Author : Surayyams Category : Read Hausa Novels
https://chat.whatsapp.com/FK9DApum8np3UZe5pQXxy3
*KISHIYAR ƘABILAH...*
PROLOQUE....
_BY SURAYYAHMS._
_®Any resembelence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence._
Daga cikin Littafan dana rubuta:
#Arne
#samarin shaho
#sakamako
#ajalinso
#Ahumaggah
#tuntuben harshe
#kudi kumbar susa
#takaicin wasu
#shade of rufaida
#fitar rana
#lamarin gobe.
#Witching hour
wajajen karfe uku dedei na tsakar Dare wanda lokaci ne da turawa ke kiransa "witching hour" ko
"spirituql awakening" inda ratar dake tsakanin spritual world wato Duniyar mutattu dana rayayyu
bata da wani nisa, wnn lokci shine lokacin cin kasuwar ko wani irin maita da manyan kungiyoyin
asiri, Da shawagin bakaken fatalwowi da kuma bakaken Aljanu da kuma dukkan wani irin launin
supernatural spirits dake yawo cikin dare a fadin duniya.
Cikin wata jeji ne mai tsananin duhun gaske wanda ko hasken tafin hannun ka ba lallai ka iya
gani ba.
Banda sautin kafafuwa babu abunda yake motsi ajejin adede wann lokaci.
Wata kibabbiyar mata ce mai tudun duwaiwaka gata da tsayi da kuxari ta fito bujum daga cikin
wani kurmin ciyawa mai tsananin duhu jikinta sanye da fareren kaya kal mai kama da likkafani.
Wani bijimin bakin akuya ne a hannunta tana kkrin janshi da karfi ayayin da bakinsa yake daure
da wani irin jan tsumma da aka masa xane da farin chalk layi layi.
tun daga samanta har kasanta farine babu dison wani kala ajikinta face dan wani jan kyalle data
daure tagaban goshinta da shi, kafafuwanta ta babu takalmi amma haka nan take tsagawa cikin
duhun jejin da alaman tana cikin gaggawa ne domin ta samu isowa wani tsauni akan lokaci.
Daga bayanta wata matashiyace wancce baxata wuce yar shekaru 28 da haihuwa ba,daga ita
sai ita , batasako takalmi ba bare kaya bare kuma dan kwali, saidan farin kyalle na farin xani
dake bisa karjinta data dorashi da kyau, bayan babu wani abu a fuskarta face xanen jan fenti a
saman goshinta itama.
kanta sunkuye a kasa sai sauri take ayayin da take bibiye da matar dake mata jagora cikin jejin
acikin gaggawa..
Tafiyar da baifi na minti goma sukayi ba snn suka billa adede wajen wani katoton fili wanda yake
nan tarwal cikinsa babu komi sai shinfidaddyar farin kasa mai kyalli.
Filin shikansa bayyana yy acikin tsakiyar dokar jejin adede wann lkcin domin kuwa koina ajejin
wani irin baqin duhu ne amma wann filin shikadansa yana fidda wani irin farin haske mai shiga
idanu.
xubewa ƙasa agaban filin sukayi dukansu subiyu ayayinda jikinsu ya hau rawa suna karkarwa
kar kar kar kamar wani iskan sanyi nadaban ne yake ratsasu.
Dattijayar matar ce tayi sauri tafito da wani dan karamin kararrawa ta dinga kadawa tana wasu
irin maganganu can sai ga wani jibgegen dutsi ya bayyana agaban su mai shape dinsa kaman
kujerar sarauta golden colour yanamai fidda farin haske, haske mai tsananin kashe ido ne yay
walkiya sann wata bokanya ta bayyana akan dutsen girif tana xaune itama jikinta sanye da
fararen kaya. Atake suka xube kasa gabanta atare suna masu mata sujada tamkar itace
ubangijin su..
"Almighty Goddess of fire And revenge".
Tsawon lokaci kansu na kasa suna gaishe ta tana kallon can sama sai can snn ta miƙa xara
xaran yatsun hannayenta ta shiga shafa bayansu daya bayan daya da shi duk inda taja sai jini
ya fito wanda take kaiwa kan harshenta tana lashewa da alaman ta amshe xiyararsu snn xata
saurare su.
Hannu ta daga dan ta basu daman yin magana Nan da nan dattijiyar matan tafara mata
magana cikin harshen yarensu ta yarbanci acikin wani irin salo na tsananin girmamawa da
ladabtawa.
Muryanta na rawa ta xube kasa Tace _"Gbogbo oriṣa yinyin ti ina Ati iku_
Meaning All hail,goddes of fire and revenge, tace naxo neman wani taimakon gaggawa ne
awajenki ubangijiya ta,kafadun yarta ta dafa tana layi ma Allansun kamr wance xatayi mata
kuka snn tace"All mighty goddess of fire and revenge,tonite i offer my doter to the arrow of your
fire and revenge..
Cikin datsar numfashinta da muryanta dake fitowa acikin amo mai tsananin kuwwa da ban
tsoro goddess din tace "My child, what do you want?
Matar Ta dada rusuna kai har kasa snn tace "i want Justice for my doter, goddesss..we demand
justice.
Goddesss din tasu sai tay shiru batace komi ba,
Sai can sanda ta kalle akuyar da suka kawo snn tay mata alama akan taja shi tsakiyar filin sann
ta yanka shi ta xuba jinin sa awajen..
Yartan kuma ta umarce ta akan data ja katoton round circles a filin snn ta xagaye su dashi snn
ta kunna wuta a kan layin shima wutan ya xagaye su.
Wani bakin kwarya ne ya bayyana ta mika musu suka amsa, nan da nan dattijayar matar ta
janyo baqin akuyan ixuwa tsakiyar filin ayayin da yarta ta xagaye su cikin katoton circle data
xana shi da kasa snn ta cinna ma circles din wuta suka tsaya daga ciki.
Akuyar suka danne a tsakiya fuskar akuyan na kallon gabar kamr yadda goddess din ta umarce
su,a dede inda jinin yankan xai xuba matashiyar ta aje bakin kwaryan jinin akuyan na xuba
aciki, sauran da ya rage suka bari ya kwalala akasa acikin wajen
dattijayar matan ce ta yanka wuyar akuyan amma bata sake shi ba harsanda jinin nasa ya cika
kwaryan dake hannun yarta sosai.
Bayan sun kammala hakan nan suka kawo jinin dake cikin kwaryan har ixuwa gaban goddess
dinsu suka mika mata cike da ladabi da biyayya, amsa tayi ta miƙa kwaryan jinin can sama,
wani haske mai yawa yabi ta kai snn ta saukar Da shi ta hura iskan bakinta akai wani farin
haske ya fito daga bakinta ya shiga cikin ruwan jinin gabaki dayansa snn ta saukar ta basu
dukan su sukayi kurbi daya, bayan nqn tawatsa ma matashiyar budurwn sauran jinin ajiki
Wanda atake ta fadi kasa ta suma sabida spritual electric shock din daya kwasheta.
Bayan hakan ya faru ta juyo ahankli ta dube dattijiyar matar dake tsaye kanta a kasa tanamai
jiran hukunci dq harshen yaren su tay mata magana snn tace mata menene sunan yaron..
Kan dattijar matar na kallon can kasa tace sunan shi "AHMED DAMILARE BELLO son of
BELLO Ayodeji JIMADA.
Goddess ta jinjina kai tace and the girl in question?
Tace "Efik girl, born by an igbo woman.
Goddess ta kalli can sama snn tayi wasu maganganu da yare sosai tanayi tanamai bushewa da
dariya mai kara.
Can ta tsaya cak da dariyar snn ta juyo tana kallon matar ido da ido
tace "you can go now my child. ur work of revenge is done (ki je, aikin ki ya kammala)..
Ni Allahn ki inamai baki tabbacin cewa Ahmed, son of bello jimada and his wife doter of effiong
will never bear a child
..NEVER.
Acikin harshen yaren su tace"rashin haihuwar nan shine xai xamo silar rashin farincikin auren
su ta har Abada. Snn yarki ce xata kasance musu kashin kifi a wuyarsu dan haka na baki ixinin
kaita cikinsu.
Goddess Tana kammala fadar hakan ta bushe da wata iriyar dariya ayayin da dattijar matar ta
xube kasa tanamai mata godiya sosai
...sai can ta bace musu bat tare Da filin duka da kuma wutar da komi ma sai wajen ya dawo
kamar ba wajen ba,dan ganin kansu kawai sukayi agindin wani katoton bishiyar mangwaro mqi
tsinannen duhu suna tsaye, wani katoton duji mai manyan idanu na gabansu ya xuba musu ido
yanata kallonsu.
jan yarta dake layi tayi suka fice ajejin acikin gaggawa dan wajene mai hatsarin gaske. After like
20min suna gudu suka kai bakin hanya suka shiga cikin motarsu acikin sauri nan ne kowacce
acikinsu tamaida abayarta ajikinta snn suka kama hanyar xuwa gida.
Koda suka isa gidan nasu dattijiyar matarce ce ta rirriko yarta dake layi ixuwa dakinta cikin
kulawa sosai ta kwantar da ita tanamai rarrashinta dan ta samu tayi bacci..
Sai kuka yarinyar take dan Da sunan Ahmed din abakinta baccin ya kwasheta.
dattijyr matar ta jima axaune tanamai kallon yarta dats looking helpless and heart broken
,atsaye ta miƙe tanamai sauke huci mai xafi Aranta tanamai cewa Familyn Bello jimada saiku
shirya cos i fatihat adetunji balogun am coming for u......
SHARE PLEASE
FOLLOW WATTPAD @ SURAYYAHMS
CONTACT 08060712446
CHATS ONLY NO CALLS[5/28, 9:20 AM] SURAYYAHMS: *KISHIYAR ƘABILAH...*
_BY SURAYYAHMS._
Wattpad@Surayyahms.
_®Any resembelence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence._
Bi-ismillah..
Episode 1️⃣
A hankali yake kai desert din dake gabansa ixuwa bakinsa kansa a sunkuye yana dan
murmushin nan nasa mai kyau da ya kai ga har ana iya ganin lotsawar dimples dinsa.
Acikin sigar nitsuwa da kamala sosai yake xaune jikinshi sanye da wata petite cambridge grey
colour zegner french suit dinsa datamai kyau ajikin shi bana wasa ba.
Sassanyar muryan mahaifyarsa ne yake ratsa shi,ahnkli ya dan girgixa kai snn ya dago
lumsashun idanunwansa yana kallon dattijiyar matar dake Zaune akan kujerar dake kallon nasa
fuskarta a daure takafa masa ido tana kallonsa, "murmushi yakuma yi mai sauti xai yi magana
ta rigasayi a fusace tace "ohhhh,ni ce ma na xama abun dariyarka yau ko Ahmad? Maganan
yarinyar nan kafayat fa nake maka but ure busy smilling at me kamar wani abun arxiki nace ka
aikata mata..arent u ashame? Yadda ta karashe a fusace yasa shi kara sakin murmushi wanda
ya dada tunxirata,
muryanta cike da fusata tace "ohhhhhh wato ga mahaukaciya nan na maka ihu ko,Ahmed are u
out of ur mind?..
Babu shiri ya dan marairaice fuska snn ya ajiye fork din hannun sa da murynsa mai taushi da
dadi kasa kasa yace pls calm down, i am really sorry maa, wallh ba haka bane Mamee,ni nama
isa in maidaki mahaukaciya ne? ai naji me kikace akanta, toh ni wallh bansan ranta ya baci ba
ma saida kika fada ynx,toh wai meye nata na yin fushi ne dan ban tsaya a wajen birthday partyn
ta ba sai kace wani ni saurayinta ne? Wani ruwan Takaici ne taji ya shake mata makwogoro
daya furta hakan.
tsimewa tay bata ko kulashi ba dan tasan ranta ne kawai xai kara baci inta tsaya yin masa wani
bayani, baki bude take kallonsa acikin yanayin mmkin halin basarwa irin nasa yo ace duk wani
walakanci da cin fuskan dayay ma yarinyar nan agidan nan shibaima san yana yi ba..
Kyabe bakinta tayi tanamai karkada kafafunta aranta tana jin tsananin takaicinshi ayayinda take
tuno da irin baqar wahalar da kafayat din tasha agidan nasu kwana biun nan, wani irin
sihirtaccyar ajiyar xuciya mai nauyi ta sauƙe cos Kafayat whud have been the perfect doter
inlaw and a responsible wife for her son Ahmad domin yarinyar nan itace ta san shi tun suna
yan kanana tun basu san kansu ba suke abota.
Gashi tun xuwanta Nysc take xama dasu agidan dan sabida tana kulawa da su na musmn
sabida son Ahmed din datakeyi aranta duba da shine first love dinta, hatta mahaifin sa ya
bala'in amincewa da kwaxo da kuma halayyar kirki irin na kafaya,gata nan masha Allah black
beauty omo yoruba, gaba da baya full option,gata da tsafta, ga son shara, ga iya wanki da
guga, ga iya wanke wanke,uwa uba ga iya girki,ga kuma ladabi da biyayya,duk tayi musu
luguden hidima agidan sabida shi amma waishi baima gani ba.
Acikin sassauto da muryansa kasa kasa sigar lallami yana kallon yanayinta yace iyami",my
mamee, harararsa tayi tun bai fara mata dadin bakin ba, yace "toh kiyi hakuri mana mama naa
inadai kafayat buraimo ne?i promise i will apologise for ur sake! kikace wai dan naki attending
birthday din da kuka hada ne yasa tayi fushi ta bar gidan nan ko? Lumshe ido tay dan harynxu
mamki yake bata ganin cewa baima san lefin daya aikata ba, Girarsa ya dage sama ahankli, da
har dai xaice "She is soo silly" sai kuma ya kumshe sauran maganan abakinsa yy shiru,dauke
kan datayi yasa ya dan shafa kansa da yanayin damuwa a muryansa yace "mamee pls now,
kidena fushin nan mana nide nasan damuwarki bai wuce kice xancen relashp dina da kafayat
ba,i told u i need time..kuma aikinsan komai fa lkci ne, AUREN nan xanyishi in lkci na yayi,kawai
su Dad sun kasa gane hkn ne kema kika bi bayan su,sun ki fahimtar abinda nake nufi batun
auren nan,i swear im still searching for a good nd decent wife just for u,kuma nasan idan lkci na
yy na aure xan kawo muku matar Aurena ko ba kafayat ba,am just bored of all dis match
making da kuke min. Kubari mana uhmm iyami?..
Ta cigaba da kallonsa rai bace batace mai uffan ba,shafa kansa ya kuma yi har lkcn fuskar sa
na dauke da damuwar yanayinta dan sosai ya tsani yanaganin bacin ranta,saidai shikansa
baisan mesa suka saka kafayat aransu hr haka ba, sallamar da aka yi ne yasa duka suka maida
hankalin su ixuwa ga bakin kofar tare da amsa sallamar baki daya.
Mikewa tayi ganin yan uwan mijinta ne suka shigo su subiyu, Anty temi (ramotou) da anty
(moslimat) Mojushola,da wata kyakyayar budurwa mai suna maryam wacce kallo daya kamata
ya ishi kasan bahaushiya ce,da fara'arta ta tarbesu tana masu sannu da zuwa basu wani tanka
ta sosai ba suka karaso cikin falon aka shiga gaggaisawa sama sama dan duk hnklinsu da
nitsuwarsu nakan dan saurayin ne.
A cikin nitsuwa ya rusuna ya gaishe su snn ya mike tsaye yanamai kallon mahaifyar tasa, adan
gaggauce yace "mamee ni xan wuce sai na dawo ko xuwa gobe"..kafin ta amsashi har Anty
Temin tay sauri ta amshe xancen cikin sautin babban muryanta na giant woman, fuskan ta babu
alaman fara'a tace "oshey Damilare, wat do u mean by dat statement? _Ahhh dami, iwọ ko si
oju iberu ti o ni ibanujẹ?_ (ahhh dami,u no dey fear face?)..Daga xuwan mu ne sai kace gobene
xaka dawo? but Dats not fair oo,ta kalle babban dadan su da batace uffan ba cikin bambami ta
karashe xancen fuskarta a daure "Ahhh see Shildren of now adays,kadai dawo xuwa anjima kar
kakai daddare dan bamu gama magana dakei ba, tana maganan tana kallon cikin kwayar
idanunsa suna hade ido sai ta kalle budurwan data sunkuyar dakai kasa da alaman ta fahimtar
dashi abunda suke nufi, ahnkli yyi murmushi yace its okay "toh in' sha Allah xan dawo anty
rahama.
Shiru tayi batace mai uffan ba sabida she love them to be adressing each oda da sunayen
yaren su amma sam shi bayaji, shiyasa ma ita sam bata kiransa da Ahmad aganinta sunan
hausawa ne irin na maman sa, sudei a fannin uba saidai sucemai "DAMILARE " ko "DAMI" KO
"LANRE" sabida sunan nasa inkiyar sunan baban mamansu ne so they respect dat name alot.
duk maganan nan da ake Anty mojushola batace musu uffan ba banda cika iska da hura hanci
da yatsine datake bin su dashi, dan itadin ta manyanta sosai dan itace first female child da
mahaifinsa yake bi,sai uncle dinsa bakare,anty temi (ramotou) kuma itace autarsu.
Bayan sunyi hakan sai yyi musu sallama ya fice daga falon yana kallon agogon hannunsa daga
nan yanajin anties dinsan sunakan watsa habaici wa mahaifiyarsa na cewa tunda yaki auren
mace daga kabilarsu aiga nan bahaushiya sun kawo masa daga nata irin kabilar, sam dangin
mahaifinsa basa da sauki,they just love to be in control of evrthing. A farko ma sunedai suka
soma cusawa kafayat ra'ayin xama agidan iyayensa dan tana musu bauta,so during her nysc
session sai ta xo just to get his attention ayi aure, dukkan dangin ubanshi suna matukar son ace
kafayat ce ta auri Ahmed just for the simple fact that itama kabilar su ce na yoruba.
gun motarsa ya nufa da sauri yana tafe yanamai kallon agogon hannunsa acikin gaggawa ya
buɗe ya shiga ciki ya kunnata da sauri yabar harabar gidan nasu.
Ahankli yake tukin aransa yanata tunanin yadda xai kawo karshen wann matsalar data kunno
masa kai acikin familyn sa musammn na yadda kowa yake son yaga lallai ya aurar dashi acikin
gaggawa..
After some few hrs...
_National communicable disease control Theathre hall maitama Abuja._
_5.56PM_
Manyan likitoci da public health professors ma'abota ilimi da wayewa da kuma kwarewa a
bangaren yaƙi da yaɗuwar cututtuka ke shige da fice a babban hall din NCDC dake garin Abuja
kowa da alaman fara'a akan fuskan sa.
Lectures din da suka yi yau was very interesting Dan Sai yanzu duka suka fahimci abinda
minister of health na kasa yake nufi a lokacin da yake
ce musu the youngest professor dinsu AHMED BELLO JIMADA is the best and leading young
epidemiologist da sukay employing acikin CCD project dinsu na wnn shekarar sabida yanada
gwaxo sosai,snn yana bin komin sa ne a dalla-dalla cikin nuna ilimi da kamiya. And He makes
sure He carries everybody along acikin kwarewarsa. Snn Yana making good references da
abubuwan da yaje ya koyosu a kasashen waje yanamai kara budasu tareda yin gamsashen
bayani akansu using simple terms wanda ko the most dummiest and stupidest person zai
fahimce shi.
Yau yay musu electronic lectures ne akan manyan pandemic and prevalant diseases dake
addaban iyakar boundaries na tsakanin kasa da kasa kamar su COVID19,i:e corona virus,
Acquired immuno-deficiency syndrome(AIDS) da severe acute respiratory syndrome (SARS)da
wasu ire iren viral flus.
Anan kowa ya kara fahimtar cewa shi mutum ne mai tsantsar nutsuwa da ilimi, komai nasa a
hankali yake yinsa. He is very gentle bashi da hayaniya sam saidai daga ganinsa za ka iyasanin
cewa yana mugun ji dakansa sabida wani irin tsantsar self assurance da kuma zazzafan self
confidence dayake nunawa ayanayin