gamu da doc Ahmed and she tot dat namiji
irinshi nadaban wanda yazo daga wani waje zai iya sauya mata rayuwarta na har abada.
She is bruised, hurt, and used many times by men shiyasa kwata kwata bata da cikakken
nitsuwa acikin zuciyarta game da irin namijin datake so arayuwarta, sau tarin yawa kawayenta
suna gaya mata cewa itace da laifi da take nunawa maza cewa batasan darajar kanta ba,.
Asalin Adiaha irin matan nan ne masu sanyin zuciya,helpless,hopeless and self critizing, gani
take kamar kowace mace ta fita sa'a shiyasa duk sanda akazo mata da kalaman soyayya na
yaudara take saurin amsarsu da wurwuri dan itama so take tay rayuwa mai dadi irin na sauran
yan mata. Bata tacewa bare kuma tantacewa.
Idan taga kawayenta nayi wa maza yanga sai taga kamar sunfiye nuna isa ne da rayuwar karya
ita kuma aganinta saukar da kai wa namiji shine hanyar da zaisaka yaji yana sonka. Haryau a
haka take daukar karatun maza. Wanda suke gaya mata gaskiyar kuma gani take kamar
basusan me sukeyi ba. Deirs nothing wrong in being soft and kind, inta fadi hakan sai taji
kawayenta suna ce mata not to men of this generation.
Yes,koda ace ma wani bin kawayen nata sunada gaskiya wajen cewa wasu mazan mugaye ne
mayaudara ne amma batajin kamar doctor Ahmed dinta yana cikin irin wayann mazan da ake
fassarasu
Tun haduwatta da shi shine kadai namijin da bai nemeta akan gadon shi ba, hatta romance din
sai a wann karon daya dawone taga ya bata fuska har yana taba jikinta. Tasha jin labarin cewa
only real men who loves u truly sune sukeda self control kmr doc Ahmed din. Shiyasa kowani
rana takejin tana karason shi dan shine kadai ya fito daban acikin dukkan majazan datayi
mu'amala dasu arayuwarta izuwa yanzu.
Gani take kamar asalin sonta yakeyi,shiyasa bayason taba jikinta a araha kamr sauran maza,
dan babu wani namijin da zai ganta full mace tsayayya har ya iya danne sha'awa da
kwadayinsa akanta sai shi،.
Idanuwanta a lumshe take wann tunanin ayayin da soyayyar Ahmed uake dada ninkuwa acikin
ranta adede wnn lkcin motsin datajine yasata dago kai ta kalle wasu mata subiyu sun shigo.
Dayar matar tace
Adiaha Kiyi sauri ki taho ki shirya lokcin cin abincinki yay.
A ladabce ta amsa mata sann ta sauko kasa, ta dauraye jikinta tay asalin wanka snn ta daura
towel dinta ta wuce wani killataccen daki.
Tasaka hannu zata jawo wani towel din kenan taji anbiyo bayanta a sadade gabanta ne yay
mugun fadi ta juya sai taga wata mata sanye da mayafi akanta ta shigo.
Lokci guda taji kirjinta na bugawa matar na karasowa kusa taganeta da wani irin shauki suka
rungume junansu sosai dan saura kiris ya rage tay ihu tace grand ma, matarce tay maza wajen
toshe mata baki.
Hawaye taf idonta ta riko kakar nata hanmunta na rawa sosai tace 'grand ma har yaushe kika
iso?
Murya kasa kasa tace
Jiya naxo cikin dare jikata.
Tace Ahmed ne ya kiraki ko? I know he will ai na fada maki yanasona sosai, Grandma i almst
tot dat hala bazaki xo nan ba ,komi ma baxai faru dani ba,pls help me i just cant losse Ahmed..
Kakar tata tace shushhhh snn ta ciro wasu kaya nadaban ta mika mata tace" banda lkcin yin
maganan anan kiy marmaza ki saka wyann kayan ajikinki, naxo nan ne a matsayin masu kawo
muku abinci..huryy up befor thy notice us Muyi mubar nan our flight is in 30 min
Da mamaki Adiaha take kallonta tafara shiri cikin kankanin lokci suka sace jiki suka bar gidan
suka kama hanyar airpot atare Isarsu keda wuya suka samo baifi saura minti 5 jirginsu ya tashi
ba.
Duk farinciki ya mamaye adiaha batama tunanin komi aranta alkcin harsanda jirginsu ya tashi
snn ta juyo ta kalle garinsun zatay ma kasarsun bankwana sai kuma taji wani irin aranta jin
kamar rayuwarta gabaki daya ta budawa wuta ta konashi. Ahankli komi ya shiga dawo mata
kanta tafara tuna cewa "hala fa shikenan dagayau din nan bazata kara dawowa nan garin ba
nahar abada..the tot of loosing all her family strike her badly, sai taji jikinta ya mutu murus da
jimamin rasa su. Tun daga nn tay shiruuuu tanajin grand ma tana ta mata bayani akan yadda
sukayi dasu Ahmed.
Har tagaji tau shiru adiha Bata amsa ba,dan tunda ta aje kanta akan kujera take kukan zuci, she
remain sobby and emotional har suka iso garin yola da kakarta.
Wani hadadden anguwa aka kaisu na masu shi.
Gidan alhaji Aliyun babbane dake shidin babban dan kasuwa ne.
Yaransa duk sun girma sunyi nasu gidajen har jikokinsa wasu sunyi aure, matarsa ta fada masa
komi akan batun lamarin Adiaha shiyasa bai damu da kawota da tay ba. Tun isowarsu gidan
Adiaha takejin kanta daban duk taji kmr ta rasa nitsuwarta, duk damuwar rabuwa da gida sai ya
rufeta ta rasa wani irin tunani guda daya zatayi.
Da kyar ta iya cin abinci tay wanka ta fara bacci saboda dama jiyan bawai baccin ta samu ba.
Yanayin Adiahan ne yasaka kakartan ta nemi abata lkci ta dawo hayyacinta dan tasan akwai
wuya da rudani acikin wann lamarin nan nata.
Ita kanta shaidace ba abu mai sauki bane rabuwa da iyaye da yan uwa, ba abu mai sauki bane
rabuwa da rayuwar daka taso aciki tun kana dan karami. Tasan Dolene tadan bawa Adiaha
dama don ta samu space din da zatay tunani mai dan tsawo akan lamarim rayuwarta.
Ya kasance duk wani kalar hukuncin da zata yanke akan rayuwarta ya zamo nata ne ba abisa
tursasawar kowa ba.
Daga can gidan fattening kuwa anjira aga fitowar Adiaha amma sai shiru.
Dake sunada client dayawa sai basu damu ba sundauka tana daukar lokcinta me wajen
shiryawa, hatta waccan tsohuwar data dan bata shawara tay tsammanin cewa Adiaha zata yi
tunani mai kyau tasaka a daga aurenta dan abata cikakken lokacin da zata kimtsa jikinta amma
sai shiru.
Har wajajen karfe sha daya na rana da basu ganta ba yasa akaje dakin aka duba sai akaga
bata nan, dudduba ta sukayi agidan kafin suka aika gidan iyayenta inda atake hanklin kowa ya
tashi aka fara neman Adiaha..