Mejo Najeeb Book 1 Compelet Autar Alheri

Author :  Autar Alheri Category :  Read Hausa Novels

Chapter   7 / 38

18K to 21K   out of 111.9K words

Umma...shidai
k'ala bece mataba kawai juyawa yayi tafiyarshi..da kallo tarakashi tana tasbihi ga uban gijinda
yabata wannan yaron Allah yasani tana mugun son najeeb cikin y'ay'anta tana rokon Allah
yabata ikon b'oye soyayyar shi kar Y'an uwanshi sugano tafisonshi akansu domin tasan tabbas
Hakan zehaifarda matsala atsakaninsu.

Shikuwa Yana fitowa yafice daga gidan kotakan k'anenshi bebiba dayaji suna masa adawo lpy
Allah ya kiyaye...a perking space yasamu captain Jameel tareda zugar yaranshi, ruwan roba
yakarb'a ahannun captain Jameel d'in yawanke bakinshi kana yashiga motar domin befito da
Hankey ba Kuma shidai yatsani wannan kiss d'in da Umma kemishi akan lips sedai ba yadda
zeyida ita mahaifiyarshi ce babu abunda zatayi agareshi yace aa Amma Badan Hakanba tayaya
zebari wai mace ta tsotsar masa Baki, Allah yasauwak'e mishi wahala da kayan K'azanta.
Dawannan tinanin motocin su sukabar gidan inda suka nufi airport kaitsaye acan suka samu
general aliyu datashi zugar. Suna Isa kuwa babu wani b'ata lokaci jirginsu yatashi zuwa k'asar
nigar......!





MEJO NAJEEB PAID BOOK NE akan nera 500 kacal game bukatar complete dinshi kuwa 1k ne
domin complete dinshi yafito idan kishirya biya Zaki iya tura kudinki a wannan account d'in
2276776261 sha'awanatu kasim UBA Bank kana kitura shedar biyanki a wannan nomber
09112799371 on WhatsApp ko kikira wannan nomber 07037092176

Autar alheri ✍️




‍♀️‍♀️‍♀️‍♀️‍♀️‍♀️


*MEJO NAJEEB*


(Labari me sark'ak'iya ban al'ajabi rikici zalunci soyayya cin Amana dakuma romantic )


Daga alkalamin Autar alheri ✍️

MEJO NAJEEB PAID BOOK NE YANZU MUKE FREE BOOK 1 IDAN MUKA SHIGO BOOK 2
SHINE ZAKI BIYA KARKI KARANTAMUN ABUNA BATAREDA KINBIYANI HAKKINABA
MUDDIN KIKA FITARMUN DA BOOK KO KIKAKARANTA BATAREDA KINBIYANI HAKKINABA
KEDA ALLAH.
Book 1

Page 19 & 20

Inaga wannan page shine end book 1 free yak'are idan kinada bukatar complete dinshi Zaki
biyan 1k domin samun complete inkuma update kikeso Zaki biyan 500 kacal. Idan kinshirya biya
Zaki iya tura kudinki a wannan account d'in 2276776261 sha'awanatu kasim UBA Bank kana
kitura shedar biyanki a wannan nomber 09112799371 on WhatsApp ko kikira wannan
nomber 07037092176.

"Jirginsu nasauka a k'asar nigar sukad'auki dauki mota drop zuwa fadar shugaban k'asar nigar
Alhaji Abdulsalam Idris suna zuwa sukasamu damar shiga fad'ar shugan k'asar kasancewarsu
sojoji basusha wahalar shigaba dudda cewar ba sojojin k'asar bane Amma daganinsu kansan
cewar ko acikin sojojin Nigeria manyane. Abakin k'ofar shiga office din shugaban k'asar suka
tsaya inda Fe,A d'inshi yashiga gun alhaji Abdulsalam Idris domin nema musu iso abunshi
dudda cewar babusu acikin jadawalin wanda zegana dasu aranar Amma haka akasama musu
gurbi dole kasancewarsu manyan mutane dukda k'ananun shekarrunsu ammadole abasu girma
sbd manyan muk'amansu....fitowa f,a yayi yagaya musu zasu iya shiga domin ya,isarda

sak'onzuwansu. Hahan yasa suka shiga office d'in kaitsaye. Azaune suka sameshi akan kujerar
office d'inshi kyakkyawan dajjo farin buzu mecikar haiba da kamala. Gaidashi sukayi cikin
girmama dudda cewar sunzone da b'acin Rai Amma kwarjinin dattijon yahanasu bayyanarda
b'acin ran nasu.
Shima agunshi hakanne domin Hakan kawai yaran suka birgeshi Hakan yasa ya amsa musu
cikin sakin fuska da kulawa, daganan yabasu wurin zama...seda sukazauna cikin girmamawa
suka shiga koramai bayanin abunda yakawosu kamar Hakan "ranka yadad'e munzune akan
wani al'amari dayake faruwa ak'asarmu sabida bamuji komai daga manyanmuba gameda
wannan abun shiyasa mukazo muji Koda Saka hannun k'asar nigar ne ake wannan aikin.
Tsayawa general aliyu yayi yad'an Kalli dattijon kamun yacigabada fad'ar "wannan abun kuwa
bakomai bane face aikinda sojojin k'asar Nan keyi a Nigeria Kuma munga babu Saka hannun
kowacce hukuma ta sojojin Nigeria akan wannan al'amarin shiyasa mukazo domin abun yayi
k'amari Kuma way'anda suke wannan yak'in dasu bay'an Nigeria bane Y'an south African ne.

"Murmushi wannan kyakkyawan dattijon yayi kana yace "kunada gaskiya Y'an samari dudda
cewar bansan sunayenkuba Amma suturar jikinku tagayamin mukamanku acikin hukumar soja,
to zance na gaskiya dasaka hannunmu awannan aikin yafad'a Yana kallon najeeb dayaga tinda
aliyu yafara magana kanshi ak'asa yake.
Murmushi yayi kana yacigabada fad'ar "abunda yasa muka Bada umurnin yinshi kuwa shine
way'annan mutanen hak'ar ma'adanan kasashen mutane sukeyi nacikin k'asa wanda bakowane
ze iya fahimtarsu ba sedai kafin sukaigayin abunda suke buk'ata general faruk ya'ankara da
b'arnarda suke Neman yiwa Niger Hakan yasa yafarmakesu alokaci d'aya to dasukaga Hakan
sesuka gudu izuwa Nigeria tinda Basu samu abunda sukeda buk'ataba anan shiyasa suka
tsallaka can. Ganin Hakan yasa general faruk yasanarda shuwaga bannin hukumarsu inda
sukazo Neman Saka hannuna akan suriskesu Nigeria tinda Basu samu nasarar kamasu
ananba suka gudu. mutin biyu kawai suka kama Kuma basune manyaba acikin wannan
kungiyar tasu dake wannan ta'addancinga k'asashen duniya.. D'an shiru yayi Yana kallon
yanayinsu kafin yacigabada fad'ar "wannan abun nasu ba'iya nigar da Nigeria yatsayaba har
kasashen k'etarema domin kuwa hukumar sojojin ganah nemansu sukeyi hakama chadi,
kyamarun, India, Pakistan, dakuma k'asarsuma wato south Africa...dukkan way'annan kasashen
nemansu akeyi ruwa ajallo Kuma ankasa samun nasarar kamasu annanema akasamu kama
mutin biyu Hakan yasa dasuka tsallaka Nigeria mukanemi izinin shiga Nigeria yin wannan aikin
agun shugaban k'asarku Amma bamuda masaniya akan hukumarku sedai inada tabbacin cewa
shugaban k'asar Nigeria ya tattauna da wasu daga cikin manyan sojojinku akan wannan
problem d'in. To Amma Kuma ance daga cikin sojojin Nigeria akwai way'anda kejagorantar
sojojin nigar acan yobe tareda general faruk. Yak'arasa zancen Yana kallonsu.

Kallon najeeb aliyu yayi yaga haryanzu be d'ago kanshiba Hakan yasa yamayarda kallonshi
akan dattijon yace "ikon Allah gaskiya duk bamada wannan masaniyar ranka yadad'e Amma
abincinkenda mukayi babu wani sojan Nigeria awurin gaskiya barama kaga yafad'a yana bud'e
computer dinshi dakoyoshe suna tareda ita shiga nunamai abubuwanda kefaruwa acan

yayi....cikin mamaki alhaji Abdulsalam Idris ke kallon video tabbas babu sojojin Nigeria aciki to
Amma ya'akayi Hakan tafaru? Yayiwa kanshi tambayar da bame bashi amsarta ayanzu....cikin
mamaki Yakoma kallon general aliyu kana yace Tabbas babu sojojin Nigeria anan Amma
abunda shuwaga banninku suka gaya mana kenan domin harda bayanan sojojin dasuka
jagoranci aiki sukaturo mana.. Se wannan lokacin mejo najeeb yad'ago kanshi tareda bud'e
Baki cikin sweet voice dinshi dayagama sauyawa sabida b'acinrai yace "please ranka yadad'e
kozamu iyasamun bayanan sojojin? Kokuma sunansu da hukumarda suke aiki please. "D'an
shiru dattijon yayi kamun yace gaskiya bayanansu basa office d'innan Amma sunansu ance
D'aya MEJO NAJEEB SAHABI KHAMIS DALA da GENERAL ALIYU HAIDAR AMEEN...Ido
suka waro atare kamun sukalli juna cikin mugun mamakin wannan k'ullin da'akamusu. Maganar
alhaji Abdulsalam Idris ce tadoki dodon kunnensu inda yake cewa "Amma bayanansu kubari
nasaka adauko muku nabarsu a gida, Kuma ance zak'ak'uran sojojine way'anda Nigeria
kejidasu ahalin yanzu tabbas zasu iya kama way'annan b'ata k'asar sedai idan basuso yin
Hakanba domin yakanyu atare sukeda Y'an zagon kasan k'ila da had'in bakinsu ake wannan
abun Amma ba wanda yakeda tabbaci akan Hakan sedai aikinda zasuyi ayanzu shine ze
tabbatarda gaskiyar Ina suka dosa, idan akwai Saka hannunsu ko babu...Yana kaiwa k'arshe
najeeb yamik'e tsaye domin harnaman jikinshi tafarfasa yakeyi inda wata Irin zufa tashiga
ketomishi Tako Ina sabida mugun b'acin Rai da tashin hankali, kenan so akeyi ab'ata musu
suna shiyasa aka shirya musu wannan abun akasanarda cewar sune kejagorantar sojojin
Nigeria da Niger alhalin ko sanin antura ayi wannan aikin basuyiba wannan wanne Irin
sharrine....shikuwa general aliyu yayi namujin k'ok'ari wurin b'oye nashi b'acin Ran inda yacewa
alhaji Abdulsalam base an karb'o musu bayananba sungane ko suwaye kejagorantar aikin
sabida Hakan zasu samesu acan. "Murmushi kawai dattijon yayi tareda yimusu fatan alhairi
sukayi sallama kana general aliyu yabibayan mejo najeeb datuni yafice.

Aharabar gidan gwamnatin yasameshi harya shiga mota, shiga Shima yayi kamun yadibi najeeb
d'in yace "miye abunyi mejo? Inazamu dosa yanzu? "Nigeria jihar yobe yafad'a
atakyaice...dagajin Hakan aliyu bek'ara cewa komai yayinda captain Jameel kebinsuda Ido
domin ko general aliyu dabecika nuna b'acin ranshi afiliba yau kallo d'aya zakamishi kasan
ranshi amugun b'ace yake. Amma Hakan yabarsu kawai yanabinsu da Ido tinda Basu shiga
dashi cikiba balle yasan abunda aka tattauna gashi Kuma yaji za'akoma Nigeria ko hutawa
basuyiba..... kaitsaye airport memotar yakaisu suka biyashi, shikam yayi tafiyarshi. Anan suka
Siya ticket d'in y'amma, bayan sunbiya suka zaunanan suna jiran lokacin tashin jirgin yayi.
kamun wannan lokacinne suka samu sukayi wanka suka canja kaya acikin airport d'in domin
akwai dakunan bak'i. Se bayan sund'an hutane yatinada fruit salad d'inda Hajiya Umma tabashi,
D'an tsaki yaja tinawada amotafa yabarshi Hakan yasa captain Jameel tafiya yasiyo musu
yoghurt da gasarshiyar kaza, anan suka d'anci sukayi sallah, Basu jima dagamawaba lokacin
tashin jirgin yayi Hakan yasa suka fito kawai tareda koma hawa jirgi domin juya Nigeria.

A abuja jirgin yasauka Hakan yasa suka shiga Neman wanda zekaisu Legos ko yobe state
Amma firrr ba'asamuba babu yadda Basu bugaba Amma babu jirgin ayau sedai gobe sukuwa
bazasu iya Jira har gobeba..suna yatse suna tinanin yazasuyi kowada abunda yadameshi
musamman Mero najeeb dayakejin ciwonshi nason tashi gakuma b'acin Rai karfin haline kawai

yakeyi....captain Jameel ne yak'araso inda suke tsaye Yana fad'ar "Sr wlh ba'asamu jirgin
dazetashiba Koda da yammane wai sedai jirgin ruwa idan Muna buk'ata Shima yanzu zetashi
Kuma Anambara state zeje idan ya'ajiyemu a yobe se yawuce Amma ta gombe zebi. "Okay
badamuwa bara muhaushi kawai zefi ai, cewar general aliyu Yana kamo hannun mejo najeeb
d'in. Domin shidai komi beceba sabida yanayin ciwonshi se k'aruwa yakeyi gaya inbanda
fad'uwa babu abunda gabanshi keyi da tsinkewar zuciya, Amma yadakewa ranshi domin komai
kwakwarka baka Isa kace yanada wata matsalar ba sedai kallo d'aya zakamishi kasan cewa
yanacikin mugun b'acin Rai dubada yadda kyakkyawar fuskarshi ke ahad'e kamar besan
minene dariyaba...dahakan suka hau jirgin kuwan inda suka d'auki hanya atake semuce Allah
yasaukesu lpy..


Gombe

Bacci sosai Isseta Tayi har garin Allah yawaye Rana tafito tukunna ta Farka, ahankali tabud'e
sexy eyes d'inta tanabin wurinda kallo seyanzu tatina abunda yafaru adaren jiya wani Irin
kukane taji yazo mata lokaci d'aya domin Bata tab'a tinanin ita za'ayiwa wannan k'azafinba wai
Anya kuwa Abba shine yahaifeta? Tayiwa kanta tambayar da bamebata amsa....kanta dataji
andafane yasakata d'agowa ahankali tanabin wanda yadafata da kallo, wannan k'awar ce ta
maah tsaye akanta tana sakar mata murmushi..itako ganin batasantabane yasa tabud'e Baki
ahankali zatayi magana kenan, taji ankoma shafa kanta akarona ukku..atake abunda takesan
fad'a yab'ace mata Kuma tamanta komai dayafaru ajiya Sam an shafe mata komai nadamuwa
kamar ba itaba..Hakan yasa itama sakar mata murmushi kawai tamik'e domin Tayi sallah sabida
tamanta komai na kunci arayuwarta..alwala Tayi bakin kogin kana tazo tad'an share wurin kawai
ta tada sallar domin kayan jikinta Basada D'an kwali balle ta shimfid'a tinda sleeping dress
ne...seda ta idarda sallar kana aka kawo mata abunci. Aiko Tayi zaune taci abunta seda Tayi
hani'an kana tad'ora da ruwa. Bayan tagamane tazauna tana jiran fitowar maah...

Acikin gari kuwa tinda halima take kukanta innarta Bata hanataba domin itama jitakeyi kamar
zata saka kukan kawai Dan karta karyawa y'ar tata zuciyane. Halima nacikin wannan halinne
tamik'e zumbur kamar wadda aka tsikara tafice daga gidan cikin sauri tonowada inda zata iya
samun k'awar tata..
Zaune suke ak'ofar gidan megarin gombe mlm Musa ne se wasu hadiman fadar daga gefe
kuwa wasu attajiran alhazawane kezaune kusan su shida...gyaran murya megari yayi kana
yace "mlm Musa kajidai bukatar da wannan bawan Allah ketafeda ita tason Auren d'aya
dagacikin ahalinmuna Fulani Kuma nasandai kasanshi domin ba boyayyen mutin bane a
Nigeria duka balle jihar gombe. Jinjina Kai mlm Musa yayi kana yace Tabbas nasanshi ranka
yadad'e. "To masha Allah tinda kashaidashi abunda yasa nace akiraka kuwa shine tinda yafad'i
buk'atar shi tason kamilalliyar yarinya me hankali jama'ar fada danikaina mukaga ba wadda
tadace da wannan siffofin inba y'ar wurinkaba wato maryama Hakan yasa nace nabashi ita
domin y'arka ai y'ata ce Kuma Dama aimune waliyan y'ay'an duk wani dattijon kirki dake
garinnan. Cewar megari....wata Irin zabura mlm Musa yayi tareda share guminda yawanke

masa fuska Yana zare Ido tin lokacinda megari ya anbaci Sunan maryama, cikin har had'a
magana yace "mar..mar.. maryama ranka yadad'e? "Maryama kuwa megari yak'ara fad'a cikin
tabbatarwa. Kana yak'ara dacewar sabida Hakan suna buk'atar ad'aura Aure subiya komai
inyaso daga baya suzo tafiya da amarya dakuma danginta domin suga inda y'ar su zata zauna.
"Cikin tashin hankali rud'u fargaba mlm Musa yace Amma ranka yadad'e..dakatar dashi dagacin
garin yayi tahanyar fad'ar"mlm Musa badai jayayya zakayida hukuncin megariba? Kumadai
nasan badan bakasan inda za'akai y'arka bane tinda uban mijin nata Dan garinnan ne Kuma
sananne kowa yasan alhaji marigayi mahaifin wannan alhajin yafad'a yana nuna D'aya daga
cikin alhazan. Kana yacigabada fad'ar "Kuma kasan matsugunnin shi a birni sedai indan tozalta
megari Zakayi kanuna be Isa da ahalinkaba. "Aa dagaci kabarshi yafad'i ra'ayinshi ai yarshi ce
yanada wannan damar cewar alhajin.

Nisawa mlm Musa yayi Yana tinanin abunda zece awannan lamarin yasandai be Isa yace yakori
maryama daga gidanshi ba sabida rashin tarbiya tinda gashi cikin dubbannin y'anmatan gari
anfiddata daban idan kuwa yayi Hakan kamar yadab'awa kanshi wuk'ane..Kuma baze iya
jayayya da hukuncin megariba domin yayi mishi dukkan gata, sa'annan baze iya amincewada
wannan aurenba domin besan a'ina zega amaryarba. Gakuma babban tashin hankali shine
lokacin bukatar ta yakusa agun mamallakinta koyaya zek'are dasu idan suka tuhumeshi?
Yatambayi kanshi...yayinisa cikin wannan zancen zucinda yakeyi kawai yaji ana sanarwar
and'aura Auren maryama da D'an wannan alhajin.domin shirunda yayi Yana tinanine yasa
sukayi tinanin ya,amincene shiyasa yayi shiru sabida kalaman dagaci, tofa abisa wannan shirun
nashi aka d'aura wannan auren na maryama�

Tashin hankali kenan wanda ba'asakamishi Ranawani Irin gumine kewankewa mlm Musa jiki
wanda ke tsatsafowa tindaga cikin kanshi har izuwa yatsar kafarshi, yakasama mud'e bakinshi
balle yasamu zarafin yin magana, guminnan kawai ke ketomishi Daya share wannan se wani
yak'ara yankowa tako'ina..wani Irin nadama da danasani ne suka shigo rayuwarshi lokaci d'aya
nadama yakeyi akan tin farko rayuwar maryama ahannunshi har izuwa wannan lokacin Daya
koreta harkawo yanzu da aka d'aura aurenta batareda sanin ko ita d'in wacece ba....megarine
yakatse mishi tinani inda yake mik'o mishi sadakin maryama nera dubu 500k tareda kud'in
gaisuwa Dana Saka Rana duk alokaci d'aya...hannunshi na karkarwa yakarb'a...kana akayi
addu'ar Neman albarka da Auren sa'annan way'annan alhazawan sukayi musu sallama suka
tafi...se alokaci me gari yayi mishi cikakken bayani akan wannan al'amarin bayan yasallami
kowa sunrage su biyu kawai.....shidai mlm Musa bece komaiba dudda bayanin da megari yayi
mishi Amma Sam hankalinshi baya jikinshi, Hakan yasa megari salkamarshi domin atinaninshi
kofargaba yakeyi kar yarinyar tak'i amun cewa ko mahaifiyarta. Dan k'aramun murmushi yayi
afili yace "indai maryama ce baza'ayi wannan jayayyar da itaba.(nikuwa nece Humm megari
kenan Aida matsalar maryama ce abun zezo dasauk'i Amma wannan matsalar kam to sedai
Allah ya kyauta �). Shidai mlm Musa Yana barin wurin megari kaitsaye gidanshi yanufa kamar
ze kifa sabida tashin hankali gabaki d'aya yafita hayyacinshi bukatar kawai yakeyi yaganshi
agaban mama bintu domin Susan matakin d'auka akan wannan sabon al'amarin.

Lagos

Banana island

Zaune take a perlor ita kad'ai tana duba li


MM _ NN


Book 2

Page 21 & 22

"Wani irin zabura takomayi batareda takowaiwayi abinda takauraba balle tasan minene Hakan
tasake kwasa aguje tanufi jirgin tana ihu tana ƙarawa, sosai take tura jirgin kamar wani abun
wanda zata iya turewa sedai ko gizau beyiba amma takasa fahimtar ba'abunda zata iya
awurin.....shikuwa najeeb yakasa koda ƙwaƙƙwaran motsi sakamakon ruwa naƙara ta'azzara
ciwonshi Hakan yasa yafara fita hayyacinshi sedai dudda wannan halin da yake ciki Hakan
behanashi hangotaba yadda taketa haƙilon son ture jirgin.

General aliyu ne yafito asukwane shida captain Jameel sakamakon tsinkayo faɗuwarsu
dasukayi kuma sunga yarinyar tatashi amma shi komotsi beyiba, suna ƙarasowa general aliyu
yaɗagoshi yana faɗar subahanallah mejo miyasameka Hakan badai dama bakada lpy ba?
Yafaɗa Aɗan rikice.."yasalam wlh rashin lafiyarshi ne tamotsa inaga akwai abinda yaɓata
mishiraine, cewar captain Jameel. Ɗan shiru yayi kafin yakoma cewa "innalillahi wa'inna
ilaihiraji'un yanzu yazamiyi dashi acikin wannan ruwan wanda koda agida muke baya buƙatar
likita balle anan. "Yanzu dai duk ba wannanba kamashi mufiddashi daga cikin ruwan tukunnah
semusan abunyi, cewar general aliyu Haidar. Hakan kuwa suka kamashi aka fitar dashi daga
cikin ruwan inda suka samu wurinda sukaga shimfiɗar Isseta suka kwantardashi batareda
sunsan me shimfiɗar ba...baki general aliyu yabuɗe zeyi magana kenan yahangota tana tsalle
tana duka jirgin ruwan cikin matsanancin kuka. Ido yazaro yana faɗar "tofa itakuwa waccan
yarinyar wacece ko'acikin jirgin tafitone? Takasa komawa? Yatambayi kanshi, kamun yace to
Amma fa kamar kuka takeyi baradai muga yafaɗa yana nufar wurinta kaitsaye.

Isarshi keda wuya yaji tana faɗar "nashiga ukku wlh Allah bazan yaddaba kunkashemun
mahaifiyata kunrabanida farin cikina wlh Allah seya sakamun innalillahi wa'inna ilaihiraji'un
maahhh dan Allah kitashi kuɗaga jirgin maahh tafito kundanneta wayyooo maahh
sunkasheki..Hakan kawai Isseta kefaɗa cikin kuka da muryar matsanancin tashin hankali
atareda ita.

"Innalillahi badai mutum jirginnan yatakaba shine dalilin tsayuwarshi? To inba mutin yatakaba
mezetsaidashi anan? Wani gefe naxuciyarshi yabashi amsa, ya salam shine abunda yafito daga
bakinshi kafin yanufeta cikin sauri ganin tana ƙoƙarin nutsawa acikin ruwan, cikin zafinsu na
sojoji yadamƙota tareda ɗagata cak yafita cikin ruwan da ita...sosai take wutsil wutsil

daƙafafuwanta tana dukanshi amma besauketaba seda yafita ruwan. Aiko yana ajiyeta takoma
zabura zata komawa tana gunjin kuka tanufi Dede hanyar tsakiyar gulbin, Shima cikin azama
yaƙara rufamata baya sabida ganin zata hallaka kanta, tana gabda shiga ruwan yamiƙa hannu
yariƙeta akuma Dede wannan lokacinne ruwan sukayi wani irin toroƙo suna tsartuwa asama
tare jelar kifin maah sekawai ta bayyana gaba ɗayanta...amugun tsorace general aliyu yaja
baya yana zaro manyan idanuwanshi, dagashi har captain Jameel dake bayansu yana kallon
duk abinda ke faruwa acikin ruwan...itako Isseta wani irin ihun murna ta buga tareda rugawa
aguje tana faɗar maaahhh tanufeta...cikin tashin hankali general aliyu daya ƙame wuri ɗaya
sabida ganin wannan halittar Afili wadda betaɓa ganiba arayuwarshi se a tv dominshi bema
yadda da akwaita azahiriba se yanzu dayaganta, wannan dalilinne yasa tashin hankalinshi
yakasa ɓoyuwa, tofa cikin wannan tashin hankalinne yaje taro Isseta gudun kartaje gareta ta
hallakata..amma ina yamakaro domin tuni Isseta ta isa gareta

7 / 38