Author : Surayyams Category : Read Hausa Novels
take nema daga wajenshi na cewa bazai guje mata ba duk rintsi duk wuya
zai kasnce yana tare da ita harsai sun cimma burin su na aure.
Cikin rashin wata mafita Ahmed Yace mata karta damu babu inda zaije snn har yay magana da
brothers dinsa shi ata fanninshi kusan ma a shiryesuke ita kawai suke jira.
Sosai wann maganan ya faranta mata rai snn ya kara mata karfun gwiwa gani take a brain dinta
kamr dagaske ne Ahmed yana mutuwar sonta aranshi.
Nan ta soma masa bayanin abubuwan da zai iya faruwa yau izuwa gobe Dake duk abababen
daya shafi a'aldarsu ta dabbaka bautar Allolinsu ne tun na kaka da kakkani, nan Tafara gaya
masa yadda akeyin wnn festival din, suna cikin maganan sai tafara ji ajikinta kamar wani ya
labe yanata kallonsu saidai kodata juya baya tana dubawa bata ga kowa awajenba.
Tay murnushi snn Tace masa dodonin Allolinsu zasu bayyana yau asarari da siffofi mafi muni da
kuma ban tsoro Dan haka bazaiyu yau tazo wajenshi ba harsai an kammala komi sabida wann
festival nayau din is very spritual for all the tribes din dake wann yankin nasu basu kadai ba.
Yanzu haka dodonin nasu suna kiillace ne a makewayensu inda ake ginashi da fresh palm tree
leaves mai tsawon dayakai 15fts sabida ba a bukatar kowa yay ido biyu dasu harsai lokcin
fitowarsu sarari yay.
Suna cikin wann hirar tasu cikin nishadi sai ganan motsin kafafu ata bayansu da alaman
mutane suna tahowa ta wajensu agaggauce.
Dukan tara tara kirjin adiaha yay tay saurin kwace hannunta ana Ahmed snn ta leƙa ta bayanta
agurguje kafin nan ta dawo da baya jikinta yanamai barkewa da wani irin rawa mai tattare da
rudewa.
Mahaifiyarta tagani tare da wani crier sun tattaro kattin maza har su guda uku masu jini ajika
sun runtumo manyan sandu na a hannayensu suna tahowa ta inda suke dashi. Gabanta ne yay
mummunan fadi dan sai yanzu ta gane cewa dagaskene dazu da jikinta ya bata ashe tuntuni da
akwai wanda yake lekensu da alaman shine yaje yakai gulma.
Tsabar bugawar da kirjinta yakeyi sama sama numfashinta yake hawa, ta juyo a rikice ta kamo
hannun Ahmed tace masa dolene ya boye kansa anan wajen inda suke kar mahaifyarta tazo
ta ganshi su tada wata fitina harsu jawo ace za'a kashe shi.
Yace mata shi bazai buya ba saidai in ya tafi
Ta dada lekawa taga sun riga sun iso kusa dasu inhar Ahmed ya juya ya tafi toh tabbas zasu
bishi sumasa illa awajen dan asananinta da fushi da fada suka rabu da mahafiyarta dazu agida
dan haka koda tazo nan hala ma bazata tsaya ta fahimceta anan din ba.
Jawo hannunshi tay cikin gaggawa da narkakken magiya idanunta cike da tsananin tsoro
tanace masa karyay mata taurin kai, duk yabi ya gaji da lamarinsu, amma hakann take janshi,
nn ta bude wani old sac tace masa ya daure ya shiga ciki ta rufeshi, da taurin kanshi da komi da
kyar dai ya shiga ciki ta rufeshi acikin wani katoton buhu snn taja ta tsaya awajen abunta.
Tana kammala rufe bakin buhun saigasunan sun fantsamo cikin wajen a hargitse, "wher is
he?tambayar da kowaa ya jefo mata kenan aka barta da zare ido tana kallonsu.
Da kyar Taja taci fuska jin yadda mahaifyarta ita kanta take cika ta da tambayoyi akan mutumin
da akace anganta dashi saidai batace mata uffan ba
Matasan nan kuwa atake suka fara bincika wajen suna hargagi kusan dik inda suka taba sai
sun buga ma wajen sanda dansu razanar da su sosai, aganinsu inma boyeshi tay ai zaiji tsoron
rasa ransa ya fito amma ko motsi Ahmed baiyi awajen ba
Duk borin da Adiaha tay musu na cewa ita kadai ce awajen bai hanasu komi ba har jikin sac din
suka bubbuga wanda yay sanadiyar jima Ahmed ciwo agefen kunnenshi.
Da kyar dai suka hakura suka kyaleta musammn ma da adiaha taki ta amsa tambayoyin su.
Crier kuwa yace musu tabbas yaganta anan tare da wani hausa man yasaka jallabiya snn da
dukkan alamu sun saba da junansu sosai.
Hade da mahaifiyarta da wayann matasan duk suka taru suka mata barazanar cewa indan ta
yarda har suka ganta da irin wayann mutanen da crier ya fada toh zasu mata abunda bazataji
dadinshi aranta ba.
Inhar yarinya budurwa fara biye biyen strangers irin haka She will be question by the gods.
Sanin hakan yasaka mahaifyarta tamata jan karfi ta tasota agaba har suka kai gidansun atare.
Tun ahanya take turawa Ahmed tex duk ta damu da yadda ta barshi awajen shikadai, ta tura
masa sako ajere yafi sau takwas tana tambayarsa koyana lpya, ciwo kansa ya dingayi sabida
buga sac din nan da suka dingayi da karfi. Tsabar baison wani fitinan kawai sai ya rubuta mata
cewa he is fine, hakan ma ai bakomi bane. Sosai hnklinta ya kwanta daya rubuta mata hakan.
Daga isarsu gidansun kuwa wani sabuwar cece kuce ne ya kaure a tsakaninta da mahaifyarta.
Mrs grace ta matsa daa cewa lallai sai Adiaha ta fito fili ta gaya mata wayene mutumin da aka
gansu tare da shi.
Tun Adiaha tanajin shakka da nauyin fada harta soma fayyace abun ahankli ahankli, matsalar
shine sudin suna bala'in mutunta iyayensu dan haka bata iya fitowa fili gatsau ta fayyace mata
komi dake wakana a tsakaninta da Ahmed ba
Kawai ce mata tay aynzu tana da wanda take so, shiyasa gaskiya bazata iya auran zabin da
aka mata ba.
Wann bai dame mrs grace sosai ba dan ta riga tasan halayyar yaran zamani da canze canzen
ra'ayi na banza.
Babban Damuwarta shine ta tabbatar da cewa ba wani hausa man din bane kamr yadda labari
yazo mata dazu
Da kyar ta samu nitsuwa aranta akan hakan, sann ta tutsiye yarta adiaha akan data gaya mata
wanene wann masoyin nata,daga in ya fito, snn waye shi? tsoro da fargaba saiya hana Adiaha
iya furta komi, tin mahaifyar tata nabinta cikin lallami harta soma fahimtar cewa da akwai
abunda yarta adiaha take boye musu. Gashi dai crier din nan ya riga daya fayyace mata siffar
yaron ya tabbatar mata da komi, amma sam batason ma ta fara amincewa da hakan aranta dan
aganinta inhar hakan ne toh kwakwalrta ma bazai iya daukawa ba bare ajega ta furtashi da
bakinta wani yaji.
Duk wani wayo da uwa takeyi domin ta samo bayani awajen yarta saida tay ma Adiaha saidai
the more tana tursasata ta fada the more tana fahintar cewa da akwai babban lamarin da
adiaha take son gaya musu mai girgizawa da kuma nauyi sosai wanda shine take boye musu
ayanzu.
Tun ba'aje ga bayyana komi a fili ba jikin mrs grace ya soma mutuwa, jiknta a sanyaye tace
"Adiaha, ki rantse da ubangiji cewa baki da wata alaka da wani bako
Dayazo garin nan..
Adiaha tay shiru kanta na can kasa harsaida hakrin mrs grace ya kare ta daka mata tsawa snn
tay motsi ta dago kai tana kallonta awani irin yanayi na rashin sanin inda zata fara furta wann
maganan
Nasu da ahmed a fili.
Ahankli Tace mum, its true ina da wani saurayi, he is not from here...
..amma ina sonshi,..ina son Doctor Ahmed
..shinake son na aura..
A rikice mahaifyartan take kallonta ayanayin shock ta kunce zani ta yar akasa snn ta daka wani
rikitaccen tsalle snn tace "Doctor who?kikace A..Ahmed,ewoooo a Hausa man?.Adiaha a hausa
man, cikin girgiza kai tace _mba nu_ banji ki da kyau ba..zoki min bayani i dint get u..
Adiaha bata iya cewa uffan ba tafara ja da baya baya sabida tsananin tsoro, acikin bambami ta
karashe cewa mumy im serious ooo, ni dai shi kawai zan aura. .
Mrs grace ta harzuka ta na shirin cafkota ta firgita ra ruga aguje ta shiga dakinta ta kulle kofarta
da key jikinta na tsananta rawa jin inda mahaifyartan take dada kwala mata ihu cikin tambayarta
daga waje.
"Adiaha you must come out and explain urself ooo..
Shiru tay ayayinda ta jingina bayanta da jikin kofar tana jinta tana ta rusa mata buhun masifa
mrs grace sosai ta fara fahimtar inda yarta adiaha ta dosa, duk sai taji jikinta ya mutu, After a
while adiaha sai taji shiru bata karajin motsinta a bakin kofar ba.
Da kyar ma ta leko ta windo taga ko ina shiru da alaman babu kowa agidan nasu ji take hala
duk anje ne ayi shirin festival dan haka ahnkli ta bude kofar ta fito tana mamakin inda
mahaifyarta zata kasance ayanzu.
Wayar Ahmed ta kira bai dauka ba ta tura masa text messg ta gaya masa cewa mahaifyarta ta
soma fahimtar komi game dasu tunma bata fayyace mata ba.
Ficewar mrs grace agidanta yau sam bai mata kyau ba dan kuwa koda taje tay kyakkwan
bincike abakin mutane saiji take ana ce mata lallai ana ganin adiaha da wani bakon mutumi
wanda basu taba ganinshi ba.
Kanta duk ya daure, Wani tunani tay snn ta wuce gidan dan uwan mijinta uncle uno,tana isa
direct ta aika aka kirawa mata yarsa ekaete.
Agaba ta sakota har gaban iyayenta inda tasan bazata iya boye musu komi dake tafe da yarta
adiaha ba.
Haka suka saka ekaete agaba ta tambayoyi har saida tay musu bayanin komi batare da son
ranta ba..
Ita kanta ekaete din sai data jibgu sosai awajen iyayenta data kammala fayyace musu kan
lamarin..
Tsabar rudewa da mugun gudu mrs grace tay hanyar jeji tana kuka tana mai kiran sunan
mahaifin adiaha, tunma kafin ta isa gareshi muryanta harya soma dishewa..
A gigice ta isa gaban bukkan da mijintan ya gina Lokacin yana kan bishiya yana hutawa.
Da asalin yarensa na calabar ta soma gaya masa cewa ya sauko kasa kawai yaje yagani da
idonshi Tarihi zai memeta kanshi agidansu
Tace masa Yarsu adiaha ta kawo namiji dan hausa tace lallai sai shi zata aura kuma hartana
zuwa wajen shi batare da sannunsu ba, Kafin ma ta kammala fada masa sauran bayanin na
cewa yarsa na cikinsa harta yanke hukuncin cewa zata sauya addini tuni zuciyarsa tay fat fat ta
buga garin saukowa kasa cikin gaggawa nan ya rikito ya fado kasa sumamme.
Daga nan asibiti kawai aka wuce dashi inda atake yan uwansa suka kewayeshi,koda ya samu
ya dan farfado tun akan gadon yake famar tsine ma yarsa adiaha, yanamai cin alwashin cewa
zai kasheta ya huta da bakincikin datake so ta gundura masa anata daddaneshi ana bashi
hakri. Ekaete ne tay kkri wajen sanar da adiaha halin da ake ciki batare da kowa ya sani ba,
dan ko kadan bata son ta rasa aminiyarta akan namijin da tasan hala basonta yakei ba.
Tunda Adiaha taji abunda yake faruwa da mahaifinta a asibiti take bari kar kar dan atake ta fara
jin wani irin fargaba da tsananin tsoro mai rudarwa yanamai nakasa mata gabobin jiki
Tasan tabbas sukayi ido hudu da mahaifinta yau kasheta zaiyi har lahira dan haka dolene ta san
abunda zatayi, tunanin
Duniyan nn tay amma da kyar ta samu wani mafita kwara daya wanda bata da kwakwaran
tabbaci akansa amma tasan shine iya hanyar tsirar wanda zai iya kubutar da ita daga mutuwa
awajen mahaifinta ayau.
Sako take shirin rubutawa wa Ahmed sai kuma taga kamar sakon bazai iya fayyace masa
muhimmacin plan din nata ba.
Acikin sanda ta sudade jiki ta wuce hotel din taje ta sameshi, yau ko zama batay ba ta hau
gaggaya masa abubuwan da takeson yay acikin gaggawa kafin yamma yay. Nan ta aje masa
phone number da home adress na kakarta tace masa duk yadda za'ayi dai yanemeta ya gaya
mata halinda takeciiki.
Tana kammala masa bayanin komi tay masa sallama cikin yanayin gaggawa ta barshi ta komo
gidansu adan gaggauce dan batason wani ya biyota abaya bare har asan inda Ahmed yake
bare ajega zancen cutar dashi.
Dan aynzu ji take kamar Ahmed din nan shine kawai rayuwarta ..
Tana isowa compound din gidansu ta samu daf lkcin an dawo da mahaifinta daga asibiti ganan
yan uwan da elders na zuriarsu duk an taru a tsakar gida ana jiran aga kalar hukuncinn da
iyayenta zasu dauka akanta kai tsaye.
Da kyakkwar shirinta tazo dan haka ta zube kasa tafara birgima tun daga gate tafara kuka mai
yawa tanamai nuna nadamarta akan abunda yake faruwa.
A farko duk sun dauka tsorone ya sakata ta rikice amma daga bisani da sukaga cewa ta kama
kafafun mahaifinta tana kukan fitar rai tana cewa ta tuba duk sai jikinsu kuma yay sanyi.
Tay kneeling agaban kowa tana kukan makirci harda majina ta shiga gaya musu yadda ta hadu
da ahmed da irin son datake mishi, sai kuma ta wayence tace musu aynzu tay nadamar abunda
tay na cewa zata aureshi bayan tasan irin baqin cikin da hakan zai jawo ma iyayenta.
Atakaice dai Adiaha ta nuna musu cewa ta yanke alakarta da Ahmed
Yau Snn ta tuba hardace musu ta amince ayi mata auren kawai da duk wanda sprit of the
ancesstors dinsu ya zaba mata ayau awajen festival.
Yadda ta dinga neman gafararsu da zuciyarta har Saida ta bawa kowa tausayi kowa jikinshi yay
sanyi aka fara tausayinta sosai..
Duk da haka saida aka dan yiyyi mata masifa aka kara ja mata kunne
Nn mahaifinta ya yanke hukuncin cewa daga an zabi mijin adiaha awajen apeasing gods dinsu
yau, gobe da sassafe za'a fara shiryata domin bikin aurenta.
Ahaka suka tsaya da maganan kowa yaje ya hau shirin fita wajen festival hnkli kwance dan
adiaha sam taki ta nunawa kowa cewa badagaske takeyin dukkn wayann biyayyar ba hatta
ekeate ma saida ta boye mata wnn shirin nata.
A bangaren Ahmed kuwa iya abunda tacemai yay shidin yayi, ya tura ma kakar tata sako, snn
sukayi waya sai tace masa zata biyo jigi tazo calabar daganan zasu taho yola tare da jikarta
adiaha, amma kafin nan tana da bukatar shima ya je gida yataho da nasa magabantan domin
ayi maganan aurensu a lokci guda komi ya wuce musu. [5/28, 9:20 AM] SURAYYAHMS: *KISHIYAR KABILA... 13*
BY SURAYYAHMS.
Bayan sun kammala waya da hjy hajara a tsanake Ahmed ya dau wayarshi ya nemi lambar
yayansa wato brother hamzat dimeji snn yay masa bayanin komi acikin nitsuwa.
izuwa yanzu har ya yanke hukunci akan cire ransa ya gama sadaukarwa domin ya fahimce
kamar Adiaha da kakarta baza su taba kyaleshi ba harsai anyi auren nan.
Nan ya fadawa brother hamzat cewa hjy hajara tace masa acan yola zasu hadu bayan tazo ta
dauke Adiaha daga nan.
umartan sa brother hamzat yay akanda yabar garin calabar din immidetly for his safety kar ma
azo ace shine ya sace musu yarinyarsu.
Yace masa marmaza ya shirya ynzu ya taho ya samesa, zasu hadune awani protea hotel acikin
garin jos daga nan zasu san abunda zasuyi.
Babu bata lokci Ahmad yahau tatattara kayanshi yay booking available flight tun karfe 2 na rana
ya wuce airpot around 3pm sai gashi nan agarin jos direct ya wuce hotel din domin haduwa da
dan uwanshi brother hamzat.
A fannin Adiaha kuwa bayan komi ya lafa aka fara shirin zuwa wajen festival din nasu na
karshe. Duk abunda akeyi hanklinta baya jikinta amma hakanan ta waske take biye musu.
Yau Kowa yasako kayan shi mai kyau na A'alda sunyi matukar kyau snn aka haɗa wani gigantic
stage perfomance a village square inda za'a yita nishadi ayi rawa na karshe.
Lokacin gabaki daya mutanen communityn duka an taru an fito kwansu da kwarkwatnsu an
kewaye filin wajen.
wajajen karfe biyar da rabi na yamma aka harɓa ritualistic volley of canon shots wanda dashi
ake kiran Sprits din Allaloinsu dasu izuwa sarari.
Jim kadan kowani dodo ya fara bayyana daga mabuyansa, kowanne yana fitowa a style dinshi
suna tahowa izuwa filin taron daya bayan daya ayanayin siffansu Mafi duhu da muni da kuma
tsananin razanarwa.
Kowani halittar dodo yakan bayyanane a siffar fatalwa shiyasa siffarsun yake da matukar muni,
duhu da kuma firgitawa sosai,kowanensu ya fito filin sai yayi rawa snn ya wuce snn wani ma
yabiyo bayansa, Jama'an gari kuma suna bibiyarsu abaya abaya suna wakoki suna rawa mai
kyau da burgewa.
Adiaha da iyayenta da dukkan mutanen garinsu kowa ya fito ana rawan atare, bayan anyi rawa
anyi wasannin dodoni sann aka dauko tumbin doya aka kai har shrine inda ake tsammanin spirit
na allolinsu yana wajen. Bayan Cheif priest yay yan maganganunsu na yaren mutattu ya miƙa
doyoyin gaban shrine din nan ma akayi rawa.
Daga bisani ya saka hannu ya dauko doyan yanamai sanar dasu cewa goda of they lands sun
amshi ziyararsu sun kuma saka albarla akan abincinsu na wann shekarar dan haka kowa zai
iya cin abincinsa batare da wani shakku ba
Duk wani shagali na al'ada anyishi har da batun aure na yan matan da suka girma chief priest
da elders da iyayen yaran duk aka taru aka tsaida kwakkwarn magana snn aka saka musu
ranar shagalin bikin aurensu bisa al'adan yarukansa.
Anan aka kammala tattauna komi dazai wakana aka fara shirya hidiman bukukuwan yan
matan,Adiaha da sauran yan matan da ake shirin aurar dasu din kaf aka fara shirin fara yimusu
shiri da kuma hidima da sukaa sabayi na al'adansu.
Saidai tsabar matsuwa irrina iyaye da gaggawa anan atake suka miƙa yarsu Adiaha agidan da
ake kai amare domin a farayi musu al'adansu na "fattening"..
Agidan ne bride to be zata zauna a kula da ita na musamman, zata zamo bata aikin komi and
the elders will take very good care of her harsai tay bulbul tay kiɓa tay fresh