Author : Surayyams Category : Read Hausa Novels
auren dole
za'ayi ma Ahmed da yarinyar danko ruwan da adiaha ta kawo musu awajen shi baisha ba abun
duk saiya dame hajy hajara ganin inda Ahmed yake dan babbasar da komi.
Bayan tafiyarsu ne hjya hajara ta dinga yima Adiaha surutayya akan behaviours din Ahmed.
Takaici kamar zai kashe tsohuwar ganin yadda Adiaha take ta murnan kayan tsarabar gaisuwar
Da suka lodo suka kawo.
A tunaninta soyayya ne yasaka aka kawo mata kayan tsaraba na Alfarma.Ga goro, ga buhunan
abinci,manja, gishiri,doya,kudin katoton rago, banda kananan carton carton na wasu abubuwan.
Suna zama zasu ci abinci grand ma ta kasa hkr Cike da masifafen mita Tace Adiaha kina bani
kunya fa, am actually ashame of u today.. Dolene ma yaron nn yana hura mana hanci ni banga
laifinsu dasuce su zasuyi komi ba saboda kin nuna masu we are nothing,memakon ki kare
martaban familynki ure here getting excited kinzo nan kinata murna akan abun duniya bakiga
yadda yaron nan yake daukar kansa agabanmu tamkar wani sarki ba...
Why is he behaving like temakonmu zaiyi, mune zamu bashi mata amma
Shine yake mata fadi da jan aji ? See oo My grandoter, ki bude idonki dan Bai kamata ace Duk
wann wahalar da kikayi akansa kwana biyun nn ace ko minti biyar bazai samu dominki ba,
Atleast ai yasan halin da kika shiga ciki na rikici da iyayenki akansa but im deeply suprise all he
has to say to u is congrat, Kai kai..nide wann abu baimin ba. He is such a jerk.
Adiaha ta bata rai sosai tace grand ma wai sau nawa zan gayamaki ne haka fa Ahmed yake, shi
bamai son magana sosai ba idan kin fahimce shi sosai zakigane cewa he is a good man.
Hjy hajara batace komi ta nade hannu cikin mamaki tanata kallon yadda maganan yy ma
Adiaha zafi tanata hargagin fushi.
Nan ta fara kare Ahmed akan dukkan korafin da kakartan tay, harda ce mata ai yanajin kunyan
yayunsa ne shisa bai sake jiki da ita ba, snn dan yace mata congrt akan zanca addini ai dama
badan shi ta sauya ba.
Babu ta yadda zaka kushe Ahmed agaban Adiaha batare da kawo maka wani dalilin da zai kare
shi ba. Sai cewa take ai tausayin halin da take ciki da iyayenta tare soyayyar dayake mata ne
yasaka familynsa suka ce zasu mata komi na hidiman auren and she is happy nd grateful for
that.
Adiaha ta dauka duk wasu kalmomin nata datake kare Ahmed dashi agaban grandma masu
ma'ana ne saidai batasan da cewa Maganganun datake furtawan yanayiwa kakarta ciwo aranta
bana wasa ba.
Aranta cewa take Adiaha is blind and desperate about this guy. Batasan da cewa mutuncinta
take sayarwa ba. She wont have value to them musmn ma indan sunajin kansu a matsayin
cewa sune sukayi komi na aure.
Ta rasa abunda zata ce mata kawai ta fasa cin abincin ta tashi cikin fushi ta koma dakinta
tabarta awajen ita kadai tana ta bawa kanta dalilai akan Ahmed na cewa lallai yana sonta ne
sosai shiyasa zai aureta
Jin abun yafara dan damunta saita tura masa sakon tex a sabon layin sa and she foolishly told
him cewa grand ma dinta is not really pleased with him, ganin hakan ne yasaka ya daure ya
kirata suka fara gaisawa.
Rabon shi da kiranta awaya tun ranar da suka rabu a calabar dan yace mata bayason tana
kirarsa koyaushe musmmn ma indan tana tare da familynta.
suna kammala gaisuwar Yy kmr bai karanta tex din sosai ba, sai Yace mata ta memeta masa
meyene grand ma dintan take cewa akansa..
Tafara gaya masa duk abunda kakarta ta fada da irin bayanin da itama tay mata akanshi.
Ahmed ya daure fuskan sa sosai cikin yanayin basarwa da bata rai yace "Toh shikenan naji,.zan
gayawa yayunq sai azo ayi magana a tsaida batun auren tunda grand ma dinki tace bata aminta
da halina ba.
Adiaha ta kwalo ido waje tace "Ahmed meyasa zakace haka? Da Bai amsa ta ba sai jikinta yay
mugun sanyi dan Sam batay tsammanin jin hakan daga gareshi ba.
Tuni yanayinta ya canza cos its seem he is gaslighting her now sabida yasan babu yadda ta iya
dashi, Cike da bugun zuciya da damuwa Adiaha tace Ahmed pls ni ba hakan nake nufi ba, kay
hakuri karkakai maganan gaba,grand ma is just being worried about me sabida yadda taga na
rabu da iyayena duka akanka.
Cikin yanayin hade ransa Yace " okay, yanzu kenan laifina ne da iyayenki suka rabu da
rayuwarki Ko dama akaina ne kika zanca addini? Zatai magana cikin katseta da shakurarren
murya yace "silent,ya isa haka.
"kar ke ko kakarki ku fara tunanin daura min wani laifi akan wani abu daya shafi rayuwaki dana
iyayenki sabida ni aurenki kawai nace zanyi Amma bance ki canza Addini ko ki bijirewa iyayenki
akaina ba...ya lumshe ido jin tafara kuka tanamai neman tafara bashi hkri, ya kuma bata ransa
muryansa kasa kasa cikin shan qamshi sosai yace ..'look ni ba hkuri nake so daga gareki ba, i'
m quite disapointed in u ryt now, kukan ki bazai nuna komi min ba, nifa bangane miki ba, shin
aurena zakiyi dan Allah ko dan in bauta miki dake da kakarki? Wn ai duk laifinki ne, dan inba
kece kika nunawa kakarki cewa ure blaming me for ur personal issures a mind dinki ba da hala
bazata fara dora bururakarta akaina ba.
"Me kakarki takeso?dan nazo gidanta shikenan sai In lashe kafarki ko in goyaki a baya na? Da
nace zan aurekin is dat not enough for u ppl? why wud ur grand ma expect me to take all the
burden of ur pain...nine na dauke ki daga gaban iyayenki ne ko nine nace ki rabu dasu?
Cikin tashin hankli Adiaha tace Ahmed pls listen bahaka bane kasaurareni mana
Tashi zaune yay cikin katseta tare da nuna mata bacin ransa a fili, Adiaha tafara kuka sosai
ganin ya dau abunda da zafi sosai ,ransa a harzuke yace bana da lkcin wnn rigimar, yau
alhamis ne, kije yanzu ki gaya mata cewa inhar bata aminta dani ba toh suy gaggawar fada ma
yayuna kawai mubar garin nan yau yau,as for kudin sadaki da duk wani abunda muka kawo
gidanta karsuji tsoron kin fadin mana komi mu bamu damu da wani abun duniya da muka kawo
muku ba,ina son kusani cewa auren nan fa ba dole bane akaina, ko akace muku babu mata ne
da suka fiki a duniya?ya kyabe bakinsa cikin yanayin basarwa, muryansa a kasa kasa yace
"Ohh pls, she can marry you off to wanda hanklinta ya kwanta akai for all i care, amma dai
bazan dauki laifin da banawa in dorawa kaina ba,and no one shud think of controlling my life,
akanme?mace zan aura ko rai zaku ban?..
Cikin shesshkar kuka Adiaha tace Ahmed ka dau magann nan da zafi mesa zaka fadi haka
Yace Da zafi mana, daga na bada sadaki yau ko kwana daya baiyi ba sai afara tunanin juyamin
tsarin rayuwata?ni ba karen mata ba, in a al'adanku maza suna bautawa mata mu bamu yi, our
women are expected to be very peaceful nd respectful...
nide na fada maki, Better do sumting about it koni na fadawa yayuna da kaina..u can't insult my
family..snn bana wasa da martaban iyayena ko acikin mafarki, idan har kunada matsala dani
then we wll call this weding off and leave.
Yana fadin hakan ya katse wayarsa Adiaha tay rigib ta sulale kasa ta dinga rabza kuka tana
cewa hello hello Ahmed pls listen, ba haka bane, sai shiru, ji tay tsoro da fargaba mai tsanani
yana neman dabaibayeta.
Kukan datakeyi anan yajawo hanklin kakarta izuwa dakin hankli tashe ta yo kanta tana
tambayarta ko lpya? Cike da bori ta haura mata tana cewa duk laifinki ne Ahmed yaji haushi
yana fushi dani..grand ma why wud u complain about him dat way, gashi ai yace ina
disrespecting familynshi, yace babu ruwanshi, wai idan kina da matsala dashi zai fasa aurena
kinema min wani..
Hjy hajara ta rike kirjinta dataji ya dau zafi sai ta rasa baqincikin Adiaha kona ahmed din zata
fara dubawa.
Tace Reema kina hauka ne Meyasa zaki je ki gaya masa maganan da mukayi dake anan gidan
tsakanina dake? Na fada ne dan in wayar miki dakai why wud u tell him ashe bakida wani sirrin
kanki komi aka gaya a gidanku sai kigawa Ahmed?
Tana kukan tace oho..
Nide kisan yadda xakiyi Ahmed ya dena fushin nan dani sabida duk kece kika jawo min,ai gashi
nan yanata cewa wai zai fadawa brother dinsa cewa zamu fara controling din rayuwarshi dan ya
kawo sadaki na..
Grand ma what if he call off the weding? I wll kill myself, wallai bazan iya rayuwa babu Ahmed
ba.
Hjy hajara batace komi ba tsaban bacin rai jikinta sai rawa rawa yakeyi shikadansa sosai, a
mugun fusace ta dauki wayar Adiaha ta dinga kirar layin Ahmed waidan ya dquka ta gaggaya
masa bakaken maganganu masu zafi ta huce takaicinta amma sai bai dauka ba.
Suna cikin hakan saiga Alhj Aliyu ya shigo dakin, ganin yanayin su yasaka ya fara neman karin
bayani, hjy hajara hartana kunfan baki da hawayen takaici tafara maida masa maganganu,
Tace "Alhaji kafa nemo yayun yaron nan, kace musu suzo yau yau su tattara abun duniyansu an
fasa auren..sudin wa? Sudin banza.."Me Ahmd din nan ya taka? meyake ji dashi da har zai
gaya min baqar maganan dayaga dama akan dan zai aure jikata? Akwai maza dubu wanda
suka fishi kyau da kudi,shi ba komi bane agaban wasu mazan wllh, shashasha dashi ma wanda
baisan halacci ba, wani irin wahala ne yarinyar nan batasha akansa ba har shine yau zaixo
yana dagawa mutane kafada da jijiyar wuya dan anfadi masa gaskiya? Ai gaskiyan kenan
baidamu da halinda Yarinyar nan take ciki ba, gani yake kmr sadakan kobo za'a bashi sam
baiya kallon mutane da daraja katon bayarben banza.
Anan ne adiaha ta gane cewa ashe kakarta neman Ahmed take donta ci mutuncin awaya amma
badon ta bashi hakuri ba.
Anan ma suka fara wani sabuwar cece kucen ran hjy hajara ya baci sosai alhaj aliyu kuwa
yanata lura da zallan kalaman tsagwaron rashin kunyar da Adiahar ta kara fandarewa da shi.
Alhaj aliyu daya fahimce komi yajawo matarsa gefe suka bar dakin ya dinga rarrashinta har
saida zuciyarta yay sanyi sann yafara gaya mata cewa hikiman daya ne zai iya budewa Adiaha
ido ta gane cewa shayi ma ruwa ne, wann hikiman shine su kyaleta ta aure Ahmed din,yace
mata nan da bada jimawa ba ita dakanta zata dawo bayan ta shiga hanklinta ayayin da duniya
ya gama koya mata wayo.
Da kyar hjy hajara ta Amince da wann shawaran dan taso ace kawai afasa auren kodq mutuwa
Adiahar zatayi, Abun nada matukar ciwo kana kallon jininka zai fada acikin halaka boro boro
amma ka kasayin komi akai.
Saida ta nutsar da zuciyanta sosai snn ta iya danne komi aranta tay hakuri snn ta daura niyyar
bin shawarar da mijintan ya bata akan Adiaha.
Ata fannin Ahmed kuwa tunda ya kammala waya da Adiahq bai sake kallon inda wayar take ba,
duk tulon miscals dinsu da suka masa shi baisan sunyi ba, wajen hotel din da suka kama yaje
ya samu abokinshi Banji yana zaune nan yafara gaya masa situation din, yace masa ai kakar
Adiaha tana son ta dora masa laifin komi shiyafara tunanin fasa auren ma sabida baison rainin
hankli.
Banji ya sha mamakin jin hakan, musmmn yadda Ahmed ya fayyace masa maganan da sigar
cewa sunason suyi controlling dinsa with emotional blackmail dan ace ai tunda sabida shine
Adiaha ta bar iyayenta da addininta dolene ya bauta mata sai yadda sukayi dashi.
Ran banji sai ya baci sosai dayaji hakan, suka ta bambami sunata kushe halin irinna matan da
suka kasance yaren kakar Adiaha dake ita inyamura ce,.
Saidai Duk da hakan Banji baiyi fushi sosai da Adiaha ba, yay tunani mai kyau akanta dan
yasan abun da tay ma abokinshin da wuya sosai.
Yace ma Ahmed yay hakuri yaji tausayin yarinyar sabida tana sonshi sosai..
Ayanzu ma basai an fada masa cewa Adiaha tana mutuwar kaunarsa ba, banji yace bakowace
mace bace zata bar komi nata tazo domin namiji kai hatta kafayat dasuka dade suna tare baya
zaton zata masa irin wnn sadaukarwan da Adiaha tay masa.
Abokinshi Banji ne ya dinga lankwasashi da dalilai kafin nan zucyarsa tay sanyi har ya rusuna
yabar zancen, suka fara wani hirar na daban.
Tambayarsa yakeyi yadda zaiyi da kafayat bayan ya aure Adiaha
Ahmed Yace bai sani ba.
Amma yasan bazai bawa kowa hakuri dan bai aure ta ba, yace "rayuwar shi ce, dan haka yana
da ikon da zai canza ra'ayin sa akan duk wacce yaga dama witout owing them any explanation.
Banji baice komi ba duk dama yasan akwai kura agaba.
Washe gari ranar juma'a hjy khadijatu ta idar da sallah kenan ta turawa kafayat tex message
mai cike da nuna kulawa tanamai tambayarta ya jikinta kuma yaushe zata dawo, ko tazo ta
daukota ne sabida gobe ne za'ay walima na komawa sabon gida and she wants her to be deir
tunda a matsayin ƴarsu suke daukanta.
She care soo much about kafayat dan tunda akace mata batajin dadin jikinta kusan kowani lkci
suka hadu da mijinta saita tambayeshi ko yay waya da ita amma ko wani lokci amsar dayane
dukansu basu samu damun magana da ita ba
Gara gara ma shi dayake yakan samo musu bayani awajen mahafyarta.
Kafayat na zaune a bakin gadonta ta farka a barci kenan zata shiga wanka
Taji shigowar sako,jikin ta duk a muce yake dan kwana biyun nan tunanin Ahmed ne kawai yake
fado mata acikin ranta musammn ma da Alfah yace babu aure a tsakaninsu.
Maganan ya shige jikinta da kwakwalrta sosai harma fiyeda yadda itakanta take zato.
Duk zuciyarta a hatsale yake da damuwa Tana kammala karanta tex din hjy khadijatu memakon
taji sanyi aranta sai taji fushi da damuwa mai yawa ya hautsina mata jiki, agefe ta jefar da wayar
tare da jan wata doguwar tsaki dan inhar akace Maganan Alfah ya zamo gaskiya to babu
shakka an cuceta.
Jin kanta takeyi very frustrated with her life har yau haushin kowa da komi takeji aranta.
Wanka tay ta fito ta sanya english wear riga da skirt blue colour ta baza kitson attacemnt dinta
ya sauko har gadon baya yana shan iska, nan ta sauko kasa izuwa falon kawar mahafinyar tata,
ko ina yay shiru acikin gidan da alaman ita kadaice tasamu har sun kammala karyawan su sun
fita. Ido ta daga ta sake kallon agogo ganin karfe bakwai da rabi saura na safiya
Mamaki takesha aranta dan tasansu da baccin asara, sai tarasa miyene mai matukar
muhimmancin haka har da zai fitar dasu da sassafen nan. Wani zuciyar yace mata hala harkan
business dinsu ne yasaka sukayi sammako
Nan ta zauna tafara hada tea makanta dan saiyaune tafara jin dama dama ajikinta, cikin
nitsuwa tasha tea din da two slice of bread, ta dade azaune awajen ganin basu dawo ba har
wajen karfe goma na safiya hakan yasaka taje kitchen tafara fere doya ta tafasashi yay laushi ta
hau daka sakwara.
They have varieties of soups a fridge cikin kankanin lokci ta hada komi abunta hadi da cewa
batada gwuyar aiki arayuwarta, bayan ta kammala komi ta fito dashi falo tanakan ci batare da
sanninta ba awajen wani irin baccin bazata ya kwasheta.
Ata wani bangaren kuwa
Hjy fatihat da kawarta hjy rakiya sune agaban goddes sunata kallon ta acikin wani kwarya.
Wani ruwa goddes ta miƙawa hjy fatihat tace ta zubashi akan setin inda zucyar Kafayat yake
daga cikin kwaryan.
Babu musu ta amshe goran ruwan goddess tana fada mata wasu kalmomi da yarensu itama
tana nanatawa ahankli ta juye ruwan akan kirjin kafayat duka tana kammalawa sai gq wani irin
yawun bacci mai yawa ya fara fita daga bakin kafayat yana zubowa acikin kwaryan
Bayan ya taru sai kafaya din ta bace musu a kwaryan bat.
Dariya goddes ta bushe musu dashi alaman aiki ya kammala, kafin nan ta daga kwaryan can
sama tare da yawun kafayat din, tana saukarwa ta saka hannu aciki tq dauko wani garin magani
a cikin kwaryan da ya bayyana dakansa,nan ta miƙa musu tace su bawa kafayat garin da shine
zasu cimma burinsu acikin sauki.
Zuciyarsu fari tasss suka bar wajen goddesss suka dawo gidan suka samu kafayat tanakan
bacci tuwonta haryay sanyi sosai.
Saida suka kammala tattaunawarsu snn hjy fatihat tace duk da sun karbo maganin daukar
fansa amma batason tay ma yarta komi na dole arayuwarta, dan haka kafin suy amfani da
maganan sai tay magana ta fahimta wa kafayat.
Hakan kuwa akayi kafayat ta farka a daburce ganin kan kirjinta ya gama jikewa da ruwan da
batasan daga ina yafito ba
Ganin ta daburce sosai saisuka hau lallabata sunace mata wai Ac ne ta mance bata kunna ba
da kuma damuwar auren Ahmed damilare data saka Aranta
Nan Suka zauna kamar mutanen kirki suka fara lallashinta sunata bata shawara kamar iyayena
na gari, hjy fatihat ta nuna mata cewa ita dai harga Allah bawai bata son Ahmed bane, kawai
bata son yarta ta aure namijin da baisan darajarta bane kwata kwata,tacewa kafayat inda ace
Ahmed yana sonta kamr yadda take sonshi da sosai zata goyamusu baya, amma duk wata uwa
bazata so taga yarta tana bautawa soyayyar namiji ba a sune sukesonkan ma ya ka kare bare
ace kaine kake sonsu.
Duk suka taru suka kashe ma kafayat jiki ta hanyar nuna mata cewa duk abunda sukeyi dan